Showing 135001 words to 138000 words out of 145491 words
hankalin ƴarta Hannat
u ta dawo gida wai mijinta ya saketa. Gaba
ɗ
aya Umma ta sake hargitsewa jiki ya koma
ɗ
anye sharaf. Sai da aka kira Smart ana fa
ɗ
a masa ne ya saka aka kaita asibiti. Satin ta
ɗ
aya aka sallamonta. Gaba
ɗ
aya Salim ya koma kamar zararre. Sai kuka yake yana jam
a Umma ALLAH ya isa akan itace ta ja masa. Ai dama nakan tudu ya fa
ɗ
a duk bala'in data ƙulla akan Smart sai ya dawo kansu. Gashi nan kuwa. Ta cucesu ta zalunce su bazasu yafe ba. Ranar da matar Salim ta gudu da ƴaƴansa bayan ta saida gidan da shi ya ka
ɗ
ai
ya rage masa ai ka
ɗ
an ya rage a
ɗ
aureshi a turu saboda tsabar zaucewa. Umma ta dinga kuka dan dama dai Salim
ɗ
in ne abin tinƙahonta...........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU K
AMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar
biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐
𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
6
️
⃣
2
️
⃣
.......A
ɓ
angaren Garko family ma dai ALLAH ya bama Dada da Baba Garko lafiya har sun dawo gida Nigeria. Sai
dai Dada ƙarfin hali kawai take. Gaba
ɗ
aya ta zama wata shiru-shiru. Sai da kaga ta tasa hoton Maman Mawaddat da na Sultana gaba tana kuka. A yanzu Baba Garko kan zauna ya lallasheta da mata nasiha. Hakama amaryarta takan ƙyautata mata duk dan dai ta kwant
ar da hankalinta, haka ma ƴaƴanta basa gajiyawa wajen tattalinta saboda an tabbatar musu zuciyarta idan har ta buga shike nan kuma. Dan haka kowa baya wasa da al'amarinta. Lulu kanta ba'a barta a baya ba wajen lallashin Dadan. Dan tana kallonta tamkar Mawa
ddat
ɗ
in ta ne data rasa. Akoda yaushe cikin yin video call suke da ita....
__________
★
Shirye-shiryen bikin Maryam ya kankama sosai, dan takowane
ɓ
angare shiri kawai akeyi. Ana saura sati guda
ɗ
aurin aure Smart da iyalinsa suka iso gida Ni
geria. Ƙasar da yay kewa. Tarba ya samu maiban mamaki da ga al'ummar ƙasar tasa da ƴan uwa da abokan arziƙi. Dan da ƙyar suka iya baro airport sai da taimakon jami'an tsaro. Yayinda ya samu rakkiyar masoya har gida. Anan ma ya samu yaran anguwa da iyaye su
na jiransa. Sai ga Smart na hawaye dan farin ciki. Ya tabbatar da mutane rahama ne. Duk wanda yace maka yana sonka da ƙaunarka ya gama maka komai a rayuwa. (Ya ALLAH ka barmu da masoyanmu. Duk wanda ya somu dominka ya rabbi shima ka soshi shi da zuri'arsa
baki
ɗ
aya.
❤
️
❤
️
❤
️
😘
wannan nakune masoyan alkairi
🙏
).
Anan
ɗ
in ma dai da ƙyar ya samu suka shiga gida saboda yanayin Lulu. Dan cikinta yayi girma sosai wannan karon fiye dana AA. Ga kuma kullum
cikin laulayi take dan tunda ya fara tsufa bata da wani
ishashen lafiya. Duk da dama dai haka taketa fama tun da cikin ya shiga watanni biyar. Babu kunya yau kam Smart ya rungume Ammah da Abbah a gaban jama'ar gidansu. Ya kuma rungume ƙannensa su Mubarak da yasan suna matuƙar kaunarsa. Kannensa mata nata kawo
masa gaisuwar girmamawa harma da wanda suka girmesa kamar wani sarki. Tunda Ummah ta leƙo sau
ɗ
aya ta gansa bata sake maimaitawa ba,
ɗ
aki ta shige tana sakin wani irin kuka mai ƙona zuciya. Smart ya koma kamar wani baƙin bature. Ko makaho ya laluba yasan k
u
ɗ
i da jin da
ɗ
in rayuwa da
ɗ
aukaka sun zauna sai dai fatan gamawa da rayuwa lafiya.
Shiko sanin bata da isashiyar lafiya har
ɗ
aki yaje ya gaisheta tare da duk sauran matan Abba har aunty Amarya. Ita kanta Mama a ru
ɗ
e take, kawai dai tana ƙoƙarin dann
ewa ne kar ai mata irin kallon da akema Umma. Dan ƙamshin Smart kawai rikita zuciya yake. Saboda kowa ya gama sanin hankalin Ummah fa a tashe yake. Wasu a cikin yaranta har abun nata na basu kunya.
Bayan yaci ya sha daga girkin mahaifiyarsa data mu
su girki da kanta dan Lulu bata iya cin komai sai kunun gya
ɗ
a. Shi ka
ɗ
ai taima sha na hauka dan motsi ka
ɗ
an taji yunwa yanzu. AA na hannun iyayensa wannan ya
ɗ
auka ya ba wancan haka aketayi. Yaron birgesu yake gashi fes kamar ka lashe, komai na ubansa bai
bari ba. Zuwa yanzu ya
ɗ
an fara magana sai dai ba gane abinda yake nufi akeyiba ma sosai. Kwanciya Lulu tayi danta hutama ranta. Yayinda su Ammah da Smart suka bu
ɗ
e shafin hira dan Gwaggo Sa'adah na gidan da su aunty Bilkisu da Hawwah. Daga baya sai ga Abb
a shima ya shigo duk da su Smart
ɗ
in sun je sun gaishesa...
Washe gari aka kawo lefen Maryam daga gidan su Ahamd. Lefe ne na nunama tsara dan an nuna dukiya kam babu ƙarya. Ƙwaƙwalwar Umman neman zautuwa takeyi. Dan kasa jurewa tai yau ma sai kulle
kanta tai a
ɗ
aki. Ga dangin Ammah dana Abba nata zuba mata habaici batare da sun duba cewa ƴar uwarsu bace ba. Anyi komai cike da girmama juna da mutuntawa dan suma sun bada tukuyci mai tsoka. Bayan wucewar ƴan kawo lefe Smart ya
ɗ
auki Lulu da AA da Asma'
u suka nufi gidan su Lulun. Daddy da su Amrah sunyi farin cikin ganinta, duk da kuwa jiya harda su a ƴan tarbarsu. Basu koma gida ba sai dare. Mommy ma taji da
ɗ
in ganinsu. Tana ta tsokanar AA. Hira sosai Smart suka sha da Daddy, dan anan suka yini sai baya
n sallar azhar suka nufi gidan Uncle Yousuf. Anan
ɗ
in ma dai hirar aka sha, samun su twins da sukai can yasa Smart da Lulu fahimtar akwai wani abu tsakanin Hussain da Asma'u. Hakan yama Lulu da
ɗ
i sosai ita da Smart. Basu bar nan ba sai bayan la'asar. Sun n
ufi gidan Baba garko inda suka ƙarasa yinin. Itama dai Dada harda kukanta dan ta fahimci dai wa
ɗ
an nan ma'aurata kainuwa ne dashen ALLAH. Sannan FURAR DANƘO ne damasu ace za'asha farau-farau abune mai wahalar gaske. Jiki lu
ɓ
us suka koma gida dan Lulu tayi
laushi. Ammah taita ma Smart fa
ɗ
an miyasa bai barta acan ba yaketa yawo da ita haka. Shi dai murmushi kawai yayi yana kallon Lulu dake masa gwalo ƙasa-ƙasa. Washe gari yana tare da Ahmad da Coach, acan ya yini sukasha hirarsu da ubangidansa. Bai dawo gidan
ba sai dare dan har Malam na Yakasai yaje ya gaidar bai manta alkairi ba nan ma....
Al'amarin biki ya kankama sosai, Smart ya ha
ɗ
ama amarya gidan mijinta da kaya na kece raini da nunawa tsara. Yayinda aka fara events da aka shirya wanda ya kafa
ya tsare ya hana Lulu zuwa ko
ɗ
aya saboda yanayinta. Daga ƙarshe ma da yaga hayaniyar gidan na mata yawa sai ya dinga janyeta zuwa masaukinsa. Acan suke kwana sai da safe ya dawo da ita
nan ta yini cikin danginsa. Lulu ta amsa suna matar babban Yaya. Dan k
omi aka buƙata bata jin ko
ɗ
ar zata fidda a jakarta ta bada batare da tabi takan mijinta ba. Sai wasu a ƴan uwa suka fara tsogumin ai ta kankane komai sai abinda taso take badawa. Tun anayin ƙus-ƙus har zancen ya fito fili yakai kunnen su Ammah. A take Amm
ah ta nuna
ɓ
acin ranta akan hakan, yayinda Smart da shima ransa ya
ɓ
aci ya basu amsa da ai kai da kaya duk mallakar wuyane. Shi kansa a ƙarƙashin say
ɗ
in Lulun yake bama dukiyarsa ba. Ballema ko sisi bai bata ba duk abinda suka nema ta basun ku
ɗ
inta ne. Wa
nnan zantukan nasa yasa jikunansu yin sanyi, dama dai cikin dangin Abba ne da ƴaƴan Mama da wasu ana Ummah masu gulmar. Sai aka koma ƴar sinne kawunan jin kunya.
Ana gobe
ɗ
aurin aure akai dinner. Ita ka
ɗ
ai Smart ya bari Lulu ta halarta. Shima kuma yaj
e. Dan tare sukaje tana gefensa riƙe da hannunta AA daya maƙale masa da ga hannun su Abdull
ɗ
auke a kafa
ɗ
arsa. Sun isa a lokacin da kusan kowa ya gama zuwa. Dan har biki ya fara. Dan haka gaba
ɗ
aya attention na mutane ya dawo kansu musamman yanda mc ke kwa
rzanta wanene Smart
ɗ
in da matsayinsa a wajen ango Ahmad da ma Amarya Maryam. Nan fa dangin Ahmad
ɗ
in masu
ɗ
an jijji da kai irin na dangin miji suka shiga hankalinsu. Dan sun fahimci abinda sukeji basu yarda ba ashe gaskiya ne. Dan kamanin Smart da Maryam
a bayyane suke. Nan fa ƴammata suka ru
ɗ
e da ganin matashin
ɗ
an ƙwallon da duniya ke yayi mai ji da ku
ɗ
i. Sai dai Lulu dake fama da cikinta tana nane da abunta. Duk yarinyar data kama tana kallar mata miji kuwa zatasha harara. Shiko Smart nata ƙunshe dariya
dan yana sane da matar tasa. Amarya da ango sunsha ƙyau har sun gaji, yayinda bakin Ahmad yaƙi rufuwa. Liƙi sosai daya ru
ɗ
a hall
ɗ
in Lulu da Smart suka dinga zuba musu harda AA da Ahmad ya
ɗ
aga sama yana sumbatarsa da fa
ɗ
ama mc cewar a sanar kowa ya sani
wannan surukinsa ne. In sha ALLAH yanda suka taru anan bikin aurensu haka wataran zasu taru bikin auren AA da matar da zasu haifa masa. Wannan zance na Ahmad yasa kowa dariya a wajen tare da addu'ar ALLAH ya tabbatar da hakan. Ba'a tashi ba Smart ya
ɗ
auki
matarsa suka gudu dan taje ta huta saboda bata jimirin hayaniya yanzu....
Washe gari aka
ɗ
aura auren Ahmad Rabi'u Ƙoƙi, da amaryarsa Maryam Mika'il Mawashi akan sadaki naira dubu
ɗ
ari biyat bayan sakkowa da ga massalacin juma'a. Ɗauri aure ne daya
samu halartar manyan mutane a dalilin gidajen biyu. Tare da
ɗ
unbin masoyan Smart da ga jihohi daban-daban. Anyi walima da yamma. Zuwa bayan isha'i aka shirya kai amarya
ɗ
akinta. Yayinda kaf yayunta harda su Sadiq ƙanana suka taru a falon Abba domin mata n
asiha. Tasha kuka sosai har muryarta na dishewa. Dan yayun nata sun mata nasiha mai ratsa zuciya. Bayan an kammala Smart da Salim da Zubair da Kamal suka sakata a danƙarereiyar motar da Smart ya siya mata suka kaita gidan mijinta da rakkiyar mata iyaye gud
a biyar kawai. Da zasu taho ne ta rungume Smart tana kuka da jera masa godiya
. Murmushi yayi a hankali yana mai lumshe idanunsa kafin ya
ɗ
agota a jikinsa. Fuskarta ya riƙe cikin hannayesa yana girgiza mata kai alamar tayi shiru. Daga haka ya shiga gaya mat
a da
ɗ
a
ɗ
an kalaman da saida ta saki murmushi. Sannan ya kamo hannun Ahmad ya saka masa nata a ciki ya
ɗ
an bubbuga kafa
ɗ
arsa ya fice yana maida hawayen da suka cika masa ido shima. Smart na matuƙar so da ƙaunar ƴan uwansa matuƙa a rayuwa. Akwai shaƙuwa sosai
a tsakaninsu duk da bawani sakewa yake da su ba. Dama sauran duk sun fita harma sun shiga mota. Yana zuwa shima ya shiga kawai suka wuce........
✍
️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GAS
U KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shed
ar biyanka anan
👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
🥰
Zafafa
🫶
🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu
😭🙏
_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠
📲
🫗
𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍
𝘿𝘼𝙉𝙆
'
𝙊
.....!!
🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏
𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍
𝒄𝒆
🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐
𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓
6
️
⃣
3
️
⃣
.......Washe garin da aka miƙa Maryam gidan miji Mawashi family suka tashi da tashin hankali biyu. Na farko
shine gano Huwaila
ɗ
auke da cikin shege na watanni biyar. Tashin hankalin bayyanar wannan ciki kuma yasa Ummah yanke jiki ta fa
ɗ
i. Inda fa
ɗ
uwar tata ta zama sanadin samun paralysis. Smart na masaukinsa yana barcin gajiya Lulu a jikinsa ya samu kira da ga S
alim. Dole ya shirya ya nufo gidan da Lulu data dage bazai barta ita ka
ɗ
ai ba. Sun sami gida a rikice. Ko Ummah ba'a
ɗ
auka ba zuwa asibiti sai da yazo ya fara fa
ɗ
a. Bayan ankai Ummah asibiti suka samu tabbacin ta samu shanyewar
ɓ
arin jiki gida suka dawo da
ita bisa shawarar doctor bayan anyi treatment
ɗ
inta yanda ya kamata. Ummah dai an tafi, dan babu abinda ke motsi a
ɓ
arinta na dama sai ido da kai. Amma daga wuyanta zuwa yatsanta ma ƙafa komai cak. Sai
ɗ
ayan
ɓ
arin haggun kawai. Babu abinda take sai hawaye
. Dan bakin ma idan tayi magana ba'aji sosai sai yawu ke fita babu ko ƙyawun gani.
Smart da Salim suka tsare Huwaila. Zata musu wani kwana-kwana tasha maruka a hannun Smart. Salim ya rufeta da duka da ƙyar aka tsaida shi saboda lalurar dake a jikin
ta. Wahalar da tasha yasata fa
ɗ
in gaskiyar cewar saurayinta ne ya mata lokacin suna tare da Umma a gidan Kawu Jibirin, idan tace ta tafi makarantar islamiyya sai ya
ɗ
auketa a hanya su tafi hotol ko
ɗ
akin abokansa. Ran kowa ya
ɓ
aci Abba harda hawaye yana ja
ma Umma ALLAH ya isa da jin nadama bisa nadama akan aurenta. Dan bai tsira da komai ba sai baƙin ciki da tashin hankali tun daga ƙuruciya har zuwa yau. Garama yanzu da Smart ke ƙoƙarin dawo da su Salim a hayyacinsu. Dan a yanzu haka jira yake a kammala bik
in nan ya gyarama Salim shagunansa da suka ƙone. Smart yasa an nemo wanda yayma Huwaila ciki tare da iyayensa. Da farko ya musa harda cewa shi baima ta
ɓ
a ganin Huwaila ba, sai da Smart yay masa jan ido harda maruka biyu a gaban iyayensa babu ko kunyar idon
su sannan ya fa
ɗ
i gaskiya, amma yace ai bashi ka
ɗ
ai bane tana kaima wasu. Huwaila ta sanya kuka da rantsuwa da shi ka
ɗ
ai take tarayya, hasalima shine ya fara saninta
ɗ
iya mace, tana ma da shedar hakan. Ansha rikici sosai har sai da Huwaila ta kawo recordin
g na wayar da suka dingayi da ta dinga ajiyewa sannan fa shegen yay laushi. Inda aka tsaida magana da zaran ta haihuwa za'a
ɗ
aura musu aure. Sauran ƴamatan gidan kuma ya basu tabbacin nan da wata uku kowacce ta kawo mijin aure in ba hakaba shi zai za
ɓ
o mus
u. Hakan ya saka iyayen jin kwanciyar hankali. Dan sai ga Mama sarkin ru
ɗ
iya yau na sakama Smart albarka. Saboda ba ƙaramin tayar mata da hankali batun cikin nan na Huwaila yay ba, dan itama tana da
ɗ
aya a
ɗ
akinta mai rawar kan tsiyar da giggiwa. Haka ta t
asa ƴaƴanta gaba wanda basuyi aure ba tana roƙonsu ALLAH Annabi su taimaka mata su rike mutuncin kansu karsu kasheta tun lokacinta baiyi ba kamar yanda Huwaila ta zama sanadin Ummanta. Sun daiga yanda tarbiyyar ƴaƴan Ammah a gidan ta jawo musu alkairi.....
Samun lafawar ƙurar biki ta bama Smart nutsuwar fuskantar ƴan uwansa. Yayinda ya nutsu wajen nemawa ƴan uwansa maza da matan ma abinyi. Tare da zagaye dangin mahaifiyarsa dana mahaifinsa kaf yay musu alkairai
masu tsoka da yaketa samun albarka shi
da zuri'arsa. Shine har dangin Mama dana Aunty Amarya, dan ita Umma danginta sune dangin Abba sai dai na
ɓ
angaren mahaifiyarta. Gefe
ɗ
aya kuma ya samu damar gina wasu manya-manyan mall guda biyu da kafa business daban-daban. Tare da yin amfani da ƙungiyar
Lulu ya tallafama yara da
ɗ
an yawa akan karatu. Masu shaye-shaye a ciki ya kaisu rihab. Dan Nadiya dake ta lalla
ɓ
a rayuwarta a yanzu tare da Ummita tsaye suke akan ƙungiyar. A cikin wannan halin bikin Ummita da Usman ya tashi suma. Haka Lulu taita ƙoƙari n
an ma akayi komai da ita. Ta kuma bama Nadiya shawara akan ya kamata itama ta samu miji mai irin ciwonta suyi aure tunda yaron data haifa ya rasu. Ranar Nadiya tayi kuka sosai, tare jerama Lulu da Smart