Showing 162001 words to 165000 words out of 182667 words

Chapter 55 - AMEEENATOU COMPLETE

Unknown   

30 Aug 2026

36

Jamaal dinba.

Sama sama suka jajanta kafin suka fito Dan tafiya gida sbd doctora sunce ba zata kwana ba tana sake hutawa gida zaa koma da ita sai zuwa dare ko gobe su

sake zuwa gidan a dubata.

Suna fitowa Hafiz da babbah da maman fadeela da Ayesha suka fice daga asibitin a motar Hafiz.

Fara biyawa gida yayi ya ajiyesu har lokacin Ayesha bata Cikin cikakkiyar hayyacinta sbd tsoro da tashin hankali da mummunan firgi

cin zuciya datake Ciki na abinda duka yafaru da abinda taji akan mutuwar Mum dinta Dan haka Suna isa gidan dakinta ta shige ta rufe tareda zubewa qasa ta fasa Wani irin Kuka Mai tsima zuciya da tausayi tana tinanin ta tabbata kenan ita batada kowa yanzu sb

d Mam ne take tinanin Dad dinta da zaici gaba da zama mahaifi kuma ubanta Amma yanzu tsoron Jin sunansa ma da akeyi.

Bayan barin kowa asibitin sai alokacin Dad Omar ya sauke ajiyan zuciya Mai Dan taqaitaccen sauti Yana miqewa ya nufi dakin Kai tsaye

Shima ya shiga Cikin nutsuwa da kamewa kaman ba Cikin tashin hankali ya fito ba.

JAMAAL da har lokacin Idanuwansa Basu dawo daidaiba sbd zuciyarsa datake tsananin tafasa da Kuna har lokacin ya dago ya Kalli Dad Omar din wanda Shima Idanuwansa suke sauy

e Cikin yayi kokarin daidaitasu da kansa.

Janye Mum din yayi daga jikinsa Yana miqewa tsaye bayan ya sake kissing gefen fuskanta ya juya ya fice

Siddeeq ma bayansa ya bi uncle Ahmed ma sannu yayi mata tareda juyawa ya five daga dakin bayan yaja kofar a

ka bar su iya su biyun Cikin dakin.

Shiru dakin yaji Babu wanda ya motsa bare magana.

Itace ta fara dagowa ahankali ta kallesa Taga Idanuwansa kafe suke akanta Yana mata Wani irin kallo zuciyarsa na tinanin da Mam yayi nasarar illatata Yaya zasuyi

shi da Jamaal??

Takowa yayi ahankali tareda isowa har inda take tukuna ya zauna inda Jamaal ya tashi tareda miqa mata hannunsa Yana kallan Cikin tsakiyar Idanuwanta data kasa kallansa sedai ta dago hannunta da yayi mata Dan nauyi ta miqa masa tana Dan r

intse Idanuwanta.

Kama hannun nata yayi da nasa tafin hannuwansu na haduwa a tare suka sauke Wani ajiyan zuciyan shekarun da suka debo tin kuruciya na jira da fatan wannan ranar.

Dagowa tayi ahankali ta kallesa Shima ita ya zubawa Idanuwansa da jan d

a sukai har Lokacin Bai washe ba sbd radadin dayake cin zuciyarsa.

Tasan zuciyarsa tafasa takeyi kaman ta 'danta akan duka abinda Akai mata Dan haka ahankali ta daga hannunta daya wanda baya Cikin nasa ta Dora a gefen fuskansa ahankali ta shafa Cikin sa

nyi da nutsuwa da tsananin kulawa da so da rarrashi tana sauke hawayen da zuciyarta ta kasa riqewa sbd feelings da yawa.

Rintse Idanuwansa yayi Shima ahankali tareda sake damqe hannunta dayake Cikin nasa Yana Jin zuciyarsa na sanyaya ya Bude Ido ya sake

zuba mata su zaiyi magana ta Dora hannunta ahankali kan lips dinsa tana kallan farar lafiyayyar fuskansa data manyanta sedai kyansa da ajinsa da lafiyan fatarsa tin ta kuruciya haryanzu Suna Nan musamman yanzu da asalin Hutu da kwanciyar hankali ne da Arz

ikin gaske suka ratsasa komai nasa kaman ma yafi kyau a yanzu.

Cikin sanyi da nutsuwa tareda son tausarsa ta Bude Baki da rashin kuzari sosai tace

"It's okay,am okay inshallah Babu komai,banajin komai yanzu."

Ajiyar zuciya ya sauke me sanyi Yana D

ora hannunsa kan hannunta dayake kokarin sauka daga fuskansa ya maidasa datareda Dora nasa akan nata din Yana sake sauke ajiyan zuciya Cikin nutsuwa da kulawa tareda zafin zuciyarsa daya ragu ya furta

"Thank you for being okay"

Jin tayi zuciyarta na

narkewa da kalmansa Dan haka Idanuwanta suka ciko da hawaye sedai Bai bari sun saukoba ya janyota jikinsa ahankali ya shigar da ita tareda rungumeta Yana sauke ajiyan zuciyan data itama hawayenta suka sauko tana sake lafewa jikinsa.

Shiru sukai tsawon

mintina ahakan kafin ta Bude Baki Cikin sanyi da nutsuwa tafara fada masa abinda yafaru komai da komai tanajin Yana sake qanqameta alaman yankar zuciyarsa zancen yake Dan haka ta qarasa da rarrashinsa tareda nuna masa komai ya wuce inshallah.

Bayan rada

din abinda Mam din yayi mata babban shock dinsa shine yanda sukasan waye Arfat Amma sukai shiru tsawon lokaci batareda tada hankalin komai ba ko rigima wanda yasan itada Jamaal din sunyi hakan ne sbd tsananin respect dinsa dasukeyi da Kuma son bawa Arfat d

in da AM tsaro Amma duk da hakan sun basa tsananin mamakin daya sakasa Jin jikinsa yayi sanyi Dan baisan Jamaal zai iya masa hakan ba bayan ya Gano Arfat jininsa ne tsatsonsa ne Kuma ya zabi janyewa daga auren ya hakura yayi shiru sbd tsananin biyayya da b

in dokar maganarsa.

Itace mara lafiyar Amma kusan itace take rarrashin sbd yanda tasan shi da Jamaal Babu abinda zai hanasu daukan mummunan mataki.

A tasa zuciyar kuwa bazai bari Jamaal ya taba Mam ba sbd mahaifine koman zamansa Shedan Dan haka shine

dayake daidai dashi zai dauki matakin akansa daidai yanda ya dace sbd zai nuna masa Shima jinin SEELAHs dinne idan sun manta hakama akwai sirkin Ashlawa a jikinsa.

Babu jimawa doctors suka sallameta suka fito hannunta Yana Cikin na Omar Amma jikinta Ya

na Dan hade Dana Jamaal suka nufo mota tana tafiya ahankali.

A motar Jamaal zata koma gidan Dan haka Siddeeq ne ya Bude mata motar Yana komawa gefe.

Hannunta dayake Cikin na Dad Omar ya kalla kafin ta dago ta kallesa Shima ita ya kallan cikin kulawa

da nutsuwa yace "its okay Babu abinda zai faru bazamuyi abinda Bai kamataba, Jamaal ma is out of it,be okay."

Gyada Kai tayi ahankali sbd batason daga Jamaal din har Omar suyi abinda zai Bata imaninsu ko halinsu akan Mam Dan haka ta sake sauke ajiyan zu

ciya tana cewa "thank you" da qaramin sauti tukuna ta shige motar.

Jamaal ne ya rufe mata kofar tareda juyowa ya Kalli Dad din shi har Lokacin Idanuwansa Basu dawo daidai ba shi kadai yasan abinda yakeji.

Dad Omar rungumesa yayi Cikin tsananin kauna

da sanyi Yana cewa

"Karka damu zanji da komai karka tabasa ko kadan

Abinda kayi masa na Rabasa da komai ma yayi sbd shine Abu mafi Ciwo da karya rayuwa hakama hakan ne ya tabasa yayi wannan zarewan daya aikata hakan so ka cire komai ka Kula da Mum dink

a."

"Thank you Dad" Jamaal din ya furta Yana Jin zuciyarsa na Dan sanyaya wanda ayanzu 'yar Dad dince kadai ganinta zai qarasa wargaza nauyi da zafin dayake rage a Cikin zuciyar tasa.

Motar suka shiga siddeeq ya tada suka bar asibitin

Shima Omar din

Ahmed ne ya dawo da motarsu gabansa aka Bude masa ya shige take suka bar asibitin Suma.

Hanyar gida suka kama Omar na shiga tinani kala kala masu zafi da Ciwo da masu sanyi da nutsuwa.

Koda suka isa gida babbah ya sanarwa dasu dadah abinda ya faru D

an haka hankalinsu Mum Nur da Didi harma da dadah din ya tashi sai a Lokacin dadah ta hau sama gurinsu Ameenatou Dake fama da kansu ta samu Ameenatou din ta Dan samu sauki tana zaune Ashley na yanka mata apple da watermelon tanaci ahankali ta qara haske so

sai tareda yin bulbul sai alokacin dadah take sake lura da hakan sedai ganin batajin Dadi sai Bata Wani Yi musu dogon bayaniba ta Dan fada musu sama sama tana zaunawa gefen Ameenatou din Dan sake dubata.

#MAMUH

[6/6, 11:26 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*

142

Cikin kulawa Dadah take kallanta tana tambayar menene yake damunta ne?

Numfashi Ameenatou din ta sauke ahankali tana kasa kallan dadah.

Ashley dadah din ta kalla tareda sake tambayarta Cikin kulawa tana shafa wuyan Ameenatou din dayake dan sau

ran zafi.

Cikin sanyi Ashley tace

"Dadah zazzabi ne yake damunta na yawan Aiki sbd Bata son hutawa"

Kallan Ameenatou dadah ta dawo tayi tana cewa

"Budurwan Babbah gaskia Nima na lura da bakyason hutawa,

Meyasa kikeson takura kanki tinda Babu m

e Miki fada Koda Baki tafiba,

Kinga gashinan yanzu kina fama da zazzabi,

Dan Allah ki kiyaye kinji,

Banason wannan zazzabin sbd Abu kadan yake sakaki Ciwo sosai ayita fama kibi ki galabaita."

Sai alokacin ta dago ta Kalli dadah da Idanuwanta da suke

son cikowa da hawayen tausayin dadah da batasan komaiba kafin ta zame ta kwanta jikin dadah din tana lumshe Idanuwanta.

Dadah cikeda kauna da kulawa ta gyara mata kwanciyar a jikinta tana Jin tsananin kaunar 'yarta na qaruwar mata.

Koda su Dad suka d

awo kawai sama sama aka sake tattaunawa tukuna aka bar maganar sbd batada dadin cigaba da tattaunawa sedai Mum Nur tace anjima zasu tafi gabaki dayansu su dubo Dr Aleena din da daddare.

Dad Omar ne ya bada umarnin a bari sai zuwa gobe gabaki dayansu sai

su tafi dubota din sbd yau dai Kam akwai sauran shock a tattareda SEELAHs din.

Haka suka bari zuwa goben wanda Hafiz uncle Ahmed ya Saka ya sanarwa SEELAHs din Jadens na Nan zuwa gidansu dubiya acan zasuyi dinner.

Mum Aleena sosai ta ringa rarrashin

Jamaal tareda nuna masa samun saukinta kafin ya sake Dan dawowa daidai,

Siddeeq ma Saida Mum din tayi da gaske kafin ya Dena blaming kansa akan hakan duk da Jamaal yace karya sake Jin ya fada hakan sbd yasan idan Siddeeq zai bari a dauki ransa to sedai a

dauka Amma idan Yana kusa bazai bari ayiwa Mum dinsa hakan ba Dan haka ko a tinani bayason Siddeeq din na fadar hakan.

Maman fadeela ma Ayesha data rikice gabaki daya take kulawa da ita haka dai suka samu gari ya waye suka tashi da nutsuwa da kwanciyar

hankalin ajiye komai kaman yanda Mum din ta fada Dan haka Mum ita farin Cikin ma zuwansu da akace takeyi sbd zata ga Arfat wanda ta kwanaki da yawa Bata sakasa a idonta ba.

Maman fadeela ma haka ta ajiye Ayesha tayi mata nasihar data Saka jikinta mutuwa

ta rungumi qaddara ta barwa Allah komai tinda Jamaal da Mum Aleena sun karbeta da dukkanin zuciyarsu ta godewa Allah badan hakan ba Allah kadai yasan gantalin rayuwar da zai sameta Amma gashi tana Cikin rufin asiri da kauna da kulawa kaman wadda takeda uw

a da uba a duniya.

Hakan ya Saka itama Ayeshan rungumar kaddara ta barwa Allah ta 'dan sake,

Maman fadeela kitchen ta shiga Cikin masu Aikin gidan Dan kulawa da girke girken da zaayi na baqin sbd sanin daga Nan gidan har jdens din lafiyayyar cima suk

e ci Mai tsari da kyau.

Ameenatou dole ta tattaro karfi da kuzari ta warware sbd kada a gane halinda take Ciki sbd babbah daya fara mitar rashin lafiyanta tasan baya wasa da lafiyarta ko kadan.

Dad dinta ma Cikin kulawa ya sanar da ita fitar tasu b

ayan ya sanar da kowa maganar aurensa da Dr Aleena wanda ya Saka kusan kowa shock bayan wainda suka san da auren sedai Babu wanda yayi Wani magana bayan ta congratulating Dad din da sakawa auren albarka sbd Basu dauka hakan Wani damuwa ba Ameenatou ce kawa

i ta tafi gurin Mum Nur har bedroom dinta tana isa ta rungumeta ahankali Cikin sanyi da tsananin kulawa batareda tace komaiba ta nuna rarrashinta da jinjina mata kaunarta na sake cike zuciyarta sosai sbd Mum Nur takai uwa ta Dade da wuce matar uba a gareta

shiyasa take jinta har Cikin ranta.

Ahankali ta Bude bakinta Cikin sanyi tace

"Mum Nur Allah ya Saka Miki da mafificin alkhairinsa duniya da lahira,

Allah ya qara Miki hakuri da juriya tareda lafiya,

Thank you for being calm Mum Nur,

I love you"

Ahankali Mum Nur taji Wani sanyi da nauyin datake ji a kirjinta tin ranar da Akai auren ya fada mata sbd Babu wanda ya zauna da ita ya rarrasheta bayan mijin nata wanda yayi iya kokarinsa gurin rarrashinta da nuna mata kauna da tsananin girman datake da

shi a Idanuwansa sai Ameenatou din yanzu data rarrasheta batareda dogayen magana ba Cikin sanyi da kaunar gaskia Dan haka rungumeta tayi ahankali tana sauke numfashi me sanyi tana sake Jin har ranta tasamu sanyin komai game da auren.

Cikin kulawa da nut

suwa ta Bude Baki tace

"Thank you my baby,and I love you too"

Shiru sukai har Lokacin am na jikin Mum Nur din Suna debowa junansu kewa da Dan susar da zuciyoyinsu sukai ita am na mahaifiyarta da Bata duniyar ita Kuma Nur na kanta sedai Kuma yanda Dad

Omar Bai hada farin Cikinsu da komaiba ya sakasu Jin nasa farin Cikin na karbansa hannu bibbiyu da zuciya daya Suna tayasa murna har zuci musamman am din da yanzu ne take Jin asalin tarihin soyayyar Dad din da Dr Aleena tin Yana asalin baqar fatarsa baida

Wani gogewa sosai kaman yanzu.

A dakin Mum din suka wuni su biyun tana kokarin cire mata duk Wani abin damuwa ko makamancinta tinda da daddaren ranar zasu gidan SEELAHs din.

Jikinta ma jinta Yi ya warware sosai ba laifi sbd harga Allah taji auren a

farko kafin Kuma suka samu nutsuwa dashi hakama tasan mahaifiyar Jeey dinta bazata taba cutatar da Mum Nur ba sbd itama she's calm.

Ashley ma ta taho da ita suka qarasa wunin tareda Mum Suna debe mata kewa tareda nuna mata irin kaunar da suke mata harta

qarasa sakewa zuciyarta fes sukai lunch dinsu a sama su duka harma da Didi data taho Fatmah Kuma batanan ta fita zuwa spa sbd yau zata ga Jamaal.

Dadah ma sosai ta sake ganin girman Mum Nur suka Taru aka wuni Cikin walwala da farin Ciki har yamma tayi

tukuna kowa ya watse suka tafi dakunansu Dan sallan magrib da fara Shirin fitar.

Arfat Ameenatou tafara shiryawa da kanta Cikin wasu Ted Baker set na Yara Riga da wando navy blue sbd sune best kalan da akafi Siya a kayansa sbd sunfi komai fidda kalar fa

tarsa me kyau da tsananin haske.

Jacket ta Dora masa Akai da Valentino fcap itama navy blue sai jacket dinsa da talkarmansa na berluti dasuke ash me duhu qamshinsa me sanyi wanda sak turaren Dad dinsa ne ya zu ake masa amfani dashi sbd Jamaal din da kan

sa yake siyowa Yana bawa Ashley tana masa amfani dashi Wanda a duk lokacinda am taji qamshin jikin Arfat sai ta kusan hadiye numfashinta sbd tinanin Jamaal din na kusa sai take dena Saka masa indai ba Ashley datace itace take siyo masa ba ya shafa masa.

Itama wankan tayi ta shirya Cikin doguwar fitted abayar da dakanta aka aunata aka Dinka mata daidai jikinta shape daidai a Dubai dataje tareda Mum Nur a Lokacin.

Babu kwalliyar komai ajikin rigar bayan black crystal dasuke Saka rigar motsawa tana Dan d

aukan idon fidda asalin kudin da aka zuba gurin siyarta.

Qaramar veil Ash me duhu kalar takarman Arfat da jacket dinsa ta nade kanta dashi.

Babu kwalliya a fuskanta bayan eye Kajol me kyau dayake Cikin idonta ya qarawa Idanuwanta haske Yakuma sakata

yin kyau ko man Baki Bata shafawa lips dinta ba hakanan ta fito tana fidda qamshi me sanyi sai wayarta Dake hannunta.

Ashley ma dagowar rigar ce a jikinta me shegiyar tsada datake rawa da veil data nade kanta dashi itama qamshinta yafi na Ameenatou tash

i sbd ita Ameenatou saika kusantota kake jinsa har Cikin ranka sabanin ita nata Yana Dan tashi tinda ba igiyoyin auren kowa kanta gashi itama natan tsadar ne dashi.

Kaman hadin Baki itama Fatmah doguwar rigar ce a jikinta me shegen kyau da kwantawa a ji

ki maroon da black hakama Babu me makeup a cikinsu.

Didi ma doguwar Rigar Lafiyayyan lace ne ajikinta daya kwanta sai Mum Nur da ita Kuma Wani shegen material ne da kallansa kawai zai sakaka sanin ba kudi kadan suka siyesa ba Amma baida kwalliya sosai v

ery simple and unique doguwar Riga da mayafin da itama Rollin nasa tayi sai ta koma kaman yarinya a cikinsu Ameenatou din.

Dadah da babbah bazasu samu daman zuwa ba Dan haka su kadai zaa bari.

Hafiz kuwa Yana fitowa Cikin lafiyayyun Cesare attolini b

lack da suka fiddo kyansa da wayewansa fuskansa fresh da Hutu kawai.

Kallo daya Fatmah tayi masa ta dauke Kai tana barin gurin Shima Bai Kalleta ba ya qaraso Yana kama hannun yaronsa Wanda yake murnan ganinsa sukai gaba.

Sai a Lokacin Dad Omar ya fit

o Yana saukowa Cikin black Kaftans na Armanis da suke bayyanarda shine Asalin jden din a cikinsu sbd ilimin da wayewan bama daya ba sbd shine tushe.

Hannu ya miqawa Ameenatou Dake kallansa Cikin tsananin kaunarsa ta kama tareda shigewa gefen jikinsa kaf

in Mum Nur ta kama hannunsa daya suka fito Kai tsaye motocinsu Dake jere ana jiransu suka nufo.

Motar Dad Omar shine a Ciki da mum Nur sai Ameenatou.

Dayar motar kuwa Hafiz ne da Ashley sai Arfat da Fatmah sai dayar uncle Ahmed da Didi da Arry.

Ba

rin Mansion din sukai Kai tsaye tareda nufar asibiti suka fara duba Siyam wadda dangin Mum dinta suka taho Dan samun saukinta su tafi da ita gurinsu Wanda Dad Omar Bai Musa Hakan ba zai aikasu India idan taji sauki zasu dawo da ita hannunsa sbd shine zai r

iqeta dan shine mahaifinta kaf duniya a yanzu.

Sunji dadin hakan sunyi masa godia tareda jinjinawa zuciyarsa kafin suka fara Shirin tafiya idan ya kammala musu komai.

Zuwansa asibitin da iyalansa kaf ya sake basa girma sosai a Idanuwan dangin Mum Sar

rah din akan Siyam.

Suna barin asibitin Kai tsaye gidan Jamaal din suka nufa wanda Suma acan angama shirya dining room da komai gidan tsaf kaman Babu tashin hankalin daya faru a jiyan Kuma dayake tsarin ginin turawa ne Babu mahaukacin girman Nan sedai k

usan kana shiga zaka San gidan turawa kazo ga Babu hayaniya

Chiefs dinsu da Maids dinsu duka sun tafi bangarensu Babu Wani bako bayan su Yan gidan.

Siddeeq ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login