Showing 102001 words to 105000 words out of 200647 words

Chapter 35 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

26

dare

SU ABA

Tunda ya sa suka yi shiga ta manyan mutane ya fito da su daga gaban Mama ya zamo a tsorace suke , domin koda suka zo gidan bawan Allahn nan wanda sarai habubacar ya gane gidan su Mudansir ne su Dukansu a tsorac

en suke , kuma sun kama kansu kowane da abinda yake ayanawa a cikin zuciyarsa

Tsakin da Aba ya yi a zaunen nan ya fi cikin kwondo, ya tambayi lokaci a wajen Mubarack ya fi a irga, wanda ke rike da wayoyinsa, yana yi yana sake duban wajen da aka basu abi

n zama da lemu ya ja wani uban tsaki ya dubi Muhammad ya ce" Muhammadu ka ga Ni aka sauke da lemu a wajen nan, sai kace dan yinwa? to wai an sanar masa sakona na jiya kuwa?"

Muhammad ya sada kai ya kasa bashi amsa, shi kuwa ya dube shi shekeke kafin ya

dauke kai ya ce" Yan buro'uba ya'yan gimbiya du baku da isashiyar tarbiya, ina magana kana wani sune kai kamar da gaske, bayan a cikinku aka samu mai son mai jan ido"

Su dai Allah ne ya kawo su wannan lokaci sun sani, kuma shine zai raba su lafiya da sh

i wannan ma sun sani, sunna fatan Allah ya raba su lafiya tun kafin ya sauke haushinsa a kansu, su basu san me suka zo nema nan din ba, kuma ance mai gidan na nan, ama a kala sun dauki sama da awa a zaune, cikin ikon Allah mai gidan bai fito ba, sun rasa a

binda yake faruwa ,sunna fatan ko menene Allah ya kawo musu shi da sauki

An sake daukan kusan minti goma, Har Aba ya mike fuuuuuu yana baza babar riga zai kama hanyar fita aka yi salama daga kofar shigowa ta cikin gidan aka shigo

Elhaji Umaru Musa ne

ya shigo da farar jalabiyarsa , bayansa kusa Mudansir ne da ya'yan Mudansir din da kuma kanninsa biyu, suka karaso suka zauna kusa da su Abubakar, shi kuwa Elhaji Umaru din ya tarbi Aba da ya dakata ya mika masa hannu yana fadin" Asalamu alaikum Elhajin A

llah, Barka da dare, a yi hakuri, a yi hakuri ban san kai bane a lokacin da Madame ta sanar min na yi bako an kawo min abinci ne, sai da na kamala na fito mun zauna zamu yi shawara da yara aka sanar min bakon fa kaine kuma kana nan"

Aba ya amshi hannun

nasa suka gaisa yayi murmushi bai ce da shi komai ba ya koma ya zauna

Bayan sun zauna Elhaji Umaru ya ce" Elhajin Allah maman yara ke cewa bakon na Mudansir ne? ina fata lafiya?"

Aba ya dubi Mudansir dake sine kai, shi walahi yaron sai yake masa kama

da yan daudu, kuma jan ido kam eh gaskiya jan ido gareshi ama shi fa bai ga jan ido na dakankan namiji, kardai aje dan shanye shaye ne Karima da uwarta suke so?, ji yake kamar ya janyo shi ya ci ubansa, inama ace fada ya kaure a nan ya hada shi da ubansa

ya musu dukan tsiya su Sidik su kama masa, dan walahi dai a yadda yake gannin uban Mudansir din nan shima ba wani abun kirki zai yi ba

Kai ya dauke ya fuskanci Elhaji Umar ya ce" Kwarai Elhaji, tafiya ce ta dole ta kawo Ni gidanka, a kan yaran nan na z

amani, yarinyar wajena na yiwa miji, ta bi dare ta bi yaron wajenka gayanan, karshe dai na tsinci abubuwa mararsa dadi a wayar da ba Ni na bata ba, shine ya bata ba da izinina ba, shine na zo in SAMEKA dan mu san yadda za'a yiwa tufkar hanci"

Elhaji Uma

r ya dubi yaron nasa cike da jin haushin shima zai yi abinda yayansa ya musu kennan? ya ce" Mudansir? kaima sahun da Lukman ya bine ne zaka tono? kaima y'ar mutane kake son lalatawa? Mudansir an yiwa yarinyar miji shine zaka je ka dauketa daga gidansu? wan

nan din ai bai dace ba, kan me yasa kuke haka ne ya'yan nan?""

Aba yayi tsurutsuru yana kallon uban, a hankali ya ce" Elhaji yi hakuri, ama waye Lukman din?"

Elhaji Umar ya ce" Yayansa ne ai, haka yaron nan ya je ya samu y'ar mutane ya hure mata kun

ne ya janyo mana masifa kala kala a gidan nan, dan haihuwarsa biyu da yarinyar karshe dai aka aura masa ita suke zaune gayanan kana ganninsa yara basu tafasa Bama suke konewa?"

Aba ya yi wani irin kama an wanka masa mari ya turo hula gaba, ya mayar da

ita baya, ya sake turota gaba, kai karshe ya cireta yana fifita ya ce" Shikenan, an gama da Ni, innalilahi wa inna ilaihi raj'une abin yayi nisa ashe nake neman bakin zaren, kannin dan iska ai dan iska ne, kai bayan tarin sakwanin daren farkon ku ka ga da

ren ko baka gani ba?"

Wata irin kunya ta sa samarin ya'yan b

aba kasa kallonsa, shi kuwa Aba gannin ya'yan Elhaji Umar sai wani shanshan kanshi suke ya samu ya yi tsalan albarka ya riki Mudansir kafin ubansa ya mike ya sakar masa rankwashi a tsakiyar k

ai ya jijiga shi yace" Dan ubanka amsa daya nake so, ka ga daren farkon nan da y'ata ko a gaba?"

"Subahanallah Elhaji ya da haka, sake shi dan Allah sake min yaro, tunda nake ban taba saka hannuna a kan y'ayana ba, Ni bana dukan yarana, dukan yaran me y

ake haifarwa banda kiyaya tsakanin ya'yan da iyayensu? sake shi, ko me ya yiwa yarinyar ka ai ana iya samun masalaha, ko me kake so sai a duba a gani idan zai yiwu ama ya zaka rike min yaro haka sake shi Elhaji kar abin ya kai mu da gannin bakin junna dan

a kan y'ayana Ni sai in kai karar ka kuma a zo ana cewa na kai karar makoci" mahaifin Mudansir dake kiriniyar amsar Mudansir ke fadan haka da karfi ko Aba zai ji shi

Aba ya sake riΖ™e Mudansir da kyau ya ki saki rai bace ya ce" Da ikon, da d'an naka , da

yan anguwar masu gulma uwarku ta ci uwa tarrrrrrr! waye kai! wa ya tsaya maka a nan duniya? me ka tanada ? ka jima baka rufeni ba a kan y'ayana sai inda karfina ya kare, kai zaka daina langwui ka fada min ka ga daren farkon da y'ata ko sai na murde banzan

abin uban kowa ya huta da mugun iri d'an yan iska?"

Da sauri Lukman ya nufo da karfinsa yana fadin" Kai Elhaji ka sake shi mana, ai ba'a taba yin d'an iska daya ba, idan kana kiransa d'an iska ita y'ar taka mecece? ai ba da karfi ya dauko ta yayi iskan

cin da ita ba idanma yayin, ka sake shi walahi kar in........"

A haukace Sidik ya dago, kafin Lukman ya kai karshen aya ya dauke shi da gigitacen mari , sannan ya ja zai kai masa naushi Muhammad ya rigaye shi, Sarkin fada kuwa dama tuni ya tare dayan

yace" Kai, kar ka shiga harkar manya "

Rai bace Sidik ya ce" Kar ka yarda, kar ka saki ka zagi ubanmu, ka barsu su yi magana, ka barsu su ganewa junna, ba ruwanka, idan kuwa kace da ruwanka ba laifi ka gwada walahi sai mun fitini rayuwarka !, kuma ai ku

nna da y'an mata a gidanku na rantse da wanda raina ke hannunsa in dai Ni jinnin Elhaji Ya'u ne sai na nuna muku shegantaka biki ce!"

Aba ido yake zarrowa, yana kallon samarin ya'yansa a tsaye, haka kuma haba habar mutane ta fara yawaita yan bayar da ha

kuri da rabiyar fadan

Baban kamili da ya shigo ne ya karaso inda su Aba suka sarke junna ya saka hannayensa yana fadin" Subahanallah, subahanallah subahanallah, ku saku, ku saku, subahanallah, haba haba jama'a da girmanku da mutuncinku kuke irin haka? h

aba dan Allah idan yara sun hada rikici ai zama ake yi a sasanta bale ya'yan nan namu na yanzu idan muka ce su zamu biya sai mun rasa wanda zamu gaisa da shi a titi"

Tsakiyar su ya shiga, Aba yana haki ya dubi Sidik ya ce" Daukon hulata mu je, Elhaji

Umar zan nuna maka mu irin namu son ya'yan ba irin naku bane, domin sonsu bai sa mun gaza tsawatar musu ba, kuma ka sani zan je in binciki y'ata idan har ya ga farkon daren nan da ita kafin daren yayi alkur'an sai na masa dandatsa, yaro kana da gaskiya ba'

a dan iska daya, biyu ne, Ni na ga kattttt, ku wuce mu je , da neman aure muka zo tunda ta wulakantamu ta watsa mana kasa a ido ta nuna shi take so, sai dai ashe girman na jiki ne kawai Allah ya kawo da furfura , yaro kuwa kannin d'an iska ah d'an iska ne,

mu je!"

Mudansir a tsaye yake, jikinsa a mugun mace, gaba daya hankalinsa a tashe, yana kallo suka bar gidan, ya juya da sauri yayi ciki wajen mamansu ya saka mata kuka

Hankali tashe take tambayar abinda yake faruwa? , a rikice ya ce" Mama, mahaif

in Karima ne suka dawo ai, maimakun a bishi a laluma a kashe fitinar dake faruwa a sasanta a bani aurenta shikenan dan ya shakeni shine baba ya fada masa magana, Mama walahi kin ga mutumen nan ba zai taba bani Karima ba, kuma in fada maki sai ya saka bana

a uku a cikin garin nan, dan kuwa du inda baba yake tunanin rigimar mutumen nan ya wuce nan!"

"ina yake d'an naki? yana ina? Ni kam ya'yan nan sune zasu yi sanadiyata a duniyar nan, kai kuwa du ya'yan dake cike a garin nan ka rasa d'an wanda zaka bi s

ai ta wannan dan balakin? me take da shi da zai sa ka janyowa ubanka masifa? ka san waye shi? ka janyo bamu yi maganar fahimta ba ya bar gidan nan , ka san cewa shi a daku bata ce masa komai? wannan wace irin masifa ce?" Elhaji Umar Musa ke fada rai bace

Hajia rukaya ta girgiza kai, rai bace itama ta ce" To ai kare ne ya take sawun kura, kaima wa'inda kake bin ai ba na rufin asirin bane, Ni dai zaku kashe ba kowa ba, Allah ya sa bai hadata da ciki ba dan walahi ba ruwana sai dai ku karata, na fada muku,

kai da ka ji kunne baku da gaskiya ai sai ka bi hanyar da ta dace a samu masalaha, d'an naka yace yana son yarinyar, sai ka san yadda zaka yi ka daidaita rigimar" Daga haka ta yi wucewarta ciki, domin alkawarin da ta daukarwa kanta shine ba zata taba bari

tashin hankalinsu ya taba lafiyarta ba.

(Wannan kennan)

Tuki Aba yake yi cikin shiru da tashin hankali, ya'yansa kuwa tunda suka shigo mota ya bi su da kallo yana karrawa babu wanda yace masa komai har suka karaso kofar gidansa , Sidik ya fita dag

a motar ya karasa a Ζ™afarsa, Aban ya bi shi da kallo ya ga irin yadda ya'yan nasa suka zama samari, sai da wani abu ya dan tsirga a zuciyarsa

Kai ya dauke ya shigar da motar ya fice ya bar sauran da wani irin sauri bangaren su Hajia

A HANKALI Muhamma

d ya ce" Kai wai ina akwatin Mama ne? da aka dawo da mu ba nace maka mu barta a kusa ba ta yiwu mu kuma yin yajin kwana kusa ba?"

Dariya yayi yana hangen hanyar ya ce" Ko mun je maido mu za'a yi, Ni kam bari in boye dan na san yau ko wa yake gidan nan b

a zai hanna gidan nan kamawa da wutar balaki ba, Allah ya sanyayawa Mamanmu baiwar Allah KARIMA sai janyo mata masifa take yi, ama ka san Allah, Elhajin nan da ya'yansa sai sun ga rashin mutunci, mu za'a tabawa uba?"

Muhammad ya yi murmushi ya fita shim

a ya ce" Barsu, Wadinnan ai daidai muke da su, ku zo mu yi gyaran kofar nan tun yanzu dan gobe da wahala mu samu time, ina sauran samarin gidan ne?"

Sidik daga ciki ya ce" kai ku bari a gama haya hayar cen, idan bai sakar mana uwa ba ma gyara masa gidan

in kuwa ya koreta sai mu kara gaba, walahi idan Karima ta sake janyowa mama wata fitinar sai na zane banza marar hankali!"

Haka dai suka yi zamansu sunna tataunawa kafin sauran su dawo daga aiken da Mama ta musu.

A tsiyace Aba ya shigo yana ihun f

adin"

07/12/2024, 15:13 - samiraharounayacouba:

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*FARKON GANIN IDONA*

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*

πŸ‡³πŸ‡ͺ

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR

ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sa

jida Nijar thank you

😍

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DUK NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN LADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA K

OKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAƘIN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR

*Shafi na ashirin da takwas(28)*

*TALLAH, TALLAH, TALLAH*

https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf

YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI S

AURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN

KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*

πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ

πŸ‘‰

0912 262 1080

LABARI

A tsiyace Aba ya shigo yana ihun fadin" In

nalilahi wa inna ilaihi raj'une, innalilahi wa inna ilaihi raj'une gimbiya! An ci amanata, an cin min ina barci, an ga daren farko, gimbiya! gimbiya kina ina"

Mama dake saman salaya tana ta addu'a ta yi wuf ta mike har hijabinta na tadeta kamar zai kida

ya m da kasss ta yi sauri ta rike tana haki ta shiga rarumar wurare tana neman ky din dakin nata bayan a daf da ita ta ajiye da zata fara sallah

Da sauri Khadeeja ta mike zaune tana zarro ido, a lokacin da yake kara matsowa ihunsa na tayar da kowa a gid

an Domin harta mama Fateema sai da ta zabura zata fito kuma sai ta dakata ta yi tsaye tana sauraro saboda wani tunani da ta yi cewar haka kawai ma matarsa tace yakan tada irin haka wani lokacin cikin dare

yana matsowa suma sauran ya'yan sunna farkawa g

aba dayansu a tsorace har gware suke yi sannan suka hade sunna kallon kofar da Mama ke kokarin budewa da ky din nata, cikin ikon Allah ta gaza kamo na dakin tsabar firgita da ta yi

Murya a raunane Lubna ta ce" Mun shiga uku, waye ya tabo Aba?"

Khadee

ja ta yi tsuru , dama ba barcin ta yi ba, idannuwanta sun rine sosai, gaba daya daren bai fara Bama ama ganni take yi yayi tsayin gaske, dan ta kasa samun barci kasa kasa ta ce" Koma waye ya tabo mana rigima kuma shi da Allah gaskiya saboda Bama yannayin

guje guje!"

Kofar ya dora hannu yayi bugawar farko zai yi ta biyu Mama ta bude ta bayyana a gabansa tana haki ta ce" Lafiya? waye ya mutu? ko auren aka fasa?"

Aba ya zarro ido yana kallonta ya ce" Bakinki ya sari danyen kashi na safe irin bakin nan,

auren waye za'a fasa din? to ai ko mutuwa na yi na bar salahu a daura auren nan da kike tsaye kumatu na maki rawa kina janyo min alkaba'i ko kunya bakya ji!"

Mutanen da suka biyo shi sunna tambayar lafiya? kanneen amarya ne su biyu ne suka kalli junna ,

sai amaryar da ta bude kofarta ta yi tsaye tana kallonsa dan ta san halin abinta, idan ta yarda ta shiga abinda ya shafi gimbiya da shi itace a matsala ba kowa ba

A hankali Mama ta ce" Elhaji gani na yi dare fa ya tsala, kuma ai ka san gidan cike da m

utane, dan Allah mu je"

Aba ya girgiza kai ya ce" Ku kuka ga dare, mu a balaki muke, Mu je ina? gimbiya an wulakantani, an wulakanta maki Ni, an zage Ni tasss innalilahi wa inna ilaihi raj'une gimbiya yanzu aka shaΖ™ar maki kwalata"

Mama ta zuba masa

ido, sam bata yarda wai an zage shi an kama kwalarsa ba, haka kuma bata so koma meye ya fada a idon bakin mutanen da suke gidan yau, labarinsa suke ji, harta fateema ba zata so ta ji ko ta ganni gannin idannuwanta ba, Allah ya taimaketa ma bata fito ba, t

a kuma san ta farka dan kuwa hargagin Elhaji in ya fara ko me kake yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login