Showing 24001 words to 27000 words out of 200647 words

Chapter 9 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

7

tunanin, ki tashi ki je makarantar ki nuna taimaka maki na yi na dauko ki, walahi dan kawai ku sa a raina maku wayo ne zaku ringa irin haka, in ba wannan ba ina hadinki da

wata matar uba har ki ringa kuka irin wannan dan kawai ta ganki da

saurayinki?"

Jikinta bai daina bari ba, tana dubansa ta ce" Kana tunanin idan nace mata haka zata yarda da Ni? dan Allah kana tunanin zata yarda?"

Ya bude motarsa yana jan tsaki ya ciro kudin da suka yi zai bata wanda jiya da dare ta nuna masa tana

so, itama babu abinda zata yi da su mahaifiyarta ce ke so kuma ita tace ta tambayo mata a wajensa , ya miko mata ya tayar da motar ransa bace yayi tafiyarsa, dan shi abin ya mugun bata masa rai, meye kare balatana romansa? matar uba ai a ci uwar junna da i

ta ne kawai ko kowa yayi harkar gabansa, ama zata wani duka tana kukan nan kamar ranta zai fita dan kawai ta ganta a motarsa? mtsssssssss wannan babyn in ba dan sunnan babanta ba kai da ya watsa banza a bola shi baya son harkar yawa walahi

A lokacin da

ta shanyo kwana tana rabe rabe a lokacin aka buga karaurawar tashi wace ke ba kowa damar fitowa, tsari da tsaurin makarantar yayi daban da sauran makarantun garin, shi yasa ko sauka ba irin in ka ga dama zaka sauka bane,

Da sauri ta nufi inda direbansu

ke ajiye mota ta bude ta shige cen baya ta buya jikinta bai daina bari ba, gashi tana son kiran mamanta ta sanar mata sai dai ta san ko ta sanar mata babu wani abin da zata iya yi mata na ceto daga hannun babansu idan har ya ji maganar nan, wannan din dai

da suke yiwa kallon makiyiya itace zata iya karbarta daga hannunsa kanta tsaye sai dai dukkan ya sauka a kanta, gaba daya komai na duniyar ya tsaya mata, hankalinta ya gama tashi fiye da tunanin bawa

Ba'a dauki lokaci ba yan uwanta suka zo du suka shis

hige, sai dai du wanda ya ganta a ciki sai yayi mamakin ganninta a baya , a bayanma cen boye, kuma kanta a cikin cinyarta tana kuka, duba da ita kulun sai sun yi jiranta in aka tashi kuma kiri kiri take shigewa gaba ta zauna a yi ta balaki tace walahi ta f

i karfin shiga bayan mota, tun sunna biye mata su daki junna a hanya sai baba direba ya tsaya ya raba har suka bar mata gaban cen ta karata , sai gashi yau ta shige baya kuma tana kuka

Khadija ta kalleta ya fi sau uku tana jin kukanta na shiga zuciyarta

har suka karaso gida suka sauka bayan ya shige da motar har cikin gidan

Direct dakinta ta kufa , khadija na biye da ita har suka shige , a tausashe ta ce" Hala a wani exam kika fadi shi yasa kike kuka? tunda ana ga ai ba dukanmu ake yi a makaranta ba ,

ko baki da lafiya ne?"

Ta dago zata bata amsa Lubna ta shigo itama tana dubansu ta ce" Wai kukan me kike yiwa mutane? ko laifi kika yi ne?, walahi idan laifin da Aba zai yi duka kika janyo mana ba zan taba yafe maki ba Karima, haka kawai sai ku ringa j

anyo mana fushin Aba kulun yana saukewa a kanmu, bakwa gannin zuwa yanzu mun kai mizanin da bulala ya dace ace ta daina hawa fatar jikinmu ne?"

Da tarin takaicin abinda ta janyowa kanta ta dago a zafafe ta ce" Sai ki fadawa wace ta kware wajen janyo man

a dukan ai ba Ni ba, Ni har duka nake janyo mana? sau nawa na taba janyo mana dukan a rayuwa? ama ita ana rufe

sati ne bata je ta janyo mana ba? Allah ya isana ko waye zai hadani da dukan yau walahi !"

Lubna ta tabe baki tana fadin" Ni na san ba banza b

a kike kuka, kuma na san ba dan makaranta kike yinsa ba, mu dai zamu barki da Allah idan kika janyo mana wata masifar, ke Anmy ki je ki duba hardarki kin san yau da yama muna da harda dan malan yace satin gaba in dai dayarmu bata kawo hardar gaba daya ba

tabas za'a yi bikin sauka banda ita, ki barta ta ci kanta tunda ita bata da mutunci"

Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta yi waje tana yan dube dubenta da tunanin yau ko ina Mama ta tsaya? duba da lokacin sauka yayi daga asibiti, dan Yawancin lokuta a gida

suke samunta in dai wajen aiki ta tafi, sai idan ta biya wani uzurin ko ta je gidan Hajiar Larabawa

Ko da mama ta zo bata nemi dayansu ba, lokacin makarantar islamiyya na yi suka tafi su Dukansu, kusan Karima ta rigayi kowa tafiya, gaba daya jininta a

akaifa yake , hankalinta ba a jikinta yake ba, du ta firgice ta fige, ko hardar da aka zo karba kasa bayar da Tata ta yi, malan yayi ta fada saboda an ware su sun kai su talatin da uku zasu yi hardar sauka a ajin manya, dama sun yi saukar to malan baba ba

ya yarda sai an yi harda, hardar ce suke ha

ɗ

awa kuma sun kusa gamawa domin a bakara suke daga kasa ne suke yin sama, kuma yace sai sun kawo kowace tasss sannan za'a gabatar da saukar, shi yasa suka maida hankali sosai, ama ita yau tana cikin mutun bakwai d

a malan yace in sha Allah satin nan da zai zo idan basu zo masa da hardar da aka yi yau ba da kuma karashen wace aka biya yau ba ba zasu shiga cikin rukunin masu saukar ba, da wannan suka sauko daga islamiyya kowa ya kama gabansa

Khadija bata nufi gida

ba, sai ta dauki hanyar gidan umma tsohuwa dan a irgenta tana iya zuwa a tsaitsaye ta gaishe da ummar sannan ta je gida dan haka ta nufi gidan hankali kwonce

A lokacin da ta dauki Layiin da zai sadata da gidan ne idannuwanta suka yi mata gannin da ta ji

ma bata ji tashin hankali da bacin rai irinsa ba

Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, nan take idannuwanta suka so rufewa sakamakon abinda ta gani din

Yaya ne fa, yaya Abdul karim ne fa, tsaye da sabira a kusa da runfar mai pampo sabirar na magana tana

murmushi shi kuwa yana tsaye hannunsa cikin aljihun wandonsa yana kallonta ko sauraronta? oho

Da sauri ya dago da kyau gannin wace ke kallonsa a tsaye, gabansa na faduwa shima, dan haka kawai ya ji mugun tsoron hakan ya tsirga masa

A hankali Khadija

ta ja ta tsaya, sannan ta juya ta shiga tafiya idannuwanta na son rufewa

Da sauri ya biyo bayanta yana kokarin dakatar da ita, sai dai irin duban da ta juyo ta yi masa ya saka shi tsayawa cak hankalinsa na son tashi sosai yana kallonta a tausashe ya ce

" Anmy, ina zaki je bamu yi magana ba?"

Khadija ta sake kallon fuskarsa da kallon da ita da kanta bata ta

ɓ

a Sannin zata iya kure fuskarsa da shi ba, daidai nan kuma sabira ta karaso yannayin fuskarta zai nuna maka itama tana cikin yannayi na bege ko na

me? Allah shi ya san abinda ke cikin nata zuciyar

Bata bashi amsa ba ta dauke kai ta nufi hanyar gida tana jefa kaffafuwanta a duk inda ta samu

Tana shigowa gidan ta yi kicibisss da Lubna dake kai kawo hankalinta du a tashe duba da magariba na gabato

wa kuma Khadija bata shigo ba, bayan du inda baba yake ya kusa shigowa gidan shima, dama ga wata banzar cen dake neman jaza musu balaki, ga kuma yar na saba din nan zata janyo musu budewar wasan, ita kuma yau gaba daya bata son duka har cen cikin zuciyarta

Hannunta ta damko, sunna shiga falo Khadija ta ja ta tsaya, sai kawai ta fashe da wani irin kuka tana dukewa nan hadi da dora hannu saman kai tana jin kamar zuciyarta ce zata balo ta fito daga bakinta

A rikice Lubna ta duka tana dago kanta lokaci d

aya ta cire mata hijabinta tana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ke kuma ke da uban wa kuma?"

A rikicen nan Khadija ta nuna kanta ta ce" Ni, Ni khadija Ni khadija kamar zan mutu nake ji, Ni kutun d'a namiji zai rikewa zuciya bayan irin abinda n

ake gani na kuma karantawa kaina karyar kato ya ga bayana? lah ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi Sallallahu alaihi Wa Salam"

Lubna ta idasa karbar salatin tana zabura hadi da zarro ido tana kallonta, a gigice ta ce" Zan ga Annabi in na yi hali na gari

, wulakanci namiji kuwa? ke Anmy ki rufawa kanki asiri ki barni in mutu maza su kaini ba mata ba, yanzu ke ina ke ina namijin bale har wulakancinsa ya nemi kashe ki? kukan da kike na uban menene ne Ni? ke Anmy so kike baba ya ji kukan da kike yi yayi shaha

da ya yanka yan kutumar buro'uba a laye? Allah na tuba, Allah na tuba da ka yo Ni a wannan ahali na tabbata akoy dalili"

" Lubna kin san me na gani? ra'ayne da ayne na ga Yaya Abdul karim da sabira y'ar pasalinmu a rabe jikin runfa sunna zance, Ni kam

in ban ji kamar zan mutu ba me zan ji?" Khadija ta katseta rana sake neman fashewa da kuka

Wannan shine abu in ya girmeka zai ka rasa tudun dafawa wai budurwa da jika, wannan balaki da me yayi kama? fisabililahi du gigitar rayuwa da khadija ke ciki bata

ji zata mutu ba sai wannan bakon abin da bai kai mizanin a duba ba? Lubna ta daga y'ar yatsarta bayan ta jijiga khadija zata janyo mata gima giman abin dake jiransu wa'inda suke iya sakawa zuciyarta daina bugawa ko ta dawo hayacinta ta daina kukan saurayi

n da balagar kirkima bata zauna masa ba suka ji Muryar mai gigita rayuwarsu , sai dai kamar da sakakiyar fuska bayan ya dan yi gyaran murya ya ce" Lubna, zalin autata kike ci a duke a nan ko menene auta ke kuka?"

A zabure suka mike su duka , suka gwara

kai , Lubna ta koma dabar ta yi zaman yan bori kafin ta sake tashi tana zarro ido ta bi layin gaisawar da Khadija ke yiwa babansu sannan suka yi tsuru tsuru sunna kallon kasa

Babansu ya sake bin su da kallo ya tabe baki ya ce" Du sai ta dau ja walahi ka

i jikin y'ar nan baya son wahala , Allah ya ci gaba da horewa babanki in ci gaba da biya miki ac kina sha kin ji uwata? , Anmy zo nan me ta maki ne zalinki ta ci? dubi du ta dau ja y'ar albarka"

Anmy din bata je din ba, haka kuma Lubna ta yi kiri kiri t

a rasa ihu zata yi ko kuka,, tana kallon ikon Allah har ya ga dama dan kansa yayi gaba ya nufi bangaren su Mama

yana shigewa ta ja hannunta suka yi ciki , sunna shiga ta rufo kasa kasa ta ce" Yau da ya ji kukan soyaya kike yi sai ya kasheki da duka ya

huta da takaicin ki, jibeki kamar zaki yi abin kirki ashe solofiyo ce? ki ji Ni da kyau ban lamunce maki yiwa wani kuka a duniyar nan bayan wanda mahaifinki ya saka ki ba, Khadija walahi walahi idan ina raye karya kike yi ki yiwa wani namijin kuka, kin ga

ba so ba ko uban menene zaki tashi da kaffafuwanki ki fuskanci ko waye a yi wace za'a yi, shi din zan same shi in masa sumul, shi har namiji ne da zai saka ki kuka?"

Da sauri khadija ta riko hannayenta ta ce" Aunty Lubna, kar ki yi haka, ki yi hakuri d

an Allah kin ji? kar ki wani yi masa magana ki barni da shi, Ni abin ne ya min ciwo kuma kin san ke kadai nake yiwa kuka sai mama ko? maman kuwa idan har na yi mata kuka ta ji dalilin kukan kin san na kade ko? ki yafe min in sha Allah ba zan kuma ba"

Lu

bna ta sauke ajiyar zuciya ta gyada kai da hannu ta mata alamun maza ta dauro alwallah lokacin sallar magariba ya gabato, sannan ta fita daga dakin

Tana fita Khadija ta zauna bakin gadonta tana turo baki kasa kasa tace" Ni abinda ya fi kona min rai banm

a san soyaya suke yi ba ko me, to dai zan sani gobe in sha Allah, lalle Abdul zaka san daidai nake da kai, dan ba zaka gigita min zuciya da soyayarka ba kuma ka nemi raina min wayo.....'

Sai kuma ta dan yi murmushi sakamakon tuna magangannun Karima was

u lokutan, takan ce" Burinta namiji sun gayu, namijin da ya san kansa ya iya soyaya, Burinta namiji mai kudi don duk tsiya ba zata iya auren talaka ba domin da talaka da mai kudin a cikinsu kaf akoy wa'inda basa tsoron Allah, idan Allah ya ha

ɗ

aka da mugun

ga talauci ga balaki ina zaka saka ranka? gwara dai mai kudin koda da masifa akoy ya'yan banki,"

Ta sha cewa" Ke yanzu wannan Abdul karim din dake wani tareki a hanyar makaranta har kin ga abin so a nan? sai gajartar tsiya ga shegen gwali shi ba kowa ba

ba dan kowa ba"

Idan ta fadi abin nan sunna kai ruwa rana sosai har su matse junna su daki hancin junna kafin su shigo gidan kowa na kumbura ama babu wanda zai ji ba'asin fadan, dan kallon da mama da baba ke musu ko sunnan namiji aka ambata wanda ba mu

harinmu su astagfari suke ja, basu san daidaikun mazan na tayawa kuma har sauraronsu suke yi dan dai abin ne irin na yarinta haka, nesa nesa a zabga da gudu haka, abin dai gayanan dai haka.

Murmushi kawai ta yi ta girgiza kai ta mike tana sake yaye hija

bin da ta zurma tunda ta ji Muryar babansu a kanta , ta nufi bayi a ranta tana ayana' Kowa da bikin zuciyarsa, Ni kuwa bana tunanin zan iya auren mai kudi koda kuwa idona a rufe yake, menene a cikin auren mi kudin banda wulakanci da fitintinu?, burina mai

dan abinda zai ciyar da Ni ya tufatar da Ni saisa saisa dan talaucinma bashi da dadi sam, sannan baban abinda nake yiwa kaina fata Allah ya rabani da mutun mai kyau, kun ga mai kyau? jarabtar duniya kennan, shi fa namiji mai kyau bashi da mutunci a wannan

karnin, ya kifaka matan gari su kifoka haka ne, mazan wannan karnin masu kyau du shige da yan daudu suke, ko yangar sun amshe sun gama, komai su ke yi, dan jan leben nan, dan laushin fatar nan, kai komai dai da mace zata gwadawa namiji ta birge yana da sh

i, sai dai ki yi kwaliya dan ki birge kanki ba dai dan ki birge namiji ba, to me kennan? uhum'

.......Wannan itace khadija, kadan daga cikin halayar khadija, mahaifiyarta ta kasa motsawa dan tsabar tausayinta, domin gani take yi khadijarta ba zata iya c

iyar da kanta Bama koda an dafa an bata idan bata kusa da ita, kwarai raunin khadijarta ke karra sanyayar da gabanta da duk wani motsinta, bata san khadijarta ginaniya, tsayayiyar mai tsarin kanta ce ba na wani ba, khadijarta a gine take kuma tana kallon

kowa a yadda ya fito mata da idon basira ne, sai dai mu ce lokaci kan toni yannayi.

Baba na shiga dakin mama ya sameta saman salaya kanta duke tana ta jan carbi

shigowarsa ya sa ta dago ta dube shi sannan ta masa alamun sasaucin fuska dan marab

artarsa

Sake duban yannayinta yayi, tabas akoy abinda ke damun zuciyarta, ta yiwu har yanzu rigimar auren ne? auren nan kuwa shi in ba dan kar ace bashi da mutunci ba sai yace ko ubanwa ya tsaya zai kawar da shi a yi, sai dai ba zai yi haka ba, dan yan

zu haka yau Elhaji ya tabatar masa ai ogan gobe zai shigo, shi yasa yake jin farin ciki kamar me a cikin zuciyarsa

A hankali ya mata alamun Barka sannan ya ce" Idan kin gama, ki je bangarena kin san ai girkinki ne yau ama baki aika min da abincin rana b

a gimbiya, ga sani ga take sani kin haye darduma sai musmus kike yi da baki bayan ki shaki kwalata bata ce maki komai, Allah ya yafe maki kurakurenki ya sa ki gane yin musu da Ni baban jafa'i ne a rayuwarki, na tafi"

Daga nan ya fice ya barta baki bude

tana kallon kofar kafin ta girgiza kai tana tunanin da wahala kuwa ta je din a yau, domin jira take yi a dan jima sawaye ya dauke ta zauna da Karima, dan walahi idan yarinyar nan ta yi wasa a yau sai jikinta ya gaya mata daga hannun da bai taba dukanta ba,

ita kadai ta san halin da take ciki tun bayanan da aka bata na ciwon da Karima ta yi a kwanakin nan da fashin makaranta da kuma abinda itama ta gani da idannuwanta, tabas Karima ta dauko hanyar da ba zata bile mata ba ta kowani fani, ama zata kwatanta mat

a waye babanta, mece rayuwar nan sannan ta bata shawara yadda zata gyara, idan har ta yarda ta ki sauraro

zata hadata da ubanta ya dauki matakin da ya dace dan ba zata sa ya tuhumeta da wasa da tarbiyyar y'arsa ba.

07/12/2024, 14:52 - samiraharounayacouba

:

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login