Showing 138001 words to 141000 words out of 200647 words

Chapter 47 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

20

SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748

Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you

๐Ÿ˜

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ฦŠAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DU

K NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN LADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA KOKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAฦ˜IN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR

*Shafi na talatin da tara (39)*

*IDAN KINA DA BUKATAR TALLAH KI TUNTUBENI TA

LAYINA KAMAR HAKA 93811618*

LABARI

A hankali ya furta" Hajia karamahhhh???"

Khadeeja ta dago idannuwanta da kyar ta saka a cikin nasa, kirjinta zafi yake yi har yanzu abinda ya tsaye mata a wuya bai fada ba, ga maganar n

an da ta ji ya fada mata kamar haka " Ki je gida zan neme ki"

A hankali ta

ษ—

ora hannunta a saman nasa dake rike da habarta ta janye, wani haushinsa na tukota, innalilahi wa inna ilaihi raj'une wannan ai an kasheta, ita daga mai labewa da barira y'ar aji

nsu yana cin amanarta yana rantsuwar walahi ba soyaya suke yi ba, sai wanda aka dauka aka yi mata dole ashe yanada wace suke tare?

Sangartar da Lubna ta fi tsana a rayuwa da lamarin Khadeeja idan ta yi fada ta gama ta yi ta sheka musu kuka in an raba fa

danta da kyar suke rarashinta sai tace wai wani abu a kirjinta bai fada ba , ta yiwu ko sai ta ga abokin fadan nata ya summe zata ji abin ya fada matan ne ta yi, a hankali ta fara shashekar, a lokacin kuwa tuni aunty shareefat ta kirawo matan gidan sun fit

o hankali tashe

Tana kallon nan nasa tana shashekar nan kawai ta fashe da kuka ta dantse lebenta da karfin tsiya ta dubi wajen da Mufeeda take ta sake dubansa

Aunty shareefat ta rikota da sauri tana sallalami hankali tashe tana duba jikinta,domin su

basu ga ainahin abinda ya faru ba, rabiyar fadan ta gani ta auna ta kirawo mutanen gidan dan so take yi sosai Mufeeda ta idasa lalata rawarta da tsale, a rikice take fadin" Ta ji maki rauni ne? mama dan Allah sake kira min likitar nan , kin ga tana kuka t

a ji mata rauni"

Khadeeja da takaicin lamarin masu kudin nan ta ce" Aunty dan Allah kar a kirawo likita, aunty ya rabamu , ya rabamu dan Allah a barmu , aunty a barmu"

Su kam kama gane bayanin suka yi sai da Elhaji Maiga rai bace har yana magana yana

furzar da yawu ya ce" An ki a hada kun, wato ki jinyatata ko? ba za'a hadakun ba, aikin banza bari ki ji, daga ke har ubanki sai na rufe ku, ba zan yarda ba, sai na kai karar ku, mahaifinki ya dake Ni, ke kin dakar min y'a"

Matan nan kusan a tare suka

dauki salati, Mama Binta hannu a baki cike da jin kunya ta dubi AL'WALID dake tsaye yana sake kallon ikon Allah, ga wata dariyar kukan da Khadeeja ke yi da mamakinta na kama shi, domin da farko ya tsorata da kukan ne ko ta soka mata wani abu? yanzu kuwa y

a ji dalilin kukan sai kawai ya gyada kai yana kallonta , furucin Elhaji Maiga kuwa ya idasa kashe shi da dariya shi kam ina zai saka ransa ne? ga bana Hamza yana ta salalami, Muhammadu a tsaye yana kallon uncle din nasa da haushi, babansa kuwa a nesa a la

be

Mama Binta ta ce" Big Son me yake faruwa ne?"

AL'WALID ya yi murmushi kawai yana sake kallon Elhaji Maiga da ya idasa nuna masa waye shi

Aunty shareefat rai bace ta ce" To ka kai karar mana, dan Allah ka kai karar, ai koda an saurareka a wajen k

arar kai zaka kule kanka, saboda kakan kurma dai nan gidansu ne ka ga babansa nan, a gidansu ka tardo shi ka zage shi du a gabanmu mune shaida, ita kuma Maman kurma ai a gidanta ta tardota ta fara kai mata duka, wannanma mune shaida sai ka kai karar mu ga

waye zai kule kansa da kansa, mu je, daughter mu je daina kukan"

Elhaji Maiga du bambaminsa sai yayi tsit ya raka su sharefa da kallo da tarin mamakin sharin da za'a masa, ah to shari mana wai kuma wancen mahaukacin ne dan gidan nan????

Baba Hamza

da dan yannayin fusata ya ce" Ni du ban so abin nan har ya kai nan ba, yaya za'a yi ta magana daya ne? ka ga Elhaji karami kawai ka min maganin abinda ka hadani da shi tunda na yi nasiha, na bada hakuri , na yi rarashin an ki a duba furfurata a ji maganat

a, saima nema da ake yi a nuna min ban isa ba, to ba zan lamunci haka ba, na so a yi hakurin, kwarai na so a duba maganata aka kiya, bafa zan lamunci a ringa kama yan ya'ya da kokowa ba saboda abubuwan da kunnayena suka ji idan har aka aikata har da kai sa

i na yi shara'a domin kaine ka sanyo min fitina a cikin gidan nan har ka bada dama ake dauki ba dadin nan, "

AL'WALID ya nufi inda baba yake a tausashe bayan ya rike hannunsa ya ce" Na jima da nuna maka ka fita batun ka bari in yi ka kiya baba, na jima

da gane cewa ba kowa ke gane idan ana yi masa uzuri ba, yanzu ka je wajen kakan kurma ku zauna zan zo"

Ai kuwa baba Hamza ya juyawarsa yana kallon kurma dake tsale tana biyar bayan iyayenta da kakaninta sun nufi bangaren KHADEEJA yayi dan murmushi, domi

n rabonsa da ganninta haka tunda ya fada mata babanta zai yi aure ta yi murna sosai daga baya ta shigo tsoro, sai kuma yanzun nan , karshema sai ya ga ta dankara da gudu ta rigaye su shigewa ya tabbata labari ne cike da cikin ipad za'a dauko dan a bayar da

labarin nan sala sala, sai kawai yayi murmushi yayi tafiyarsa

Sai da ya bar wajen AL'WALID ya dan daga murya ya ce" Malan bismillah mana karaso plz"

Malan Abdullahi ya fito yana rabe rabe har sai da Muhammad ya riko hannunsa ya shiga tsakaninsu da d

'an uwan nasa

AL'WALID ya fuskance su a nutse ya ce" Alhamdulilah, zuwa yanzu babu abinda ba'a nuna min ba, kuma na fahimta sosai, Malan dan Allah a yi hakuri a daina shiga duk wani abu da zai janyo zubar da mutunci, kuma a yafewa Muhammad yama yi kok

ari gaskiya, domin iyaye daban ne, darajarsu kuma a idannuwan ฦดaฦดansu mai girman gaske ce, ba kowa ne zai jure wasu abubuwan da suka wuce misali ba"

ya sake duban su Elhaji Maiga ya ce" Elhaji, idan har ana bukatar magana da Ni a nemi layina in sha Alla

h, saboda nan din bana so ko da wasa irin haka ya sake faruwa.. , bismillah mu je "

Ya musu nuni da hanyar tafiya fuskarsa a hade SOSAI

Gaba dayansu babu wanda jikinsa bai yi sanyi sosai ba, saboda du abinda ake yi bai taba yi musu irin haka ba, ita

kuwa Mufeeda gaba daya jikinta rawa yake yi, a yanzu ta wuyanta take yi fiye da komai , dan haka ko da mahaifinta ya ja hannunta binsa ta yi muryarta ko fita bata iya yi da kyau suka karasa motarsa

A nutse AL'WALID da yayi waya ya ce" Muhammad, ku daka

ta a kai malan "

Muhammad sai da ya sauke ajiyar zuciya saboda dama tsoransa kar aje kafin su ajiye shi su yi masa abinda zuciyarsa zata idasa bugawa,

Elhaji Maiga ya fada mota ko magana bai yiwa direbansa ba ya ja suka tafi Mufeeda na sake fashewa

da wani kukan

A tausashe AL'WALID bayan motar ta zo ya dubi Muhammad ya ce" Ga katina Muhammad, ka same Ni ranar monday da takardunka, ka zo da sassafe mu fita"

Daga Muhammad har malan sai da suka ji sun wartsake, malan ya ringa godiya yana hawaye

AL'WALID yayi murmushi ya ce" Malan Allah ya karra lafiya, zan shigo gidan da baba in sha Allah, idan an je an fara shirin kaura...., dan Allah a kula da lafiya a kuma kauracewa duk wani abinda zai taba lafiya da nutsuwa...., malan babu mai yi sai Allah a

duniya, kuma musulunci bashi da tozarci, baya yarda da tozarci"

Daga haka kawai ya wuce wajen direban dake tsaye suka yi magana ya sanar masa idan ya ajiye su ya ba Muhammadu ky din motar ya hayo taxi ya dawo, ya sake ja baya ya harde hannayensa ya mus

u salama hadi da dakatar da kukan da malan ya fashe da shi, Muhammad kuwa kamar bakinsa zai yage dan dariya da farin ciki, sai maimaitawa yake yi Allahu akbar, shi dai yana tsayen nan yana kallonsu har suka tafi

Da farko ya so fita, sai kawai ya ji ina

zai je? cen kasan zuciyarsa ke raya mana ina zai ne kuma? sai kawai ya samu kansa da juyawa ya nufi bangaren nasa a nutse ya shige har baban falon da salama

Saminsu yayi kamar wa'inda ke wata sabga, fira suke yi da dariya su khalisat kuwa kamar zasu tas

hi sama dan farin cikin abinda shi ya gaza ganewa

Zama yayi cikinsu aka bashi abinci a nutse ya dan taba sai kuma ya mike yana kallon aunty shareefat ya ce" Maman AL'WALID me likitar tace ne?"

Aunty shareefat ta ce" Zazabi ne d'an shareefat ai da sau

ki yanzu haka sunna sama fa ita da y'ar sun dage tun yanzu litle zata kauro, mun so ta bari har a kwana biyu dai ta gama cin amarcinta lafiya sai kawai ta gudu sama"

Shima maganar sai da ya ji kunya sai kawai ya basar, ya yi saman ba tare da yace komai

ba, kaka Z kuwa har kamar ta tashi ta bi shi dan ta ga abinda zai yi a saman, sai dai ba hali dan ita kadai ce ta zauna cikin yaran , sauran du sun koma wajen Hajia Inna dan su kwontar mata da hankali, itama ta kasa ta tsare be saboda kawarta dake ta damun

ta kan dan Allah kar ta yarda ta bari wani abu mai sunna shakuwa ko makamancinsa ya shiga tsakaninsu, da dazu zata zo gidan da ta sanar mata Elhaji Ya'u fa ya zo, yanzu haka yana shago sai tace sai da yama idan ya rufe zata zo dan kuwa tana tsoronsa kamar

me.

A nutse ya shiga dakin bayan ya dan kwonkwasa

Samunsu yayi zaune tsakiyar cafet sunna buga game a ipad din Kurma

Tunda ya shigo kurma ta mike tana ta watsa haฦ™ora ta shiga yi masa yarenta, wanda shi idan ka ga ta masa rubutu to a rikice tak

e ta yadda ba zai gane yarenta ba, saboda yana gane dukkan abinda take nufi da alamun da take yi da yan hannayenta

Murmushi kawai yayi saboda fada masa take yi Mamanta ce, kuma bata dukanta dai da sauransu

Da hannayensa ya yi mata tambayar akoy wand

a ke dukanta ne dama?

Sai kawai ta dan juyar da kanta ta ki cewa komai

Ajiyar zuciya ya dan sauke da hannunsa ya yi mata alamun ta je kasa gayanan zuwa

Juyawarta ta yi da dan gudu gudu ta fita ta rufo dakin

A nutse ya dan murda ky a kofar , h

akan ya sa KHADEEJA dake kallon kasa dagowa da sauri ta zuba masa ido

"Ki je zan neme ki" Ya sake amsawa a kunnenta, hakan ya sa ta mike tsaye da sauri ta juyar da bayanta idannuwanta na cika da kwallah, ta share tana tuna kashedin da Lubna ta taba yi m

ata da ta yi mata kukan iya shege dan ta ga Abdul karim da budurwa, cewar idan akoy abinda zata yi ya ga damarta ya rainata shine ya gane tana sonsa sosai da sosai, lokaci daya kuma ta samu kanta da yima kanta tambayar "SO? WANI IRIN SO?"

Tunda ta mike

ya bi rigar dake jikinta da kallo har zuwa inda rigar ta tsaya ya samu kansa da shakun karasawa inda take, domin ya jima rabonsa da gane cewar lafiya kalau yake sai yau da duk wani ntc ya kunce masa daga kallon nan da yayi har ya ji kirjinsa na amsawa da

karfin da ba zai iya dakatar da shi ba......, ama....., ama.......sau nawa yana gannin mace da riga irin haka wace ta lafe a jikinta sosai, bai ji haka ba sai yau??????

A hankali ya ce" Yaya zaki shake y'ar mutane a gaban babanta kuma ki yi kuka Hajia k

arama?"

Khadeeja ta ji wani takaici ya shake mata wuya, ta juyo da dan hanzari dan bata san cewa daf da ita yake sosai ba tana fadin" A gaban babanta ko a gaban masoyint......"

Diffff ta tsayar da maganar saboda kusancin yayi yawa sosai

A nutse ya

ke kallon gashin idannuwanta dake kallon kasa kirjinsa na sake dokawa

hannunsa na dama ya makala a bayanta a hankali ya sarkafo shi, sannan ya dan duka ya saka dayan ya dauketa cimak

Da sauri ta rike gaban rigarsa hakan ya sa ta yamutsa rigar dan a t

sorace ta cimuimuye rigar tana rintse ido domin kawai ta zata zubar da banza zai yi ya huta da fitsara saboda ai kamar rashin kunya ne zata yi masa shi kuwa shine baba a gidan nasu ai, kuma dai babanta ai ya zamo mai kai duka ne in ana haya haya gaskiya sh

i yasa ta yi jiran jin nata itama yau, sai ta ga daukanta ne aka yi, kuma aka yi tafiya da ita har wajen gadonta

A nutse ya shinfidar da ita, sannan ya dan rankwafa kusan fuskarta yana gannin yadda ta rintse ido da karfin tsiya ya furta" Ba'a hararan mi

ji fa, babu kyau, kuma Ni ban iya fada ba hajia karama"

Idannuwanta ta bude wa'inda suka cika da wata kwalar da bata san ko ta mecece ba, a hankali tana dubansa ta ce" Me yasa ba zaka ce min Khadeeja ba?, "

Bakinta da ya furta sunnan yake kallo, a ha

nkali ya lumshe idannuwansa kasa kasa yace" Hajia ฦ™aramar ya fi dai"

Khadeeja ta dan zubawa karan hancinsa ido tana dane hannunta dake so sai ya taba , haka kuma tana hanna tsoron kusancinsu bayana ta dan turo baki a hankali ta ce" A'a, sunnana yana da

dadi sosai, sunnana yana da daraja sosai, sunnana ya...."

"SHUIIIIIIIIIIIITTTTTTT" Ya fada a hankali yana dora yar yatsarsa a saman lebenta hadi da kafe leben nata da ido

Gabanta ya yanke ya fadi, lokaci daya kalaman da Aba ke fada yana fada suka f

ado maka a lokacin da yake fadin KARIMA mai jan ido? wato mashayi ko hariji? , a lokacin da Mama ta damki hannunsa suka fita daga cikinsu suka je suka sasanta

Idannuwansa sun tsoratata, yannayinsa ya tsoratata, a lokacin ta ga wata jijiya a gaban goshinsa

wace bata sanshi da ita ba, bugun zuciyarsa kuma ya kara kaimi fiye da dazu....lokaci daya tsoro ya gama mamayeta na yannayinsa

A hankali ya furta" Baki da lafiya, ki huta plzzzzzzzzzzz, idan zaki fito zuwa bangaren su Baba, ku saka hijab Hajia karama

hhhhhhhhh, kin ga gidan cike yake da mutane kuma du ba yara ba....................."

Buga kofar da aka yi a karro na biyu ya katse maganarsa a dole ya lumshe idannuwansa yana dan juyawa dan daidaita kansa sannan ya ja baya sosai ya bata space, wanda da

yayi sai da ajiyar zuciya ta kwace mata, tsoron da take ciki ya karu, zazabinta ya karru ta ji kamar zata summe

A nutse ya juya ya dan kalli yannayin jikinsa ,

Wata irin kunya ta kama shi a nutse ya dan juyo ya kalleta, sai kuma ya yi murmushi ya nufi

hanyar fita daga dakin gaba daya yana jin kansa na neman daukan ciwo, wato abinda ya jima bai ji bane ke son bayano masa lokaci guda

Da ya bude dakin yana gannin kurma sai ya kasa fita saboda ya jima rabonsa da fita da shiri mai sunnan shiri koda ta kwa

na, hakan ya sa a yanzu du ya tsargu da kansa

Kurma ta masa nuni sannan ta yi masa yaran kurumcinta wanda ya gane cewar kaka Z ce tace ya zo

Ya dan dubi kurma da tunanin kaka Z kuma? lafiya? kai ko dai kurma bata gane ba?, shi dai yayi mata nunin ta

je gayanan , bayan ya ji ta fara sauka ya fito ya rufe dakin ya nufi nasa dan sai ya cenza tufafi , lokaci daya yana duba wayoyinsa dan tunanin ko sun yi ta kiransa , ko babu lafiya? dan bai ba dalilin da zai sa a irin wannan lokacin kaka Z ta yi kiransa b

a in dai ba wani abu mai mahimmanci bane.............................

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

07/12/2024, 15:21 - samiraharounayacouba:

๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ

*FARKON GANIN IDONA*

๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ

*LABA

RI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login