Showing 6001 words to 9000 words out of 145491 words
a tashi zuciyar, dan a yanzu haka bai fara a
iwatar da plan
ɗ
insa bane akan Lulun sakamakon rasa inda Smart yake da yay shi kuma. Dan tun washe garin da Smart ya baro 9ja yasa malami binciko masa shi amma ƙasa ko sama babu labarinsa. Amsa
ɗ
aya suke samu a bincikensu shine ya
ɓ
oye kansa dan kar ya sak
i Lulu. Duk da dai suna zargi Uncle Yousuf ne ya
ɓ
oyesa amma a
ɗ
an tsukunnan sun ƙara tsananta bincike kasancewar har yanzu basu sami wani point ba akan hakan. Dan shi Uncle Yousuf
ɗ
in ma ya sake baro Nigeria
ɗ
in zuwa harkokinsa da ya bari bayan yayma Dadd
y tas da tabbatar masa da cewar ya zare hannunsa akan al'amarin Lulu, dan ya fahimci goyon bayan da Daddyn ke batane a baya ya bata lasisin biyema Dada tabar gidan aurenta. Saboda ya tabbar da babu ha
ɗ
in kan Lulu Dada bazata ta
ɓ
a iya
ɗ
auketa a gidan aurent
a ba harta
ɓ
oyeta gashi ana neman wata uku kamar wasa.
*_NIGERIA_*
Sosai Daddy yana cikin wani hali na azabtuwar zuciya game da abubuwa da yawa. Na farko shine
ɗ
an uwansa dake fushi da shi. Ƙaunar da yakema Yousuf a zuciyarsa daban ce a wannan d
uniyar, dan zai iya rantsuwa ko ƴaƴansa baya musu irin wannan ƙaunar har Lulun da ake kallo ya fifita. Na biyu rashin sanin inda Lulu take har yanzu, tun yana
ɗ
aukar al'amarin wasa Dada zata dawo da ita bayan wasu kwanaki har lamarin ya fara bashi tsoro. L
okacin da yaje UK duba Baba Garko har roƙonta yay akan tayi haƙuri Lulu ta koma gida koda bazata koma gidan mijin ba, dan tabar aikinta da mutane ke matuƙar buƙatarta. Amma sai Dada ta murje idanu tai masa tas dole yaja bakinsa yay shiru dan yana
ɗ
aga mata
ƙafa kodan darajar sunan uwa da take amsawa. Sannan fa Daddy dama can Uncle Yousuf ya fishi zafi, shi dai barsa da zuciyar tsiya kamar
ɗ
an kuturu. Abu na uku wani salon rainin wayo da Alh. Sulaiman ya
ɗ
an fara kawo masa da nuna shi yanzu a shirye yake da
shi akan komai, sai zuciyarsa ta fara bashi anya kuwa bada ha
ɗ
in kan Alh. Sulaiman
ɗ
in Dada ta
ɗ
auke Lulu ba kamar yanda yay zargi tun farko. Idan ko haka ne to tabbas a wannan karon ya shirya duk wacce ma za'ai ayi shima. Wannan tunanin ne ya zaburar da s
hi yau daga gida daya fito yace driver ya wuce da shi office
ɗ
in Alh. Sulaiman Sufi Garko. Sanda suka iso ma shi bai kai ga isowar ba, dan haka sukai zaman jiransa. Baifi mintina bakwai ba a tsakani sai gashi shima. Sai da ya shiga da kusan mintina hu
ɗ
u dr
ivern Daddy ya shiga ya nema musu iso. Alh. Sulaiman da tun shigowar Daddy cikin Companyn aka sanar masa, yana shigowa kuma ya shaida motarsa yay wata dariyar mugunta da bama sakatariyarsa umarnin shigo da shi.
Tunda Daddy ya shigo Alh. Sulaiman da
yay wata kishingi
ɗ
ar iskanci a kujera yana jujjuya kansa ya saki murmushi mai ma'anoni da yawa. Yi Daddy yay kamar bai gansa ba, sai ma ya kai zaune duk da ba'a bashi damar hakan ba. “Ina fatan kana lafiya?”. Daddy ya fa
ɗ
a a takaice. A gatsine Alh. Sulaima
n ya amsa masa da “A office ka sameni ai ba'a gadon asibiti ba”.
“Kuma haka” cewar Daddy a gatsine shima. Batare da ya jira cewar Alh. Sulaiman
ɗ
in ba ya cigaba da fa
ɗ
in, “Sulaiman ina kuka kai min yarinyata?”.
“Ka shirya ganinta yanzu kena
n?”.
Idanu Daddy ya tsurama Alh. Sulaiman cikin
ɓ
acin rai, sai dai kafin yace wani abu Alh. Sulaiman
ɗ
in ya ƙyalƙyale da wata dariyar mugunta yana miƙewa tsaye. Takowa yay inda Daddy yake ya ja kujerar dake kallon wadda yake zaune shima ya zauna tar
e da
ɗ
aura ƙafa
ɗ
aya kan
ɗ
aya. Fuska ya tsuke ya zubama Daddy dake kallonsa cike da tsana idanunsa shima. “Isma'il Ibrahim Jiƙamshi! A da kana
ɗ
aukar duk zantukana matsayin kurari ko? Kana tunanin bazan iya illata rayuwar Mawaddat ba dan kawai tana
ɗ
iyar ƙ
anwata?. To kayi kuskuren sanin waye ni, dan zamanka da ni na tsawon shekaru bakwai bai maka amfanin komai ba kuwa. Bari kaji wlhy wlhy da ace na san da wannan sirrin a hannun Mawaddat ƙanwata kafin mutuwarta, ni da hannuna zan kasheta bayan na amsa, sai A
LLAH ya taimaketa ta mutu a karan kanta kafin na sani
ɗ
in, amma duk da haka bata tsiraba ta barma ƴarta gadon laifinta. Dan haka Isma'il ina maka garga
ɗ
i na ƙarshe, ka bani camara
ɗ
in nan, ka kuma saka a ranka baka ta
ɓ
a sanina ba har abada,
in ba hakaba, a
wannan karon saina wargaza rayuwar kaf family
ɗ
inka bata Mawaddat kawai ba. Dan haka za
ɓ
i ya rage naka....”
Murmushi Daddy yay mai ma'anoni da yawa duk da yasan duk abinda Alh. Sulaiman
ɗ
in ya fa
ɗ
a zai aikata fiye da hakan. Amma cikin nuna halin ko
in kula idonsa akansa kyam ya ce, “Sulaiman kenan. Ka manta ni Isma'il
ɗ
in wanene nima. Sannan banda haukarka a tunaninka baka camara na nufin gogewar abinda ka tafka da in kaf family naka sukaji sai sun maka tsanar da sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa. To
idan ka manta bari na tuna maka, bayan abinda Mawaddat ta
ɗ
auka nima ai nasan komai, ko toshewar basirar taka takai ka manta cewar komai na sani tunda da bakinka ka kirani ka sanarmin abinda kayi kuma na gani da idona, hasalima tare dani ka
ɗ
auki yarinyar
ka kai ƙasan gotter ka jefar. ai ba abinda Mawaddat ta
ɗ
auka bane kawai hujjar. Sannan na biyu Sulaiman kada ka manta a tafin hannuna kuke kai da su Alh. Baita, idan yanzu na sanarma duniya su waye ku a ƙasar nan wlhy wlhy ba dukiya ko matsayi ba sai anyi
faca-faca da namanku da taimakon mahaifinka dan kafi kowa sanin irin tsanar da yay ma abinda kuke aikatawar. Ai dama na sanar maka tun a waccan ranar, sai na
ɗ
an
ɗ
ana ma zuciyarka rayuwa cikin fargaba da zullumi fiye da yanda ƙanwarka ta
ɗ
an
ɗ
ana min a tsa
hon shekara
ɗ
aya dana rayu da ita.....”
“Nima ai na tabbatar maka sai dai mu rayu a tare cikin zullumin da fargabar ko ka manta”. Alh. Sulaiman ya fa
ɗ
a a zafafe cikin katse Daddy. Sai kuma ya ƙyalƙyale da dariya da fa
ɗ
in, “Isma'il kenan a tunaninka
kaima ban san a yanda ka rayun bane, ko cakake ban san kaima kana rayuwa bane cikin irin yanda kake tunanin ka sani a tsahon wa
ɗ
an nan shekarun. Ka gaya min inba tsoro ba miyyasa ka
ɗ
auke ƴarka daga Nigeria da ga randa na tabbatar maka saina hukunta rayuwa
rta bisa laifin mahaifiyarta? Miyasa kaketa kaffa-kaffa da ita fiye da sauran ƴaƴanka?. Amsar itace Tsoro ne! Kana jin tsorona Isma'il!! Hhhhh tabbas wannan tsorone!!”.
Da ƙarfi Daddy ya buga decks tare da miƙewa a zafafe.........
✍
️
Tofa fagen
na manya ne yau
🚴🚴🚴
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐
𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
4
️
⃣
.......“Kai
ɗ
in banza da zanji tsoronka Sulaiman. Ka sannni kaim
a ai, ni na wuce maka kanwar lasa, sannan ni ƙadangaren bakin tulune a rayuwarka data abokanka ta yanda kuka rasa yanda zakuyi dani. Ƙarshen target
ɗ
inku shine ku kasheni dai, kuma na tabbatar muku a randa kuka kasheni wlhy ko minti
ɗ
aya bazan cika ba da
ɗ
aukewar numfashi kuma duniya zatai muku zafin da sai kun gwammace mutuwa kamar ni, dan sai mutanen duniyar sun san suwaye ku. Idan ba tsoro kuke ji ba miyya hanaku aikatawar a tsahon shekarun nan. Miyasa kuka kasa bayan kunada kowacce irin dama? Miyasa bak
u aikata bane sulaiman? Ku kashenin mana? Maza ku kashenin idan kun cika ku tsagerane dan ALLAH!!”.
Matuƙar razana Alh. Sulaiman yayi da kalaman Daddy, cikin
ɓ
acin rai da zafafuwar zuciya ya nunashi da yatsa lips
ɗ
insa na rawa. “Haka kace ko?”.
“Haka nace Sulaiman, idan kuma bakaji ba na sake maimaita maka. Kuma wlhy na baka daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci
ɗ
iyata ta dawo gareni inba hakaba sai na sakaka nadama irin wadda sai ka gammaci mutuwa da rayuwa. Dan duk inda kasa ƙafa ka sani ni Isma
'il ƙaddararka biye nake da kai. Plan
ɗ
inku na gaba shine sakama Yousuf cocaine a kaya yayinda da zai baro ƙasar Chaina zuwa Nigeria. Bance ku fasaba dan ALLAH, amma ku sani wannan shine mabu
ɗ
in farko na kiran mutuwarku. Ni Isma'il kallon kitse kukema rogo
kawai, dan ko poisining
ɗ
in Baba da kukayi na barku ne kawai bisa wani dalilina na tarkon dana
ɗ
anama rayuwarku. FURAR DANƘO NAKE, A SHEKARA ANA DAMU BANI FARAU-FARAU. Mawaddat kuwa bazan sake cemaka ina take ba, in dai har ita
ɗ
in jinina ce da kanta zata
maido kanta gida bisa bigiren bijire muku. Ku muje zuwa wasan a yanzu na shirya masa....”
Har Daddy yabar office
ɗ
in Alh. Sulaiman da yay sumar tsaye bai iya dawowa a hayyacinsa ba. Sai da Daddyn yay banging ƙofar ne ya zabura wata zufa na feso
masa a illahirin jikinsa. Bai ma san sanda ya since hular kansa ya hau fifita da ita ba jikinsa ma wata irin rawar shiga ru
ɗ
ani da tashin hankali. Ji yake kamar mafarki yakeyi, shin Isma'il da ya sani ne haka wai shin ko canja shi ankayina? wagga al'amari
haka kamar a mahwalki. Shiy yasan Isma'il nada zuciya kam tabbas batun yanzu ba, amma bai ta
ɓ
a tabbatar da zai iya wani yunƙuri ba bayan kafiyar daya sanshi da ita kawai musamman da yaga tunda suka fara ƴar tsamar nan Daddyn nayi tamkar yana shakkarsa a k
oda yaushe, lallai ya yarda bakatsinan mutum abin tsorone yau. Da ƙarfi ya hanka
ɗ
a kayan saman table
ɗ
in nasa da nuna ƙofa a kausashe ya furta “Isma'il You really are playing with fire!!!....”
(
😂
Daddy ni kaina ka shayar dani mamaki, ashe jinin k
atsinawan dai na aiki a jininka)
*_CANADA_*
Sosai hankalin Dada ya sake tashi ganin yanda Lulun tai wani masifar
ɗ
ashewa ta ƙara haske sosai, ga komai nata ya ciko musamman ƙirjinta. Dan ma zazza
ɓ
in daya tasota gaba
ya
ɗ
an saka jikin nata girgiza ƙasa ka
ɗ
an kwana biyun nan. Tambaya bayan tambaya Dada ta shiga jeroma Dr Olivia akan mike damun jikar tata haka. Kai tsaye Dr Olivia ta sanar mata Lulu na
ɗ
auke da ciki wata uku da kwanaki biyu. Tamkar an fasa irin ƙaton du
tsen nan mai girgiza yanki da gidajen wajen gaba
ɗ
aya haka maganar Dr Olivia taima Dada saukar aradu a tsakkiyar ka. Cikin razani da zabura ta maimaita kalmar “Ciki!”
ɗ
in zuciyarta na bugawa. Dr Olivia ta sake
tabbatar mata da hakane. Wata muguwar ashariy
a Dada ta lailayo ta dire akan Smart. Tare da fa
ɗ
in, “ALLAH ya tsinema wannan shegen yaro dangin talauci dangin jaraba. Yanzu nan sai da dai ya
ɗ
irka mata ciki. Amma Mawaddat kema ƴar banzar yarinya ce. Randa na
ɗ
akkoki da ga gidan yaron nan har tambaya na
ita jera miki akan yanayin dana ganki amma kikace min fa
ɗ
uwa kikayi ashe-ashe miƙa masa jiki kikai ya lalube”. Sai ga hawaye suna cika idon tsohuwar nan dan
ɗ
aurama kai masifa. Kasancewar da Hausa Dada tai maganar duk sai hankalin Dr Olivia ya tashi ta shi
ga tambayarta ko lafiya. Rai
ɓ
ace Dada tace mata ba komai tana zuwa. Cikin rawar jiki ta fito tana neman lambar Alh. Sulaiman
ɗ
anta...
*_LONDON_*
Iya ƙoƙari yana yi wajen ganin ya ajiye matsalolinsa gefe ya fuskanci rayuwarsa ta yanzu
da cigaban da ya riskeshi. Sai dai hakan ya gagara matuƙa duk da akoda yaushe yay waya da Ammah ko Abbah ko Uncle Yousuf da Coach shawara suke bashi akan ya dai ƙara daurewa. Ammah kan masa nasiha mai ratsa jiki da tabbatar masa in sha ALLAH komai zai zama
labari, kuma in har Mawaddat matar da zai rayu da itace duk abinda za'ai sai ta dawo garesa. Wannan ƙwarin gwiwar da mahaifiyarsa ke bashi kan ƙara ƙarfafa masa gwiwa. Sai dai hakan bai hanashi kasancewa cikin mafarkin Lulu ba a duk sanda zai kai kwance d
a sunan barci. Al'amarin ma har yana neman zame masa jiki akoda yaushe a koda yaushe cikin wanka yake. Ya kasa manta dare mafi daraja da muhimmanci da ya zama wani babban jigo a cikin zamansu na kwanaki ashirin da shidda. Tunashi kansa yay murmushi ko ƙara
mar dariya harma da tausayawa. Duk da ashi kansa yasan darene da bazai iya tantance komai yanda ya kamata ba illa dai yasan a shi kansa yasha wahala balle ita. Amma sambatunta ko neman agaji zai ce na wannan dare ya kasa manta komai.
Yau ma kamar
kullum cikin shiri fita wajen training ya fito daga dogon ginin estate
ɗ
in da masaukinsa yake zaune mai hawa kusan
ɗ
ari da hamsin, a hawa na tamanin da biyar yake dan haka ya sakko ta lifter har zuwa block A, sanye yake cikin dogon wando na sport da riga
mai dogon hannu itama dai irin wandon ce. Sosai ya canja gaba
ɗ
ayansa tamkar wanda dama tun farko yake rayuwa anan
ɗ
in. Fatarsa ta sake gogewa ya sake yin haske da kwarjini da cikar kamala a cikin wata uku kacal tamkar wani baƙin bature. Yawan training da
sukeyi ya sake bu
ɗ
e masa halittun ga
ɓɓ
ai da sake kasancewar sa tsayayyen mutum da za'a iya kallo a jarumi. Kunnensa manne yake da bluetooth yana magana a hankali kamar baya so alamar waya yake amsawa. Ba kowa bane face Ahmad da yay kiransa, duk da yanayin
da yake a yanzu na sake zama shiru-shiru da rashin son magana idan Ahmad
ɗ
in yay kiransa yakan
ɗ
an sake suyi hira. Da
ɗ
an gudu-gudu ya fara tafiya jefi-jefi yakan
ɗ
agama wanda suke
ɗ
an wucewa kamar shi a hanya hannu. Yayinda yake cigaba da magana da Ahmad
ɗ
in. Da ga estate
ɗ
in nasu zuwa inda suke training
ɗ
in akwai ƴar tazara sai dai ba wata mai yawa ba sosai, amma duk da haka yakan jure tafiya a ƙafa koma cikin
ɗ
an gudu-gudu kamar yanda yake yi a yanzu domin fara motsa jininsa kafin ya isa. Hakan na ƙara m
asa ƙarfi da zaburarwa a yayin da ya shiga fili sai karsashinsa ya ƙaru. Sosai sabon baturen Coach
ɗ
in nasu ke yaba ƙwazonsa da jin cewar za'a mori yaron matuƙa idan aka ƙara tsayawa akan al'amarin sa zai zama babbar kaddara, shiyyasa akoda yaushe yake sak
e jan Smart a jikinsa da ƙara masa dabaru kala-kala dan Smart irin mutanen nan ne masu shiga ran mutane a komai nasu, ga shi baida hayaniya sam, yanayin da yake ciki ma ya sake maida shi miskili a yanzu duk da hakan ba halinsa bane a
baya. Amma hakan bai h
anashi zama abin so ga wasu ba hatta a cikin teammate
ɗ
in nashi. Alhamdullah yana ƙoƙarin maida hankali tare da ajiye gyambon dake mamaye a zuciyarsa gefe domin fuskantar abinda yaje yi a yanzu, wannan ne karo na farko da zai tunkari babban wasa link na ƙa
sar da za'a fara, Yana alfahari da hakan duk da team
ɗ
in nashi ƙarami ne. Cikin zafin nama ya iso inda sauran team mate
ɗ
insa suke. Babu
ɓ
ata lokaci suka shiga abinda ya tarasu, sosai yake nuna ƙwazo dake firgita al'amarin wasu a cikin abokan nashi bisa da
lilai masu yawa. Na farko shi ka
ɗ
aine baƙar fata
ɗ
an Africa a cikinsu, na biyu musulmi, na uku baƙon da har yanzu bai wuce watanni uku da kwanaki ba a cikinsu, amma yana taka leda da sunan training mai firgita zuciya. Ga yanda Coach
ɗ
in nasu yay masifar ma
ida hankalinsa kansa a
ɗ
an ƙanƙanin lokaci na basu mamaki. Yau
ɗ
in ma dai mamakin daya saba basu ya basun, dan har aka tashi babu alamun gajiyawar raunin jiki dana ga
ɓɓ
ai a tattare da shi. Sai dai su a zahirine kawai suke ganin haka, shi a karan kansa can
ƙ
asan zuciyarsa cike take da rauni. Ga wani irin fa
ɗ
uwar gaba da ya tashi da ita yau