Showing 93001 words to 96000 words out of 200647 words
kalla sannan ta kawo masa, hannayenta har sunna rawa ta miko masa , kirjinta kuwa yana sama da kasa tarin bacin rai da tashin hankali ta ce" Ka gani? da nake f
ada maka su suke tsokanata su suke jana da fitina ka gani ko? wai zaka yi aure, wai jibi zaka yi aure tana gayatar ilahirin mutanen Nijar da ketare, duba ka ga a cmmnt section ana ta tambayarta ba'a gane ba aure? da wa? bata ba kowa amsa ba sai wannan da
yace ashe gari zai yi tumbatsar mamaki auren honorable da Mufeeda kalli amarta, kalli abinda ta rubuta, wai ba da Ni bane...., ka ga abinda take yi min ko? walahi yarinyar nan ba zan taba yafe mata ba, du abinda take min sai na rama, in ita tana yin haka n
e dan ta bata min rai bata san baban abu take tabowa ba? ba damuwa, zata ga abinda zan yi mata!"
Gaba daya Mufeeda ba a hayacinta take ba, irin yadda take magana sama sama ido waje jikinta har yana rawa kawai yake kallo daga shi har kannenta
Kai ya
girgiza ya juya zai yi tafiyarsa, danma yama ta yi a inda suke tsayen innuwa ta karaso da sun sha dukan rana da noncence din Mufeeda
Ya kama marfin motarsa zai shiga ta yi gagawar riko hannunsa tana fadin" Bab yanzun ma laifin nawa zaka gani ko?, yanzu
nma gani zaka yi nice mai laifi ko? ka duba fa ka gani irin abinda take min"
"MUFEEDA!, CIKA NI!" Ya fada a mugun kausashen da ya sakata sakin hannun nasa Tana duban fuskarsa
Rai bace ya dago hannunsa da ky din dake ciki ya nunata ya ce" Gaba daya ba
ki da nutsuwa? gaba daya baki da linzami a harshen ki? Ni zaku mayar shashasha ke da kannenki? Ni zaku fito kunna ihu a gabana kunna wulakanta junna da ahalina? ok, dan khalisat ta
ɗ
ora haka a Tiktok shine wannan daga Muryar? i said shine na furucin zaki h
alaka y'ar uwarki? da matata kike a yau a gidana yaya zaki yi kennan in hakan ta fito maki?"
Kanta ke sarawa, babu abinda ke jijiga nutsuwarta irin fadansa a duniya, sai kuma furucinsa masu tsauri ne sosai yau a kunnayenta
Da sauri ta shiga murza go
shinta tana kallonsa, sai kuma ta girgiza kanta tana furta " No, no No, ta san abin nan da ta yi baban abu ne da zai fidani a hayacina, ta sani sarai ta yi, su burinsu su ga bayana ne kawai , burinsu kennan fa! bab yaya zaka ce da matarka nake, dama Ni ba
matarka bace? kuma ko matar taka nake ai ba wannan maganar, aure fa take nufi, kai ka yi aure da wata macen ina duniya? hahahahhaa lalle khalisat!"
Tunda suke bai taba kai hannunsa shi AL'WALID da kansa a jikinta ba sai yau, a yau dinma dan ya dawo da i
ta hayacinta ne ko menene? gaba daya rainin wayonta nema yake yi ya wuce misali, abinda ba zai taba dauka ba, Shi bai taba duban budurwa da nufin zai zauna da ita, ita kadai ba a duniya, karya ne, kuma ko macen aure wace suka zauna har Allah ya raba basu t
aba yin magana makamaciiyar wannan ba, to a kan mema zata nemi
ɗ
orawa kanta ciwon da bashi da magani? ciwo ne, baban ciwo ne marar Tabas, domin shi da kansa bai taba tunanin za'a kawo masa magana irin wannan a rayuwarsa ba, har yanzu matar da akace za'a au
ra masa din fa bai tantanceta ba, ta yiwu ta leko ta koma za'a yi saboda daga inda ta tsaya ta hararesu ta juya baya tunanin tana da wadataciyar tarbiyyar da zai yi zaman aure da ita, shi kuwa ba zai dauki raini da wulakanci ba! kwarai zai je ya samu moma
karama kan abinda ta yi, bai dace ba, ta yi neman fitina, Duda bai san girman abinda ke tsakaninsu ba, ama bai kamata ta
ɗ
ora abin nan a Tiktok ba, kai subahanallah bai san me suka dauki social media ba, ace kai jira kake yi komai ka kai ka watsa duniya? k
ai baka da sirri ne a rayuwa? komai sai ka kai ka watsawa duniya? mtsssssss
Habarta ya dago ya saka idannuwansa cikin nata, ga kannen nata kuwa yuuuuuuu a gefensu a tsaye,
A kausashe ya ce" Na taba yi maki alkawarin koda Allah ya sa mun yi aure da
ga ke ba kari?"
Mufeeda kallon cikin idannuwansa kawai take yi
Ya dora da fadin" Ki yiwa kanki adalci, ki kiyayi furucin bakinki, idan har kina cikin hayacinki kin san cewa ko alkawarin aure ban taba yi maki ba, saboda Allah keda komai ba Ni ba, du y
adda zan so zama da ke sai ya aminta, kin sha son na yi alkawarin nan na fada maki bana alkawarin abinda ba Ni nake da shi ba, kina tune? i mn kina cikin hayacinki kina tune?"
Mufeeda ta lumshe idannuwanta, a kausashe yake yin maganar, ya dan duko da ts
ayinsa daidai ita, ya kare tsakaninsu da kannenta, sai dai a kausashen kuma kasa kasa sosai ta yadda duk wanda ya ji abinda suke fada balakin son jin gulmarsa ba kadan bace, hakan ya sa gaba daya tsigar jikinta ke tashi, kanshin turarensa ya idasa hade jik
inta,
A hankali ta rike damatsunan hannayensa, a lokacin ne kuma JARUKE ta kashe musu hoto , domin su ji suke sasantawa ake yi harma ana daf da shan minti
A nutse ya dora da fadin" Ban taba saka maki sasari na, ina cikin manema aurenki ne nah?, ko
a yanzu bata cenza zani ba, sai dai yannayinki na yau ya sa ba zan je da bukatar a hade bukatar gidanmu da tawa ba, dole zan karbi bukatar gidanmu kafin in gama gane tawa bukatar, domin kwarai ta yaro kyau take bata karko!......., Mufeeda ba karya khalisat
ta
ɗ
ora ba, jibi zan daura aure, ba yana nufin na rabu da ke bane, ki nutsu ki je ku shirya ku tafi , kin fahimta?"
Auta ta zabura ta matsa ido waje ta
ɗ
ora hannaye saman kanta kirjinta na bugawa
wato lokuta da yawa idan sunna nuna mata AL'WALID na
basu tausayi in suka tuna halayarta da kuma aurensu shi da ita, du sunna nufin zata wahalar da shi zata saka shi a wani hali na abin tausayi sai tace da su basu san waye AL'WALID ba, da suke ganninsa nan shiru shiru ya fi kowa iya rigima, kuma baya tsoron
uban kowa idan abin yayi ya tashi kansa tsaye yake yi sai dai du abinda zaka ji ka ji, gani suke yi a wai ne, domin su dai wani lokacin har ya zo kasar ya bar kasar maganar kirki bata hada su, dan sai su ga ko kallonsu baya yi bale yace da su sannunku su k
uwa dama ba gaisar da mutun suka iya ba gaskiya ko waye kai in ba kai ka fara ce musu sannu ba sai dai ku ringa kallon junna da su, haka suke, du basa yarda gani suke yi wai ne sai yanzu da yake tsaye kikam a gaban YAYARSU da suke tsoro kamar me,domin Mufe
eda irin yaran nan ne yan balaki, ko a cikin kawaye ta adabi kawaye ba maza ba mata bale a cikin gida, ko a gidansu ita ake yiwa biyayya kuma in abu ne in ta yi tsaye tace ba zata yi ba ba fa zata yin ba sai dai mahaifinsu yace zai lalabata daga baya ta ya
rda a yi, babu mai shigar mata daki ko mamansu, babu mai taba kayanta , bale da Allah ya ha
ɗ
a soyayarsu da AL'WALID gaba daya abin sai ya idasa rikicewa girman kai,, isa, fada , kala kala, ko a cikin gari an santa yawanci kawayenta mrs AL'WALID suke kirant
a da shi, dan kuwa babu wanda bai santa da haka ba, sai gashi idonta idonsa bayan yanzu yanzu ta gama alwashin yar gidansu ta
ɗ
ora ne dan ta daga mata hankali dan ta tsokaneta , ya dubeta, ido cikin ido ya rike habarta a tsaye a gabanta ya sanar mata? su k
am yau ai sunne suka shiga uku ba kowa ba
"A........Au......Aure dai aure? Mufeeda ta fada bayan ta dantsa faratunanta a cikin damatsunan hannayensa, tana jan numfashi da kyar sannan ta sake matse dan space din da ya rage musu ta hade jikinta da nasa da
n bata jinsa da kyau , kuma tana da bukatar jin nasa da kyau din
Idannuwansa ya dauke daga fuskarta ya ja baya, ama cikin ikon Allah da wata bakuwar masifar kamar an mana musu gam, sai ta sake matsowa ta matse shi
Du yadda yake gudun nuna mata bacin
rai a yau so take yi sai ya nuna mata, gaba daya jikinta kuwa rawa yake yi kamar an jona mata chkng
A hankali ya ce" Ki ja baya"
kai take girgizawa tana kallonsa ta ce" Dan jiya mun yi fada da yan gidanku ne zaka ce zaka yi aure? dan ka daga min hank
ali ko? idan ka yi aure bab ai ka san zaka sakani a uku ko? bab me na yi da zafi haka? dan kawai ka rikitani ne zaka ce zaka yi aure? wani irin aurenma wai...na gaske ko na wasa......................? bab dubeni dan Allah dubeni dubi fuskana da kyau mu yi
magana du bana ganewa , ban ganewa bab.....bab......., aure? walahi idan zaka horani ka guji irin wannan horon, in wasa kake min ka daina, zaka kasheni ne, kana iya kasheni ne, dubi kirjina, taba kirjina ka ji, bab du laifin da zan yi maka gwara ka zane mi
n jiki da ka ha
ɗ
a kanka da wata macen ko Wacece , bab kana tunanin a duniya akoy wata mace da zaka ha
ɗ
a kanka da ita? ko wace ta shani kafin ni dan bata duniya walahi da sai na yi mata abinda zai gigitata!, bab du yarinyar da zata rabeka ta rabarwa kanta m
asifa da balaki, domin walahi walahi sai na gigita farin cikinta, sai na wulakantata, sai na sakata ta shiga uku........ ka ga ka bari dan Allah, ka cire belt dinka ka zane min jiki in haka zai sa ka huce da wannan maganar ka ji????"
Ta karashe tana son
ɗ
ora kanta a kirjinsa bayan ta yi dage, sannan ta
ɗ
ora hannun nata a wajen belt din dake kugunsa hawaye na zuba a fuskarta tamkar an kunna pampo, tunda take bai taba fadin abin da ta ji ta gigice irin na yau ba, bai taba fadin abin da ya nemi sakata a wani
hali irin na yau ba
AL'WALID ya rike hannunta da wani irin saurin da bai taba Sannin yana da shi a jikinsa ba, da sauri ya zuba mata kausasun idannuwansa da matsanancin mamakinta, ina zata kai hannunta? innalilahi wa inna ilaihi raj'une....... Allah ya
tuba tunda marigayiya ta rasu ai babu macen da ta kara matse masa waje irin haka sai yau, lalle badalar yarinyar nan yawa ne da ita in aka
ɗ
auki kalaman bakinta kuwa kamar ba addinin musulunci a tare da ita
Matsar da ita yayi da kyau ya shige motarsa
ya rufe da karfin da ya sa ta rintse ido sannan ya kunna motar ya figeta ya fice a gidan, dan kuwa shi dai bai taso ya ga ana dukan macen da ake yiwa kallon wace za'a iya hada gado da ita a gidansu ba, da ace ya ga haka tabas da yau jikin Mufeeda sai ya ga
ya mata na wulakancin da ta yi masa da raini!
Kofar da mai gadi ke maidowa zai rufe take kallo bayan ya fita, lokaci daya numfashinta na neman gagarar kofar hancinta
JARUKE ta kasa yin zuciya, abu da d'an uwa ta karaso murya a sanyaye ta ce" Mofi, pl
z Mofi mu je ciki"
Mufeeda ta juyo tana kallonsu, ta juya ta kalli wannan ta kalli wannan, muryarta mai zafi yau ta nema ta rasa, murya na yi mata gargada a hankali ta ce" Kun ji me yace? wai aure zai yi jibi? kun ji kuwa? wai ko dole zai amshi bukatar
danginsa? dan Allah wai dan ya daga min hankali ne ya fada ko da gaske ne?"
Gaba dayansu sai suka gaza magana , dan auta tuni jikinta ke rawa
Mufeeda ta sake dubansu ta ce" Bai san irin darajar da yake da ita a rayuwata bane, da ba zai taba hada min
kansa da wata halittar ba, kun ga Baima gane irin kishina a kansa bane ko? bab bai sani bane, ama dan Allah kirawo direba su zo mu bi bayanshi, fushi ne kawai yayi , na tabbata da zarar ya huce shikenan zai daina maganar nan, dan mun yi fada da su ne fa ya
yi fushin nan, kun san yana da shakuwa da su sosai baya so a taba masa dangi, plz baby yi kiran Cross mu bi bayansa plz"
Baby ta gyada kai ta amshi wayar Mufeedan dake hannun JARUKE ta shiga neman layin, JARUKE kuwa tana tsaye
Mufeeda na kai kawo, h
awayen nan bai tsaya mata ba ta ce" Bai san irin addu'ar da nake yi bane du ranar da zan yi sallah ko? bai san cewa ina addu'ar da wata ta rabe shi gwara gawarsa a gabana ko? bai san ina cema Allah bana so ba? hum, lalle, bab kennan, ......"
Sai kuma ta
yi turus tana duban su JARUKE ta ce" JARUKE, yi min kiran Dady, dan Allah yi min kiransa, wannan nacin da yayi kan mu taso yanzu yanzu in ji na menene..... innalilahi JARUKE kirjina zafi yake yi, kar aje maganar nan gaskiya ce....?"
Sai kawai ta cire a
bayar dan ta fara rike mata numfashi, ta barbaza gashin kanta ta ce" Kan baban bur'''''''''''''''', JARUKE bani shi bani, wayo Allahna zan mutu, wayo zuciyata wayo na mutu na lalace, wayo Allahna zan mutu, zan mutu, hello, walahi inaga da gaske yake, hello
, hello dady, aure bab zai yi da gaske? shi yasa kace mu taho ko? dady kana jina kuwa.....? walahi ko Wacece sai na halaka..................................................................wayo kirjina numfashhhhhhhhhhhh......."
Ta saki wayar KASSSSS , ta
rike kirji tana wani irin numfashi
Ihu yan uwan nata suke yi, hakama mahaifinta da mahaifiyarta a wayar ihun suke yi, domin uban ya daga ne ta warci wayar
"MUFEEDA, Mufeeda, Mofi! ta mutu, ta mutu!" Auta ke fada da karfi tana sakin ihun kuka
Da ka
rfi JARUKE ta kamata tana jijigawa itama tana ihun ta mutun, masu gadi da abokansa ne suka karaso da gudu suka shiga tataba Mufeeda a yannayin da take ciki na rashin wadataciyar sutura , nan suka tabbatar musu da bata mutu ba, a lokacin ne kuma wayar mai g
adin ta kwashi ringin, croossss da ihu ya sanar masa ya bude masa kofa dan sunna waje
A guje ya je ya bude suka shigo da gudu da motocinsu , nan suka cicibeta suka yi mota da ita, sunna waya da Elhaji Maiga kamar zai fado ta cikin wayar yana sanar mus
u gayanan, su GAGAUTA kaita babar asibiti gayanan zuwa
Asibitin suka nufa da ita, da kannenta rungume da ita, ba wai iya Mufeeda ba, harta JARUKE dake da makamancin halayar Mufeedan zuciyarta tafasa take yi, alwashin dake ranta kuwa mai tsananin gaske
ne, ta daukarwa ranta cewa idan har da gaske aure AL'WALID zai yi sai ta jigata matar nan ko y'ar uban waye!
(Wannan kennan)
Tuki AL'WALID yayi gaba daya zuciyarsa a cinkushe
Ba dan komai sai dan irin lokacin da ya bata yana kallon ikon Allah da t
arin surprise na halayarta, furucin bakinta kuwa tamkar ba wace ya sani mai hakuri da biyaya ga umarninsa ma ba wai na iyayenta ba, a tunaninsa Mufeeda ko wuta iyayenta suka hura suka ce ta fada zata fada ne tsabar biyaya, ashe haka take magana da iyayenta
? kuma tsabar raini ta dube shi tace da mai aiki take magana, to ko mai aikin ce wace ta zama a tsakaninta da mahaifinta ai ba karama bace, kuma shakuwa akoy tsakani , koda mai aikin ce ai ba baiwarta bace da zata yi mata magana a haka, idan da tarbiya kuw
a Bama zata yi haka din ba,
sai furucinta a kan maganar auren nan, a tunaninsa idan ya sanar mata eh zata iya daga hankali, ama in har ya nuna mata abin nan ya zo ne kai tsaye maganarta na nan, zata bar maganar a wuce wajen ko? sai gashi cikin ikon Allah
magangannu da yannayinta kamar na wace bata cikin hayacinta....., hum Mufeeda kennan, ita da zarar ranta ya
ɓ
aci ko hankalinta ya tashi sai ta ringa furuci irin haka kennan? , Tabas ya san yana kaunar yarinyar saboda tunda ya hadu da ita cikin kyautata ma
sa da y'arsa take, in anguwa ta je sai ta yiwa litle kyautar wani abin, kulun cikin yiwa litle siyaya da nuna soyaya take, dole zai so ta, saboda tana kula da dukkan abinda yake so tana kuma taya shi so, a wannan zuwan ne ya fuskanci abubuwan nan, sai ya j
i du ta sire masa! hummmmmm
Tunda ya tunkaro gidan ya hangi babar kofa a bude, kuma abin mamaki mutane na dan kai kawo kamar ana yin wani abin
Sojawan dake tsaron kofar sunna gannin motar suka sara masa, ya tsayar da motar a lokacin da daya ya zo
ya sake sara masa sannan ya gaishe shi
da kula ya amsa, a nutse ya ce" me yake faruwa a gidan ne?"
Sojan nan ya ce" Baki ne ke zuwa, ance a bude gida a kuma bar kowa shiga na shirye shiryen auren naka ne sir"
Ido ya dan zarro, kafin a ransa ya