Showing 120001 words to 123000 words out of 182667 words
da baima duba ko nawa bane ya
bawa adekunle ya sallamesa Shima takowa yayi a hankali ya shigo kaman yanda sister Ashley ta Tako ta kama hannun Ameeenatou kaman yanda take mata a baya ta shigo da ita gidan tana share hawayenta takaita har Palo ta zaunar da ita.
Kasa magana dukkaninsu
sukai Ameeenatou sai kawai ta fashe da Kuka me sanyi tana kasa kallan sister Ashley.
Hakan ya Saka jikin sister Ashley mutuwa itama ta share hawayen da suka gangaro mata ta dawo gefen Ameeenatou din ta zauna tanason tabata Amma tana shakkar hakan sbd g
anin rayuwar bayan data yanzu ba daya Dan haka ta mayarda hannunta data dago Dan tabata..
Hannun Ameeenatou ta kama da hannuwanta duka biyu tareda dagowa ta Kalli fuskan sister Ashley da itama ita ta kalla ta Bude Baki a hankali Cikin sanyi tace
"Sam
e Ameeenatou dinki ce Babu sauyi akan hakan"
Wani numfashi da sanyi ne ya saukarwa Ashley lokaci daya Dan haka ta rungume Ameeenatou ta fasa kukan data dibi shekaru tana Adana Ciwo aranta batai Kuka ba sbd ko Babynta data rasa batai kuka ba sbd batada w
anda zataiwa kukan,
Tsawon shekarun Nan duk qunci da baqin Cikin rayuwar datake Ciki Bata taba zaunawa tayi Kuka ba sbd batada kowa da zai rarrasheta Dan haka zafin da ciwon ya maqale mata arai sai yanzu taji duka nauyin Yana sauka data ga Ameeenatou ta r
ungumeta da qarfi tana sake fidda sautin kukanta.
Shiru Ameeenatou tayi tareda bawa Ashley daman kukan yanda take so tsawon lokaci kafin ta saketa ta dago jajayen Idanuwanta ta kalleta kafin ta Bude bakinta tafara tambayarta lafiyanta da yanda take.
Cikin kulawa da sanyi ta amsa itama ta tambayeta yanda take.
Murmushi me sanyi Ashley tayi tana kallan nutsuwa da Class din da Ameeenatou din take tattare dashi ta sake sake murmushi tana Tina baby Ameeenatou dinta a Lokacin asibitin.
Hafiz da Shima
sai alokacin ta juyo suka gaisa ya gabatar mata da kansa
Cikin kulawa ta amsa masa tareda tambayarsa babbah sbd ta fahimci shi 'dan babbah ne.
Da mamaki suka kalleta ta sake murmushi tana cewa
"Yes na San babbah sbd shi Bai fita a bakinta ba ai ko a
wancan lokacin shine da Haroon a bakinta kafin Jamaal yazo ya shiga harya koma shi kadai ne take ambatar."
Da Wani Sabon mamakin suka sake kallanta kafin Ameeenatou ta share hawayenta tana son tambayarta tasan tanada Ciki Koda tabarta asibitin Amma K
uma ta kasa hakan sbd batasan tayaya zata fara tambayar waye yayi mata Ciki ba.
Hafiz daya fahimci hakan hakama ga dare yanayi Kuma dole ayau zasu koma Lagos saiya gyara zama Kai tsaye ya Kalli sister Ashley data kawo musu ruwan pure water masu sanyi ta
ajiye gefen Ameeenatou tanajin kaman zata hadiyeta sbd kauna ta zauna yafara jero mata bayanin Asalin rayuwarsu da komai da komai da ake Ciki har zuwa yau din da suka taho gurinta.
Shiru tayi tana sake shiga tashin hankalin da mamakin masifun da aka je
ro a Cikin tarihin komai.
Numfashi ta sauke tana sake jinjinawa Dad Omar da tausayinsa harma da girmamawa sedai Kuma Jamaal ma ko acikin zancen shine jaruminta Kuma zaici gaba da zama zataci gaba da zama yar amanarsa har abada Dan haka Bata ce komai ba
dakinta ta shiga ta dauko tsohuwar laptop dinta da duk ta goge ta kunna ta nemo folder guda data boye wadda Babu abinda yake Cikinta sai hotina da videos din da suka shafi Ameeenatou Tin daga wainda take mata ita daya tana aikawa siddeeq tin kafin Jamaal y
a taho har zuwa inda Jamaal ya taho rayuwarta ta sauya gaba daya ta koma cikakkiyar mutum Da wainda take mata idan Suna gyara Kai Bata yadda dana rigimar datake wa Jamaal harma da inda yake fama da ita gurin cin Wani abin idan ba tea ba.
Tinda suka fara
kallan abubuwan Ashley ke dorawa da bayanan da sukafi na wainda suke kalla tashin hankali da mamaki tareda tsananin shock na jin hadda irinsu wanki Jamaal din da kansa yasha Yi mata da Kuma illata rayuwar Wani akanta kafin ta dire da baby a date na ranar
da Jamaal yafara kwanciya da ita amtsayin mace tareda Bata tabbacin itace takaisa ga hakan tareda karfin son dayake mata hakama kaman yanda siddeeq ya sanar da ita kafin tafiyansu JAMAAL ne wanda tafara Gani rayuwarta ba Haroon ba,sannan ta rufe zancen da
cewa
"Dr JAMAAL SEELAH shine uba Kuma mahaifin duk abinda kika Haifa sbd da cikinsa ne a jikinki kika bar asibitin Dan haka babynki bana kowa bane na mijin da shi kadaine igiyoyin aurensa suke kanki"
Kasa motsawa Ameeenatou tayi bare iya magana sbd
numfashinta daya toshe Dan nauyin da kirjinta yayi me tsananin gaske.
Hafiz da jikinsa yayi mugun mutuwane yayi saurin riqota sbd jikinta dayake Dan rawa Bata ita numfashi da kyau.
Ashley ma da sauri tayi saurin tarota Suna Kiran sunanta a tare Cikin
damuwa da tashin hankali.
Hafiz ne yayi saurin cewa suyi asibiti kawai.
Itama Ashley Naam tayi da hakan Dan haka suka fito da ita Hafiz ne dauke da ita ya Saka motar Ashley ta shiga suna kokarin shiga yace Ashley ta dauko abubuwan buqatanta Dan Lago
s zai wuce direct baya buqatan asibitin Nan.
Handbag dinta kawai ta dauko tareda cheques din Dad Omar sbd ayau da akaga motocin da suka kawo mata ziyara Wani bayan Wani ko tana gidan sai barayi sun shigo mata bare anga ta fita.
Hafiz kuwa Cikin Wan
i irin speed ya kamo hanyar Lagos dasu har lokacin numfashin Ameeenatou daqyar yake fita Ashley na tarairayarta da Bata taimakon gaggawa.
Koda suka isa Lagos tayi laushi sosai ko hannunta Bata iya dagawa Dan haka Kai tsaye asibiti ya nufa da ita tareda
daga wayarsa ya kira Dad Omar wanda yanajin hakan Bai sanar da kowaba daga shi sai Ahmed suka nufi asibitin gashi dare yayi sosai.
Suna isa suka tararta Ashley asibitin take Dad Omar da uncle Ahmed suka shiga tashin hankali sedai Ameeenatou dataqi sakin
hannun Ashley ya hanasu magana da ita dole suka bar maganar sukaita lafiyan Ameeenatou din wadda da gasken gaske shock ne yakusan Bata attack.
Ashley da Hafiz da su Dad din Babu me magana sai gumi suke hadawa kowa Cikin tsananin fargaba har kusan asuba
tukuna ta dawo daidai sedai abinda tafara buqata shine Ashley.
Suna shigowa kallan Dad dinta tayi a hankali Cikin kasala bayan ta riqe hannun Ashley Cikin nata ta Bude Baki ba qarfi jikinta tace
"Dad wannan itace Ashley din Ameeenatou,
Itace wadda
tasan JAMAAL SEELAH ne mahaifin ARFAT...." sai a Lokacin ta fashe da wani irin Kuka Mai ratsa zuciya da sanyi tana kasa qarasawa.
Shiru duka dakin sukai Dad dinta Yana rintse Idanuwansa da sukai jajir sbd Bai dauka lamarin zai saurin cabewa da wuri ba d
uk da baima kawo tinanin Ameeenatou tasan uban danta ba Jamaal kadai yayiwa Ashley gargadi Akai.
Cikin Kuka me tsananin ratsa zuciya Ameeenatou ta fadawa Dad irin rayuwar datai tana Jin radadi a zuciyarta.
Ganin munin halinda take Ciki ya Saka Dad di
nta zaunawa kusa da ita ya Bude hannuwansa ta fada jikinsa ya rungumeta Yana Bata tabbacin komai ya wuce Kuma suna Nan akan bakansu sanin uban Arfat ba Yana nufin basa kowacce irin Dama ba duk da Shima zuciyarsa ta girgixa da rayuwar da Jamaal yayi da Amee
enatou din ya jingine komai na rayuwarsa ya koma Yana Aiki a karkashin wasu sbd Bata kariya kawai Amma Yana buqatan gama hada shirinsa na Kai Mam qasa kafin ya bawa Jamaal Dama.
Ashley ta kalla tareda kallan Dad dinta ta sanar dashi bazata iya rabuwa da
Ashely ba duk inda take Ashley na tareda ita daman alkwarine yayi mata idan Taga Ashley zasu inganta rayuwarta kaman jininsu.
Kallan Dad Omar Ahmed yayi Shikuma baida abin fada bayan sauya shirinsu zuwa na ajiye Ashley a tareda su Dan hana komai fita.
Anan asibitin suka rufe zancen Babu wanda zaisan zancen a family bayan iya su Dad ya kashe zancen kwata kwata kaman yanda ya aminta Ashley ta zama daya daga cikinsu.
Ameeenatou da zuciyarta take a nauyaye da abubuwa da yawa kasa walwala tayi hakanan
suka tattaro da safe suka dawo gida bayan anyi discharging nata.
Hannunta na Cikin na Ashley ta kamota Dan itace da kanta zata shigar da ita familyn jadens ta zama tasu Babu abinda zai sake rabata da Ashley kaman yanda sukai wannan alkwarin.
Hakama z
ancensu sun kashesa acan ko gidan Basu shigo dashi ba anbar maganar waye uban Arfat rayuwarsu zasuyi kawai sedai Kuma zuciyarta ta shiga tsaka me wuya San tinaninta dayake rarrabuwa.
Shima Dad hankalinsa ya Dan kwanta sedai Kuma Yana shakkar zuciyar Ame
eenatou din a yanzu datasan waye uban Arfat da Kuma Asalin sanin irin tsananin son dayake mata.
#MAMUH#
[5/24, 6:21 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
120
*_HONEY DROPS_*
Albishir! Albishir! Albishirrrr!!!
Kin gaji da wula’kancin miji, ke ke nan ku
llum hantara da kyara , an hana miki rawar gaban hantsi a gidan aurenki, shin ko baki San gabad’aya dadin aure ba?. Hajiyata idan kina da kyau ki ‘kara da wanka, ke ke nan kullum babu wani sauyin dandano kullum zuwa kike wajen oga yadda kike, haba mana ba
darajarki ba ne, mace ai ‘yar gyara ce, a d’in ga yi ana cleansing ana kuma spicing other room affairs. Sannan a gyara boobs d’in nan su cika su yi ma sha Allah a bar barinsu kamar guga, yanzu mace figure 8 bata burgeki ki ga ko ina ma sha Allah ga na Oyoy
oo ga na bye bye, kina da HONEYDROPS me ya kai ki shaawar wata bayan kema tsaf zaki koma haka. To gyara ki ji ni da kyau HONEYDROPS wannan shahararren kamfanin na Aphrodisiac ma’ana kayan mata sun shirya tsaf don kawo muku zafafan kayan gyara wanda zaki ma
llake oga tsaf tsananin dadinki da niimarki, kayanmu aiki suke kamar yankan wu’ka kuma babu boka ba Malam, tsananin sanin makamar aiki ne kawai. Kayanmu na saka oga kyautar dole, muna soyayya da kulawar dole, suna birkita lissafin kishiya don dole ta ha’ku
ra ta zama borar coz yan ajin HONEYDROPS a kullum sune Mowa, Muna…Muna… Muna…Muna fitattun kayan da ba su da na biyu kamar su
Infection flusher big 5k, small 3k
Breast firming sabaya 4k
Breast enlargement and hips sabaya 4k
Echoes of forever 3k
Her
royal highness 2500
Milky vjay cake 3500
Ever bond 3k
Eternal flame 2k
Love nectar 2k
Cleanser pro 2500
Endless seduction 1500
Intensive love 1500
Swan 3k
Mowa’s secret 4k
Sugar queen 7k
Cloud9 4k
Sweet16 tightening gel 4k da sauransu. Muna da
gumba kala-kala, tsumi kala-kala, muna dahuwar kaza, nama, tantabara, Ciccibi da sauransu. Muna da branches a garin Sokoto da Kano, sannan muna aike ko wani gari kowacce ‘kasa cikin amincin Allah, muna maraba da masu siyan daidai ko sari.
Za a iya tuntuba
rmu ta lambobi kamar haka
08167888934 ko
07026039714.
Ki yi ‘ko’karin ki tuntubemu don tabbas kukan damuwarki ta qare. Zaki iya tuntubarmu ta Instagram link dinmu kamar haka
https://www.instagram.com/honeydrops013?igsh=MW5saThrY3N0Z2Zjag%3D%3D&utm_sou
rce=qr
***********
Suna isa mansion din kowa sai a Lokacin yasan baa gida suka kwana ba shi babbah Baima saniba sbd Suna part dinsu.
Mum Nur ce da masu Aiki Dake aikin tsaftace koina suka tarbesu tana kallan sister Ashley wadda itama kallan Mum Nu
r din tayi tana gaidata.
Dad Omar ne ya gabatar mata da Ashley din Kai tsaye tareda sanar da ita ta dawo cikinsu inshallah zata zauna tareda su.
Cikin sakin fuska da bayyanarda farin Ciki Mum Nur ta miqa mata hannu tana Bata barka da zuwa jdens famil
y.
Godiya tayi tana miqa mata hannu.
Sama Dad Omar da uncle Ahmed Kai tsaye kowa bangarenda ya nufa sbd a matiqar gajiye suke kansu ma a cike yake da gajiyar tashe tashen hankalin da suka shiga Dan haka a yanzu da matsalar ya zama sun rufeta sun Kuma
riqe wadda take shadar a hannunsu Hutu kawai suke buqata.
Sarrah ce datake kitchen tana aikin breakfast din Arfat ta fito ta iso palon tana musu sannu da zuwa Cikin girmamawa tana karban jakar hannun sister Ashley cikeda girmamawa tayi sama dashi kam
an yanda Ameeenatou ta buqata.
Suma saman suka nufa hannunta na Cikin na Ashley sbd kuzarinta Bai gama dawowa ba.
Ashley ma jikinta Babu kuzarin sbd tsoron Allah da mamakin duniyar data samu kanta ayau aciki,
Tsari da asalin zubarwa da muhalli duk
iya take Gani ayau,
Bata taba shiga ko ganin zahiran gidan dayake da girma da luxuries koina ba sai ayau din,
A waya ko hotina or tv take ganin mansions Dan haka sai yau Taga asalin mansion wanda daga lokacinda suka shigo anguwar ma tasan ta baro Muna
Lagos ta shigo Lagos me aji,
Suna shigowa mansion din kuwa tasan ta shigo duniyar masu abin duniya uwa uba tinda suka shigo taji gashin jikinta na tashi sbd mamaki da ganin inda ake nufin anan yanzu zatai rayuwa.
A sama kuwa lafiyayyan palon Ameeenatou
ne sai bedrooms dinta Dana Arfat sai Wani daban daya iya su ne a saman Dan haka Kai tsaye ta Saka Sarrah takai kayan Ashley dakin wanda komai dayake cikinsa na musamman ne sbd duk abinda yake samanta na musamman dinne.
Lafiyayyan bedroom ne hade da mak
eken toilet me Fadi da walwala wanda Shima komai a Ciki sedai kayan amfaninta ne kadai Babu Suma Sarrah na ajiye handbag din sister Ashley din a Cikin wardrobe ta juya taje store na kayan kamshi da ire iren hakan ta dauko mata toiletries kaya guda ta taho
Dama dasu ta shiga toilet ta jere mata su.
Su brushes, toothpaste,hand wash, mouth wash, towels kusan 6 pieces Manya da qananu 4 sai Kuma sabulun wanka dasu shavers duk ta jere mata su ta sake wanke toilet din ta fito ta sake gyara dakin ta kunna ac da
humidifier ta fice.
Numfashi sister Ashley ta sauke tana sake kallan dakin jikinta na sake sanyaya kafin daqyar ta miqe ta nufi toilet Dan wanka sbd jikinta har Wani nauyi ya mata sbd kwamacalar asibitin da suka baro din.
Kafin ta fito wanka dayar me
aikin ta kawo mata dogayen rigunan Abayas masu kyau da tsada guda uku da sabbin undies da suke cikin bags dinsu ko tag baa cureba aka ajiye mata sai turarukan Da Suma na Ameeenatou ne aka dauko mata guda biyu masu shegiyar tsada aka ajiye mata gaban mirro
r tareda dai da duk abinda aka San zatai amfani dashi kafin a huta ayi mata shipping komai.
Suna gana ajiye mata komai suka fice tareda ja mata dakin wanda ya sauki sanyin ac da qamshi me sanyin gaske.
Ameeenatou ma wankan tayi ta fito ta shirya Ci
kin kaya marasa nauyi na bacci ma ta haye gadonta take bacci yayi gaba da ita me karfi sbd Cikin magani da alluran da aka saka a Cikin ruwan da aka Saka mata asibiti akwai maganin bacci me Dan karfi.
Gidan ma gaban daya daman basa fitowa da wuri Dan hak
a tsit kakeji
Itama Sarrah tana bawa ARFAT abincin safensa ta gyara dakinsa tareda Yi masa wanka ta shiryasa ta tareda maidasa bacci takaisa dakin mommansa ta ta kwantar gefenta ta fice tareda rufe dakin.
Ashley ma Jin shiru yasa itama bayan fitowa w
anka ta shirya a daya daga cikin kayan da aka ajiye mata ta nemi guri a bakin gadon ta zauna daga Nan ta zame ta kwanta itama tana son tintsawa Amma Kuma tinane tinane ya hanata sbd batasan inda rayuwa zatayi da ita ba Kuma yanzu data samu kanta a Cikin wa
inda take kauna suke kaunarta sbd Jamaal kaman yanda ta fada a gurinsa zata zauna Amma idan Ameeenatou tace ita takeso yanda take son hakan zatai.
A tsakanin Jamaal da Ameeenatou tasan kowa daman xaice shine zai zabeta,
Duka tana tsananin sonsu sbd All
ah daya Saka mata hakan ko Dan Jamaal dinne suka tallafi rayuwarta data mijinta Amma kaunar datakewa Ameeenatou jinta takeyi kaman jininsu ne daya,
Kaunace take mata kaman Babynta Dan haka kaunarce ta Saka takewa Jamaal kaunar data wuce misali sbd irin Az
ababben son dayakewa Ameeenatou tana Gani a Idanuwansa duk da bakinsa Bai furta hakanba Dan haka Bata Jin zata iya barin Ameeenatou tayi kuskuren rabuwa dashi sbd JAMAAL zai yadda ya rungumi balai Amma bazai taba sakinta ba kaman yanda ya fada mata a jiyan
ko su Dad dinta su yadda kokuma su Sha bakin mamakin dazai tada hawan jinin kowa masu sabo da masu tsoho.
Daga karshe dai itama baccin ne ya Dan dauketa Dan haka Koda Sarrah ta jero mata lafiyayyan breakfast a qaton tray ta shigo dakin Taga tayi bacci
fita tayi ta koma dashi tana rufe dakin a tsanake sbd kada ta tadata baccin.
Hafiz ma ciwon Kai Mai tsananin gaske da cunkushewan Kai Dana zuciya ne ya sakasa wanka kawai ya Kwanta Yana rufe Idanuwansa da sukai jajir sbd zuciyarsa Dake shiga tinani kala
kala musamman azababbiyar so daya fahimta a Cikin zancen Jamaal na yiwa Am,
JAMAAL irin mutanen da idan Suna yiwa Abu mugun so me karfi basa buqatan Bude Baki su fada sbd kallo daya ya wadatar ka gane Dan haka yasan Jamaal ba lallai ya Bude Baki ya fad
awa su Dad gaskia ba sedai zasu tabbatarda da hakan idan Basu aminta da aurensaba,
Sannan duka wannan tashin hankalin shine tayaya zaa boyewa Jamaal Arfat dansa ne?
Hakan zai iya yiyuwa kuwa har abada?
A baya tashin hankali da duka baqin Cikinsu shine
anwa Ameeenatou fyade an mata Cikin to Kuma yanzu sun Gano ba hakan bane,
Mijinta ne halak dinta yayi Cikin Kuma family ma ne me zai Hana a fito a fadan idan yaso a taru a boyewa wanda zaa boyewa din.
Numfashi ya sauke Idanuwansa na nauyi sbd ciwon Ka
i,.
Shi dai