Showing 30001 words to 33000 words out of 145491 words
yay alamar tunani, sai kuma ya dubeta yana cewa, “Ƙwarai anyi haka doctor, sai dai kuma an samu akasi ai a ranar bamuyi mata ba saboda yanayin mahaifarta mukace bayan kwana biyu su dawo sannan ta huta saboda sun matsa a sallameta....”
A zafafe
Alh. Sulaiman ya yunƙuro zaiyi magana Dr Olivia ta girgiza masa kanta. Ita ta ƙara fuskantar Nurse
ɗ
in da fa
ɗ
in, “Amma miyasa baka sanar min ba? Sannan da baki ka fa
ɗ
a musu ko'a rubuce?”.
Kai tsaye yace, “Nazo sanar miki sai na samu kin fita. A ru
buce kuma muka basu gaskiya, kuma ita muka bamawa ma a hannunta ai”.
“Okay zaka iya tafiya”.
Ɗan rissinawar girmamawa yay tare da ajiye mata file
ɗ
in ya fice. Yana rufe ƙofar ya saki murmushin mugunta, a zuciyarsa yace (Ƴan iska ai dama nayi alƙawa
rin saina ku
ɓ
utar da yarinyar nan. Wankin ciki kuma ina kan sani naƙi yinsa bayan nai mata allurar tsaida jini da sauri ta yanda cikin bazai fita ba. Ina Musulmi baƙar fata bazan ta
ɓ
a bari a cutar da wani musulmi ba in sha ALLAHU in dai ina asibitin nan. T
unda har naji hirarku dama nai alƙawarin taimaka mata dan na fahimci zaku cutar da ita ne bada saninta ba).
A ciki kuwa shiru Office
ɗ
in ya
ɗ
auka. Da ga Alh. Sulaiman har Dr Olivia kowa ya kasa cewa komai. Sai can ta nisa da ƙyar ta katse shirun
da fa
ɗ
in, “Yanzu ka yarda na maka aikinka ko? Sannan babu kuskurena a ciki na turata inda za'a mata wankin ciki, kaga kuma sun basu damar su dawo amma baku dawo ba, hakan na nufin yarinyar bata son rasa cikinne ko wani dalili daban.....”
Cikin wani
irin baƙin ciki da zafin zuciya Alh. Sulaiman ya furta, “Dalilinta na banza. Ciki kuma dolene a zubar da shi”.
“Gaskiya bazai yiwu ba, inba haka ba kuwa komai zai iya faruwa kamar yanda na fa
ɗ
ama Mrs Garko. Ciki kuwa harda rasa ranta. Ni kuma bazan
iya gangancin aikata haka ba a wannan ga
ɓ
ar dan zai zama taka doka, cikin wata biyar da kusan sati biyu, ta
ɓ
ashi da niyyar zubarwa ai kowama yasan ganganci ne. Kawai ku barta ta haihu tunda tana son abinta”.
“Ashe zan kashe yarinyar nan kuwa!!” Alh
. Sulaiman ya fa
ɗ
a a wani irin kausashe jikinsa har ƙyarma yakeyi. Ita Dr Olivia ma duk sai tsoro ya kamata. Nurse
ɗ
in nan ne yay knocking ƙofar ya shigo, cikin girmamawa ya aje wani file a gaban Dr Olivia a yanayin dafa tebirinta, hakan ya bashi damar zar
e ƙaramar wayar da ya ajiye batare da sun lura ba saboda rufewa da idanunsu sukayi. Daga haka yay ficewarsa yana
ɗ
an murmushi....
Fitarsa kusan da mintuna biyar sai ga Alh. Sulaiman ya fito ransa a matuƙar
ɓ
ace tamkar zai kifa a cikin sassarfa. N
urse
ɗ
in nan yay murmushi da biyo bayansa da sauri-sauri. Sun
ɗ
an yi nisa a doguwar
barandar yaji kamar ana binsa a baya. Jiyowa yay cikin sauri sai sukai arba da Nurse
ɗ
in nan. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru sakamakon tare numfashinsa da Nurse
ɗ
in
yay cikin harshen Hausa. Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Alh. Sulaiman, duk da kuwa hakan ba wani abun ai mamakin bane kasancewar matashin saurayin baƙin fata. Amma gaskiya bai tsammanin jin Hausa a bakinsa ba. “Sunana Usman B Sa'eed. Bahaushe haihuw
ar Nigeria girman Canada. Na biyoka ne nan saboda jin ina son taimakonka matsayin ƙabilata kuma addinina.”
Kamar Alh. Sulaiman zai ya
ɓ
a masa magana sai kuma dai ya ha
ɗ
iye, yaga ya kamata yaji ƙarshen zancen. Usman ya cigaba da fa
ɗ
in, “Dr Olivia bazat
a baka ha
ɗ
in kai ba dama, dan kasan turawan nan da son bin ƙa'idar abu. Sannan gaskiya ta fa
ɗ
a in har ta aikata sake zubda cikin aka samu matsala to akwai babbar ƙura da ku kanku zata iya shafarku. Karka manta anan sun san hakkin
ɗ
an adam ba irin yankuna m
u na Africa bane ba da zaka iya yin komai ba komai. Na fahimci cikin irin wanda mu mutanen Hausawa muke gudune wato na shege shiyyasa kuka matsu ku zubar. Dan haka zan taimaka muku ta yanda zaku salwantar da shi cikin sauƙi batare da kowa ya fahimta ba. Sa
i dai zai kai haihuwa, amma za'a haifesa ba'a raye ba, dan zan dinga mata allurar da yaron zaita ru
ɓ
ewa a cikin nata batare da an fargaba itama kanta bazata fahimta ba dan na gane bata so a zubar da shi shiyyasa taƙi dawowa wankin ciki”.
Sosai Da
ddy yake nazartarsa, amma abin mamaki ya kasa hango yaudara a tattare da shi. Dan Usman irin mutanen nan ne masu maida abu serious ka kasa fahimtar gabansu da bayansu. Kai Daddy ya
ɗ
an jinjina kawai tare da miƙa masa hannu. “Zan iya baka number ka sameni a
gida bayan nayi shawara”.
“A babu damuwa ai Alhaji”. Cewar Usman cikin dakewa. A zuciyarsa kam sai dannama Alh. Sulaiman zagi yake kala-kala. Dan yana ayyana sune masu fita ƙasashen waje suna zubar mana da mutunci ana kallonmu wawaye creminal. Ya b
ashi number wayan suka rabu, da ga haka ya fice a asibiti ya samu taxi ya shiga dan anan baida lasisin tuƙi. Maimakon gida sai ya nufi can wani joint a bayan gari ka
ɗ
an, wajene na sheƙe aya matuƙa dan mata na yawo ne babu sutura. A can ya samu ya huta zuc
iyarsa ta huce da samun damar yin tunani akan Usman Nurse. Ya fahimci wannan ita ka
ɗ
aice mafita kam a garesa. Dan yana son tabbas shegen cikin nan ya zube saboda shine sharar fage na farko da yake son ƙuntata rayuwar Smart da ita. Kafin ya tafi matakin far
ko akan Daddy da Smart
ɗ
in harma da Uncle Yousuf, dan akan Lulu yake son ya musu tarko su ukun ta yadda zasu koma su kansu basu yarda da kansu ba. Wannan shine sabon plan
ɗ
in da ya canja akan kowanne su. Tajuddeen kuwa lokaci yayi da zai ka
ɗ
a kansa ya bar
Canada. Dan ya gama masa aikin da yake so, dama amfani kawai yake da yaron nasa a matakin dalillai biyu. Na farko manufarsa tun fil azal. Na biyu halin ciwo da yake ciki akan yarinyar shiyyasa yake biye masa kamar gaske dan ya samu kwanciyar hankalinsa. Da
n gaskiya yana ƙaunar yaron fiye da sauran ƴaƴansa. Saboda kasancewar sa namiji
ɗ
aya tilo a cikinsu. Yana ganin bayan ya tsigesa mataki na biyu da zaibi a kansa shine bin shawarar amaryarsa akan ha
ɗ
ashi aure da ƙanwarta, dan ya gamsu da bayanin datai masa
ya kuma
ɗ
auki shawararta. Sannan ita kanta Dada lokacin gama nata aikin yayi.
Koda ya koma gidan sai bai cewa Dada komai ba koda ta tambayesa ya batun zuwa asibiti. Sai da ta ƙara maimaita masane ya ce ta saurareshi yana nazari ne. Badan Dada taso
ba dole tai shiru ganin ya ha
ɗ
e fuska. Ummita dake la
ɓ
e tana jinsu, sai dai bata so jin Alh. Sulaiman yay shiru ba. A lokacin da duk wannan cakwakiya ke faruwa Smart na can cikin farin
cikin samun nasarar cin ƙwallon da sukai tsakaninsu da abokan hamayyars
u ƴan Model Unitet a wannan ranar......
Bayan kwanaki biyu Alh. Sulaiman ya kammala yanke hukunci akan zancen Usman Nurse, sai dai bai nemesa ba sai da ya saka akai masa bincike a kansa tsaf. Inda aka kawo masa bayanai akan tabbatar da cewar kara
tu ne ya kawo mahaifinsa ƙasar Canada, amma asalinsu ƴan Nigeria ne. Anan Usman ya girma dan yana da shekara kusan goma iyayen nasa suka dawo Canada, sai dai fa yana yawan zuwa ƙasar haihuwar tasa. Usman dai a zahirance baya jin magana sam, dan duk wani
ɗ
a
ni'u na turawan nan yana zubasu musamman neman mata, kuma kamar yanda yake a turai hakan ba komai ba suma iyayensa basu
ɗ
auke sa komai ba. Bai ta
ɓ
a aure ba amma yanada ilimi mai dan babban Nurse ne shi
ɗ
in. Wannan bayanai sun ƙawatar da Alh. Sulaiman, dan
ya nazarcesu tsaf da fahimtar su a yanda makauniyar zuciyarsa ta tabbatar masa. Abinda bai sani ba Usman yarone mai matsanancin kishin ƙasarsa da ma yankinsa na Africa har ma da addininsa duk da wa
ɗ
an nan rashin jin nashi. Wannan aƙidar tasa tasa ko kullum
yake cikin yawo tsakanin Nigeria Da Canada kamar wani
ɗ
an sama jannati. Dan ko aikin ma anan da ƙyar mahaifiyarsa ta samu ya yarda yakeyi, amma duk da haka sai da yaje ainahin ƙauyensu ya bu
ɗ
e wani ƙwarya-ƙwaryan asibiti ya zuba likitoci da ke aiki a ciki
n ku
ɗ
i ƙalilan wa marasa lafiya. Koda Alh. Sulaiman ya gama tattare abinda yake buƙata sai yay ma Dada wayo akan ta koma wajen Baba, ciki Lulu kuwa su barshi ta haifi abinta kawai tunda dai Dr Olivia ta tabbatar musu akwai matsala. Ba haka Dada taso ba, sa
i dai bata iyayima
ɗ
an nata musu, ganin kum
a ya dawo da passport
ɗ
in Lulun da Ummita ya basu ya sakata jin kwanciyar hankali, dan haka badan taso ba ta shirya ta koma wajen mijinta da al'amarin nata ya sashi fara tsarguwa shima. Sai dai baice mata komai ba
tunda ta ce masa wasu kaya zata duba a Canada
ɗ
in dama kafin ta wuce........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tu
ra anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚
𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐
𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
1
️
⃣
5
️
⃣
......Ko ka
ɗ
an Lulu bata nuna damuwa da tafiyar ta Dada ba duk da kuwa a ƙasan zuciyarta cinkushe yake matuƙa, amma plan
ɗ
insu ita da Ummita ya sakata dakewa abinta ta nuna k
omai ba komai har Dada ta wuce. Washe gari shima Tajuddeen mahaifin nasa ya janye ra'ayinsa ta hanyar tura sa Nigeria da saƙo. Ko ka
ɗ
an Tajuddeen bai kawo komai a ransa ba ganin shima Alh. Sulaiman
ɗ
in yayi shiri wai zai wuce ƙasar Brazil ne yin wani busin
ess, sai dai
ɗ
an nasa na wucewa yayo sau da baya. Sabon gurin daya shirya za'a kai masa su Lulu acan wani ƙauye ko yanki za'a kirashi ma ne oho ya wuce. Wajene tsibiri ne, dan a tsakkiyar wani irin makeken ruwa mara iyakar kallo tsibirin yake. Gidajene kaw
ai na masu zuwa hutawa a wajen da yawon bu
ɗ
e ido, sai jiragen ruwa ne kawai ke iya kaika cikin tsibirin. Wajen kam a kwai da
ɗ
in zama musamman ga wanda suka je hutawa,
zaka tabbatar da hakanne ne idan kaga yanda mutane ke nisha
ɗ
i musamman ma masoya da masu
ku
ɗ
i......
Kamar kullum yau ma bata fito ba har sai da Ummita ta kamma kimtsa gidan, yay tsaf abinsa sai tashin ƙamshi da
ɗ
umi mai ratsa
ɓ
argon jiki daya gauraye ko'ina. Wando da riga ne a jikinta marasa nauyi, dan haka matashi cikinta ya samu damar
fitowa
ɗ
as da shi. Yau gaba
ɗ
aya kasala takeji, dan da ƙyar ta iya fitowa dan yunwa data addaba mata ya sata fitowa ta samu abinda zata
ɗ
an ci. Kai tsaye kitchen ta nufa inda Ummita keta
ɓ
uruntun dama mata kununta, koda tai sallama kafin ma Ummita ta kai
ƙ
arshen amsawa ita harta isa ga freight, ruwa ta ciro mara sanyi ta sha, tana ajiye bottle
ɗ
in da sauran wanda ya rage ta nufi Ummita. Fuskarta da murmushi take fa
ɗ
in, “Har yanzu ƙarnin kifin nan da Dada tasa kika dafa mata a gidan nan ya ƙi fita wlhy Ummi
ta”.
Da mamaki Ummita ta ce, “Kai aunty dan dai baki so ne kawai, amma wlhy ni banjin komai sai ƙamshin fresheners a gidan nan.”
Cikin
ɗ
an yamutsa fuska da tsaki ta ce, “Wlhy Ummita yanzu ne dai bana so, amma da ai kafin na ci miki nama naci
kifi, sai dai yanzu na rasa miya ha
ɗ
ani da shi haka ko ƙamshinsa bana so”. Da dariya Ummita ta ce, “Aikin Unborn ne ai Aunty”. Shiru Lulu tai tana kallonta kamar mai nazari kosan tuna abu, abinda ke ƙoƙarin tuna kam nasa ne a zuciyarta ya zo mata. Tabbas
Aliyu bama yancin kifi kwata-kwata idan bata manta ba. A take ta ha
ɗ
e fuska kamar a
ɗ
an ƙufule ta ce, “Ni shikenan saboda wannan cikin duk abinda baya ci nima na daina ci koda ina sonshi, sannan abinda yake so dole sai na so shi kamar abin asiri?”.
“Wakenan Aunty?”.
Cewar Ummita cikin nuna mamakin furucin uwar
ɗ
akin nata. Sai dai maimakon bata amsa sai taga ta juya tama fice a falon tana
ɗ
an dafe kai. Bata kawo komai a ran nata ba game da dafe kan ta cigaba da zuba mata kunun gya
ɗ
ar a flaks
ɗ
in d
a ake zubawa. Ta kammala idonta ya sauka akan sauran ruwan da Lulu tasha ta ajiye, ta san da wahala ta sake shansa. Dan haka ta
ɗ
auka ta shanye ta jefa bottle
ɗ
in a shara sannan ta
ɗ
auki flaks
ɗ
in da ƙaramin kofi tabi bayan Lulu. Ɗan turus tai na mamakin g
aninta baje a kujera tana barci kamar ba yanzu ta baro ta a kitchen ba. Sai tai dariya da jin tausayin ta. Ta ajiye flaks
ɗ
in itama da nufin komawa kitchen ta gyara kayan datai amfani da su a aikin itama kanta ya sara, da sauri ta dafeshi tana mai ambatar
sunan ALLAH, jin hajijiya na neman yadda ta a ƙasa da bin bango ta fito falon itama, sai dai kafin ma ta kai ga kujera ta zube ƙasa, daga haka bata sake sanin ina hankalinta yake ba itama....
Duk abinda ke faruwa Alh. Sulaiman na kallo ta camera da
ya saka musu kamar yanda Ummita ta zarga dama, wata shegiyar dariyar basanci ya saki sai kuma ya gimtse fuska duk a lokaci guda. Wayarsa ya jawo a gefensa tare da shaƙar cocaine ya wani girgiza kan nasa da wani irin style na ƙwararrun ƴan cocaine sannan y
a kai wayar kunnensa. Cike da izza ya furta “Nan da awa
ɗ
aya ku tabbatar su da duk tarkacensu suna a gabana” da ga haka ya yanke kiran batare da jiran an bashi amsa ba da ga can...
Matuƙa hankalin Lulu da Ummita ya tashi a lokacin da suka farka da
ga nannauyan barcin da ya samesu suka ga kansu a inda ba'a nan suka kwanta ba. Cikin matsanancin firgici suke kallon juna kafin su miƙe duk a zabure su fara dube-duben inda suke
ɗ
in. Falo ne madaidaici sai dai akwai komai a cikinsa sai bedrooms guda
ɗ
aya
mai
ɗ
auke da gado biyu, sai kitchen. Ko ina a kulle yake ta hanyoyin waje sai dai suna iya hango
makeken ruwan daya zagaye ko'ina da ina ta cikin gilashi. Basu iya ganin mutanen da ke kai kawo balle iya jiyo hayaniya saboda gilashin manne da ginin bullet p
roof ne. Yunwar da Lulu keji dan a yanzu sam bata da jimirinta ya sata fara jin yuuu-yuuu kamar jiri zai yadda ta. Da sauri takai zaune cikin rawar murya tace, “Ummita yunwa”. Hankalin Ummita ya tashi matuƙa dan haka ta miƙe cikin rawar jiki ta fara dube-d
uben ko zata ga abinci, cikin aminci ALLAH ta ganshi an ajiye a gefe kan ƙaramin dining table mai kujera biyu. Ɗakko mata tayi, jikin Lulu har rawa yake wajen kar
ɓ
ar abincin ta fara turawa, duk da baya mata da
ɗ
i haka takeci ko zata samu nutsuwa. Tan kammal
awa ta fara sheƙa amai kamar zata fidda har hanjin cikinta. Ta jigatu matuƙa dan Ummita har da kukan ta, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta canja kaya ta hau gado ta kwanta ta dunƙule a waje
ɗ
aya cikin rawar sanyi, kafin wani lokaci zazza
ɓ
i mai zafi y
a rufeta. Kuka sosai Ummita ta zauna ta dingayi, babban tashin hankalinta shine basu san wanene ya kawosu nan ba kuma. Duk da suna zargin Alh. Sulaiman sai dai zukatansu sun kasa zama waje guda. Sosai Lulu bata da lafiya gaba
ɗ
aya a wannan daren, gasu a ru
fe balle Ummita ta fita ta