Showing 78001 words to 81000 words out of 200647 words

Chapter 27 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

30

/>
Baba ya mike tsaye, hakan ya sa Mama juyowa ta kalle shi domin yanzu ta gama yi masa maganar irin mugun motsin nan a yannayin da yake ciki, bashi da lafiya, hawan jinninsa bai sauka ba, du yadda yake

yin karfin hali kuwa ita bai isa ya boye mata asalin abinda yake ciki ba

A hankali baba Hamza ya ce" Kana jina kuwa?"

Aba ya ce" Ina jinka Elhaji, wai kana nufin gobe jibi? ko nan da wasu watanni?"

Elhaji Hamza ya ce" Gobe jibi nake nufi"

Aba

ya dafe gaban goshi ya sake kallon Mama ya ga magungunan take ha

ɗ

awa, sai kawai yayi ciki ya shige dakinsa ya rufo ya ce" An gama, in dai kun shirya shikenan, meye na wani y'arka ta yarda? ai ta yarda bata yarda ba sai na yi, y'ayana ne fa kuma na isa da a

bina!"

Baba Hamza ya ce" Ka ga bana son fitina, ko menene ka bi shi a hankali, bana son abinda za'a zo a tada fitina ka ji dai na fada maka"

Aba ya yi murmushi yana fadin" Ka fa san namiji nake na isa da gidana, kawai an gama ina zuwa , da yama mu ha

du mu gama magana in sha Allah"

Daga nan bai wani tsaya jin ta bakin baba ba ya kashe kiran yana washe baki da murmushi

Shima baban murmushin yayi ya mikawa AL'WALID wayarsa yana fadin" Yaron nan akoy mutunci, Allah dai ya masa albarka"

AL'WALID

kuwa amsa kawai ya yi, zuciyarsa cike da tunanin irin yadda babanta ke gaggawa kamar yadda baba Hamza yake yi, gaba daya bai gane lamarin nan ba, ita fa kanta yarinyar ba zai iya cewa ga kamaninta ba, kanwar nan Tata kawai ya gane.......wai a haka za'a dau

ra masa auren da ita? gashi auren nan ga dukkan alamu sai an saka masa abubuwan tsauri masu yawa a kansa, tun yanzu ana fadin aure aka daura masa auren ake so yayi? da waye zai yi auren? girma ai girma ne , ba kuma zai fadi a gaban kowa ba

Wuta ya kashe

wa baba ya sake jaddada masa hutawa yake so ya yi sannan ya fita ya tafi dakin motsa jikinsa

A gidan Aba

Bayan ya kashe kiran da suka gama da Elhaji Hamza sai ya fada bayi ya yi wanka sannan ya fito ya saka jalabiyarsa bayan ya

shirya ya fito da ky din motarsa

Gannin mama a falon a zaune har yanzu ya saka shi sake daure fuska sosai sannan ya zo ya zauna inda ta ha

ɗ

a magungunan da ruwa ya dauka ba tare ya yi mata gardamar sha ba ya sha abinsa ya bude madarar da ta ajiye masa y

a shanye itama sannan ya dubeta kamar yadda take kallonsa ya ce" Zan je nan in dawo"

Mama ta sake dubansa da kyau, a tausashe ta ce" Ama ka ga ai na auna lafiyarka baka da lafiya, kana da bukatar hutawa koda na yau kadai ne, in ba zaka yarda da maganata

ba ka wuce mu je asibiti gado zasu baka Elhaji "

Aba ya sake dubanta, kamar ta sauko fa, saboda jiya zuwa yau yadda take yi masa magana daban da yanzu, kamar ta sauko kamar ta koma gimbiyarsa ta da, sai dai ba zai yi sake ba aje so take yi ta ga ya sak

u ta sake juye masa

Kai ya girgiza ya ce" likitocin nan naku me suka iya banda son kudi? rike mutun din da suke yi ai ba dan ciwon ya kai a rike shin bane, sunna son yan kudadensu ne kawai suke yin munafurcin nan, ama ai kin ga yanzu da sauki kuma fitar

nan mai mahinmanci ce sosai da sosai in ban yita ba akoy matsala"

Mama ta sake fuskantarsa a tausashe ta ce" Elhaji, dan Allah ina so mu yi magana"

Gabansa sai da ya fadi , ya dubeta ya ce" Ina jin ki"

Mama ta sake sada kai, sosai da sosai da yan

ayin girmamawa ta ce" Elhaji, dangane da maganar Karima ne, dan Allah ka yi hakuri, ka yi hakuri Elhaji, ama dan Allah kar ka aura mata yaron da ya koya mata bijirewa iyayenta, idan ka aura mata shi ba zai riketa da mutunci ba, kana ganninsa ka ga irin kan

gararun yaran nan da basu dauki kan kowa da gashi ba, yanzu irin wannan ne abin a hada zuri'a da shi? dan Allah ka yi hakuri ka bata dan lokaci ta fitar da wani mijin, ko kai ka sake samo mata wani mijin mai mutunci da zai riketa da amana, ama dan Allah in

na bata maka ka yafe min "

Har ga Allah sai da ya ji har cikin zuciyarsa ya karaya da lamarin gimbiya, ya Salam, zai iya rantsewa ko yanzu mutuwa ta dauke shi ya bar baya a hannu mai kyau, bale Allah ya taimake shi kaf iyayen ya'yansa uwar KARIMA ce ka

wai ke kawo masa rashin mutunci da kutse a cikin gidansa, bayanta kaf dinsu sunna girmama gimbiya sunna kuma Binta da fatan alkhairi na irin rikon da take yiwa ƴaƴansu da zuciya daya, shi shaida ne, domin malan Lubna har kyauta take yiwa gimbiya na mayafai

ne da sauransu domin a naija ta yi aure tana kasuwancinta , du in zata zo direct take zuwa gidan a zauna a sha fira da sha tara ta arziki, kuma idan zata siyawa Lubna pant sai ta siyawa sauran, ama uwar KARIMA? uwar KARIMA? ya fada hannun y'ar daba da ya

aureta

A hankali shima ya ce" Gimbiya, yanzu yarinyar da ta wulakantaki, ta bude kofa ta yi guduwarta cikin dare, ta je ta hadu da uwarta har suke son binki da shari ce zaki ce wai a kyaleta? da ki barta gimbiya in aura mata shi din, tunda shi ta zaba

kina gani fa, shi tace tana so"

Mama ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Yaya zan yi? abinda ta yi khadija na iya aikata min in ta samu muguwar kawa ko mugun mai bata shawara, shi yasa nake yi mata uzuri, kuma yaron nan walahi Elhaji sam bai kwonta

min a rai ba, tsoro nake ji ace an aura mata shi ya wulakantata"

Aba ya gyada kai ya ce" Zan daga mata kafa na duka, ama ba yana nufin zan barta nan da nan ta kuma fita ba, kuma yaron nan ki yi hakuri gimbiya shi ta nuna tana so, idan ba'a bata shi ba

ko waye aka bata ba zata zauna ba, kin ga yarinyar nan? wannan salihancin da ya sameta ba komai bane wuya ta sha, da zarar ta samu sauki zata ci gaba da abinda take yi, kuma mahaifiyarta ta riga ta hure mata kunne, ki yi hakuri daga ita har mahaifiyarta in

ba dandanawa suka yi suka ji wuya ba , ba zasu dawo hayacinsu ba, bana yi mata mugun fata , ama in har ba shi ya koya mata hankali ba , babu wnada zata saurara , babu wanda zata yiwa biyayya, ana iya samo mata wani mijinma ta je ta ringa yi masa rashin mu

tunci ta nuna auren dole aka yi mata, barni da su"

Mama bata iya cewa komai ba, sai da baban ya dan nisa ya ce" Kuma zancen auren na Anmy ne, in sha Allah jibi za'a daura auren"

Da sauri Mama ta dube shi, zata yi magana amarya ta shigo ta dayar kofar

da salama ta sha uban ado sai kanshi take yi ta karaso inda suke ta zauna tana wani iya yin nan ta ce" Elhaji Barka da safiya, yaya sauƙin jikin?"

Mama ta dauke kanta daga kanta tana duban baba ta ce" jibi jibin nan fa? ya da sauri haka ? na zata za'a

bari har a je baban hutu babansu?"

Aba ya girgiza kai yana mikewa ya ce " A'a gaskiya, in sha Allah jibin dai za'a daura mata auren, ki shirya kawai ki sanar da du wanda ya dace kin ji gimbiya? bari in zo, zan je in ga malan a sa a fara saukar Alkur'ani

a tarbi abin da addu'a saboda duk wani makiyi Allah ya rufe idannuwansa ya sa sai an gama komai hankalinsa zai dawo kanmu a lokacin kuwa daidai nake da kowa alkur'an a kan Anmy babu abinda ba zan ba!"

Yana fada yana tafiya ne, ya bar Mama sake da baki

Ajiyar zuciya ta sauke ta dauki wayarta ta zauna ta shiga saka numbar Hajiar Larabawa ta aika kiran ,sai dai tana ringin bata daga ba sai kawai ta yi kiran kanwarta ta sanar mata abinda yake faruwa, Mama karata tace yanzu kuwa zata shiga ta sanarwa Haj

iar kuma gatanan zuwa dan su fara shiri su san abinda zasu yi na tarbar baki

Tana ajiye wayar jikinta sanyi kalau ta dubi amarya dake zaune tana kallonta

Mikewa ta yi, saboda tunda ta dawo babu abinda ya shiga tsakaninsu koda na gaisuwa ne,

Ta ju

ya zata tafi amarya ta ja wani tsinanen tsakin da ya sa Mama dakatawa ta juyo tana kallonta da mamaki

Lalle in ba aure mai sakawa la hadu da kowace shara har ta mayar da kanta daidai da kai, me zai hadata koda maganar fatar baki ne da wannan yarinyar? a

ma gayanan dalilin sunna auren miji guda sai ta ringa kirta mata rashin mutunci tana kallonta

Kai ta girgiza ta sake yin gana zata tafi, amarya ta mike ta ce" Dan Allah idan dare ya yi haki na barinki ki iya rintsa ido?"

Mama ta sake dakatawa ta juy

o da matsanancin mamaki ta zuba mata ido

Amarya ta rintse idannuwanta sannan ta bude ta ce" Kwana daya kacal, ko in ce wuni daya jal kika je kika yi a gidanku ama shine aka sake kulo min wata masifar da ta fi ta da, me yasa bakya tsoron Allah ne? me yas

a kike so karfi da yaji sai mijina ya sake Ni ne? tashi tsayenki ya sa ba ruwansa da Ni, ba ruwansa da lamurana a yanzu an kai wajen da ko magana nake yi baya dubanna sai ke kadai, ko menene ke kadai ce mutun, ke kadai kike da daraja a idannuwansa, sai ki

je ki godewa bokayenki ki kuma kara musu kudi saboda gaskiya sunna yi miki aiki, ama ki sani walahi sai na karya, ko me kike takama da shi sai na karya shi, nima sai mijina ya dube Ni, kuma duka kaf abinda kike hadasa min kema sai na hadasa maki, zaki gani

in dadi ne!"

Har ta zo zata gegi mama ta wuce, Maman ta saka hannunta ta janyota gefe sannan ta dubeta ido cikin ido ta ce" Kina ji? ki ringa kiyaye shiga sabgata, saboda abubuwan dake kaina yawa ne da su, kuma dukkan abinda ya zamo na bashi mahinmanci

ina yi masa duba na kirki ne, ki je cen ki karata da mijinki, wannan ba hurumina bane, sannan ki kula ba kowa ne yake yin abinda kike yi ba, harkar boka da malan ke kika sansu ba Ni ba!"

Daga haka mama ta saki hannun nata da karfi ta juya ta yi tafiyar

ta, dan wallahi karya matan Elhaji suke ta ci kashinsa ta ci nasu, karya suke, banza dan ita ta saba bin bokayenta an gaya mata kowama haka yake kowa bashi da aikin yi kuma baya tsoron Allah ne?

Amarya ta ringa murza hannunta da mama ta rike da karfi zu

ciyarta na kunna, ita gaba daya abinda ya fi dagula mata lisafi irin yadda kamar rikicin da suke yi da Aba ya yi sanyi, kamar maganar daurin auren nan yana nan ama kuma babu wanda ya san da wa sai ita sai shi, domin tun a jiya da ta zo inda yake yace mata

ta tafi kawai shi zata bari a asibiti ta yi tafiyarta, ba damuwa dama ya san ita matar in ta yi dadi ne, yama gode da ta sa matar shan wahala zuwa inda yake , ama ta bashi waje bashi da bukatar ganninta idan ya huce sa zauna, da wannan haushin ta dawo daki

nta ta yi kwonciyarta, kuma yau tunda safe ta yi kiran Malaminta wanda ke yi mata aiki ka'in da na'in a kan a karya asirin mama, dan ya tabbatar mata Mama bakin asiri ne take yi a kan Aba da ya'yansa da dukiyarsa, ita kam matar nan so take yi ta gagareta d

u yadda take tunanin zata iya kwatar gidan Elhaji da ragamarsa matar nan so take yi ta fi karfin ta, ama ba komai sai dai su kashe junna ba tashi tsaye bane? zata gani gannin idannuwanta!

Mama kuwa tana zuwa bangarensu ta samu Lubna ta gama yi mata aik

ace aikacen da ta sa su yi ita da Khadija

Tana nufar ciki ta ce" Ina khadijar ne kike aiki ke kadai? idan kun gama ku yi wanka ku ci abinci , ina sauran suke ne, ina zuwa"

Inda inda Lubna ta shiga yi dan kuwa sunna cikin aikin khadijar ta dauko hij

abinta tace mata bari ta leka kofar gida ta dawo kafin Mama ta fito, gayanan har ta gama aikace aikacen gidan bata dawo ba

Jim kadan maman ta fito da waya a kunnenta, sai ta ga Lubna tana zurma hijab cikin gaggawa

Dakatawa ta yi tana kallonta har t

a zurma ta juya zata fita

A nutse ta ce" Ina zaki je ke kuwa?"

A zabure ta juyo tana zarro ido, sai kuma ta shiga kame kame na marar gaskiya

Mama ta dakatar da kiran da take yi kai tsaye tana dubanta da kyau ta ce" Ke zo nan"

Lubna ta juyo ta z

o hankalinta na karra tashi

Mama ta ce" Na ce ina zaki je?"

Lubna ta nuna waje ta ce" Mama dama cingan nace Anmy ta siyo, shine bata dawo ba zan bi sahu"

Mama ta zarro ido ta ce" Anmy? Anmy? ta fita? innalilahi yayan nan sai kun ja min abinda ya f

i karfina? ta je ina? zaki fada min gaskiya ko sai na wanka maki mari?"

Lubna da sauri ta ce" Walahi Mama ban san ina ta leka ba, cewa ta yi yanzu yanzu zata dawo fa"

Mama ta dantse harshe ta nufi ciki ta shiga neman katon hijab dinta tana kuma l

alubar numbar inna tsohuwa

Ringin daya inna ta daga tana fadin" Mata ku saurara in ansa kira, hello asalamu alaikum wa rahamatulah"

Mama ta amsa a tausashe ta ce" Inna, Anmy na gidanki kuwa?"

Inna ta yi murmushi ta ce" Wai y'ar albarka? ai bata

fashin majalisa sai in ta zama dole, gatanan tana rabon lemu wa matan kirki mata masu rike miji da karfin ikon Allah"

Mama ta sake dantse lebenta a tausashe ta ce" To shikenan, inna ki ce mata babansu na nemanta dan Allah, ki ce mata ta san ai yana gid

a bai fita ba ta fita, ta gaggauta dawowa inna"

Inna ta ce" To shikenan bari in sanar mata Hajia, Ni dinma zan shigo in an jima saboda wata magana da ta zo ta sanar min ita tana murnar wai ko an fasa, Ni kuwa haka kawai nake ji a raina inama an yi, Duda

bamu san mijin ba ama ina da yakinin Elhaji ba zai yiwa y'ar nan mugun zabe ba"

Mama ta gyada kai tana sake dantse lebenta, dan walahi ita kadai ta san irin dukan da zata yiwa Anmy yau a gidan nan, wato har ta je ta yi yamadidi da sirin gidan nan ko? i

ta dai in dai ta fice to a sameta a gidan inna, tunda aka kawo karin gayyatar zaman majalisar gidan inna ita aka kawowa , bata amsa ba dan abubuwan dake gabanta sun sha kanta, kai inama take da lokacin zuwa koyar dabarun zaman gidan miji? ai ita zama in ya

yiwu a yi, in ba zai yiwu ba a watse babu abinda aya dameta, ama cikin ikon Allah Anmy ta amshi katin, kuma take zuwa, karshe ma ko sisinta ba'a amsa, har nemanta matan anguwar nan suke yi in ta kwana biyu bata je ba....., lalle yau zata zauna da Anmy ta

fada mata abinda ake koya mata, kuma yau jikin Anmy sai ya fada mata

Bulala Mama ta samu ta kirki ta rike a hannunta ta zauna a falo tana jira

Ba'a jima ba Baba ya shigo da masu gyaran gida, suka duba du inda ya dace a kawo gyara komai kankantarsa

suka tafi da nufin dawowa su fara aiki a yau yau

Baba ya raka su kennan ya dawo sai dariya yake yi da farin ciki ya dubi Mama a zaune a falon da amarya domin tunda ya zo ta fito ya ce" In sha Allah bana da ku za'a sake yin haji, na baku kyautar kujerar

Makka Allah ya nuna mana"

Buda amarya ta saka, Mama ma ta saki murmushi tana furta" Masha Allah, Allah ya saka da alkhairi ya idasa nufi...."

Daidai nan Khadija ta shigo tana rabe rabe saboda tun dazu ta shigo jin kamar Yah baba a falon nasu ya hann

ata shigowa, karshema sai ta tarki wanke wanke da goge gogen bango, ta cire hijabin ta daura a kugunta tana aikinta ka'in da na'in

Tana shigowa falo ta wani sune kai ta yi dan murmushi ta ce" Barka da hutawa ina baya ina wanke wanke ne ai" kamar wace a

ka tambayeta

Aba ya saki wani murmushi mai dadi ya ce" Allah ya miki albarka uwata, sannu da aiki ama ki daina daga yau kin ji? Allah ya karra maki albarka uwata!"

Daga Mama har amarya sai da suka kalle shi kafin mama ta cire kai

Sumui sumui ta

so shigewa shegen mamaki na kamata na lamarin addu'ar nan da aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login