Showing 90001 words to 93000 words out of 145491 words
kace-kace da hawaye har idanunta sun kumbura. Kafin ta fito ne aka samu aka
ɗ
auke Hajiya Naqiba dake kwance bata da banbanci da gawa. Dole asibiti aka wuce da ita a gaggauce dan ƙafar tayi ma
sifar kumbura damm abin zattashin hankali......
*_UK_*
Wahala iya wahala Lulu tasha a wannan dare hannun Smart. Dan zata iya rantsewa ita kam bata ga banbancin sa da daren farkonsu ba, kodan ta saka ma ranta tsoron al'amarin
ne oho. Amma tabbas ko a yarda da ita ko kar a yarda Smart namijin gaske ne da ko'a cikin mazan ma zai iya amsa sunan mazaje ne. Sai dai bata sani ba ko ragwantakarta yasa take masa irin wannan kallon ko kuma dan shi ta sani bata san sirrin sauran mazan b
a.
Shi kansa sai da ya koma tausayinta, dan magana ta gaskiya fa bai raga mata ba, wahalarsa ta kusan shera
ɗ
aya da wasu watanni sai da ya fanshe abinsa tsaff. Sai dai kuma shi a karan kansa bashi da za
ɓ
in da ya wuce hakan. Bai sani ba ko tsanani
n begenta da yake a cikine ya sashi jin yau
ɗ
in babu bambanci da wancan daren da ya kasa goguwa a zuciyarsa, amma ako ina kam zaiyi alfahari da baiwa irin ta matar tasa. Dan a wancan dare shima sabo yake, yau kam ya banbance tsakanin aya da tsakkuwa. Ya ku
ma za
ɓ
i yimata mai gana
ɗ
aya ne dan cire mata tsoron nan da ya lura yay mata tasiri. (Humm gyaran su iya Tabawa bai fa
ɗ
i a banza ba kenan
🥱
🤣🚴
).
Langyare iya langyare, raki iya raki yasha shi. Kuka kam muryarta har bata fita. Tun ana bashi haƙuri
da roko da magiya har dai aka koma kiransa mugu. Yaƙushi da cizo duk ya samu rabonsa kafin duk wani ƙarfinta na neman ceton kai ya ƙare ta koma zallar hawaye da jiran mala'ikan mutuwa (acewarta
🥱
😜😂
).
Shi ya fara farkawa lokacin da alerm
ɗ
in da
ke tadashi sallar asuba ya ka
ɗ
a. Da ƙyar ya iya bu
ɗ
e idanunsa da ke jingim da barci dan basu wani jima da kwanciyar ba. Hannu ya kai ya kashe alerm
ɗ
in gudun kar AA ya tashi shima. Tunda ALLAH ya taimakesa dai har ya gama bidirinsa na daren jiyan yaron bai
farka ba. Idannunsa ya zubama fuskar Lulu dake barci kamar a wahale, shi sai ma ta bashi dariya, dan haka ya
ɗ
an murmusa da kai hannu ya shafa fuskar tata. Baki fal tsiwa da rashin ragiya amma sai tosoro da ragwantaka uwa farar kura. Ɗumin da yaji a fuska
rta ya sashi jan bargon ka
ɗ
an yasa hannunsa a wunyanta. Zazza
ɓ
ine sosai a jikin nata kam kamar yanda yaji. Idanunsa ya
ɗ
an lumshe ya bu
ɗ
e da sumbatar goshinta yana sake matseta a jikin nasa cike da tausayawa.
“I'm so sorry Final Choice. Aliyu bazai
sake baki wahala ba da ga yau kinji”. Ya sake kai mata sumba a saman hanci yana mai sake jinta sama can ƙololuwa a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya samu ta tashi sai faman langyare take masa da kukan shagwa
ɓ
a. Shi dai biye mata yake yana binta da lallashi. Dan k
o a wancan karo na farko ba'ai masa wannan langwai
ɗ
in ba. Koda yake wancan ana bori yaushe ma ya samu kanta. Dan haka yau kam ya ƙudiri aniyar rama mata dukkan tattalin da bata bashi damar yimata a waccan ranar ba. Yanzun ma taimaka mata yay ta sake
ɗ
an g
aggasa jikinta, duk da dai yasan taimakon da yay mata jiya kawai ya wadatar, yasan kam harda raki da ragwantaka dai koma yace shagwa
ɓ
a. Shine ya jasu salla yanzu ma, suna idarwa ya miƙe ya fita, bai jima ba ya dawo
ɗ
auke da kofin tea da soyayyen ƙwai. Da ƙ
yar ya samu ta sha tea
ɗ
in, kwan ko bata ko kallesa ba balle ta ci, sai maidashi yayi. box
ɗ
in magungunan sa ya
ɗ
auko ya bata na zazza
ɓ
i tasha da rage ra
ɗ
a
ɗ
i. Sai da ya ga ta sake komawa barci ya sauke ajiyar zuciya. Yasan koyaushe AA zai iya tashi shima,
dan haka ya haƙura da fita ko'ina motsa jiki ya
ɗ
an yi a gida. Ilai ko bai jima da farawar ba AA ya farka. Rarrafawa yay kan Lulu yana kuka. Hakan ya sakata farkawa. Harararsa tayi, itama kamar zata saki kukan ta ce, “Ni bazaku kasheni ba kai da ubanka wlh
y. Kai tayi idan ya jika yazo ku ƙarata”.
Kaf a kunnen Smart dake shigowa, dan haka ya saki murmushi yana ƙarasowa ciki. Tana jin motsinsa ta maida idonta ta rufe kamar barci take. Nanma murmushi yayi kawai da
ɗ
aukar AA dake neman yimasa ƙiwa kama
r jiya. Tsaff yama yaron wanka duk da dai da ƙyar akasha, dan sau kusan biyu yana neman su
ɓ
uce masa ALLAH dai ya kiyaye baisha ƙasa ba. Ganin kamar yunwa yaron keji yay zaman fara bashi tea da dama ya ha
ɗ
o ya ajiye tun
ɗ
azun kafin ya shiryashi yana nishi d
a ƙyar dan bai iyaba. Pampa's ma da ƙyar aka iya sawa sai da ya duba a net.. yaga yanda akeyi. Duk kuma abinda sukeyi Lulu na kallonsu dariya kamar ta kasheta amma ta za
ɓ
i yin likimo wai ya
ɗ
an
ɗ
ana yaji shima idan da da
ɗ
i. Shiko a zatonsa barci takeyi, sai
da ta kasa riƙe dariyarta dai tayi sannan ya farga idanunta biyu. Cikin kalar tausayi yake kallonta da fa
ɗ
in, “Yanzu nan idonki biyu aketa wannan dambarwar amma babu ko taimako Baby luv?”.
“Ku ƙarata nima ta kaina nake”. Ta fa
ɗ
a tana masa gwalo
da jan bargo ta rufe har kanta. “Haka kikace ko? Ba komai zamu rama ne ai”. Bata sake magana ba tai luf a bargo abinta tana dariya har suka kammala ya hawo gadon da yaron yana sauke numfashi
ɗ
a
ɗɗ
aya. Sauka da ga jikinsa AA
yay zai haye kan Lulu ya riƙoshi
yana fa
ɗ
in, “A'a Sweet heart abar Momy ta huta kaga Papa ya koya mata karatu duk ta jikata”.
“Yaushe ka koyamin karatun?”. Lulu da bata fahimci inda ya dosa ba ta fa
ɗ
a tana bu
ɗ
e kanta da sauri harara idonta kamar zai fa
ɗ
o. Gira ya
ɗ
aga mata da kash
e ido
ɗ
aya ya ce, “Yanzu ma malamin a shirye yake in har za'a barsa ya ƙara
ɗ
ora sabon darasi”. Yanzu ne ta farga da inda zancensa yaya dosa. Bargon taja ta sake rufe kanta da fa
ɗ
in, “ALLAH dai ya shiryeka Aliyu. Ni kutashi ku fita barci nake son yi kun da
man”.
“Amin ya rabbi tunda addu'a aka min. Amma fa babu inda zamuje muna nan tare da ke”.
“To ku koma ƙasan carpet kun ishan ALLAH”.
“Anƙi
ɗ
in”.
Harararsa tai shi da
ɗ
an nasa ta matsa can ƙarshen gado ta sake jan bargo
dan da gaske jikinta ciwo yake mata sosai, ga zazza
ɓ
i. Murmushi yayi da binta da kallo, dan yasan da gaske bata da lafiyar, yana mata hakane danta saki jikinta dai ne kawai. Wasa ya cigaba da yima AA dake son shi kawai a saukesa yayi
ɓ
arna, sai da ya tabba
tar tayi barci ya
ɗ
an janye mata bargon da ga kan fuska danta samu iska. Goshinta ya ta
ɓ
a yaji da
ɗ
an sauƙin zafin, sai kuma ya maida kan wuyanta. Shima dai alhmdllh ya fara sauka. Sai ya samu kansa da sauke ajiyar zuciya........
✍
️
_LABARAI MASU JAN
HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Day
a 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING U
S*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐
𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
4
️
⃣
2
️
⃣
______________
*3 D
AYS CLASS*
Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rarar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rarar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da
bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka can
za kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni
Class ze fara ranar jumaa insha Allah
WhatsApp group
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/E8Lzqogsm1nAFy1feTwbmA
WhatsApp 08144147273
👉
Masu bukatar tafiya da kudin
su ba scholarship ba, Muna yin study & work ko working visa, a takaitaccen lokaci, working visa Qatar munayi a sati daya, Canada study & working visa a 4 to 5 months, Oman working visa a 7 days insha Allah, Maxico Tour visa 1 month
_______________
........Kuka take sosai a gaban mijin nata da ayanzu al'amuransa ke bata tsoro matuƙa. Gaba
ɗ
aya ya sauya mata, sauyawa irin wadda bata ta
ɓ
a zato ko tsammani ba. Kai koda a mafarki ko lissafin rayuwa bata ta
ɓ
a tunanin itada Sufiyanun nata zasu kasance a ir
in wannan ajin ba. Amma a yau sai gashi wai harda mata kishiya sa'ar jikokinta da wannan shekarun nata tsofai-tsofai. Kuma ko kunyarta baya ji yake soyayyarsa kamar wani ƙaramin yaro.
Baba Garko da tunda ta shigo ta zauna bai ko
ɗ
aga kai ya dubeta
ba sai ma wayoyinsa da yake hankali kwance. Daya gama wannan zakaga wata ta shigo. Cikin jin gundura da kukan da take rera masa ya ce, “Amma dai kin san kina damuna ko? Please bana son damuwa idan kukanki zakiyi zaki iya bani waje”.
Sake
ɓ
arkewa tai
da sabon kuka kamar wata ƙaramar yarinya. A dai-dai nan akai knocking ƙofar falon,
ɗ
an jimmm yay yana kallon ƙofar kafin ya ce, “Ko waye ya shigo”. Mai aikin amaryarsa ce ta shigo a rikice, amma hakan bai hanata kaiwa tsugunne da ga bakin ƙofa ba ta gaishe
shi cikin girmamawa sannan ta
ɗ
ora da fa
ɗ
in, “Alhaji aunty amarya ce bata da lafiya, tun
ɗ
azun kuma ta hana azo a sanar mak...” ai mai aikin ma bata ƙarasa rufe baki ba ya miƙe zaram ko nauyin tsufarsa baya ji. Ƙofar ya nufa a hanzarce, Dada da kanta ya ne
ma tarwatsewa ta bisa da kallo galala, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki na sake turniƙe mata zuciya. Ba'a ko rufa minti hu
ɗ
u ba sai gashi ya shigo a rikice, ko kallon inda take baiyi ba ya shige bedroom
ɗ
insa. Cikin ƴan sakanni ya sake fitowa ya fice hannunsa
riƙe da key
ɗ
in mota ya canja zuwa jallabiya. Kasa motsawa tayi a wajen har sai da taji ƴar hayaniya na tashi ta miƙe jikinta na rawar
ɓ
acin rai ta leƙa ta window. Akan Baba garko da ke rungume da amaryarsa ita kuma tana faman yarfe hannu tana kuka idanunt
a suka fara sauka. A take zuciyarta ta ayyana mata haihuwa. Sake dugunzuma zuciyarta tayi har tana jin jiri na neman kwasarta, batama san sanda ta sulale a wajen ba ta zube saman kujera ja
ɓ
ar wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, sai kuma ta
ɓ
arke da ku
ka. Tunda take a rayuwarta, bata ta
ɓ
a shiga matsanancin baƙin ciki da tashin hankali irin na wannan ga
ɓ
ar ba. A tsahon rayuwar ƙuruciyarta ko firar kishiya bata so, kai ko ƙawa ko cikin ƴan uwa akaima wata kishiya daina zuwa gidan mutum take saboda yanda t
a tsani kishiya. Amma a yau sai gata da ita a wannan shekarun nata, harma da ciki na haihuwa.....
(
🤣🤣🤣🤣🤣
Kar kuce dariyar mugunta nakema Dadaras
😜
)
____________
★
Tun Ummah na
ɗ
aukar al'amarin ta ƙarami harta fahimci ya wu
ce da saninta. Kuka ma da hawaye yanzu ta kasa yinsa. Ƴan gidansu sunzo sai dai me suma ƙarewa sukai da fita da gudu harda masu fa
ɗ
uwa. Wajen Abba suka
koma kowa na maida numfashi, yayanta cikin damuwa ya ce, “Anya ba aljanune suka shigi Yahanasu ba Yaya M
ika'il”.
Cikin
ɗ
an ta
ɓ
e baki Abba yace, “Idan ma sune wajen bi
ɗ
ar baƙar tambayarta ta kwaso su. Ballema bana jin hakanne. Nafi ƙyautata zaton ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya. Ni yanzu jibirin ban san yanda zanyi da wannan matar ba. Gaba
ɗ
aya ta firgit
amin iyali sun kasa sakewa kowa sai zaman
ɗ
aki”.
Cikin damuwa Jibirin yace, “Amma yaya bai kamata kace haka ba. Ƙilama cikin matanka wata taimata haka kasan dai mata akan kishi”.
“Wane matan nawa? A'a ƙarya haramun. Ai duk cikin iyalina babu fa
n
ɗ
ararre irin Yaha. Nasan halin kowacce a cikinsu da abinda zata iya. Na jima ina zarginta dama da shigen-shigen nan kawai dai ban ta
ɓ
a gani da idona bane shiyyasa ban kafa hujja ba. Amma a yanzu na gama fahimtar komai. Ko wannan halin da kaga tana cikin s
ihirin da taima Aliyu da matarsa ne ya dawo mata...”
“Aliyu kuma Yaya? Aliyu Aliyu dai namu na nan?”.
“Shi
ɗ
in fa”.
“Ikon ALLAH! To shi Aliyu dake matsayin
ɗ
anta kuma zatama asiri. Miye ribarta kenan?”.
“Oho mata, ita
ta sani”.
Sosai al'amarin ya girmi kan kowa. Cikin ƙarfin hali Zaidu ya bada shawaran to ko za'a samo malamai suyi addu'a ne. Dan wannan yanayin nata abin tashin hankali ne ga kowa tunda gashi hankalin kowa a tashe, shi wlhy yanzu haka baya jin ya
u
ɗ
in nan zai iya barci lafiya saboda ganin wannan mummunar halitta da Ummah ta koma. Abba dai yace shi babu ko sisinsa a nema mata lafiya. Hasalima ya kirasu ne su wuce da ita dan bazai iya ba. Hankalinsu ya tashi matuƙa, dan sukam bazasu jajibi wannan ha
littar ba sukai cikin iyalinsu suna zaune ƙalau. Dan haka suka dage bashi haƙuri da roƙo da magiyar ya barta a
ɗ
akinta cikin ƴaƴanta harta samu lafiya sai aji dalilinta na wannan mummunan al'amari, idan ma matakin sai
ɗ
auka sai ya
ɗ
auka. Anfi ƙarfin Abba n
e kawai, dan haka yay shiru. Su suka fita suka zo da malamai, da ga tsakar gida suka tsaya aka kwala mata kira ta fito. Su kansu malaman sai da suka zabura da ganin mummunar halittar dake tunkarasu, ganin tana yo kansu gadan-gadan sukaji fa dauriya ba tasu
bace. Ai tuni suka dafe kawuna kowa ya ara cikin ta kare yana jan kula'uzai. Bayan su an sake kawo wasu malaman amma fa kowa yazo yana tozali da Umma sai dai a tsincesa waje ya dafe ƙeya. Al'amari kamar wasa sai ƙara fa
ɗ
i yake. Dan takai ƴan jarida daga g
idajen rediyo har sun fara zuwa neman labari. Sai dai suma fa suna shigowa sukai ido hu
ɗ
u da Umma labarin bai
ɗ
aukuwa garesu sai ƴar reren gudu...
Tsabar tashin hankali da hawan jini Umma ta koma ko gani batayi da ƙyau. Barci kuwa ya ƙauracema idanu
nta gaba
ɗ
aya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai wata irin muguwar rama mai ban tsoro. Babu abinda ke
ɗ
aga mata hankali sai ganin ƴaƴanta suma gudunta suke da mijinta da ta
ɓ
ata tsahon shekarun rayuwarta tana fa
ɗ
a da fa
ɗ
i tashi a kansa. tana son jin halin da Hajiy
a Naqiba take amma babu hali. Rayuwa ta mata duhu, duhu irin wanda ko tafin hannunka baka iya gani, duhu irin wanda zuciya kanta bata iya tuna komai sai ƙunci da ciwo mai ra
ɗ
a
ɗ
i. Hatta salla yinta kawai take amma bata ma sanin mitake yi a cikinta. wanka ka
m bama'a maganarsa dan tashin hankali. abinci dama yanzu ƙofar
ɗ
aki Abba ke zuwa ya ajiye mata saboda kowa tsoro yake ji, shi kansa dai tausayin rai ne ke sakashi yin ƙarfin halin ajiyewar kawai dan an hanata fitowa.....
*_
★
UK
★
_*
Sosai ta
sha barci, dan ko da lokacin salla yayi da ƙyar ya iya tashinta tayi ta sake komawa. Bata tashi ba sai gab da la'asar. Yana falo suna kicimilli da
ɗ
ansa ta fito. Tsaye kawai tai tana kallonsu har bata san