Showing 147001 words to 150000 words out of 200647 words
mata video call
Aunty shareefat ta daga tana fita daga cikin mutane , ganninsu zaune ya sakata sakin murmushi ta ce " Big Son???"
A tausashe ya ce" Maman AL'WALID, kun fito ne?"
Aunty shareefat ta girgiza kai tace" Walahi sun ki yarda mu juyo wai kakan kurma yace
sai ya zo, yana hanya shi din dai muke jira, ba zan iya rigimar kakan kurma ba idan muka taho din a kaina zata kare"
Ya dan dage girarsa yana son tambayar to me zai musu idan ya zo din? sai ya share kawai a hankali yace" wai kuka take yi tana son ganni
n Mama da sisters dinta...., ko in kawota ne?"
Aunty shareefat ta dan zarro ido a hankali ta ce" Yanzu? a'a bari in kai wayar ki gansu ta vidio call Daughter kin ji? in yaso daga baya sai ki zo kin ji?"
Khadeeja da ta dan raba kusancinta da shi bata
san lokacin da ta matso tana murmushi hadi da gyada kai ba, shi kuwa sai kawai yake kallon wannan kasan idannuwan nata yana sake mamakin dimple a kasan ido jama'a?
Zuwa ta yi ta shige ta karasa har inda su Mama suke ta yi salama sannan ta shiga a lokaci
n Mama na tufke gashin Lubna, lubnar na fadin" Mama Allah zan je kitson goben in sha Allah zan je"
Mama ta ce" Karma ki je Lubna, da hannayena ai sai in maki a gida tunda ba zaki je ki yi mai kyau ba"
Dariya Aunty shareefat ta yi bayan ta shigo ta ce
" Mama da ya'yanta kin boye a nan Mama, kai na jima rabona da in ga mutun mai kunya irin taki masha ALLAH, kin ga ga Hajia karama fa a waya tana rigimar Mamanta"
Mama ta dan zabura domin kawai sai gannin mutun biyu ta yi a zaune sunna kallonta, da sauri
ta duke tana rufe fuska ta ce" Innalilahi"
Ai kuwa Khadeeja dariya take har tana kwonci a saman jikinsa ta nuna masa ta ce" Walahi an shamaci Mama, Lubibin mama kitson karfi da yaji ake maki? ina karime an mata, je ina yar rainin wayon nan take, wai ya
aka yi na ga kwana
Ι
aya tak da bana nan Mama ta karra fari?"
Yan matan kuwa ina, ihu da kokowa suka karbe wayar tuni suka yi waje da gudu, aunty shareefat kuwa dariya take har tana kama ciki ta ce" Mama dago ai sun tafi da wayar "
Mama ta dago tana
dafe haba ta ce" kai auntyunsu fisabililahi ya zaku biyewa yarinyar nan?, na zata ita kadai ce ai"
Aunty shareefat ta ce" A'a Mama, tare take da shi ai , kai walahi Mama kin ban dariya"
Ita dai Mama ta yi murmushi zuciyarta na sakuwa da tunanin a wan
i hali Khadeeja take? dan kuwa ita du gani take yi Khadeeja na cikin matsi da takura saboda har yanzu kallon jaririyarta take yi mata
Yan matan mama tunda suka fuskanci wanda ke kusa da ita sai suka ringa gaishe shi da girmamawa sannan sai su yi shiru,
sun kasa ci gaba da ihun da suka fara da murnar gannin junna, hakan ya saka shi murmushi ya dan mike ya bacewa gaban camerar, sai dai a yanzun sai ita ta kasa motsin kirki domin a kujerar dake facing din Tata ya zauna ya zuba mata ido
Lubna na murmushi
ta ce" Innalilahi su iyani a gidan miji, ke hijabin meye wannan kika maka kamar zaki je fatawa, iyeah dage mu ga kwaliyar mana? su Anmy an samu duniya ko tunamu bakya yi ko? dazu da muka cewa Mama muna son zuwa wajenki tace mu je mu fadawa Aba, ke dai mun
zata ya saku ne kwana biyu da yake cikin haba haba na dariya, Karima tace da shi Aba muna son zuwa gidan ANMY, wa bilahilazi da ya makota sai da Mama ta wuni tana diga mata maganin ciwon kunne......"
Ai kuwa suka bushe da dariya har Karimar saboda dazu n
e fa rabon a yi, ya dawo gida yana fadin a tashi a shiga shirye shiryen tarbar baki, ya sako su Mama a gaba yayi kiran su Mama Fateema ya basu kudi masu yawa yace maza a je a siyo zabi a zo a soye, jus kuwa dama na kwali aka jibge, yana ta haba haba din na
n ne suka je zungui zungui suka yi tambayar nan, ai ita da ta yi tambayar da ya makota da su din da suka bale a guje sai wajen babarsu, ya bi su cen din ya dudura ashar dinsa son ransa tana tsaye tana kallon sa, har cewa yake yi mutun ya jawa ya'yansa kun
ne ko ya'yan kuka su janyowa uwarsu jifa , shi ai yanzu zai saka ido sosai kar a je a rikita masa y'a a gidan mijinta
Du yadda Khadeeja ta so dane dariyarta sai da ta gaza, ta saka dariyar tana rufe bakinta, hakan ya saka shi zarro ido yana sauraron na
wayar dake bada dukan da dayarsu ta sha abin mamaki sunna sheka dariya
Kasa jurewa yayi ya amshi wayar ya kalle su, ai kuwa da sauri Lubna ta mikawa Karima, Karima ta sakarwa ameerah, ameerah ta mikawa ummi sunna sunne kai, da sauri ummi ta kife wayar t
ana zarro ido kasa kasa ta ce" Mun lalace ashe yana nan?"
Ya katse kiran ya karasa inda take ya zauna yana murmushi ya ce" Ikon Allah, ya zaku ringa yi maka dariya?"
Khadeeja ta dago tana kokarin hanna kanta dariyar ama ina, tana nuna masa ta ce" Ka
kuwa san yadda Aba ke maka? da baiban hannu yake yi, idan ya kauda maka hannun nan ko waye kai sai ka hantsila, ga KARIMA da tsoron duka, ko yaya aka yi ta yarda suka sakata a gaba wajen wannan jihadin????
π€£π€£
" ta idashe tana yin wata dariyar har tana dant
se lebenta
A hankali yake dauke dubansa a kanta, sai kuma ya maido, dariyarta na saka shi a cikin wani yannayi na shaukin dake son fin karfinsa
A hankali ya kama hannunta guda ya matsota jikinsa sosai, lokaci daya dariyar Tata ta dauke ta kalli fusk
arsa ta bude baki murya a dan hargitse ta ce" Au, dama nace me za'a dafa ne?, abinda zaka ci yau. da d.............."
Hade sauran maganar ta yi sakamakon bakon al'amarin da ya ziyarci lebunanta wanda bata ta
Ι
a kawowa ranta shi ba, lokaci daya kirjinta
ba wani irin bugawa sannan ta so janyewa
A hankali ya saka dayan hannunsa ya sake hade jikinta da nasa ba tare da ya saki lebunnan nata ba, idannuwansa kuwa a lumshe suke tamkar ya samu wani gagarumin abin da yake Ζishirwa, hakan ya hanna masa gannin k
okarin sumewar da take yi ya ci gaba da shafarinsa har sai da kiran sallar isha'i ya shige kunnayensa sannan ya dakatar da abinda yake yi a hankali idannuwansa lumshe kirjinsa na bugawa da sauri da sauri
Idannuwan nasa ya bude ya sauke dubansa a kan fus
karta dake duke kamar zata nutse, jikinta kuwa rawa yake yi kamar an jona mata chkng
Murmushi ya dan sauke, a nutse ya mike daga saman kujerar dan kar ya rasa sallah domin ya san da sai ya sake dauro alwallah, dan haka ya dan duko inda kanta ke kasa a
hankali ya ce" Kar ki shiga kicin plz......., nd abinda zan ci a yau......ai yana tare da ke"
( Innalilahi nan kwate ce ta rubuta
πππππΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
)
Kai baka san baba Ya'u ba ko? kaikaikai han, to ai
hikenan ba zamu ce maka komai ba ka yarda dai ka aikata, ka yarda!
βΉ
οΈ
βΉ
οΈ
βΉ
οΈ
ππππ
41
07/12/2024, 15:25 - samiraharounayacouba: Ido ta zarro ta sake sunne kai har sai da ta ji karar rufe kofar ta zabura a tsorace ta yi tsuru tsuru sai kuma ta ringa furt
a " Innalilahi na shiga uku, wayo me kennan? na Bani me yake nufi? wayo Allahna "
Tana tsugunen nan gaba daya jikinta na rawa rawar nan har aka tada sallar isha'i sannan ta mike kamar an zare mata laka ta nufi bayi saboda yin wanda da dauro wata alwalla
h , ba dan ta tabbatar hakan ya zame mata wajibi ba, a'a, ko daya, dan dai kawai a cire shaku ne!
A gidan Aba kuwa bai jima ba ya shigo gidan fuskar nan tasa tamkar gonar auduga ya karaso yana sake yin salama, matan na amsawa
Kaka B ce ta ce "Barka d
a isowa kakan kurma, sannu da karasowa"
Aba ya saki murmushi ya ce" Barka kadai Hajiar tsoho ya hakuri da tsohon cen? , ba fa kurma bace bb ce Hajia"
Aunty shareefat ta ce" Kai yaya yanzu baban naka ne ake hakuri da shi? a'a ai babanmu shine damo Sar
kin hakuri"
Aba yayi dariya ya ce" Na rabaki, mutumen nan ina hakuri da shi sosai da sosai, yauwa y'ar albarka bari in ga gimbiya, ina take ne? Gimbiya"
Da sauri ya wuce ciki, aunty amarya dake dakinta tunda aka ringa shigowa da akwatunnan nan ta kas
a zama ta yi dakinta ta zauna ta ringa sauke ajiyar zuciya mai zafi ce ta yi wuf jin muryarsa ta fito tana tsane ruwan da ta yi saurin diba a kofi ta shafawa fuskarta ta dube shi tana fadin" Barka da zuwa Elhaji, ai zuwa na yi na yi sallar isha'i, gamu da
baki masha ALLAH "
Aba yayi murmushi kasa kasa ya ce" Wa bilahilazi duba ki ga abin arziki, kai shi fa mai kashin arziki haka ne, du tsiya sai ya nuna kansa sai abinsa ya bi shi, koda yake a jikin uwar ne, tunda nake ban taba baiwa mace sama da million
daya kudin kayan aure ba sai ita, ga Khadeejan larabawa ta bi layi, ina take ne? wai me kike a dakin ne Gimbiya?"
Ya karashe yana nufar dakin Mama ya kama ya bude ya shige
Amarya ta rintse idannuwanta wani abu na sake tokare mata kirji, har yanzu ta
kasa sabawa da halayar mijinsu, karya ne yayi magana daya a ta biyun bai yaba matar nan ba, karya ne yayi magana bai sako maganarta a ciki ba, ta rasa me ta fi ta, me ta fi sauran matansa, a da ta kaiwa mahaifiyarta kukan cin fuska ne, sai mahaifiyar Tata
ta sanar da ita cewa wasu mazan basu iya kara da danne harshensu wajen yabon matansu ba, hakan ke sakawa a yi ta samun sabani saboda wasu ba zasu taba iya amincewa da haka ba, itama da farko ta so yi masa bore a lokacin da take amarya ya ringa rakata yana
nuna mata ai ba abinda take tunani bane wace ma wata gimbiya? sannu a hankali ya daina wannan din yake fitowa kiri kiri yace yau fa za'a yabi gwani, dan bakin ciki ya rintse ido nai. shi yasa take cewa bokan Usaina bashi da imani da tausayi ko kadan, ya k
washe komai ya dora a kan Usaina kadai, kuma dan balaki an kasa karya mata alkadarinsu, har sai tana tunanin an ci riba sun fara dambatuwa kwana biyu sai ta ga sun daidaita!
A hankali ta karasa bakin kofar zata saurara aka bude kofar su Lubna suka fito
da dan gudu gudu hakan ya sa suka gwaru da amarya da ta duko kunnenta zata yi sauraro
Aba dake tsaye ya gama cewa wai uban me suke yi sun zo sun likun mata basu san halin da take ciki bane ko bakin ciki za'a masa Allah ya dube shi ne shi bai gane ba, y
a nuna musu kofa yace kafin ya irga uku kar ya ga kafar daya a dakin , ya sa suka rukuto a guje suka bude suka gwaru da amarya wace Ζarara suka fara gannin irin yadda ta duko kunnenta da kuma mikewar da ta yi a tsorace
Hannaye Aba ya tafa yana zarro ido
ya ce" Lah munafuka, innalilahi wa inna ilaihi raj'une munafuka, labe kika koya? yaushe kika fara labe? innalilahi wa inna ilaihi raj'une dama labe mana kike yi? la ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi Sallallahu alaihi Wa Salam, ke hala har a bangarena id
an aikin gimbiya ne leke kike mana? kardai aje irinku ne ke daukan vidion abokanan zamansu dan su yada su kashe musu aure? ke ko dai gimbiyar kike so ne Ni wala haula wala kuwata ila bilah yau na shiga uku"
Da sauri Mama dube shi , a tsorace ta kalli in
da yan matan suke ta ga tuni suka karrawa bujensu iska saboda ita rayuwa lalabata ake yi, bale da aka fito maka a mutun aka nuna maka hanyar da zaka bi ka tsira da Mutuncinka idan ka tsaya aka motsa maka kwakwaluwa ai ka gama janyowa kanka tsiya
Wata i
rin ajiyar zuciya ta sauke ta kai zaune tana fashewa da kuka tana fadin " walahi sai ya lalata min tarbiyyar ya'ya da mugwayen kalaman bakinsa , wayo Allahna wayo na shiga uku"
Shiru yayi yana kallonta kasa kasa ya ce" Kukan gaske ne ko na wasa?"
Mam
a ta dube shi hawaye na zubowa ta ce" Kukan wasa ne, nace na wasa ne baban Ishaq, yanzu ba zaka rufawa kanka asiri ka rufa min ba mu hadu mu tatala yan yaran nan har Allah ya rabamu da su lafiya? shine kake budar baki kana inkayi da kalamai ire iren Wadinn
an a gaban yaran nan?, yaya kake so ne gobe idan ka ji sun fada suma? yanzu fa mutun ake kiwo ba daba ba , haba dan Allah, ke kuwa....."
Ta nuno amarya da ta yi tsuru tsuru ta ce" Ke ba zaki yiwa kanki wa'azi bane mu zauna lafiya? ke ba ruwanki da hakin
mutun, haka kuma ba ruwanki da na Allah? haba dan Allah, kin iya yin abinda zai zo kulun ya hautsina mu ya hadasa mana tashin hankali a cikin gidan nan ya hade daga Ni har ke ya yi fata fata da mu kuma ki dora min da cewa nice ke janyo maki bakya tsoron A
llah ne? ki sani duniyar nan ba matabata bace, ki aikata alkhairi ma lalube ne bale ki dage kan lalle sai kin kuntatta min!"
Ta dakatar saboda ji da take kamar zata kifu, ta
Ι
ora da fadin " Me zaki labe ki ji? me kike son ji? me yasa zaka barta a kofa k
a rufo kofa ne? du laifinka ne, kai ke janyo min magana, du matsalata kai ne, kai ne ke sakani a damuwa, kai ne ke janyo min ana zagina, Ka zage ni, matarka ta zage ni, yan cikin gari su zage ni, du dan ina aurenka ? na gaji......na gaji.....na gaji.......
.." Ta karashe tana dukewa hadi da fashewa da wani kukan
A hankali Mama Fateema ta shigo bayan ta janyo hannun amarya ta kara kofar dakin ta rufe, ta nufi inda Mama ke duken nan ta duka ta kama hannunta a hankali ta ce" Aunty, haba Aunty, dan Allah dago
ki dubeni, innalilahi wa inna ilaihi raj'une me yayi zafi ne har haka? me yake faruwa ne?"
Kamar yarinya karama Mama ta fada jikin Mama Fateema bata bata amsa ba tana kukanta
A hankali Mama Fateema ta kalli Elhaji da jikinsa ya mutu murus kamar an y
i masa tsinanen duka, a sanyaye sosai ta ce" Baban ANMY, a taimaka a je a duba bakin nan wasu har sun tafi fa, Hajia Binta da aunty shareefat din ne kawai ke nan ,, kar su gaji da zama"
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya dubi takardar check din da ya
shigo da ita, muryarsa kasa kasa sosai ya ce" Dama zuwa na yi in tambayeta nawa ya dace a dora matsayin tukwuicin masu kawo kaya?, ban san me ya faru kafin in shigo ba har ya tunzura min hankalinta haka....., Ki yi hakuri Gimbiya " Ya karashe yana dubanta
da kyau, wanda hakan ya karya mata zuciya ainun har ta zuba masa ido a boye tana ji kamar ta mike ta bashi hakuri, sai dai ta ki mikewar , sai Muryar Mama Fateema da ta ce" Ka yi hakuri yaya, in sha Allah ko menene zai wuce, ka yi hakuri dan Allah, a saka
abinda Allah Ya hore, Allah ya karra budi"
Kai ya gyada ya juya zai fita ya ga amarya a tsaye tana jijiga
Wani haushinta ya kama masa wuya ya daga hannu zai kwadeta ta yi kusan su Mama da gudu
Rai bace ya nunata da yatsa ya ce" Ke kam wai uban me
kike min a gidan nan banda hada husuma? na rasa ya aka yi kike nan har yanzu ko dai zuwa kika yi kika min asirin duk rintsi kar na sau ki?, Ni zaki hada da matata ko? Ni zaki yiwa labe ki hadani rigima da Gimbiya bayan ba Laifina bane?, du masu yiwa gimbi
ya karyar tana min asiri Allah tsine musu albarka su ji duniya uban kowa ya huta, to idanma asirin take min sai me? ta je ta yi na yafe mata duniya da kiyama, yo a halin nan nawa idan ya zamo du duniya bani da wanda ke taroni ai dan wuta konane zan zama, k
e kam tabas yau ba zaki kwana a gidan nan ba, kawai ki je gidanku na....."
"Kin gani ko? walahi idan ka saki matar nan nima na saku" Mama ta fada da karfi tana mikewa tsaye
Da sauri ya saba babar rigarsa ya juya bayan ya harareta ya ce" Aikin banza
aikin wofi, wai shishiginma ka rasa wa zaka yiwa sai kishiyar dake sonka da tsiya, sai ki bitan in gani, ke bari ki ji, cikin nan dake saka ki wulakantani