Showing 69001 words to 72000 words out of 182667 words

Chapter 24 - AMEEENATOU COMPLETE

Unknown   

30 Aug 2026

51

Bata tana sake zurfafa a tinanin abubuwa da dama da Suka sauya daga Ameenatou din Daya kamata ace sun gane Amma sbd ganin rayuwarta ma ta sauya gaba Daya ya Sakasu daukan duka akan kanta ne Daya juya.

Karfe Hudu na yamma Babbah ya dawo gidan dauke da ledan fruits Daya siyo a hanyarsa ta dawowa daga inda ya samu Yana Dan shiga kasuwancin dabbobin Daya Saba.

Zazzabin Daya tarar da Dadah ya Sakasa mamaki Yana zaunawa yace

"To lafiya dai kuwa?

Mey

a sameki ne tinda lafiya kalau muka fita muka barki kina aikin gidan,

Ko cizon sauro ne? To Amma Kuma ai bamada Wani sauro tinda Akai akai anawa gidan feshi sbd yar buduwata da banason sauro ya ciza"

Ajiyan zuciya ta sauke idanuwanta sai a lokacin suka

cika da wasu hawaye masu tsananin radadi da ciwo ta dago ta Kalli Ameenatoun Dake kwance tana bacci ita Kuma tanai mata fita.

Ajiyan zuciya ta sake saukewa a Karo na uku kafin ta dago ta Kalli Babbah Daya zuba mata ido Yana jiran abinda zata fada Dan b

ayason delay a gurin Bada labari ko Fadar Abu.

Sanyi jikinta yayi hakama muryanta tace

"Babbah Ameenatou ciki ne a jikinta ga dukkanin alama Dan ni dai na kasa tabbatarwa a rude nake Kuma itama da kanta tace baby a cikin Ameenatou....."

Kallan A

meenatou din yayi kafin ya juyo da kallansa kan Dadah yace

"Meyasa haryanxu kin kasa sabawa da yanayin tashin lafiyanta,

Kinsan yanzu batasan me take fada ba batasan Menene wannan ba bare wancan."

Girgiza Kai dadah tayi idanuwanta na sake cikowa da

Hawayen da suka gangaro mata tace

"Ciki Kam akwaisa da alama Dan gashinan a bayyane harya fito Dan kuwa da alama zaiyi wata hudu komai fiye,

Kullum saitace cikin Ameenatou tsalle sosai na dauka idan tana Jin yunwa take Fadar Hakan shiyasa duk ta fada s

aina Bata Wani abin taci da alama Motsi ne yake mata.......

Ajiye kankanar Daya dauka zai Sha Babbah yayi Yana sake kallan Ameenatou din dakyau ya dawo da kallansa kan Dadah idanuwansa na sauyawa yace

"Wai maganar me kikeyi??

Cikin haihuwa ko me??

Gyada Kai tayi hawayenta na sake gangarowa.

"Ni bangansa ba to" ya fada muryansa na sarqewa.

"Nima wlh bantaba Gani ba sai yau Amma wlh Babbah naga ciki me girma Kam ni Amma na kasa yadda da cikin mutum ne a jikinta,

Nidai muje asibiti a duba mana

Dan jinina Neman Hawa yakeyi da wannan babban tashin hankalin dayafi kowanne dayake Shirin bayyanar mana"

Wani azababben zufan tashin hankali ne ya fesowa Babbah lokaci Daya a ko Ina jikinsa,

Hannunsa dayake Dan rawa yakai goshinsa ya share tareda qur

awa Ameenatou idanuwansa dasuka qarasa sauyawa gaba Daya suna yin wani Jan tashin hankali da masifa.

Kaman tasan abinda ake ciki ta juya Kwanciyarta ahankali zuwa Dayan bangaren Wanda Hakan ya bayyanarda cikin sosai take Babbah ya sarqe da yawun bakinsa

da suka kasa wucewa sbd muguwar bushewan da maqoshinsa yayi take.

"Innalillahi wainna ilaihirrajiun,

Innalillahi wainna ilaihirrajiun,

Badai ciki ba wannan sedai koshi ne yayi mata yawa Amma tayaya zaa samu ciki a jikin yarinyar datake budurwa Babu m

iji,Babu hankali Kuma tana can killace asibitin da baama barin kowa shiga sai dole.

Wurgi yayi da kayan gabansa Yana miqewa tsaye jikinsa na sake jiqewa da zufa ya Saka takarmansa Yana cewa

"Shiryo asibiti zamu yanzu basai gobe ba"

Miqewa dadah ta

yi tareda shiga daki ta shirya ta fito ta dauko hijab ta tayarda Ameenatou ta Saka mata suna kokarin fitowa Hafiz ya dawo ya tsaya Yana kallansu cikin mamaki Amma Kuma ganin Babbah a mummunan halinda Bai taba ganinsa ba a ciki ya Sakasa Maida kallansa kan

Dadah da jikinta yake a mace gaba Daya Babu kuzarin komai,

Ameenatou ya kalla itama yaga ita baccinta ne ma Bai isheta ba fuskanta duk a daure sedai itama a kasalance take.

Magana zaiyi Babbah ya dakatar dashi ta hanyar cewa suje kawai.

Ciki ya sh

iga ya ajiye ledan siyayyar kayan tea da wasu abubuwan Daya siyo ya fito ya rufe gidan ya biyo bayansu zucuyarsa Shima tini tayi nauyi ta shiga Wani mummunan damuwa Yana fatan ba wani abin ne ya samu Ameenatou dinba Dan zuciyarsa bazata iya dauka ba Dan ya

nzu haka duka nemansa akanta ne sbd ita yakeson yaga sun samu sauyin rayuwa itada iyayensu.

Mota Babbah ya tsayar ko Gani sosai bayayi sbd yanda zuciyarsa ke bugawa da hawan jinin Daya kamasa take Amma bazai iya tsayawa ba idan ba asibitin suka Isa ba l

ikita ya kallesa ya fada masa gaskia duk da yasan gaskiyar zata iya illata rayuwansu gabaki dayansu Dan Ameenatou itace hasken zuciya idanuwansu da illa Daya gareta tamkar radadin mutuwa ne garesu.

Shiga motar sukai Hafiz na gaba ya kasa tambayar komai

sbd fargaban abinda zaa iya fada masa duk da Bai taba kawo tinanin ciki ba sbd abune da yama manta da cewan ita macece ma gaba Daya.

Suna Isa asibitin Hafiz ya sake shiga rikitaccen tinanin ko Wani ciwon ne ya kama Ameenatou Dan haka ya matso da sauri y

a kama hannunta Yana kallan fuskanta zaiyi magana Babbah ya silale qasa ya zauna Yana cewa Hafiz yayi komai likita zasu Gani yanzu yanzu.

Jin Hakan ya saki hannunta nauyin zuciyarsa na qaruwa ya Isa inda ake yanka Kati ya biya komai take aka Basu Kati s

bd Babu layi Kuma asibitin private ne Dan haka duka abinda ya samo haka ya tattarasu Akai komai akace a shigo da ita.

Dukkaninsu suka shiga dakin ganin likitan.

Kallansu Dr yayi da mamakin ganin su dukan yace su fita ita kadai zasu bari.

Hafiz ne

ya samu karfin yi masa bayanin matsalarta ta Rashin hankalin.

Hakan ya Saka Dr din Dan kallansu yace to yanzu Menene matsalanta.

Kallan Babbah Dadah tayi kafin ta Kalli Ameenatou din

Shi Kuma Hafiz su babban ya kalla Yana jiran Jin Abinda ya kawosu

.

#MAMUH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_

Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200

*

_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

[

5/18, 12:38 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*

#ZafafaBiyar

97

*_AISHA's COLLECTION_*

Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?

Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?

Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo

muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..

Hajiya da kayan da kika sani da Wanda

Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,

ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancew

a a cikin kasuwanci damu...

Join our group to see lot of our amazing products

👇

Location: LAGOS

We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

************

EDD din Ameenatou sauran sati uku Hafiz ya shir

ya kudaden da suka Tara na haihuwar ya cewa Babbah interview aka kirashi Abuja ya tafi Lagos kwanansa biyu Yana yawo a tsakanin companies din JDENS Dake Lagos Babu nasara harya Yanke shawarar dawowa dai sai Kuma ya tafi Dayan kamfanin Wanda shine ma ya far

a zuwa daga farko.

Cikin ma'aikatan da zaawa interview ya samu ya shige daqyar Allah ma yasaka da takardunsa ya tafi Daman Dan Koda Allah zai basa wani aikin duk da basuda raayi ko kadan na zaman Lagos Kuma.

Director din kamfanin ne ya kallesa lokaci

nda ya gama jero masa bayanin Omar Jaden da kansa yakeson magana dashi idan da hali Kokuma a Isar masa da Sako Dan Allah.

Sake kallansa yayi a wulaqance zai kira securities Hafiz din yayi saurin sanar dashi 'yar Jden dince ta cikinsa ake magana Akai yay

i masa alkawarin ba karya yakeyiba.

Sake mamaki da takaicin zancen yayi sbd a saninsu Jden baida 'ya ko 'da.

Rantsuwa da magiya cikin qasqantar da Kai Hafiz yaci gaba da rokonsa akan Sako kadai yakeson ya sanar masa Wanda yayi masa alkawarin wlh tall

ahi sai Jden yayi masa matsayin da baiwa kowa ba akan wannan sakon.

Tsoki director ya sake Yana daga wayarsa ya kira securities kawai.

Da sauri Hafiz ya Ciro numbernsa Dake dauke da cikakken sunansa Dana Babbah ya ajiye gaban director Yana magiya da

rokonsa akan wannan sakon kadai yakeson a isarwa Jden din batareda cewa komaiba.

Jansa securities sukai ciki zafi da wulaqantawa suka fice dashi har wajen gate suka miqawa Yan Sanda Dake waje suna Jira.

A station Hafiz din ya kwana washe gari suka sa

kesa da kansu ya fito a wahalance yunwa da zazzabin wahala na Neman illatasa Amma hakanan ya daure tareda dangana ya hakura akan maganar Neman Jden yabarwa Allah komai inshallah zasu samu mafitan da zasu reni babynsu da kansu.

A ranar ya tattara ya shig

o motar dawowa gida.

Bayan dawowansa jinyar wahala datake cin jikinsa da rayuwarsa yayi tsawon kwanaki Amma dole ya daure ya tashi yaci gaba da fita nema sbd Babu me nemowan sai shi.

Acan kuwa director bayan tafiyar da Akai da Hafiz samun kansa yayi

da rarrabuwar tinani,

A iya saninsa Sir Jden Bai taba haihuwa ba Amma Kuma kaman yanda ake magana dukkanin dukiyarsa sunan AMEENATOU ne Akai Wanda da yawa suke cewa sunan matarsa ne data rasu wasu Kuma suce matarsa ta rasu bazai yiyu yaci gaba da Saka s

unanta akan kadarorinsa ba da dukiyarsa,

Wannan shine sirrinsa Daya da kowa ya rasa gane gaskiyarsa ko maanarsa,

To idan da gaske wannan yaron yakeyi Jden nada 'ya Kuma tana hannunsu???

Idan ya miqa sakon zai iya samun matsayin dayake buri kuwa??

T

abbas zai gwada sbd a banza wannan matashin bazaiqi fadan komaiba ya Bada number kawai da suna Wanda Hakan na nufin Jden din na Gani zai iya gane komai kenan??

Kwana biyu director yayi Yana shawara da Tinanin gwada sa'arsa Dan haka a kwana na hudu ya da

uko sakon Ya zubawa takardar idanuwansa dakyau ya qarewa sunan Hafiz Nuhu babbah da Nuhu babbah sai Kuma AMEENATOU NUHU BABBAH da manyan baqaqe kafin numbernsa a qasa.

Shiru yayi Yana sake karanta sunan AMEENATOU din Wanda yanda yake rubucen Nan kusan h

aka sunan yake rubucen a cikin zuciyarsa na tinanin Allah yasa Hakan ne a zuciyar Jden.

Shi kansa baida matsayin magana da Jden din direct Wanda ya Yanke alaqar komai da Nigeria Yana jinya Amma a saninsu ya warke a kwanakin akace Amma dai babu Wanda yas

an a qasar dayake.

Da Sir Ahmed suke magana Shima kusan sai Wanda yakai yake iya magana dashi sbd shi kansa babba ne me girman da sai me babban matsayi Amma shi dayake Yana cikin masu yawan gaidasa a waya Dan haka Yana communicating dashi Kokuma yace Ya

na bibiye dashi sbd duk sati Yana tura masa sakwan gaisuwa sbd Baya daukan waya sedai ka ajiye masa Sako.

A yanda takardar take hotonta kawai ya dauka tareda turawa Sir Ahmed din ta Whatsapp sbd yasan ko ya kira ba dauka zaiyiba Dan haka ya tura Yana fa

tan gwajin sa'ar da yayi ya zamar masa alkhairi.

Ameenatou na shiga satin haihuwanta Hafiz yaje Nasarawa ya qarasa siyar da Rabin gidansu ya dawo da kudin suka Siya mashin din da zai fara sana'ar Dan Acaba Sbd dole Saida Hakan tinda haihuwa zaa musu,

Rago suka siyo aka daure na radin sunan abinda zaa Haifa,

Sauran kudin Kuma abinci suka Siya da Yan kayan buqatan Ameenatou wadda zuwa lokacin gadan gadan sauki yake zuwan mata sbd halin quncin dasuke ciki tini ya Dade da tafiya da walwalanta.

Kudin s

un qare Dan haka Dan sauran abinda ya rage suke lallabawa Dan kuwa kudin da suka tanada na zuwa haihuwa tini suka shige a lalura Amma suna da tsammani tinda Acaba Hafiz din yakeyi Wanda shi Kuma a nasa bangaren Bai fara ganin haske ko Daya ba a Harkan acab

an.

Ana gobe EDD din Ameenatou zai cika kaman a mafarki cikin dare Dadah taji Wani irin sautin kuka me karfin gaske daya Saka dukkaninsu fitowa rikice suna nufo dakinta Babbah na cewa haihuwa ce.

Hafiz Jin yayi gabansa yayi mummunan faduwa sbd Babu k

udin komai a jikinsa hakama tausayin Ameenatoun yake ji kaman zai fasa kuka.

Babbah ne a gaba suka shiga dakin gabaki dayansu suna kunna hasken wutar dakin da Babu komai acikinsa bayan katifa da jakar kayanta ta sakawa.

Ganinta zaune tsakiyar katifa

rungume da cikin jikinta kanta aqasa tana Wani irin kuka sosai Mai tsananin tsima zuciya Wanda Bata taba yinsaba a rayuwarta tinda aka haife takeyi dukkanin jikinta na Wani irin rawa.

Tsayawa Dadah tayi cak daga inda take sbd take ta fahimci meyake faru

wa itama take Hawaye suka balle mata jikinta na tsananin sanyi tana kasa qarasawa.

Babbah da Hafiz ne sukai kanta da sauri sedai hannu Dadah ta miqa ta riqe hannuwansu tareda girgiza musu Kai tana cewa

"Ku barta tayi kukan ta dawo daidai ne Inshallah

"

Da sauri Babbah ya juyo ya Kalli Ameenatoun idanuwansa na cikowa da wasu irin hawayen farin ciki da baqin cikin lokaci Daya sbd ta dawo daidai ta samu kanta da wannan mummunan kaddarar ta haihuwa irin wannan da ko ita bazata Tina waye yayi mata wannan

zalincinba.

Hafiz kuwa kasa riqe nasa kukan yayi yafara Hawaye kukansa na cin karfinsa ya fasa ahankali Yana qarasawa gurinta ya ambaci sunanta cikin radadin zuciya murya na karyewa.

Ambatar sunanta da yayi ya Sakata cusa kanta cikin kafafunta tana

sake fashewa da kukan dayafi na farkon tsima zuciya.

Rawa muryan babbah keyi Yana riqe kukansa yace

"Ameenatou sai hakuri,

Haka Allah yaso,

Kaddararmu ce wannan,mudai fata da burinmu Daman kece Kuma tinda munsamu kinzo hannunmu cikin Aminci da yard

arsa ai mun gode masa wannan Rabo Kuma shima dai mum Barwa Allah komai mun karba allah zai Saka mana ga duk Wanda ya Miki Hakan, inshallah zamu samu kyakkyawan sakamako daga ubangiji,Abdul ya tafi sedai addua shima,Haroon ma sedai adduar......

Kasa riqe

kukansa yayi ya fasa Wani kuka mara sauti me tsananin ciwo da radadi Yana sauke Kai sbd dukkaninsu baqar Rana ce wanna garesu ta haihuwan Nan,

Da ace aure ne akan Ameenatou da haihuwar Nan da sunfi kowa farin ciki da murna Amma shikenan yanzu basuda wani

farin ciki bayan fatan saukanta lafiya ta tashi lafiya itada abinda zata haifar musu.

Hafiz ma kuka yakeyi sosai kaman qaramin yaro sbd dawowanta daidai sai yanzu ne zasu koka rashin Dan uwansu da sukai Abdul.

Dadah ma kukan takeyi an rasa me magana

a cikinsu Daren tsit hakama gidan tsit sannan dakin ma tsit sheshekan kukansu ne ke tashi kowannensu zuciyarsa kaman zata mutu sbd radadi da Kuna tareda damuwanda basusan Yaya zasuyi ba Kokuma ta ina zasu fuskanci rayuwa yanzu.

Kukanta yafi na kowannen

su tsananin radadi da azabar zuciya sbd batasan ma Me ake nufi da duka bayanan da akeyiba abinda ta sani kawai shine Haroon ya rasu hakama Yaya Abdul to Amma a Ina ta samo cikin jikinta?

Aure Akai mata da wani batareda tana cikin hankalin kanta ba........

.

Fashewan ruwan nakuda ne masu karfi ya Saka dukkaninsu dago jajayen idanuwansu suna kallan ruwan dayake gangarowa daga karkashinta.

Dadah na ganin Hakan tayo kanta sedai Kuma take azabbiyar ciwon mara ta tinkarota gadan gadan cikin tsananin ciwo da

azaba ta dago jajayen idanuwanta ta Kalli dadah Dake tambayarta nakuda ta taso ne?.

Fitowa su babbah sukai daga dakin sbd sosai nakudar ta taso mata me azabar radadi.

Rikicewa Dadah ke Neman yi Amma sbd dare ne dole ta nutsu tafara taimaka mata tind

a Babu Daman zuwa asibiti yanzu hakama Babu Daman Kiran Mai Taimkawan.

Cikin qanqanin lokaci Ameenatou tafara ficewa hayyacinta sbd azaba da wahala,

Hafiz kuwa sai duba wayarsa yakeyi Yan fatan gari ya waye da wuri ya fita Neman kudi kafin a haihun

Babu komai na abinci Kokuma abin Sha a gidan bare kudin siyan magani.

Babbah kuwa gabaki Daya fita hayyacinsa yake Neman yi da ciwon kirji ya taso masa sosai sbd ranar yau din tana dawo masa da tinanin komai na ranar da Aminatunsa take nakudar haihuwan

Ameenatoun Kuma a ranar ne ya rasata rashi na har abada.

Nakudarta tayi nauyi sosai Dan haka tafara gabalaita karfinta yafara karewa daqyar suka samu Safiya tayi Hafiz ya fita jiki na rawa zuciya ba kwari Neman abinda zai samo ya kawo ko asibiti ne s

ai atafi akaita.

Yana fita Dadah dataga tana Neman rasa 'yarta fita tayi hayyacinta ga hadari me tsanani ya Hadu ana kokarin fara yayyafi ta fita ta Nemo Hafsatu me karban haihuwa Dake maqota dasu.

#MAMUH

[5/18, 12:38 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*

#ZafafaBiyar

96

*_AISHA's COLLECTION_*

Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?

Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?

Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sar

i,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..

Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba

na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,

ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...

Join our group t

o see lot of our amazing products

👇

Location: LAGOS

We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

*************

Cikin sanyi da nauyin zuciya Dadah ta Bude

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login