Showing 72001 words to 75000 words out of 200647 words

Chapter 25 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

42

mula je ba wajen Maiga muka je ba, kuma a cikin yan maular d'ana AL'WALID Ni na ga Maiga da IDONA!, ba zaki

taba Sannin daga maki kafa muke yi, ba zaki taba Sannin su waye ahalin gidan nan ba sai kin shigo, da takamar gidan mijin naki ne sai ya gagareki zama, daidai muke da ke, muna fatan zuwan naki muma!"

Mahaifiyarta ta dubeta a nutse ta ce" Me kike ci na b

aka na zuba khalisat?, ki yi shiru kawai..............ki yi shiru dan mu mun san waye shi, zata gane shayi ruwa ne tsohuwar mace"

Mufeeda ta yi murmushi tana sake dora kafa daya kan daya zata yi magana ya bude kofar madubin nan ya shigo

A nutse ya ka

raso wajen kafet din falon idannuwansa a kan Hajia zainab ya ce" Barka da warhaka kaka z"

kusan a tare suke gaisar da junna, Kalisat kuwa na gaishe shi

Ya dubi khalisat da murmushi ya ce" Maman AL'WALID me zan samu? da gani an kawon wani abin dadi ko

?"

Khalisat ta yi dariya tana sake gyara zamanta, dama akoy yannayin barkonci a tsakaninsu, yakan tsokane su lokaci zuwa lokaci, yakan shiga cikinsu idan ya zo ya same su a baban falon Hajia inna, yana jiran iyayensu kowace da sunnan kaka A, wato kaka A

mina, kaka z, wato kaka zainabu, sai kaka B wato kaka Binta, ƴaƴansu kuwa kowace yakan kirayeta da maman AL'WALID hade da sunnanta , yana daraja su, yana basu girman da ya dace, sai dai hakan baya hanna shi yin hukunci ko jan kunne da babar murya, idan wat

a ta yi laifi ba ruwansa da shi jika ne a cikin gidan yakan zauna da ita su fahimci junna, ko dan shine namiji baba? ko kuwa namu na Hausa ne wato mai shi a hannu shine mai girman daraja? shi dai yanada darajar nan a gidan su mai girman gaske, kuma idan ya

tsawatar ana yi masa biyaya, a yanzu haka budurwa hudu ce bata da aure a gidan, sauran kowace na dakinta, sai masu aiki da jikoki dake gidan, a haka ake tafe da rayuwa ana yinta yadda hali ya bada, a cikin jikokin ne Allah ya albarkacesu da maza, sunne ke

kama masa wasu abubuwan na gidan idan baya nan, domin baba dai yana nan ne, ama ya ajiye komai a yanzu bautar ubangijinsa kawai ke gabansa, sai yanke manyan hukunci ko tsawatarwa idan AL'WALID ya yanke wani hukuncin mai tsauri ya kuma kin yin hakuri.

Bayan ya zauna, Mufeeda da ta je kicin ta dawo dauke da jug ta ajiye ta zuba masa tana murmushi ta miko masa tana fadin" Bab, ka jima, ko abinci baka ci ba fa?, ya dace yanzu ka ci abinci kafin ka ci gaba da gannin wasu"

Jus din da ta miko masa kasa am

sa ya yi, ba dan komai ba sai dan irin yadda ta matse masa waje, uwa uba irin suturar dake jikin yarinyar.....bai san me yasa Mufeeda ke son wulakantar da kanta har haka ba, bai kuma san me yasa take yi masa kallon shashasha ba, domin shi ba mutun ne mai s

aurin shiga rayuwar mutun ba, ama kuma yana da tsantseni da kiyaye hakokin addininsa sosai da sosai

Yayi tunanin idan ya bi Mufeeda da ido zata cenza wasu abubuwan, sai dai ga dukkan alamu dole sai ya yi mata maganar, dan ba zai yiwu ba, matar aurensa ba

irin shigar nan ta dace da ita ba, ko kadan, haka kuma wannan yawon ba na matar aurensa bane!

Da yan yatsunsa kawai ya mata alamar ta ajiye, dan haka ta zauna rike da abin shan, Bata ajiye ba, tana jiran su gama rokon su tafi sai ya sha, dan ita bata ga

wani cenji a tare da shi ba, bata ga laifi a zama daf da shi ba, bata ga matsala a kawo masa jus da ta yi bata ga matsala a shigarta ba, uwa uba a tunaninta wata bukata ce ta kawo su Hajia zainabu wajensa, dan haka tana jira su gama su tafi, kuma walahi s

ai ta tarda Hajia zainabu da khalisat har daki yau ta musu rashin mutunci, ita khalisat zata zaga? zaginma da ubanta? ba laifi zata je itama ta zagi Tata uwar ta ji idan da dadi, zata tuna mata in ba son abin duniya ba uban me ya ha

ɗ

a Hajia zainabu aure da

Elhaji Hamza? tsoho da shi ama ta zo ta zauna, har ta haifi khalisat da shi ana cewa khalisat din auta? kai har ubanta fa ita sai ta zaga, zasu san da daidai da su zasu zauna, babu wanda bata gane munafurcinsa ba,, kaf dinsu, kuma daidai take da su.

ka

n Hajia zainabu a kasa bayan ta sauke ajiyar zuciya, cike da kisa irin Tata ta himar da take samun duk wani abinda take so a wajensa , wato ta hanyar sada kai da yi masa biyayar da shine ya dace ace yana haka a gabansu ta ce" ranka ya dade, damuwa ce mai

girman gaske take damun mu, kuma ina so in kawo kukana ne a gabanka kai tsaye saboda kakan yara ya ki ya dube mu bale ya tsayar da abin, .....haka kuma na fi ace a gabanta na fada idan har na yi mata karya sai ta musa....."

Da dan mamaki yake dubanta, s

ai dai bai ce komai ba, Mufeeda kuwa da ta ji wannan abin gabanta banda dokawa babu abinda yake yi, tashin hankali da tsoro na shigarta da tarin tunanin me kennan? yanzu idan har suka kawo kararta wani irin hukunci zai yanke mata? basu san halinsa bane da

zasu kawo kararta wajensa? ai baba suke fadawa duk abinda ta yi musu ba shi ba ko? innalilahi

Hajia zainabu ta

ɗ

ora da fadin" Ka ga, a duk lokacin da Mufeeda zata zo gidan nan, sai ta nemi wani abu na cin kashi ta yi mana, bata girmama kowa a gidan nan

, bata bamu daraja, ka yi hakuri ba na fada dan in hadaku bane, ina so ne ka sanar mata ta gane mun san cewa gidan nan naka ne, kuma mun san cewa ko bayan ran Elhaji in dai mu muna raye zaka rike mu, dan Allah ta bamu lafiya da mu da iyayenka mu yi zamanmu

lafiya, in abinci ta tarda wani na ci sai ta yi masa gori, in ac ta tarda a kunne sai ta kashe, in zance ta tardo yara na yi sai ta nuna a kan me za'a tsaya ana zancen a filin gidan mijin da zata aura, ka ganta nan a yanzu haka shigowar nan da na yi zagin

a ta yi wai na zo maula, shin mantawa take yi da karfin zumunci ne? ko maular na zo ai babu ruwanta tunda ba aljihunta zan taba ba ko....." Sai kawai ta shiga gargadar murya hadi da sakin hawaye tana jan hanci

Khalisat kuwa ta sada kai tana jin haushin

mufeedan nan sosai a ranta

Shi gaba daya abin daure masa kai yayi, ya dago ya kalli Mufeeda da ta yi tsuru tsuru ya fi a irga, yana sake kallon su Hajia murya na rawa Mufeeda ta ce" bab walahi ba haka bane, Ni ba.........."

"KARYA ZATA YI MAKI?" Ya

katseta da muryarsa a hankali, sai dai a mugun kausashen da ya saka idannuwanta cika da kwalah

kallon da ya kafeta da shi kuwa mai tsauri ne wanda ya sake daga mata hankali

dauke dubansa ya yi a kanta ya dubi Hajia

A hankali ya ce" Waye yace ma

ki nan gidana ne?, eh sunnana ke saman takarda, shima dan Elhaji ya ki cewar in maida sunansa........, ban ja da shi bane dan ban san akoy ire iren su Mufeeda a jikina ba"

Ya dan dakatar ransa na tafarfasa sosai, domin yayi mamaki matuka da abin nan, wa

i a haka bata fayyace masa wasu abubuwan ba, a haka idannuwansa basu ga wasu abubuwan ba, takaicinsa shine a kan gida take musu wannan abin? ikon Allah ita da ya dace ace itace tsani da zasu hau su tarda shi da dukkan bukatunsu? domin sarai ya san wani lok

acin sunna jin kunyar samunsa shi yasa ya kasance mai yawan kyauta da yawan kyautata musu koda ba sallah ba, ko wani bikin ba, domin kakanin nasa babu wace ba'a saka mata isasshen kudi du karshen wata a account dinta, su kuwa iyayen nasa yakan yi musu kyau

ta mai daraja a duk lokacin da hakan ya kama..........., in banda shirme irin naa Mufeeda tana tunanin zai yi aure ya zauna a gidan nan da iyalinsa ne? wannan gidan ya zamo familly Hause ne, duk wanda yake da bukatar zama kofa a bude take zai samu wajen za

ma da abinci da wuta da ruwa in dai yana raye kuma Allah ya ci gaba da buda masa, sai dai in dukiyarsa ta kare ne hakan zai ragu, ama ba wai ace da ransa da lafiyarsa ba matar da zai aura wace yake da burin ta zamo mace mai kyauta mai sadaka mai girmama wa

ni ma ba nasa ba, itace ke aikata haka? subahanallah.........

A tausashe ya dora da fadin" Ama daga yau, in sha Allah zan sake zaunawa da shi in kwatanta masa cewar gidan nan naku ne, kunna da iko da shi, ba wai ku ba hajia ko wani yake da bukatar taima

ko a nan ya zo, gaba dayanmu mutuwa zamu yi mu barshi a duniya......."

Ya sake ajiye maganar da Muryar mai sauki, ya dora da fadin" Ki yi hakuri, in sha Allah babu wanda zai sake zagin ku da fuskata"

Farin ciki ya mamaye zuciyarta, daga ita har khali

sat, domin abin nan yana daga musu hankali, idan akace yana gari kowa baya sakin jiki yayi abinda ya ga dama dan sun san tana kusa da gidan, idan ta shigo ta ga wani abu tsaf zata wankeka a gaban ko waye, kuma Elhaji Hamza yace su kyaleta wata rana sai lab

ari

Su dinma hakuri suka ringa bashi sannan suka mike suka tafi bayan sun yi salama

Shiru wajen ya dauka bayan tafiyarsu na wasu yan mintuna kafin ya mike ya juya ya nufi hanyar coridor din dakinsa

Da sauri ta mike ta bi bayansa muryarta na rawa,

tuni hawaye sun bale mata ta ce" Ama, ai ta kamata ace ka tambayi Ni me suke yi min ko? bai dace ace ka goyi bayansu daga fada maka magana ka yarda ba ko?"

Dakatawa yayi, domin ba zai so ta bi shi dakinsa na barci ba, uwa uba ba zai so wani ya ganta a

wajen dakinsa da irin wannan shiga Tata ba, Duda ya san abinda suke fada kasa kasa , ya kyale kowa ne dan babu wanda ya halice shi bale ya ji tsoron sa

A hankali tana dubansa ta ce" Dan Allah ka yi hakuri kar ka dauki fushin nan naka da Ni, ka ga yau f

a kace zaka same Ni a cen gidan , baka je ba, kuma na zo zamu yi fada? Ni bana so mu yi fada, ka yi hakuri su suke jana nima na rama"

A kausashe ya ce" Mufeeda! ki kama kanki, ki bani space in gane Wacece ke, domin a yanzu ya zama dole in sake duba wac

ece ke!"

Yana gama fada ya juya

Da sauri ta ce" Yanzu nice baka san Wacece Ni ba kuma yau?"

Ya juyo yana dubanta ya furta" Yes!, ban sanki ba, dan kina boye min abubuwa da yawa, ki kalli shigar jikinki, a haka kika fito kika zo inda nake, an gaya

maki ni shashasha ne da zan auri macen da bata kishin kanta?, why zaki ringa tardoni gidanmu a irin wannan time din? ke bakya tsoron kadaicewa da ni ne ko sabawa kika yi? excuse me but dole in tambayeki bakya tsoron mu tsaya daga Ni sai ke a wajen da komai

ke iya faruwa ne ko sabawa kika yi?, nd Mufeeda ashe kina da bakin zagin ahalina?????, ashe baki da kunya?????......., thank you fr al, yanzu ki tafi dan bana son in juye maki a nan!"

Ya karashe yana daga mata murya dan baya so ta karra koda second daya

ne tana yi masa musunta na rainin wayo

MUFEEDA jikinta rawa yake yi, domin tunda take da shi bata ta

ɓ

a gannin bacin rai a fuskarsa irin haka ba

Da sauri ta juya, ta fara tafiya ta dakata ta juyo tana kallonsa hawaye wasu na sake bale mata, shi kuwa

a tsayen nan da yake ita din yake kallo shima , ama kuma ba wani alamu ko diz na tashin hankalin yannayin da take ciki a tare da shi, dan kuwa mamakin ta ya fi komai damunsa, har tunani yake yi dama a cikin mature akoy shashashai?, shi da yake son daukan m

ace mai shekarun da suka zarce na yarinya dan baya son ire iren halayar nan ne, baya son mace mai raini, baya son macen da saboda rufe jikinta kadai sai ta hadasa masa ciwon kai, ashe suma manyan akoy masu irin halin nan? ya salam,....to ko abinda ya sa Ba

ba ya kuge kan maganar auren nan ne?........

'AURE.....' zuciyarsa ta sake maimaita masa, ya sake bude idannuwansa a kan Mufeeda wace ta fashe masa da kuka sosai tana tsugunne dan kuwa ta sani ba zata iya tafiya a haka ba, idan ta tafi ta barshi a haka

zuciyarta bugawa zata yi, idan har ta tafi da kalaman nan da ya fada ba zata iya rintsawa ba yau

'Ya maganar auren ? har yanzu yana kan bakansa?............' ya sake tambayar kansa, sai kawai ya dauke idannuwansa daga kanta ya juya ya nufi ciki, ba dan

bashi da zuciyar tausayi ba, ko daya, dan kawai ya sani ne idan ba mugun fushinsa ya nuna mata ba ba zata daina abinda take yiwa ahalinsa ba, shi kuwa a kan su sai ya daina kowace mu'amala da ita, dan baya son raini sam!

Hankalin Mufeeda sake tashi

yayi gannin ya kada yayi tafiyarsa, mikewa ta yi tana kukan nan ta juya ta nufi waje, da nufin tarda baba ta fada masa dan kuwa ta sha kaiwa baba karar AL'WALID din, lokuta da dama idan ya juye mata baban ne ke yi masa magana ya dawo daidai

Sai dai ta

na fitowa ta nufi bangaren baban ta samu Su khalisat da iman da Raisa sunna tsaye sunna magana, kuma abin akaicin sunna ganninta suka bushe da dariya

Zuciyarta, da rabon a yi suka hasalata suka saka ta nufe su rai bace bayan ta sake share hawayenta ta

ce" Khalisat, Imane, Raisa, dariya kuke yi min bayan kun hada baki kun hadani da AL'WALID ko? ba damuwa , abinda baku sani ba ina jiran lokaci , idan lokacin tawa dariyar ta yi ku kuka da kanku, ba wai ku ba, a nan duniya inaga babu wace ta fi kusanci da

shi kamar musakiyar cen ko? to walahi sai na rabata da shi bale ku, baku da hankali, baku san me yake jiranku ba, fushinsa na dan lokaci ne zai sauko mu sasanta junna, kun san a nan duniya shine gatanku, duk wata takamarku sai na daidaitata ba iya ku ba ha

r wa'inda ke gidajen aurensu ama kuma basu bashi lafiya ba, da Ni kuke maganar!"

07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba:

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*FARKON GANIN IDONA*

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*LABARI DA RUBUTAWA*



*SAJIDA NIJAR*

🇳🇪

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maiku

di Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you

😍

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DUK NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN LADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA KOKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAƘIN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR

*Shafi na Ashirin (20)*

*TALLAH, TALLAH, TALLAH*

https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1

oUlKAT6ldQEXOf

YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI

HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

👉

0912 262 1080



LABARI

Zuciyarta, da rabon a yi suka hasalata suka saka ta nufe su rai bace bayan ta sake share hawayenta ta ce" Khalisat, Imane, Raisa, dariya kuke yi min bayan kun hada baki kun hadani da AL'WALID ko? ba damuwa , abinda baku sani ba ina

jiran lokaci , idan lokacin tawa dariyar ta yi ku kuka da kanku, ba wai ku ba, a nan duniya inaga babu wace ta fi kusanci da shi kamar musakiyar cen ko? to walahi sai na rabata da shi bale ku, baku da hankali, baku san me yake jiranku ba, fushinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login