Showing 186001 words to 189000 words out of 200647 words
da neman taimakonsa da nema mata lafiya a ransa da kuma sake nema mata afuwa .
A tausahshe ya tambayeta idan zata bi shi? Gida wajen baba Hamza?
A dan birkice ta ce" Wajen baba? Baba zai sa a sake rufe
ni shikenan in daina ganninka, ka ga baba yace nice na kashe babanka wai, yaya za'a yi in kashe babanka? Ai litle ma sheda ce da mai sunnana a lokacin ai sunna nan ko khadeeja?"
Anmy ta sauke murmushi a tausashe ta ce" Mama, ba zaki yi haka ba ai, kuma
baba ne da kansa yace a kawo masa y'arsa ya ganki, ba zai sa a rufe mana ke na, muna son ki mama"
Kamar wata yarinya haka ta ringa murmushi tana fadin" Ko khadeeja? Kin tabbata?, baba fa ya tsane Ni fa"
Anmy ta girgiza kai da kula da tarin tausayin m
ijinta da mahaifiyarsa ta ce" A'a Mama, baba yana son ki, ke y'arsa ce ai ya fada ma"
Mama ta ringa gyada kai, aunty SHAREEFA ta mike ta ja masu aikin mama suka je dakinta suka duba abinda zata anfana du suka kwaso mata, sannan ta saka masu aikinta su
shirya summa zuwa dare a zo a dauke su saboda maman da su ta fi sabawa zasu ci gaba da kula da ita a cen dinma...., da wannan suka tarkata suka yi baban gida
Sunna zuwa suka tarar an gyara bangaren da su Hajia suke, dama bangare bangare ne a appartemen
t din, wanda suke bangare biyar ne harda na baba, su Hajia kuwa su uku ne , baba bai yi ta hudu ba, sai kawai aka sakata a dayan bangaren, su Hajiya Binta suka tarbeta aka turo Hajiya Inna itama harda ita a yan tarbar Tata, cike da tausayawa yannayin da t
a dawo, domin da farko buya ta ringa yi a bayansa tana cimuimuye rigarsa tana leko su ta jikinsa tana faman fadin a sanar musu bata kashe mijinta ba, ba zata kuma ba, idan ma ya dawo ba zata kashe shi ba kuma, sai a hankali ta yarda ta fito, harma ta saki
jiki a hankali da su har ya zamo ta zauna cikin su, kuma yanzu da suke gidan ya yi iya yinsa har ta fahimci cewar yanzu yana nan tare da ita zai je yayi wanka ya dan huta ne sai ya dawo, harma ta yarda ita da kanta ta ringa masa byby tana rike da hannun ku
rma har ya tafi sannan ta sake yin tsuru tana kallon su Hajiya dake kokarin ganin ta
ɗ
an sake da su , su dinma.
A lokacin da suka wuce dakin Khadeeja yana cire tufafin jikinsa domin ya sanar mata ta shirya su je gida, za'a yi daurin auren sisters dint
a, du irin yadda take cikin zumudi sai ta boye a hankali ta rungume shi ta baya ta yi shiruuuuuu
Irin yadda kirjinta ke bugawa a hankali a hankali ya saka shi juyo da ita ta gabansa ya rungumeta sosai a kirjinsa yana dan sauke ajiyar zuciya
Murya a t
ausashe ta ce" In sha Allah, mama zata samu lafiya, kar ka saka damuwa a ranka plz"
AL'WALED ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce" Kamar mama ta samu.....kamar ta samu tabuwar hankali.....Hajiya karama ko jinnin mahaifina ne yak..."
"Bata kashe sh
i ba, wanda ya kashe shin ai yana gidan yari har yanzu, kowace mace da irin yadda take tafiyar da kishinta, kar ka yi mamaki akoy wace ko mahaifiyar mutun tana iya yin kishi da ita......, laifinta daya ne kuma wanda ta yiwa ya yafe mata....su waye mu da za
mu dubeta da shi? Mama bata kashe aba ba, ba ita ta kashe shi ba Aban litle" ta fada a tausashe tana sake shiga jikinsa....., shi kuwa yana ta sauke ajiyar zuciya kamar wanda dama abinda yake jira ya ji kennan kamar bai san abin ba, kamar wanda fadin abin
magani ne a wata cutarsa
A hankali ya dago habarta ya kura mata ido, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi kasa kasa ya ce" Ina son ki....."
Khadeeja ta lumshe idannuwanta tsigar jikinta na tashi
A hankali ya sake furta" Ina son ki Ro
hi"
Yanzu kam har sai da ta jimke hannayenta a jikinsa da dan karfi
A tausashe ya ce" Idan kina haka....., ba zamu iya zuwa wajen daurin auren ba fa....., sake gwadawa zan yi ko ma samu ciki "
Yanzu kam sai kawai ta dake shi da gudu ta yi bayi tan
a dan ihun jin kunya, wanda ya saka shi sakin murmushi ya bita da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin zuciyarsa na sakewa sosai da sosai sannan ya fice ya je nasa dakin shima dan ya shirya
Kusan sallar magariba suka fito daga gidan suka dauki ha
nya, a dole suka dakata dan yayi Sallah a masallaci, dan ya dauke mata kewa Sai kawai ya kamo mata tiktok ya bude mata data ya fice tare da direba
Kallo ta shiga yi hankali kwonce, lokaci daya kuma msg na shigowa a WhatsApp dinsa , msg din kuma na numba
daya ya fi shigowa yana karawa harda callll kamar jira ake yi ya bude datar
Har ta share wani call din ya sake shigowa, a lokacin ta gyara zata dauki hoto da wayar ne cikin tsadadan lesss dinta mai ruwan Golding, sai kawai ta shige msg din dan tace zai
bada amsa idan ya dawo, Sai gannin voice note ta yi rututu, da hoto da kuma missss callll da rubutacen sako
Abinka da wayar da ba'a saita mata harkar bude hoto ba, tana shiga hoton ya bude da kansa ne , kuma abinda ta gani a hoton shi ya nemi dauke gan
ninta hadi da jinta lokaci guda, har ya zamo kura nasa idon da ta yi bata san cewa an fito daga masallaci ba har direba ya bude ya shigo, har sai da ya bude shima zai shigo ya ganta a gefen da take, wato bayan direba take zaune kasa kasa ya ce" Madame dan
matsa , ba zaki zauna a bayansa ba, ko ya baki in ja ne?"
Khadeeja ta dago da sauri saboda sai a lokacin ta ji mutun, kuma ta ji Muryarsa
Irin kallon da ta masa ya saka shi
ɗ
an dubanta da kula ya furta" Are You ok?"
Ama khadeeja ta kasa ce masa uf
fan, sai matsawa da ta yi tana kashe hasken wayar kirjinta na wata irin masifafiyar bugawa kamar zai balo ya fito daga kirjinta
Gaba daya jikinta rawa yake yi, gumi na neman wanke mata jiki, du kuma sanyin acn cikin motar sai ta ji kamar iska ta yi mat
a kadan, kamar ana zafin balaki
Du irin yadda ya ringa tambayar ko lafiya? Khadeeja ta kasa amsa shi sai farcen karamar yatsarta da ta saka a bakinta tana ta faman cirewa har ta fara cizon yatsar
Kasancewar sun kusa gidan ne aka fara kiran sallar d
a wuri suka iso, sunna isowa bata tsaya ta saurari riko hannunta da yayi ba sai kawai ta fice tana ajiye masa wayar a nan saman kujerar ta yi ciki kamar zata kifa, ko kula bata yi da Aba dake kokarin fitowa da kunnu a baban faranti na baba da aka gama yanz
u yanzu ba
Da sauri ya bude motar zai fita, sai kuma ya dakata ya dauki wayar yana kallonta da tunanin me kenan?, yanzu yanzu fa yana magana da matarsa lafiya kalau Allah ma kuwa...., me yake faruwa me aka yi? Me ya rikitata? Ko bata jin dadin jikinta n
e?
Aba kuwa har zai dura ashar ya gane wace dan haka ya wani saki murmushi ya ce" Ke anmy ya zaki wuce babanki a kan hanya? Dawo mu gaisa yaushe rabona da ke yar albarkana tun fa jiya ko? Dama ina so mu yi zance na uba da y'a in ji in komai kalau bari
in ba tsohon cen kunnunsa in zo kafin yan daurin auren su karaso saboda cewa na yi a daura idan aka fito daga sallar isha'i"
Khadeeja dake haki bata iya cewa komai ba sai gyada kai da take yi, wani irin jirri na dibanta da jin karnin kunnun aba har ciki
n kwakwalwarta da kirjinta, bayan ta gyadawa Aban kai sai kawai ta shige tana rufe fuskarta da sauri ta bi ta bayan gida ta nufi ciki ta baya , tana shiga ta shige dakin Mama ta banko kofar ta cire mayafinta ta yar a nan , ta cire dan kwalin ta yar ta ring
a haki kamar mai kamun athsma ta
ɗ
ora hannu a kai zata fasa ihu mama dake tsaye da dan kwali zata daura shigowar khadeejan ya sa ta dakatar da mamaki tana binta da kallo da sauri ta ce" Subahanalah, ke? Lafiyarki???"
Khadeeja ta juyo da karfi, dan wall
ahi bata zata, zata samu wani a dakin ba, a hankali take girgiza kai, sai kawai ta duke a nan ta fasa kukan da take ji zai kashe ta idan bata yi ba
A tsorace mama ta furta" innalilahi wa Inna ilaihi raj'une anmy lafiya? Me yake faruwa? Me ya damu mijin
naki? Ina babanki? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, me yake faruwa??????"
A tsorace mama ta nufi kofar dan a gaskiya tsoro ya kamata mai karfin gaske, har sai da Khadeeja ta dago tana kukan nan ta ce" Mama sunna waje, innalilahi mama wallahi hotonsa n
e da wannan wace akace budurwarsa ce, mama ya rike habarta, wallahi ya rike habarta innalilahi wayo Allahna zan mutu na shiga uku na lalace"
Mama ta juyo da karfi ta yi turus tana kallonta, daidai nan lubna ta shigo bayan ta buga da salama zata yi magan
a itama ta ja ta tsaya haka kuma da sauri ta maida kofar ta rufe ta shigo da kyau tana fadin" Subahanalah, mama lafiya? Me ta yi kika doke ta?"
Mama ta gyada kai, cike da takaici ta yi kyaftu ta nuno su da yatsa ta ce" A'a yankata na yi, nace yankata na
yi Lubna, kin ga na rantse idan ta yi wasa da Ni dukanta zan yi a gidan nan, Ni zaki kashe ina ta kaina ki fasa min kukan iskanci kukan jin dadi a kan kishin miji? Ke yanzu dan kin ga hoton mijinki da budurwa ne kike yin wannan? To ai gwarama ki daina sab
oda namiji ai ba dan ke kadai aka halicce shi ba, idan ma kika saka haka a Tanko ai wahalar da kanki zaki yi, in ba iya shege irin naki ba ke ubanki nawa yayi? Kenan dai ba zaki nutsu ba ko?, ai na zata kin nutsu anmy, na zata kin nutsu fa, ashe da sauran
ki ko? Ki yi aniya ki daga min hankali in nada maki na jaki a gidan nan!"
Mama na gamq fada ta daura dan kwalinta ta dauki hijabinta ta zumbula ta fice tana mako musu kofar
Da sauri Lubna ta karasa ta kama Khadeeja tana mikar da ita a tausashe ta c
e" Anmy, shigowa da kula kuma? Waye ya taba min ke?"
Khadeeja ta RINGA shasheka ta ce" Yaya za'a hannani kuka? Kin kuwa ga hoton? Kin kuwa san wacece ita a duniyarsa? Ana ta dauki ba dadi da shi a kanta fa, yaya za'a yi ba zan damu ba?, kin san a yaya n
a ga hoton? Jikinsa da nata a hade, jikin Aban litle mai daraja ya hade min da nata? Shikenan an cuceni, an gama da Ni, an gama cutata, shikenan an wulakantani, wayo zan mutu, taba kirjina ki ji inaga shikenan lokacin yayi......."
Lubna ta dubeta shekek
e kafin ta nuna mata yatsa ta ce" ke da kaniya ban hannaki kuka a kan namiji ba?"
Khadeeja da tarin takaici ta ce" To ai sai ku kashe Ni ku huta, an gaya miki baban litle namiji ne?"
Lubna ta dubeta da mamaki ta ce" na bani, kamar ya????"
Khadeeja
ta ce" Ina nufin wallahi ba banzan namijin da ba za'a yi masa kuka bane, to in ban yi masa kuka ba in yi me? Wallahi mijina ya isa a masa kuka, kuma sai na nemo ta dan ubanta na daki banza, wayo Ni wayo kaina"
"Eh lalle bari mu sake dukawa a yi mana au
ren nan, dan wallahi wannan lamari da ya gigita Anmy ba karami bane, gwara dai a mana auren nan mu tafi mumaa" Lubna ta fada tana dauke kanta hadi da dan girgiza kai
Khadeeja ta yi sororo tana kallonta ta ce" Ama dai kin san Ni ba y'ar bace kar ki fasar
ani mana"
Lubna ta tabe baki ta mike tana isa wajen kayan mama ta dauko turarukan da mama ta tanadarwa khadeejar tana fadin" Sai dai kar a kuma , su anmy ai an gama shiga gari, ga dai kayan karin gyaran zaman auren nan, kin ga kayan nan wallahi makudan
kudade mama ta kashe ta siya maki su , wasu muka hada maki da kanmu, wallahi ki kula da kyau ki yi anfani da su yadda ya dace, idan sun kare kuma sai ku kawo kudin ku a muku wasu dan ba zamu tsaya muna muka bati ba"
Khadeeja ta dubeta tana janyo hannunt
a ta ce" Lubna, dan Allah ki zauna ki kwontar min da hankalina, walahi ban nuna masa komai ba fa, kuka ne na yi dan in huce da"
Lubna ta dubeta da kyau ta ce" Kin tabata baki yi a gabansa ba???"
Khadeeja ta gyada kai tana kallonta
Lubna ta sauke a
jiyar zuciya a tausashe ta ce" Haba kema, anmy a gabanmu sau nawa idan aba ya fara neman aure irin yadda mama ke yi?????, shikenan ke da bama neman auren ne yake yi ba sai ki gigice haka? Ina amfanin kokarin da mamanmu ke yi dan ta jure ta cije ta yi wats
i da komai zai je a wajenki ????, kina gani aure aba zai yi Ama a kulun darajar mama daban take, a gabanki ai irin hidimar da zai yiwa mama ma daban ce, ke shaida ce ko hudubar da yake yi idan ya hade mu da sabuwar matarsa da mama a kan tsakanin matarsa da
mama ma daban ce....., ke yanzu a ganninki da mama zuwa ta yi du auren da zai yi ta ringa iface iface ta ringa biye masa da ta kawo warhaka cikin hayacinta?....., wallahi da tuni ya fitar da ita a hayacinta inma wai tana gidan nan....., dan kuwa tsaf zai
masheta birin wasa in dai Abanmu ne...., kuma ba shi kadai ba, in fada maki kaf maza haka suke, abinda kika san baki isa ki iya Hanna su ba gwara ki hade ki yi watsi da abin ki yi sabgar gabanki ina mai tabbatar maki sai kin fi kima da daraja a duniyarsu f
iye da wace suka gano din suka auro din, kuma in aka yi rashin dace ta shigo da rawar kai wallahi dai ta zama kamar tinkiya a gaban nasu fa"
Khadeeja ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Ni da so samu na yi, karma yayi yan matan"
Lubna ta yi murmu
shi tana rike hannayenta a tausashe ta ce" Ba zan so ki fara da haka ba, dan zaki wahalar da kanki, ki wahalar da iyayenmu, sannan ki wahalar da mu....., kin ga du abinda ake zumudi ba dare ba rana bako ne, idan ya riga ya zama na yau da kullum anfani ake
yi da shi
ɗ
an abu ne da ya zama dole a yi amfanin da shi a rayuwa........, anmy misali abinci.....du ranar da kika ga sabo yaya kike ji a ranki? Ama idan kika jera kwanaki kina anfani da shi fa? Wani lokacin zaki cenza shi har na kwanaki kafin kuma ki ji
ya mugun biyo maki a rai......, to ki dauka haka.......du kyan mace, du takamarta ana wayar gari mijinta ya so wace bata kama farcenta a komai ba....., zaki ga wani auren idan namiji yayi ana cewa ikon Allah wai kin ga Amaryar? Saboda an raina yannayinta d
uba da uwar gidan yadda take, wannan kuwa ba wani abin mamaki bane ai Anmy, yannayin namijin kenan, abinda ku baku gani ba shi ai ya gama kanowa, wato bakon gida, bakon wuri, sabon waje, shine zaki ga da an kwana biyu kuma komai ya daidaita kun dawo kun za
ma daya sai kuma a koma kan maganar wace ta fi iya hakuri, iya tafiyar da shi, iya girki da tatali da komai ta fi kwatar zuciyarsa......., to kin ga kuwa mutanen da Allah ya basu irin wannan baiwar mai zafi zaki ce ki saka damuwarsu a ranki, tabasssss zaki
halaka kanki a banza saboda su ba wannan ne damuwarsu ba, idan suka riga suka hango ki kame kanki ki yi ta addu'a shi ya fi alkhairi, ba sai kin zubar da darajar ki, ki bari ya gama gane ki ba, daga baya ki ce zaki wani ja zare...., wani zaren? Wanda kika
gama tsinkawa a gabansa! Ai kin gama bude masa komai ya gane cewar sai da shi zaki rayu, in wata ta rabe shi kina iya mutuwa meye kuma zaki birge shi da shi....., Ni Bama zan yarda ya gane kishina a kansa ba Allah kuwa"
Khadeeja ta ringa samun kwarin g
wuiwa, har ta ji zata yi masa uzuri ta ji me hoton ke nufi idan har ya yi mata maganar....saboda ta kula Aban litle yana da kula sosai da tausasawa........
A hankali ta ce" Ke wai ya aka yi tumbin gimbiya na ga ya karu? Ita da bata da tumbi?"
Lubn
a ta zarro ido ta mike tana fadin" bari in yi kiran su Karima su kauro nan mu hadu, dan Ni kadai ba zan iya da lamarin ki ba, ke kam kin kunna yanzu kuma kin tashi daga rikicin da kika shigo