Showing 159001 words to 162000 words out of 200647 words

Chapter 54 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

13

aunty shareefat ta same su khadeeja na zaune a kujerar nan a

nutse tana sake duba magungunan Inna da komai da komai bayan ta aunata ta duba date na expire din magungunan ta ga har lokacinsu ya cinye ta sake duban Hajiya Inna da mamaki , zata yi magana aunty shareefat ta ce" Ah ga dukkan alamu jiki da sauki daughter

AM, ga maganinki ki sha , Inna lafiya ake hawaye ? " ta karasa ta talabi Hajiya Inna da kyau tana dubanta hadi da taba jikinta, duda zata yi mamaki kwarai matuka idan akace saboda jikin ne Hajiya Inna ke kuka, domin ita dai a kusa kusa bata ga mai juriyar

babarsu ba a kan ciwo da jarabawar rayuwa, du halin da take ciki takan yawan yin murmushi ta furta alhamdulilah ala kulli halin. Gannin hawayenta yanzu ya sa ta ji hankalinta na neman tashi ama sai ta yi iya yinta ta dane

A hankali khadeeja bayan ta h

adiyi maganin ta ajiye kwalbar ruwan ta fuskanci aunty shareefat a tausashe ta ce" Mama, magungunan Hajiya du na ga date din su ta wuce, ko wa'inda take sha a wani wajen ake ajiye su ba a box din asibitinta ba?"

Aunty shareefat ta sauke ajiyar zuciya ta



ɗ

an sake riƙe hannun Hajiya a tausashe ta ce" Daughter AM, Hajiya ai ta jima rabonta da shan magani, shi yasa kika gansu a nan a ajiyen nan"

Khadeeja ta dubi Hajiya da dan mamaki, ta sake duban aunty shareefat wace ke ta hankalta da yanayin Hajiyar

A hankali ta

ɗ

ora da fadin" Kin ga Hajiya ko? Rana daya ta ce a barta haka, a lokacin da ciwon nan ya sameta kin san hauka hauka muka yi, mune wannan asibitin, munne wannan likitan, munne wannan kasar, munne wancen kasar, munne na Hausa, ya zamo kulun ciki

n huda ta ake yi kuma kulun cikin hadiyar magunguna take, ga na Hausa a gefe a lokacin ko malaman sai mu basu taimakon magunguna saboda irin yadda baba ya cika dakin cen nata da magungunna na taimako daga mutane mabanbanta daga kasa kasa, sai dai cikin iko

n Allah sauƙin na shaƙar numfashi ne kawai, sannu a hankali ya zamo komai bata iya yi, har sai da ake ta faman yi mata massage ne aka samu take motsa hannayen ta da kanta ita da kanta....., to a lokacin da yake yi mata ne ta dakatar da komai tace ta gaji,

a barta haka, a kyale ta haka, babu yadda bamu yi ba take ta gaji ita fa a barta haka, a lokacin Alhaji karami ya kusa shekara bai yi tafiya ba, kulun cikin nacin lalaba da rarashi kan dan girman Allah ta yi hakuri a ci gaba da neman magani sai Hajiya tace

ita fa a barta ciwonta ai kawai na rai ne, ciwon da ake neman magani baya sauki kawai kaima ka san abokin tafiya ne, dan haka a barta, karshema ya zamo da mun dauko maganar magani sai ta fara mana kuka, gashi hawan jinnin da hankalinta ya tashi yake motsa

wa, sai kawai muka hakura muke bi da adu'a sai idan mun ga ciwon ya tashi sai mu yi kiran likita idan ya zo ya dubata ya bata dan abinda zai kwantar da ciwon shikenan "

Ta karashe maganar tana dan shafa gefen fuskar Hajiya Inna a raunane ta ce" Innata,

bari in kirawo maki docter, kin ga jikin ki ya motsa ko? In je in kirawo shi?"

Hajiya Inna ta bude idannuwanta da suka rine sosai, a hankali ta ce" Shareefat, ba zan ga likita ba , ko ya zo ba zan gan shi ba, in dai har babanku ba zai janye fushinsa a k

an mahaifiyar yaron ki ba , ba zan ga likita ba, ba kuma zan sha maganin ba, dama ai na zame masa kaya idan na mutu tai zuwa gobe shikenan sai a kaini a birne sai ya ci gaba da kwana rayuwar da ya fi so wace babu wanda ya isa ya kwabe shi ko ya bashi shawa

ra "

aunty shareefat hankalinta ya sake tashi, hakama khadeeja saboda irin yadda jinnin hajiyar ya hau , ko mai kannanun shekaru ce tana bukatar magani da wuri, bale ita da take cikin jinya

A hankali aunty shareefat ta ce" Innata, kar ki hada ciwon k

i da fushi, dan Allah yauma ki yi aiki da halayyar ki da ta fi komai burge mu da zame mana abin koyi wato hakuri da adu'a , ina da yakinin Allah ba zai bar big son cikin wannan rayuwar saboda shi din mai addini ne, mai alkhairi ne, mai jin kan talaka ne, m

ai tausayin marayu ne,"

"SHAREEFA kina sane da labarin wanda sallah ce yake yi da karatun Alqur'ani a kebatacen waje dan samun nutsuwar yin ibada cikin nutsuwa da kwanciyar hankali , ama saboda mahaifiyarsa ta zo ta kirayi sunansa sau daya, ta sake dawo

wa, ta kuma dawowa da bai amsa mata ba ranta ya bace ta yi fushi ta yi addu'a cikin fushin nan, karshe du ibadar tasa Allah ya jarabe shi da kaucewa layi?, ai ba'a garaje da lamarin uwa, duk wanda ya dauki uwa da wasa walahi walahi ya gama tabewa, komai ta

laucin mahaifiyarka, komai mummunan halayanta , ka yi kokarin ka ka yi mata biyayya har Allah ya raba ka da ita lafiya, idan ka kuskure ka yarda ka saba mata Allah ne zai hukuntaka, SHAREEFA in tambaye ki, idan AL'WALED ya rasu a yau kunna da abin yaki ko

Muryar da zata daga amo ku daka tsawa a saurareku a wajen da aka halicce ku ne? Ku yi kokari ku yi ta kanku fa, walahi walahi ita ta ji dadi saboda wanda ta yiwa a gaban ku ya yafe mata, kuma hukuma ta amsheta ta je ta yi kaso har na shekaru goma sha takwa

s, sauran maganar kuma inaga tsakaninta da Ubangijin ta, wanda in dai zata yi kyakkyawan tuba zai yafe mata, shi kuwa fa d'anta? Menene hujarsa na rashin kasancewa da mahaifiyarsa da yi mata biyayya a kan hanyar da bata sabawa Allah ba a gaban ALLAH?" Haji

ya Inna ta katse aunty shareefat ta fadi maganganun nan tana fashe mata da kuka

jikin aunty shareefat na rawa ta juya da sauri ta fita dan nemo babansu, domin idan Hajiya Inna ta rikice din nan tana daga musu hankali sosai ne.

Khadeeja kanta jikint

a rawa yake yi, ta zauna daf da Hajiya Inna ta rike hannayen ta , hawayenta na zuba ta gefen kumatunta a raunane ta ce" Inna, dan Allah ki yi hakuri, in sha Allah komai zai daidaita kin ji Inna? Ama idan kika tsayar da shan magani da gannin likita Inna ciw

on tsanani zai yi, Inna idan ba rai ya bar gangar jiki ba'a tsayar da neman magani, bale ai Bama cire rai da rahamar Allah ko a cikin tsananin azaba muke, da ace an yarda an ci gaba da massage din nan Inna ina mai tabbatar maki cikin ikon Allah da yanzu ke

da kanki kike yiwa kanki komai saboda gayanan jijiyoyin sunna saki har sun saki na wuta da hannaye, wallahi da sosai an samu kuzari, Inna muna yaki bakin rai bakin fama ne fa, koda yanzu zamu mutu idan muka anfani kanmu da kanmu zamu fi jin dadi fiye da a

ce muna kwance ne munna jira, Inna babu abinda ke saurin kashe bawa irin tunani, damuwa da tashin hankali dan Allah Inna ki bani dama docternki ya ci gaba da zuwa ya bani kula da massage din in ringa maki a hankali har Allah ya bamu nasara a samu ki ringa

motsawa da kanki, dan Allah innnn"

Riko hannunta da Inna ta yi da dan karfi ya saka khadeeja dakatar da maganar da take yi tana dubanta a lokacin kuma suka jiyo Muryar aunty shareefat na fadin" Khaleesat je wajen kakan kurma idan baba na cen ki kirawo s

hi, kuma ki cema Mama b jikin Inna ne ya tashi"

A hankali Inna ta ce" Khadeeja....., Ba fa zan sha ba ki yi hakuri, in dai har babanku ba zai janye ba nima ba gudu, ba ja da baya!, idan na bar masa duniyar zai fi jin dadin nunawa jikansa sosaya, makauni

yar soyaya!"

Khadeeja hawayenta ya tsananta, kumatunta suka yi wani irin ja sai murza hannayen Hajiya Inna take yi tana jin kirjin ta na mugun bugawa da tarin tsoro da tashin hankalin abinda ke iya faruwa,

Ba'a wani dauki lokaci ba su baba Hamza suk

a shigo da AL'WALED, wanda zuwansa kennan, ya kasa hakura be a dole ya garzayo ya zo dan ya ga jikin khadeeja

Da kyar ya iya hakuri baba Hamza ya rigayeshi shiga dakin sannan ya shigo, cikin hanzari ya karaso inda khadeeja ke rike da hannayen Hajiya Inn

a tana murzawa a hankali a hankali ya duka gaban gadon ya hade hannayen duka biyu a cikin nasa, wato na khadeejar da na Hajiya innar a hankali yana murzawa, ta dubi khadeeja wace zubar hawayenta ke kokarin kasara dukkan kuzarin da ya shigo da shi

A hank

ali ya sake riƙe hannayen a tausashe bayan ya dauke idannuwansa daga cikin na khadeejar wace ya saukar mata da muguwar kasala da wani karin rauni a zuciyarta har ta kasa kallonsa tsai cikin idon, ya sauke kan fuskar Hajiya Inna a hankali ya furta" Ne yake

damun zuciyata ne? Me ya daga hankalin sarauniyar AL'WALED ne?"

HAJIA Inna dake jin Muryar baba Hamza na cewa docter ya zo yanzu yanzu ko me yake yi ya bari ya zo ta

ɗ

an daga Muryar ta daidai karfinta ta ce" Sai ya zo ya sakani a coma sannan ya dura min

maganin ta hanci, au bata baka sakona ba shareefat? Bata sanar da kai ba cewa nima na kiya ba? Alhaji to bari in sanar da kai, na rantse harshena ba zai dandani magani ba idan har baka janye maganar da ka yi shekarun da suka wuce a kan yaron nan da mahaif

iyarsa ba sai dai in mutu a haka!"

Gabansa ya yanke ya fadi, hakama gaban Al' Walid

Da sauri ya dubeta hankalinsa na neman tashi, khadeeja ta ja hannunta dan tana din fita domin babu kowa a daki sai su kadai, ama yana rike da hannun ya ki saki kuma g

ashi kamar za'a yi tashin hankalin da ya girmami kwakwalwarta

Jikin baba Hamza nan da nan ya dauki rawa yana duban ta ya ce" Ama ba nace kar a saki a min maganar nan ba? Me ya ha

ɗ

a maganar nan da rashin lafiyar ki? Me yasa zaki daga min hankali a kan ab

inda kika san ba zan taba dubawa ba?"

Aba ya'u dake falo sai baza riga yake yi yana dan karkatar da kai sai kuma ya dubi Hajiya Binta da aunty shareefat ta dakatar kasa kasa ya ce" To wai ba asibiti za'a Kaita bane? Khaleesat tace jikinta ne kuma sun yi

shiru a daka leko mana manan matar tsohon cen"

HAJIA Binta ta yi murmushi ta nufi coridor din a lokacin da Hajiya Inna ta ce" HAKANE, babu wani abu mai mahimmanci sai maganar lafiyata? Hamza ba zan sha din ba!"

Da karfi AL'WALED ya jimke hannayensu

, yana fitar da idannuwansa yana duban Hajiya a hankali ya furta" Innata "

HAJIA Inna ta Dube shi ta dauke kanta a lokacin da ran baba Hamza ya sake

ɓ

aci ya nunota da yatsa ya ce" Nine zaki kama sunnana gatsau ki ce ba zaki yi din ba? Nine zaki yiwa ras

hin kunya a kan gaskiya ta? To shikenan kar ki sha maganin, nace shikenan ki yi yadda kika zaba!" Daga haka ya juya yana jefa kaffafuwansa da kyar idannuwansa na neman rufewa ya fito corridor a nan HAJIA Binta ta dauki salalami saboda yadda ya kusa makuwa

da kasa da kyar ya rike garu

Da sauri ta nufo shi ya daga mata hannu ya ce" kar ki saki ki tabani, ba dai du bakinku daya ba? Ki je ki ce mata kar ta sha maganin sai me, nace sai me? Na rasa gogo da malam ma na rayu rasssss gani? Babu abinda zai sameni

ku je ku yi yadda kuke so, ba zan janye kudurina ba!"

A dole AL'WALED ya mike bayan ya sassauta musu jimkar da ya musu ya dan duko ya kama hannun Hajiya a hankali ya dora a gefen fuskarsa ya dan shafa Muryarsa kasa kasa sosai ya ce" Idan kika yarda kika

min wasa da lafiyar ki, Nine zaki rasa Inna........ za'a maki abinda kike so, ama ki ga docter, zai zo yanzu idan ya bada magani ki sha shi"

HAJIA Inna ta turo baki tana dauke kai, ya bita da kallo cike da mamakin fushinta na yau, tabbas HAJIA Inna na

cikin mutane masu sassaucin da ya sani a duniya wa'inda suka yi ƙaranci a rayuwarmu ta yanzu.

A hankali ya dubi Khadeeja da kanta ke kasa, fuskarta ya talabo wanda hakan ya sa ta dago idannuwanta da sauri ta saka duban ta a cikin nasa

Idannuwansa ya

lumshe kasa kasa ya furta" A sassauta min, dan Allah a sassauta min hukuncina"

Hawayen da ya cika idannuwanta ya sake balewa, a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya hade hannunta da na Hajiya kasa kasa ya furta" ina zuwa"

domin Muryar Alhaji ya'u ce sama

sama yana fadin" kai, innalilahi kai meye wai, bude idon bana son lumshe lumshen nan haka kaji ke yi su cuci mutun sai dai ka shafa ka ga sun bar duniyar, ka ga bude min idannuwanka, wai meye? Lafiya lafiya muka rabu da kai fa, waye ya taba min uba?"

Ya f

ada da karaji saboda irin yadda Alhaji Hamza ke shasheka kamar mai cutar athma

Alhaji Hamza Muryarsa na rawa ya rike hannun elhaji ya'u ya ce" wai ba zata sha magani ba saboda matar da ta kashe mata d'anta, wai ba zata sha magani ba bayan ciwonta ya tas

hi, mu tafi, mu yi tafiyarmu, kaini wajen Usainar larabawa in yi zamana a cen"

Talabarsa aba yayi hankalinsa na neman tashi ya ce" Kai ina, lumshe lumshen nan ne bana so, wace ba zata sha maganin ba, sai ta sha ko wacece Ni za'a dagawa hankali a sa uban

a ya ringa lumshewa?, ka ga ringesa a nan in Shiga in ba wace ta ki shan maganin maganin ta sha in fito mu yi tafiyarmu, nima ba zan Barka ba kar a kashe min kai a min asara ina dalili!"

Yana aniyar ringesar da baba Hamza AL'WALED ya karaso ya tsaya y

ana kallonsu kafin ya gyada kai yana tabe baki ya karaso ya rike hannun aba dake zarro ido ya ce"

07/12/2024, 17:27 - samiraharounayacouba: Ta fice a dakin ta nemi sauka kasa, domin ta sakawa ranta in dai bai dakatar da ita ba zata tafi ta yi kwonciyarta

wajen HAJIA Inna hankali kwonce ne, idan har zai iya yaki da zuciyarsa har ya bude baki yace wai ya tsayawa mahaifiyarsa dukkan bukatunta a tunaninsa bukatun nan na yau da gobe ne ka

ɗ

ai uwa keda bukata a wajen d'a? To kuwa zata nuna masa itama aiki irin na

yarinya da danyen kai irin na y'ar ya'u!

Shi da kansa bai gane cewa bin bayan yarinyar nan yayi ba sai da ya riko hannunta ya dauko ta daga kokarin saukar da take yi daga dwstr ya koma daki da ita ya zaunar da ita ba sai da ya saka idannuwansa a cikin

idannuwanta da ta yiwa kalar tana daf da fashewa da kuka ya fahimta

Ido ya dan zarro mata bayan ya yi mata nuni da hannunsa ya ce" kar ki soma, kar ki saki hawayen nan su zubo"

Kai ta gyada sai kuma ta fashe masa da kuka ta shige kirjinsa tana matso

kwalar dole a shagwabe tana furta" ba zan bari su zubo ba hawayen, ba zan bari ba, AM sorry elhaji karamihhhhhhhhhhhhhh"

Gaba daya neman fita a hayacinsa yayi, rikicewa ya nemi yi, du irin girman shekarunsa da tunanin cewa a yanzu a duniya babu, karya n

e, ba'a yi ba ba za'a yi ba irin abin nan, gayanan yana samunsa ba tare da shi kansa ya fahimta ba

A birkice ya dago fuskarta ya share fuskar ya mika hannunsa ya janyo wayar tasa a hankali ya rubuta numbar mahaifiyarsa bai ko dubi lokaci ba ya aika kira

sannan ya saka handsfree ya ajiye wayar a tafin hannunta

RINGIN daya jal wayar ta yi aka daga, sai dai yau ba'a fara yin magana ba sai saurarawa da aka yi ana jira a ji maganar mutun

Da ido khadeeja bayan ta langwabar da kanta ta masa alamun yayi Ma

gana mana??

A hankali ya sauke jajayen idannuwansa a kan wayar, sai kuma ya sake duban ta, yadda ka san itace ke rike da wani abu da zai saka shi yin magana , tana sake langwabar da kanta ya budi baki a hankali ya furta " Asalamu alaikum"

Zumbur ta m

ike daga kwoncen da take a gadon alfarmar dake dakinta, a hankali ta furta" Wa alaika salam, gudaliya......, kai ne? Ya Allah, ya Allah......."

Sai kuma ta yi dif, da sauri ta furta " kaine ka yi kirana? Kai da kanka? Kana ina? Baka da lafiya ne? Wani a

bu ya sameka ne? Ina kake ne? Ina baba ne? Ina Hajiya Inna? Ina matarka? Kowa lafiya dai ko? Ina mamanka karama? Gudali kana ji na?"

A hankali ya lumshe idannuwansa, sai kuma ya mike da sauri ya fice a dakin gaba daya

Da ido ta raka shi rike da wayar

a hannunta, ga maman sai hello hello take yi

A hankali ta furta" Alhamdulilah Mama, lafiyarsa kalau, yaya jikin ki?"

Shiru ne ya wanzu a wajen na dan lokaci jin Muryar mace

A hankali Mama ta ce" Alhamdulilah,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login