Showing 9001 words to 12000 words out of 137995 words
tace,
"Ah, ah."
"Zan iya zuwa?" Ya tambaya.
"Yes pls," ta fa
ɗ
a da sauri, hawaye na sauƙa a idanunta.
"Okay," kawai ya fa
ɗ
a kafin ya katse wayar. Kifa kanta tayi a wurin, ta kama kuka.
Ƙ
arar wayarta ne ya dawo da ita hayyacinta. Ta j
anyo wayar tana jan hanci ta
ɗ
aga.
"I'm outside."
Gya
ɗ
a kai tayi kamar yana kallonta ta katse wayar. Sai da ta wanke fuskarta a toilet wanda bai
ɓ
oye kumburin idanunta ba kafin ta fito. A hankali, without making any sound da zai sa a san ta fita, ta
sauƙa ƙasa kafin ta bu
ɗ
e ƙofar a hankali ta fita da sauri. Yana tsaye jikin motarsa, ta hangoshi da rigar sanyi a jikinsa, hannayensa a aljihunsa. Har ta ƙaraso yana kallonta, ta tsaya
ɗ
an nesa ka
ɗ
an tana kallonsa.
"U sneaked out didn't u?" Ya fa
ɗ
a yana
bu
ɗ
e mata gaban motar. Shiga tayi ta zauna ba tare da ta amsa tambayarsa ba. Ya zagaya ya shigo motar, cikin motar
ɗ
umi sosai, jinginar da kansa yayi da kujera yana kallonta.
"Tell me," ya fa
ɗ
a yana kallonta.
"Ni bana son maganar," ta fa
ɗ
a tana jan
hanci, saboda har lokacin danne kukan kawai take.
"Okay..." ya fa
ɗ
a yana kallonta.
Juyawa tayi tana kallon window. Jin ya tada motar yasa ta juyo da sauri tana kallonsa. Bai kalleta ba sai driving da ya fara a hankali har suka bar street
ɗ
in. Maida k
anta tayi ta cigaba da kallon waje tana sauƙe ajiyar zuciya.
Bata san lokacin da suka
ɗ
auka ba suna shawagi tsakanin layuka silently, babu mai cewa komai. Gyara zamanta tayi tana kallonsa, ganin sai wandering suke tsakanin streets. Katse shirun tayi, ta
yi clearing throat
ɗ
inta tana kallonsa.
"Kaima ai
ɗ
an Nigeria ne koh?" Ɗan kallonta yayi yana cigaba da driving
ɗ
in ganin ta bar kukan gaba
ɗ
aya and she's ready to talk now.
"Kin ta
ɓ
a ganin wanda ba
ɗ
an Nigeria ba yana Hausa?"
"Eh mana, ai akwai wa
ɗ
anda koya kawai sukayi."
Gya
ɗ
a kai yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma yace, "Kina da saƙon da za'a kai miki can ne?"
Dariya tayi tana gyara zamanta ta jinginar da kanta da kujeran tana kallonsa.
"Ai nima zanje during summer."
"Da gaske?"
"Eh, har Dad ya barni ma, zanje in ga Mamie na." Ɗan kallonta yayi. Dis is the first time yake sanin bata tare da mamanta, now komai makes sense shiyasa kullum take Sad.
"By then ai ure a big girl, lokacin kun gama high school sai kuma college." Dariya
tayi tana kallonsa.
"Wani gari a Nigeria?"
"Abuja," ta fa
ɗ
a tana murmushi.
"Sau biyu ka
ɗ
ai fa na ta
ɓ
a zuwa," ta sake fa
ɗ
a tana kallonsa.
"Ur Dad is not from Nigeria?"
Ɗ
an shiru tayi kafin a hankali tace,
"He's from Nigeria also, amma ya
ɗ
a
ɗ
e bai je ba."
"Okay." Ya fa
ɗ
a yana parking a ƙofar gidansu ganin kamar shes now alright kuma dare yana ƙara yi. Wayarsa da tayi ringing sau karo na ba adadi yanzu ya
ɗ
auka yana duba mai kirannasa, silencing wayar yayi ya ajiye ya juyo ya kalleta gani
n kallonshi take, yasa yace,
"In kinje kenan yaushe zaki dawo?"
"Just three weeks maybe." Gya
ɗ
a kai yayi dai dai ana sake kiran wayarsa, ta kalli wayar sannan ta kalleshi. "Ka
ɗ
auka mana" bai ce mata komai ba sai ma silencing kiran da ya sake yi.
Bu
ɗ
e motar tayi ta fita ta tsaya a dai-dai window tana kallonsa.
"Good night, and tnk u for d ride."
Yana kallonta har ta shige cikin gidan kafin ya
ɗ
aga kiran da ake sake masa. Shiru yayi yana sauraron abinda ake fa
ɗ
a.
"Sorry bana kusa da wayarne
," ya fa
ɗ
a a hankali yana barin layin.
Final exams
ɗ
insu da ke ƙaratowa sosai ya sa ta mayarda hankalinta kan karatunta. Gaba
ɗ
aya tayi busy da karatu, zuwa yanzu sanyi ya fara raguwa, hunturu ya soma wucewa. Wanda a wannan lokacin shirye-shiryen zuwanta
Nigeria ya kankama. Immediately after graduation
ɗ
insu wato walimar gama high school zata wuce Nigeria. Har ji take kamar ta janyo lokacin. Sun rage ha
ɗ
uwa da Sa
ɗ
iq sai dai suna waya yana sake kwantar mata da hankali akan exams da zasu fara soon. Shima ai
ki yasa hes not much available yanzu.
A haka suka fara exams
ɗ
insu na ƙarshe a matsayin
ɗ
aliban St Emerys.
Ranar da suka rubuta paper
ɗ
insu na ƙarshe, tana miƙa paper
ɗ
inta ta fito cike da murna. Linda da ta rigata fitowa tana kallonta da dariya tace
,
"Ya kika ji Bio
ɗ
innan?"
"Worst dan Lit, kinsan manta enzyme chart nayi," ta fa
ɗ
a tana jingina da bango.
"To ni ƙwaƙwalwata ina ga narkewa tayi." Ƙyalƙyakewa da dariya suka yi. Linda tana cin sandwich
ɗ
in hannunta tace,
"We will pass, ni kain
a ma nake tunani kekam nasan dama ull pass kamar yadda kika saba." Duk da turanci suke maganganun da accent
ɗ
insu da bazaka ce ma Na'ima najin wani yare wai Hausa ba.
Ranar graduation
ɗ
insu sosai suka yi kyau cikin graduation gown
ɗ
insu. Na'ima ta gyara
hular kanta tana
ɗ
aukan enough selfies da zata tura ma Mamienta. Ɗaga kai tayi ta kalli Dad da ke zaune a row na uku cikin iyaye masu yawa da suka zo dan ʼyaʼyansu. Ga Mummy a gefensa tana danna wayarta. Murmushi ya mata ya
ɗ
aga wayarsa yana
ɗ
aukarta daga
inda yake zaune. Itama murmushin kawai tayi tana gyara zamanta kusa da Linda. Sunayensu aka yi ta kira ana basu takardar kammala secondary tare da hotuna. Har aka kira sunanta cikin speaker
ɗ
in,
"Na'ima Mustapha."
Miƙewa tayi walking across the stag
e cike da nutsuwa da alfahari da kanta. Gurin ya
ɗ
auki tafi kamar yadda aka yi ma sauran
ɗ
alibai. Hannu biyu ta saka ta kar
ɓ
i takardar shaidar kammala high school
ɗ
inta a St Emerys. Idanunta na cikowa da hawaye ta kalli camera murmushi
ɗ
auke a fuskarta, ka
fin ta sauƙo ta koma wajen zamanta.
Bayan an gama taro, sosai Linda ta rungumeta tana kuka, mascara da ta saka a idanunta na
ɓ
ata mata gefen idanu da hawaye.
"I'll miss you, da duka stupid stupid poems
ɗ
inki." Dariya suka yi tare.
Na'ima ta
ɗ
aga h
annunta tana kallon Linda,
"Dont worry, I will see you in college, plus I'm going to Nigeria this summer, ill send u lots of poems daga can."
Haka suka rabu suna kewar juna, suka dawo gida tare da su Dad. A wani gefe na zuciyarta, tana mamakin dali
lin da ya hana Sa
ɗ
iq zuwa, amma sai kawai ta kawar da tunanin ta maida hankali kan shirye-shiryen tafiyarta zuwa Nigeria da zata yi cikin sati mai zuwa.
A gidan ma sun yi murnar kammala makarantarta,duk da ba wai sun yi wani babban biki bane, bata damu
ba, domin gaba
ɗ
aya hankalinta ya yi Nigeria wajen Maminta, wadda ta cika ta da hotunan graduation ta WhatsApp, ita kuma a ƙarƙashin ko wane hoto bata rasa abin cewa.
Washegari tana zaune a
ɗ
akinta, tana sorting boxes
ɗ
inta da jakunkunan tafiyarta. Duk t
a wargaza komai a
ɗ
akin, jakunkunan kyaututtuka da tayi wa Mami, Fauza, har da Aryan duk suna ajiye a gefe. Gyalen da ta
ɗ
aura kamar
ɗ
ankwali ta sake gyarawa, ganin yana shirin suncewa, tana ci gaba da shirya kayanta daki-daki, kamar gobe ne tafiyar.
Ƙ
a
rar shigowar saƙo ya sa ta ajiye well ironed shirt dake hannunta, ta ƙarasa ta
ɗ
auki wayarta a kan gado.
"Have u started parking already?" Ta ga saƙonsa a allon wayar, tura baki tayi kafin ta bu
ɗ
e saƙon nasa.
"Ba ruwana da kai," ta tura masa, tana ƙa
rasawa ta ci gaba da abinda take yi.
"I'm sorry Ni'ima, bana garinne, shiyasa. You know I would've never missed ur grad."
"Hmm, kana ina?"
"Somewhere." Ta yi murmushi ta bashi amsa.
Haka suka ci gaba da hira tana aikinta har ta gama tsaf, duk d
a ta san ba lallai ta gama
ɗ
in ba kenan, domin zuwa ranar tafiyarta ta san zata sake samun abin da zata so ta tafi da shi. A haka har ranar tafiyarta yayi.
Kamar yadda aka tsara, jirgin ƙarfe 7:30 na dare zata bi daga JFK International Airport, New Yor
k, zuwa Murtala Muhammad International Airport, Lagos.
Tun ƙarfe 4:30 na yamma suka tafi filin jirgi, har yanzu akwai sanyi da ƙanƙara a garin, tana janye da akwatinta ta nufi check-in counter
ɗ
in. Bayan sun yi sallama da su Dad, hannunta
ɗ
aya riƙe da p
assport
ɗ
inta da takardar tafiyarta.
"Ke ka
ɗ
ai zakiyi tafiyar?" agent
ɗ
in ta tambaya da fara'a a fuskarta.
Gya
ɗ
a mata kai tayi.
Matar tayi murmushi, "You'll be fine."
Bayan duk wani bincike na tsaro ta samu guri ta zauna a kujerarta dake jikin
window a cikin jirgin, tana ajiye journal
ɗ
inta da hoodie
ɗ
inta kusa da ita.
Tafiyar za ta
ɗ
auki kimanin awanni 16 da layover guda
ɗ
aya a Paris na awa
ɗ
aya da rabi kafin a ci gaba da tafiyar; awa 7
ɗ
in farko zasu tsaya a Paris bayan sun ketare kogin Atl
antic, sai kuma awa 6 da minti arba'in daga Paris zuwa Lagos, Nigeria.
Jirgin na tashi, ta jinginar da kanta tana kallon taga, tana kallon birnin New York yana
ɓ
acewa a ƙarƙashin gajimare. Wata ma'aikaciyar jirgi ta kawo mata bargo da headphone, ta kar
ɓ
a tana kallon matar dake gefenta wacce ke bu
ɗ
e gum.
Ƙ
arfe tara aka kawo dinner, pasta
ɗ
in da tasa aka kawo mata ma ba ta wani ci sosai ba, ta zuba ma map
ɗ
in flight
ɗ
in idanunta wanda yake nuna suna nufar tekun Atlantic.
Har tsakiyar dare kafin bacci
ya
ɗ
auke ta, ta ha
ɗ
e gwuiwowinta ta jinginar da kanta a taga.
Ko da ta farka sama yayi jaa, dai-dai lokacin suka sauka a Paris. Sun
ɗ
an huta, tayi amfani da wifi
ɗ
in Airport
ɗ
in ta tura ma su Dad da Mamie saƙo cewa sun sauka lafiya a Paris kafin ta taf
i neman abin ci kafin jirginsu ya tashi.
Lokacin da suka iso Lagos ƙarfe 3:40pm agogon Nigeria, bata da
ɗ
e a Airport
ɗ
in ba, domin tana da connecting domestic flight daga Lagos zuwa Abuja, wanda yake tafiyar awa
ɗ
aya da rabi daga filin jirgin Murtala Muh
ammad.
Jirgin ƙarfe 7:00 zata bi zuwa Abuja, a wani café ta zauna cikin filin jirgin tana jiran lokaci.
Ta bu
ɗ
e ruwan goran hanunta ta kur
ɓ
a tana jiran lokaci da tunanin in few hours zata ga Maminta.
Ƙ
arfe 7:00 dai-dai na dare jirginsu ya tashi da
ga Lagos zuwa Abuja, ƙarfe 8:35 suka sauka a Abuja. Ta ji jiki sosai, tayi miƙa tana sauka a jirgin cike da zumu
ɗ
in ganin Maminta.
#Maimoon
09041426598
[8/14, 11:23 PM] Maimoo 3: https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
RUƊAƊƊUN ZUƘ
ATA (TANGLED HEARTS)
Yota
Barka da Sallah, Allah ya maimaita mana, to all my amazing readers how body?
😂
hope uve recovered from work overload da kuma meat overload
😂
, kallonku nake dai ba wanda ya bani barka da Sallah, kun sha kyau abinku some tsab
ar kyau even the ram paused to admire ur beauty before becoming stew
😂🤭
To now Sallah is over, so back to reading our story
🌝😌
Welcome back and stay tuned lovelies
❤
️
❤
️
❤
️
Chapter 6: A place called Home
Tana fitowa daga terminal
ɗ
in wani
ɗ
umi ne ya mamayeta, duk da dare ne amma kamar rana, haske ne darr ko ina a filin jirgin, ta juya ta kalli ko ina, kowa is busy with what hes doing, gyara gyalenta tayi tana bin ko ina da kallo kamar mai neman wani abu.
Sanye da Abaya navy blue color, k
anta yane da babban mayafin abayan ta hango Maminta, a tsaye just outside the terminal, Kyakkyawar fuskarta
ɗ
auke da
murmushi, duk wani murna da
ɗ
oki da yadda ta tsara yanda zatayi idan taga Mami sai duk suka yi evaporating.
Ha
ɗ
a idon da sukayi ya sa N
a'ima tahowa da sauri sai kuma ta sa gudu, shigewa jikin Mami tayi ta maƙalƙaleta ta fashe da kuka, Mami tasa hannu tana shafa kanta a hankali har sai da tayi shiru kafin ta
ɗ
ago ta daga jikinta tana ƙare mata kallo.
"Ke bakya girma ne?" Mami ta fa
ɗ
a ta
na share mata hawayen fuskarta
Sake shigewa jikin Mami tayi ba tareda tayi magana sai ajiyar zuciyar kuka da take sauƙewa a jikin Mami.
"Okay zamu kwana anan ne?" Mami ta fa
ɗ
a tana dariya, haka ya saka Na'ima saketa tana dariyar itama idanunta jiƙ
e da hawaye.
drivern Mami ne ya taya ta da luggage
ɗ
inta har mota yana mata sannu da hanya, ita kam tana maƙale jikin Mami har suka iso Gidan Mami dake Maitama.
Tunda suka iso Mami ke ta ina zata saka ina zata ajiye da ita, varieties of Nigerian Fo
od babu wanda bata tarar ba, bayan tayi wanka a
ɗ
akinta da Mami ta kaita a sama ta shirya ta sauƙo tana jin wani farinciki marar misaltuwa despite the jetlag, sai da suka ci abinci tare da Mami da ta tabbatar ta
ɗ
an
ɗ
ana duk abinda aka girka dominta, sanna
n suka dawo babban palour
ɗ
in gidan suka zauna, abinda Na'ima ta manta ne ka
ɗ
ai bata fa
ɗ
a ma Mami ba, duk da matuƙar gajiyar dake tattare da ita, amma kewan Mami overcomed it, ita dai binta kawai take da kallo tana murmishi.
Na'ima ta
ɗ
ago kanta daga f
ruit
ɗ
in da take sha tana kallon Mami tace
"Mami banga Big Daddy ba"
"Sai yanzu zaki tambayeshi?" Mami ta fa
ɗ
a tana harararta
Dariya tayi kamar ba ita ba tana zare fork
ɗ
in da ta kai kankana bakinta
Mami tace " yayi tafiya but he’ll be retur
ning tomorrow insha Allah"
"Allah ya kaimu" ta fa
ɗ
a tana ajiye bowl
ɗ
in kan center table, hamma tayi da miƙa da yasa Mami ta kalleta
"Ure tired, u should rest" gya
ɗ
a ma Mami kai tayi dan tana buƙatar hutun.
Har
ɗ
akinta Mami ta rakata sai da ta w
anke bakinta ta dawo sannan ta zo ta haura gadon tana kallon Mami dake zaune gefen gadon, Mami ta gyara mata duvet tana fa
ɗ
in
"Fauza da aryan sai dai su ganki da safe kamar daga sama they'll be so suprised"
Tana gyara kwanciyarta a kan lallausan za
nin gadon tace
"wallahi kuwa, finally the'll get to see me ido da ido not on video calls"
Kashe mata wuta Mami tayi bayan ta sata tayi Addu'a, ta ja mata ƙofarta.
Sai da ta fara duba twins
ɗ
inta da sun jima da bacci a
ɗ
akinsu, kafin ta wuce
ɗ
aki
nta tana dialing number Big Daddy ganin missed calls
ɗ
insa da bata lura da su ba tun
ɗ
azu.
Washegari ko da Mami ta zo tashinta da asuba ta tarar har ta tashi tana ban
ɗ
aki, haka yasa ta koma
ɗ
akinta dan yin sallah.
Tana zaune akan sallaya Na'iman ta
yi sallama a hankali ta shigo
ɗ
akinnata da hijab a jikinta da tayi sallah, ta zauna saman kujera tana lumshe idanunta, Mami dake azkar a hankali ta kalleta, azkar
ɗ
in itama ta fara yi tana lumshe idanunta har suka gama kafin ta taso ta kwanta akan daddumar
Mamin ta kwantar da kanta a ƙafafunta
" Good Morning Ma," shafa kanta tayi
"Morning sweetheart ya kika tashi?"
"Lfy Mami" ta fa
ɗ
a tana lumshe idanunta, ganin bacci ne ya fara ƙoƙarin
ɗ
aukanta a haka yasa Mami na cigaba da shafa kanta tace
"Na'ima tashi ki hau kan gado ki kwanta"
bu
ɗ
e idanunta tayi kafin ta miƙe a hankali, zare hijab
ɗ
in tayi ta haura gadon Mami ta kwanta, Mami ta bita da kallo tana jan chazbah
ɗ
in hannunta, nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.
Ƙ
arfe 11:00 dai-dai
na safe ta bu
ɗ
e idanunta a hankali tana kallon 2 cute twins da ke kan gadon dabb da ita suna kallonta, Namijin da yafi wayo ya kalli twin sister
ɗ
insa dake kallon Na'iman kafin ya fa
ɗ
a kan Na'iman kaman dama jira yake ta bu
ɗ
e ido, ganin haka itama macen ta
fa
ɗ
a kansu suna ƙyalƙyala dariya,
"Wayyo, Aryan..,Fauza.., do u guys want to break my arm, baku ga kuna da nauyi ba"
Ta fa
ɗ
a tana miƙewa zaune da su a jikinta
"Anty Na'ima from the video call" Aryan ya fa
ɗ
a yana ta
ɓ
a