Showing 198001 words to 200647 words out of 200647 words

Chapter 67 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

19

shekarunta nawa yanzu? Kawai ya shafa fatiharsa a masallaci a rabar da naman wa makota shikenan , baba kuwa Allah ya raya .

Ba shiri kowace ta bi mijinta suka juya gida

Sunna zuwa ta nufi bangarenta ta kimtsa kamar yadda

ta saba, domin kokari take yi sosai da sosai , sam bata bari ta jibge ba, hakan ya sa take samun dadin jikinta sosai da sosai

Tana cikin saka turaran wuta a dakinsa ya shigo yana murmushi da wayarsa ya hasko mata Aunty SHAREEFA da ta yi masa VIDIO call



Ai kuwa ta gyara rigar rijinta da kyau ta zauna tana amsa kiran , shi kuwa ya zauna daf da ita yana kallon yadda suke fira har suka gama suka yi salama sannan ya kashe kiran ya mikar da ita ya nufi wajen bed da ita yana kokarin cire mata rigar nan ya

ce" Mu je in murza miki kaffafuwanki kin gaji sosai maman litle"

Khadeeja ta yi murmushi tana rike hannunsa ta ce" Fisabililahi Ni nace na gaji?"

AL'WALED ya sake riƙe mata hannun ya karra nufar gadon da ita yana murmushi shima ya sabule rigar

Kha

deeja da mamakinsa ta ce" wai Aban litle da wannan tulun cikin me yake jan ra'ayinka????"

AL'WALED ya dubeta yana jin dokin jikinsa na sake murdewa a tausashe ya shiga neman rikitata kasa kasa ya ce" Kin fi kyau a haka....., kuma Allah ya taimakeni mai

hannani ihu ta je wajen kakanta..... Anmy......... Zo mu bashi madara ko ya karra karfi yayi ya fito ko?????"

Murmushi kawai ta yi, du irin yadda cikinta ya girma haka take jurewa ta bashi hadin kai, danma tunda cikin ya kai haka shi da kansa sai yake d

aga mata kafa, Ama fa idan ya tara abin baya ji baya gani sai ya amayar, bale yau da litle ta tafi ai ita ta kawowa aiki dan kuwa babanta sai ya baje kolinsa a duk inda hali ya bada.

Washe gari bayan sun karya tana zaune kaffafuwanta saman cinyarsa yana

amsa waya da abokinsa da zai shigo garin kan harkar kasuwancinsa ita kuwa sunna faman chating ta whatsup da yan uwanta har ya gama wayar ya ajiye itama ta ajiye tana dubansa saboda maganar da ya fara

A nutse ya ce" Bab a ina kike son haihuwa? Wace kasa

zamu je?"

Khadeeja ta Dube shi da dan mamaki ta ce" Maleek khalbi, wace kasa zamu je kuwa da ta wuce nan?"

Ya

ɗ

an sake duban ta da kulawa ya ce" Bakya so mu je wani wajen?"

Khadeeja ta girgiza kai a hankali ta ce" Na fi so a nan, kusa da su Hajiy

a , hankalina zai fi kwonciya, ka ga daga baya sai mu tafi idan da rai da lafiya"

Murmushi kawai yayi yana ji a ransa anya a yanzu zai iya yin wata tafiyar kuwa? Baya jin in har zai iya yi, saboda ba zai taba lamunta nakuda ta taso mata baya kusa ba, ya

na addu'a ba dare ba rana kar Allah ya sake nuna masa ranar da ya nuna masa a kan maman litle, ranar da ya kawo matarsa haihuwa ta haihu aka bashi jaririyar a hannunsa mahaifiyarta kuwa aka lulubeta aka yi mutuware da ita, tabasss ya shiga halin tashin han

kali mai wuyar fasara, yana fatan Allah ya jikanta sannan ya sauke duk wata mai junna biyu lafiya.

Sannu a hankali ta ci gaba da rainon cikinta, a gidan aba kuwa sai da yayi taronsa Ama ba mai yawan nan ba, dan kuwa ita mama bata yi Bama sai yan anguwa

da suka ringa lekowa ana sake yi mata Barka da ban gajiya har aka gama aka watse, sannan ta Hanna su Khadeeja zuwa sai zamansu suka yi, ita kunya take ji, ya'yan nan kaf dinsu wata kama ce da su kawai sai su zo su jeru? A'a Allah ya kiyaye ba zata kwashi a

bin kunyar nan ba gaskiya

Kwonci tashi asarar mai rai, a lokacin da cikin Khadeeja ya kai haihuwa ya zamo hatta baba Hamza baya wuni bai lekota ba, bini bini zaka ga wani ya leko yace dan a gaisa ne, ita abin har dariya yake bata, irin kulawar kuwa da

mijinta ke bata ya fi komai kwontar mata da hankali da saka mata nutsuwa , ya zamo bata wani fargaban haihuwar , ta gama fawalawa Allah komai tana jiran lokaci

Yau asabar, sun tashi da karfe daya na rana da nufin sauka kasa dan su ci abinci, a lokacin

da ta zo saukowa daga gadon bayanta ya rike mata, wata irin rikewar da bata taba jin irinta ba kafin ya sakar mata tauna mai zafin gaske da radadi

Du yadda ta gwanance wajen boye masa nakudar tsaye da take fama da ita lokaci zuwa lokaci a yau sai da ta

durkushe daga gadon tana rike bayanta hadi da sakin salati cen cikin wuyanta tana rintse ido

Tawul din da yake goge hannunsa da shi bayan ya sa turaren hannu yayi yawa ya ajiye da sauri ya nufota yana kamata hadi da fadin" Subahanalah, Anmy lafiya????"

Khadeeja na kokarin jurewa ta ji kai abin fa ba na dannewar nan bane dan haka a hankali ta ce" Bayana ke ciwo Aban litle, wayo marata, cikina"

Lokaci guda ya rasa abinda zai yi cikin neman a kama masa ita da kuma neman kamata shi kadai, da kyar ya i

ya rarumar wayarta ya dannawa kaka b kira cikin dan gaggawar magana ya sanar mata

Ai kuwa itama da sauri ta mike tana fadin" Ka kwontar da ita kafin in zo, kar ta zauna gamu nan zuwa idan nakudar ce sai mu wuce asibiti"

Nan da nan ta sanarwar du Wand

a ya dace ya ji sannan ta wuce da gaggawa bayan ta sanar da su cewa su yi hakuri bari ta je ta gani sai a ga abinda ya dace, dan kuwa hatta Mama khadeeja gaza motsi ta yi nan da nan ta dauki carbi ta ringa ja jikinta na rawa, dan zata iya cewa ta fi mai ci

kin nan kwana da zulumin haihuwar nan a ranta, kullum kuwa cikin ha

ɗ

awa Khadeeja abin zubar da zaki take yi, a yanzu da kyar ta iya rike kanta dan kunyar su Hajiya da nauyinsu, kar su ga du irin yadda suke tsaye a kan jikan nasu da matarsa zata nuna musu z

akewa, ama Allah kadai ya san irin yadda zuciyarta ke bugawa

Tunda aka kawota gidan nan Hajiya Binta bata ta

ɓ

a shiga dakinta ba sai yau, Allah ya sa shigar jikinta mai kyau ce, haka shi dinma dan haka bata wani ji nauyi sosai ba duba da ta rai ake yi ya

nzun

Yannayin da ta samu Khadeeja a dole ta shiga sauke kayan haihuwa nan da nan ya rungumota jikinsa suka kama masa suka karasa mota suka dauki hanyar asibiti, baba Hamza kuwa da aba suka shige motar aba sidik ya ja su, sunna tafe sunna hailala kamar

zasu je idi

Kasancewar ta jima cikin nakudar tsaye, kuma mama ta nuna mata ta cije ta jure ta yi ta doguwar tafiya ta rike addu'a in sha Allah za'a samu mai sauki ya sa sunna isa asibiti tun a kan kwana kai ya fara badowa, hakan ya rikita AL'WALED, Haj

iya Binta kuwa sai kawai ta gyarata da kyau dan kar ta dane kan har suka isa asibitin likitoci da gudu suka turo gadon mararsa lafiya aka dorata suka tura suka yi ciki da ita, shi kuwa har ya fito sai kawai juwa ta nemi kwasarsa har sai da Aba ya riko shi

tam yana girgiza kai ya ce" Ka rufa mana asiri ka mike wa bilahilazi kar ka saki ka yi mana lumshe lumshen idannuwa a wannan halin da ake ciki yau ga tashin hankali"

Baba Hamza ya kama masa suka kai shi saman kujera sannan suka saka shi a gaba da nasiha

, Hajiya Binta kuwa tana ciki wajen da mata ke jira da kayan haihuwar tana ta addu'a kuma tana jiyo duk wani motsin da ake yi a ciki har kunnayenta suka jiyo mata ihun jariri, lokaci daya ta mike tana ta hamdallah sannan ta tsaya har aka sake amsar kayan

baby aka koma tana zaunen nan har kusan minti Talatin kafin a fito da jariri boy ya sha kayan sanyi Masha Allah kato da shi, sai mahaifiyarsa da aka fito da ita itama a saman kujerar tukawa domin tuni an fitar mata da jinni an yi mata dinki, haihuwar da s

hiryatan bai wuce awa daya da rabi ba komai ya gama cikin ikon Allah aka kaita dakin hutu da ƙarin ruwa dan ta karra karfi

Cike da farin ciki kaka b ta kai musu jaririn, AL'WALED kuwa ya zuba mata ido a lokacin da take fadin" Alhamdulilah alhamdulilah,

ga yaron mu, ga yaron mu ta samu lafiya har tana dakin hutu , Masha Allah alhamdulilah"

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tare babyn yana sake zuba masa ido, sai kuma ya mike ya mikawa su aba ya nufi ciki yana bin bayan Hajiya Binta dake waya d

a su Mama Khadeeja tana fadin ai in Allah yayi nan da awa hudu sa dawo gida a

ɗ

ora ƙatuwar tukunyar wankan jego .

Aba ya zubawa yaron ido kafin ya kalli baba Hamza ya ce" Ka ga d'a kamar na turawa, Ni gaba daya ma tsoron Allah ya kama Ni, ikon Allah wai

yau uwata ce da d'a"

Baba Hamza ya ce" A'a cewa zaka yi yau kai ne da jika na hudu, haka batun yake ka tsufa malan"

Aba ya Dube shi shekeke sai kuma ya mike yana fadin Bari dai in sanarwa Gimbiya, ana cen ana munafurci wai ba'a damu ba , yanzu haka

tana cen tana karkarwa a daki ita kadai, bari in sanar mata sannan in je in dauko takwarar Tata in Kai mata ita dan na tabbata ta Larabawa yanzu da tana iya tashi da ta cira mun ganta a nan dan tsabar soyayar jika, Ni kam da sauki gaskiya ban iya wannan ra

shin kunyar ba"

Shi dai baba Hamza bayan ya yiwa yaro addu'a yana sake maimaita sunnan da babansa ya gama yi masa rada yanzun nan yana jin wata irin kaunar yaron na ratsa sasan jikinsa.....ikon Allah kamar an sake bashi mahaifin AL'WALED a lokacin da ya

na jariri, kamanun har sun

ɓ

aci, ashe zai ga wannan ranar, kai shi ko yanzu ya bar duniya alhamdulilah an ga duk ribar da ake jira........yaro ya yi kama da mai sunnansa kamar har ta baci

A daki Hajiya Binta guduwa ta yi waje ta bar masoyan nan sunna s

insinar junna, ko tace yana zaune saman kujera sai faman sinsinar hannayenta yake yi yana ta duba cikinta yana murmushi

A tausashe ya ce" Sannu Anmy....., Allah ya miki albarka, ya raya mana boy"

Khadeeja ta lumshe ido sannan ta sakar masa murmushi a

hankali tana sake riƙe numfashi dan ji take yi idan ta yi wasa

ɗ

inkin nan tsaf zai barke mata su shiga uku.

A tausashe ya ce" Kin ce a saka masa sunnan Marigayi ko? Na masa huduba da sunnan, Ama me zaki ringa kiransa da shi ?"

Khadeeja ta Dube shi c

ike da jin dadin ya yarda da ta roki ya saka sunnan Marigayin dan su farantawa baba Hamza da shi kansa da kaf ahalin gidan nan, a tausashe ta ce" Litle tace ameer ya fi, cikin biyu muka zaba Khalifa ko Amir"

Yayi murmushi yana zaunensa darr bashi da jiy

ar fitowa sunna shan firarsu , summa a waje sunna shan tasu da kuma gulma har aka maido babyn saboda sanyi sanyin waje sannan suka yada tabarma sunna jiran tuwo daga gidan Gimbiya har a sake su, dan sun ce su ai sunna nan kawai sa koma gidan da mai haihuwa

r.........

Sun dawo gida lafiya , nan fa gida ya shiga kwasar yan Barka, domin hatta Mama a ranar ta zo ita da kurma wace ta ha

ɗ

a y Nata y nata ta yi musu bankwana cewar ta koma gidansu kuma tunda dai mamanta ma ta kawo babyn, a ranar kuma aba ya kawo

hajiar larabawa wace ta yi ta farin ciki tana ƙara rungumar baby , danma basa nan za'a yi sunna domin zasu je umarah ne wace Khadeeja ta biya musu harda uncle Umar da kuma mama fateema, su kam me zasu ce da auren nan banda fatan ALKHAIRI? Sunna matukar ad

du'ar fatan ALKHAIRI da karra dangon soyaya da zumunci sosai da sosai.

Bayan kwana bakwai aka zana taron sunna, aka yi taro na mamaki, taron da ya yi kamar na daurin auren koma sama da haka domin du Wanda bai samu halartar daurin auren ba ya samu hala

rtar na sunna, ciki harda dangin mama Khadeeja , domin tunda ta samu lafiya suka je harda baba Hamza suka rinqa bi gida gida sunna neman afuwar danginta , wannan dalili kuwa ya ha

ɗ

a kwai da kwarwata shagali ba'a cewa komai sai hamdallah

Bayan taro ya wa

tse ya rage mai jego dake bayi ana faman yi mata wanka mai zaman kansa domin irin yadda ake dana mata ruwan zafi da tawul sai ta baka tausayi, kaka b kuwa ta dage sosai sai dana mata take sai da ta gamsu da gashin sannan ta fito ta dauki hijabinta ta dauki

Ameer a hannun babansa tana fadin" Bari in Kai shi Hajiya Inna zata gasa shi, ka san kowa da abinda ya fi kwarewa Ni ban iya wankan jarirai ba, Hajiya zainab kuwa ana cen ana famar salamar baki , iyayen nan naku kuwa dama ai sunna cen ana fama da waya wai

harda su Shareefat a rawa kai Allah ya kyautawa iyayen zamani"

Murmushi yayi yana

ɗ

an sake gyara mata rungumar baby din ta fice sannan ya mike ya fitarwa Khadeeja da kaya mararsa nauyi hadi da pant da auduga tare da turare kayan da turaran fesawa sanna

n ya same zaunawa yana jiranta

Mintinan kadan ta fito daga wankan, ta nade gashinta a tawul karami...., sannan ta nado wani a jikinta, ta yi jajajir sai fitar da hucin ruwan wankan take ta karaso direct inda kayan suke tana fadin" Papah litle me ake mi

n a dakina fisabililahi?"

Murmushi ya saki yana sake gyara zama ya ce" Zuwa na yi in ga matata ko ba'a yarda ba???"

Khadeeja ta saki murmushi tana buya wajen gado ta saka pant din, shi kuwa har dogon wuya yake yi sai da ta dago suka yi ido hudu ta su

ne kai da kunya ta ce" Kai dan Allah a'a fa"

Ya saki murmushi mai sauti yana mika mata hannu ya ce" Wai ya aka yi kike yin ja dauuuuuuu kamar an silalaki??"

Khadeeja ta saki dariyar da bata shirya ba ta zo a hankali ta shige jikinsa tana kankame shi

a hankali ta furta" Aban litle, i love You so muchhhh"

AL'WALED ya ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" maman Litle, kar ki sa in KARRA maki ciki fa kuma a ga laifina"

Dariya ta yi tana karra shigewa jikinsa ta yi luffffff abinta shi kuwa ya ru

ngumeta da kyau yana shafa bayanta yana jin nutsuwa da kwanciyar hankali ya sake lulube duniyarsa........

Alhamdulilah

🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

A nan muka dasa karshen wannan littafi namu mai taken farkon gannin idona....., ina fatan littafi ya

kayatar da ku yan uwa....., ina mai sanar maku cewa in sha Allah MAGE ZAGAYE NA BIYU ZAI SAUKA A SABON WATA, INA FATA ZAKU SHIRYAWA TAFIYAR? GODIYA NAKE SOSAI YAN UWA idan na yi kure a yafe min, na gode, daga alkalamin taku y'ar mutan Nijar....wato SAJIDA



55

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login