Showing 57001 words to 60000 words out of 182667 words
kulawan dayake Dan nuna mata da karban case dinta da yayi duk Yana sane,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun.
Zufa kowannensu ya sake sharewa hankali na tashi.
Dr Ibrahim ne yayi karfin halin tambayar Babbah dalilin
kamuwa da ciwonta da abinda yasa duk tsawon wannan lokacin Basu taho sunzo gurinta ba.
Ahankali Babbah ya zayyano labarin da kusan kowa ya sansa A ranar daurin auren 'dan Mam Seelah yayi taccident ya rasu tareda mahaifin matarsa da uncle dinsa Alh Omar
jden wanda tin da Akai accident din Babu Wanda ya sake Ji daga Omar din da ahalinsa.
Iya daga Nan labarin yake tsayawa koina batareda an Dora da sanin Ina amaryar take ba bare danginta tinda su talakawa ne baa sake tada nasu zancen ba.
Shiru kowa yay
i tsit na tsawon mintina kafin md ya Kalli Babbah cikin qarfin halin da kulawa yace
"Duka bayanai gasunan munji Kuma mun fahimta sosai Amma duk da Hakan sbd tabbatarwa da gudun matsala tareda cike doka zamu baka hakuri yanzu ka tafi zuwa Nan Da kwana bi
yu saika dawo inshallah zamu baka damar ganinta harma fiyeda Hakan idan ka buqata"
Shiru Babbah yayi cikin nazari da tinani kafin ya dago yace
"Ba iya ganinta nazo yi ba,sallama muke so mu tafi da ita gida insha Allah zamu nema saukin daga Allah acan
"
Daga md har su Dr Zakeer ajiyan zuciya me karfin gaske suka sauke a boye ta dr ibrahim CE ta fito fili sbd anzo inda yanzu Kam sukeson Azo Dan kuwa Babu Wanda ba tsoro da tashin hankali ne a ransa ba Dan alamun dai suna nunawa da gaske ita yar Jaden d
in ce tinawa da labaran rasuwar matarsa Da aka ringa yi a lokacin da Akai gobaran.
Wannan masifar da balain ko waye yayiwa yarinyar Nan ciki Allah ya Isa a tsakaninsu,
Dole ma suyi gaggawan binciken komai kafin jibi Babbah yazo su miqa masa yarsa su ta
fi tin kafin cikin Nan Daya fara fitowa ya bayyana su shiga masifar d batada kofar fita a hannun Omar Seelah.
Cikin girmamawa suka bawa Babbah tabbacin inshallah zuwa Nan da jibi yazo zasu duba su sallametan su basa ita din.
Farin ciki ne me tsananin
gaske ya rufesu babban yai godiya sosai suka fito.
Suna ficewa md ya miqe Ya dauko ruwan hannuwansa na Dan rawa yakai bakinsa yasha Yana Jin zafi Tako ina,
Yau da ace sunje zubar da cikin Nan Wani abin ya biyo Baya Yaya kenan zasuyi da seelahs?
Cab
dijam,
Jin yayi kwata kwata Babu abinda yakeso yanzu kaman Ameenatou tabar asibitinsu kota halin Yaya ne.
Kusan Suma su Dr Zakeer tinanin ne a ransu Dan haka take aka kira Dr Charles aka sanar dashi komai ya sauya,
Shi kansa Yana Jin Hakan ya ringa go
dewa Allah da matarsa Bata taba lafiyan Ameenatou din ba dan haka shi tin a cikin Daren ma ya fara tinanin Neman sauyin asibiti kawai Yama barta gaba Daya incase idan gaba tsautsayi yasa zancen ya dawo Baya.
Dr Zakeer ma fara neman yanda zaa sauya masa
asibitin yayi Dan hankalinsa Kuma ya tashi akan lamarin,
Bawa Babbah ita shine rufin asirinsu ayanzu to Amma Kuma dawowan Dr JEEY shikuma wani tashin hankalin ne daban duk da kaman yanda md ya fada bai nuna musu yar uwarsa bace koya dawo suma bazasu nuna
sun saniba magana Daya iyayenta sunzo an sallameta.
Cikin farin ciki su Babbah suke sukam Dan haka a masaukinsu da suka sauka na Wani hotel suka koma a shirye tsaf da Shirin tafiya kowanne lokaci.
******Sister Ashley Dake kallan Street din gabansu t
ana sanarwa me taxi din idan sun samu mutane a kusa pls suyi tambaya Dan batasan gidan datazo din ba itama.
Wayarta ce tafara ringing ta Kalli Jakarta Dake kan jikinta ta Bude tareda Saka hannu ciki tana Neman wayar.
Katsewa wayar tayi Wani kirin ya
sake shigowa ta fito da wayar tana kallan screen din
Bazata iya Tina lokaci mafi farin ciki a rayuwarta ba kaman yanzu da wani sanyi da farin ciki me tsananin gaske Daya cike zuciyarta ba ganin sunan Dr JAMAAL akan wayarta.
Hannunta har Wani rawa suk
eyi ta dauka da sauri tana hamdala farin cikinta da mutuwar jikinta duka a bayyane.
Tana dagawa kafin tayi magana muryansa tafara Ji cikin tsananin sanyi da nutsuwa yace
"Aslm alailkm."
Amsawa tayi cikin girmamawa jikinta na sanyi da yanayinsa sed
ai Bata karayaba ta gaidasa.
Amsawa yayi da murya me kama da yanayi na rashin lafiya kafin da kasala yace
"I'm sorry,bazan iya magana ba ita kadai nakeson Ji,Inason Jinta,pls can you.........
Katsesa Ashley tayi da cewa
"Dr JEEY kayi hakuri Amm
a kana buqatan Jina tukuna,
Ameenatou na dauke d........"""dip Kiran ya katse.
Wani mummunan accident ne ya faru sakamakon motar data dakesu batareda sun San da zuwanta ba ta gefensu Wanda ya Sakasu mugun bugawa da transformer Dake gurin wuta tafara Wa
tsi tana kokarin tashi.
Motar su BB da suka cirewa number tini tayi Baya duk da ta bugu sosai ta fashe ta gaba sbd yanda suka daki motar su Ashely din.
Reverse sukai suka bar gurin da mugun gudu goshin BB na zubar da jini sosai na buguwa Shima bullet
hancinsa jinin yake zubarwa kansa na juyawa Amma haka suka tsere sedai basuyi tafiya me nisa ba suka parker motar Wani gurin da Babu mutane suka fito tareda cire komai nasu suka bankawa motar wuta sbd bazasuyi wata tafiya me tsayi ba zaa kamosu hakama sun
bugu sosai Suma komai zai iya faruwa.
Mutane cikin gaggawa suka Dan taru sbd anguwan ba mutane sosai can JAMAAL ya siyawa umman gida,
Cikin gaggawa mutanen da aka samu sun shigo street din suka rufu aka motar dan taimaka musu.
Cikin yardar Allah
daga Ashley har drivern Babu Wanda ya rasa ransa amma Ashley ta bugu sosai hakama bleeding takeyi sosai daga cikinta Wanda ya Saka wata nurse Dake gurin itama cewa tana tinanin cikine a jikinta Kuma Kila fita zaiyi.
Da gaggawa aka kwashesu zuwa asibiti
sbd cetan ranta da abinda yake cikinta idan da akwai Rabon ya rayu.
JEEY kuwa tashi yayi daga kwancen dayake tareda zare roban drip Dake hannunsa ya tashi da kyau Yana sake Saka Kiran wayarta.
Cikin ikon Allah wayar Bata mutu ba Amma Kuma baa daga
ba haka ta ringa ringing Amma baa dauka.
Siddeeq ne da isowarsa kenan Poland din tareda Mam ya shigo dakin asibitin Yana kallan JAMAAL daya Dan fada yayi haske sosai idanuwansa sun qara haske ya dago idanuwan ya kallesu.
Ganin Dad dinsa a tareda sid
deeq din Wanda suka sauka kasar tare ya sakashi Dan dauke Kai Yana cigaba da Saka Kiran Ashley.
Tsakiyar dakin Mam ya iso ya tsaya akansa Shima kallansa yakeyi Yana auna irin hawan da jininsa yayi fiyeda a kirga sbd Jin JAMAAL din ciwon ciki me qarfi da
zazzabi tareda tsananin damuwan ciwon Mum dinsa daya kwantar da shi ba tsammani.
Bai taba tinanin sake zuwa qasar ba Amma bazai iya riqe kansa ba ko kadan ga zuwa ganin 'dansa Dan bazai iya komawa Nigeria dinbama da tinanin JAMAAL din ba lafiya.
Shi
ru ne ya ratsa gurin batareda kowa yace komaiba,
Mam yaqi magana ne tareda zubawa JAMAAL din idanuwa Dan kuwa yasan komai lalacewansa tinda ya Riga ya zama ubansa ya haifesa to ya gama da duk wani zafin kansa,
Shikuwa JAMAAL din da zafin kan nasa da
radadin uba Daya kasance irin nasa yake yakicewa kafin ya juyo a hankali cikin kamewa da fuskewa ya Kalli Mam din Kai tsaye ya gaidasa Yana komawa da bayansa ya kwantar tareda Maida idanuwansa akan Siddeeq da baida ikon magana duk yansa ya so batareda Mam
da Jeey din sunyi magana ba duk kuwa da yanda ya matsu ya iso yaga jikin JEEY din Dan ba qaramin tashin hankali suka shiga ba da ciwon nasa daya bawa har doctors dinsa tsoro.
Cikin Kulawa da tsananin kaunar da kulawan dayakewa jeey din a bayyane yace
"Yaya jikin Dr?"
Gyada Kai yayi a natse tareda kallan wayar hannunsa da idanuwansa Yana cewa
"Kira Ashley yanzu inason magana dasu"
Magana ya qarasa gurinsa yayi masa a natse kafin ya juya ya fice Yan daga wayarsa Dan Kiran Ashley yabarsu su biyu
a dakin.
Wayar ya ringa Kira Amma shi ko shiga Batayi kwata kwata Amma Bai kawo tinanin komaiba yaci gaba da sake gwada kiranta Dan Shima yanason magana dasu din kwana biyu Bai samu Daman waya da kowaba kansa ya cake da zafin ayyuka acan Greece sunyi y
awa ga Jamaal Baya Nan ga ciwon JAMAAL na rana tsaka da kokarin isowansa Poland hakan yasa wayoyinsa a kashe suke saida ya iso yake kunnawa yanzu.
Ashley kuwa ana Isa dasu asibiti ita aka fara karba da gaggawa sbd cikinta da itama batasan dashiba yake
kokarin zubewa.
Wata nurse data fito daga emergency ce taga shigewan da zaayi da Ashley ta zubawa fuskanta ido tana kallanta Dan ko zata mutu ta dawo bazata manta kamannin Yar uwarta ba duk da sunyi shekaru baa tare ba tinda sun Rabu ne tin kafin iyaye
nsu su tasu Dan haka take ta juya da sauri tana Ambatar sunanta.
Acikin abinda baifi awa nawaba Allah ya taimakesu cikin Bai zubeba aka samu ceto ranta itama amma dai kam sai yanda allah yayi dan tayi nisa.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenato
u!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone ban
k_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[5/18, 12:36 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
#Z
afafaBiyar
90
*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,
muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na
kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to
see lot of our amazing products
đŸ‘‡
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL
**************
Har yamma shiru Ameenatou bataga Ashley ba hakama taqi yadda kowa ya matsota bare taci abinc
i daga Wani
Duk da ciwon Dake cinta na zazzabi da rashin kuzari ko kadan Amma wuni yunwa tayi Dan taqi cin komai daga kowa.
Duk yanda nurses sukai yaqi yadda da kowa hakama taqi ko magani Tasha,
Dan haka ta sake laushi sosai zuwa yamma
Koda dare ya
yi kwance take Bata iya komai bayan ambatar sunan Ashley
Idan taji shiru ta ambaci JAMAAL idanuwanta na gangarowa da Hawaye daga karshe dai sai dare dole aka takurata ta yadda taci abincin sbd galabaitan datai da tausayinta tareda tashin hankalin labarin
accident din sister Ashley Daya samesu zuwa Daren Dan sunsan shikenan Ameenatou din ta shiga samon hauka kenan tinda kafin ta fara yadda da wani ba Ashley ba to rigima zaayi sosai da tashin hankali tareda tashe tashen ciwonta.
Su Dr Zakeer ma sabon tash
in hankali suka shiga na samun labarin accident din sister Ashley dan kuwa ta tabbata bada Ameenatou dole garesu Dan idan babu Ashley babu sauran iya cigaba da boye zancen cikin dan kuwa dik nurse da zaa sake bawa Ameenatou ba lallai ta rufa ba hakama da w
uri tana ganewa ma zanven zai fita hakama idan babu Ashley ameenatou bazata taba yadda da kowa ya fita asibitin da itaba har zuwa wata asibitin a cire cikin.
Dr Charles dayaga aikin na Neman cabewa da wannan sabon tashin hankalin Daya bullo na rashin As
hley da zai Saka haukan Ameenatou tashi
Kuma tashin haukanta daidai yake da bayyanar cikinta tinda zai iya zubewa a gaban duk Wanda Allah yace ya Gani ko gaban mutane da yawa,hakama kawai duka sunfi Aminta da barinta asibitin gabaki Daya kwata kwata Dan
haka Babu Sanya ya tsananta binciken da zasuyi dan tabbatarwa da Kuma shedan su Babbah iyayenta da duka sai an Saka a file nata Dan gaba ko kuma idan Jeey ya dawo Dan fuskewa zasuyi tsaf su Qi barin dalili ko daya dazai kamasu da laifinsa.
Su Babbah kuw
a daqyar suka ga kwana ukun Nan ta cike suka nufo asibitin tinda safe Dan a ranar Babbah yakeson barin Lagos idan aka Basu ita Dan haka da Shirin tafiya ma suka iso asibitin daganan mota zasu su dauka shata su tafiyarsu inda ko sunansu Babu me sake Ji.
Md ya Riga su babban zuwa asibitin ma sbd ya fisu matsuwa da su tafi da itan yanzu Dan tini ta haukace musu da rashin Ashely Amma sbd cikin su Kuma su Dr Zakeer sunqi barin kowanne likita ya dubata hakama sun kasa sun tsare sun Hana ayi mata alluran kwanta
wan haukan sbd anayi cikin zai fita,
Yana fita komai zai bayyana tinda dole Nurses ne mata zasuji da matsalar idan Kuma sukaji da matsalar zancen cikin ya fita kenan Dan Koda ya zube ne zancen ya fita duka dai masifar da balain Daya ne dan haka suke jiran
iyayenta yau din su bada ita Dan gwara su lallaba su bawa wannan baban nata ita akan JEEY ya dawo take zai gane ciki a jikinta basuda mafita kenan Kokuma asalin mahaifinta ya waiwayota anan yazo ya tadda ciki.
Address dinsu na Nasarawa suka aika takana
s aka je akayo bincike aka tabbatar musu da tabbas shine babanta hakama makarantar ta sunje,
Sunje asibitin can ma duka an duba musu sun gama tabbatarwa tareda hada shedan Hakan suka Saka komai a file nata tareda rubutawa Dr ibrahim ne ya Saka hannu a cik
i suka kammala komai bayan jiran Babbah Babu abinda sukeyi Dan Doctors din su duka a ranar asibitin suka kwana sbd tabbatarda Babu abinda zai Bata musu aiki kafin safen Dan Saida Dr Zakeer ya tashi tsaye akan nurses da suketa kokarin yi mata allura shiyasa
shi a yawon dakin Ameenatou ya kare cikin kwana biyun kafin ranar Bada ita tazo.
Babbah ma kaman yasan Jiransu akeyi Dan haka ya zabi zuwan safen,
Baa Basu matsala ba a gate din aka barsu suka shiga tafiya tafiya har office din md suna Isa Dr Charle
s na shigowa hakama dr ibrahim
Shi kuwa Dr Zakeer Yana ward dinsu Ameenatou din ya Saka an wata nurse ta sauyawa Ameenatou din kaya zuwa doguwar Riga black da hijab din sister Ashley fari qarami me kyau dayake cikin kayanta sbd basuda time na tsayawa ware
wasu kayan Ashely Dake hade da nata tinda yasan su can bawai buqatan kayan sukeba andai hada mata abinda ya sauwaka sbd kowa yasan iyayenta sunzo zasu tafi da ita akan sun gaji bazasu iya cigaba da biyan asibiti ba basuda hali.
Kowa yayi mamakin Hakan
sbd tinanin Ameenatou yar manyan mutane ce duba da yanda Ashley ke dawainiya da ita da yanda ko abinda take amfani dashi daban ne Dana kowa asibitin,
Ko slippers na banza Bata sakawa bare sauran abubuwan amfaninta Amma ace Hakan?to Amma tinda ba huruminsu
bane likitoci sun sallameta basuda abin fada bayan kallo da fatan samun lafiya duk inda aka tafi.
Babu wani Bata lokaci sharuddan ciwonta da yanayin yanda zatasha magani da Kuma yanda Bata yadda da kowa duk sukai musu bayani Daya bayan Daya tareda cewa
suyi kokari su ringa zuwa ana dubata zuwa gaba sosai haka.
Kaman yanda suke a matse hakama Babbah yake amsawa da ya gane cikin matsuwar Shima Dan fatarsa idanuwansa su sauka akan yar budurwansa ta shigo hannunsa.
Ko rufe Baki baiyiba ga amsar karshe
sister fareeda ta shigo office din da Ameenatou wadda daqyar ta yadda tazo sbd ance mata gurin Ashley zaa Kaita.
Idanuwan md Dana Dr Ibrahim da Charles akan Ameenatou da yanda zatai reacting idan Taga su babban duka suke zuciyarsu a Dan rikice da farga
ba Dan Hakan ne ma Dr Zakeer yayi saurin sallaman sister fareeda din yace ta tafi sbd Yana bayansu tana ficewa ya rufe office din Yana dawowa gaban Ameenatou din daga bayanta dayake Yana kallanta lokacin ne ta dago kanta fuskanta a rame idanuwa duk sun fa
da ta narke idanuwanta Dan yiwa Ashley kukan barinta datai.
Babbah,Hafiz da Dadah kuwa idanuwansu kaman zasu fado kasa sbd fitowa da gwalo mata su da sukai suna kalla hankali tashe da Kuma tsananin kewa da kaunarta me karfin gaske Dake azabtar dasu na r
ashinta.
Akan fuskan Babbah idanuwanta suka fara sauka ta tsaya cak daga Jan numfashin kuka datake Shirin yiwa Ashley.
Ko kyaftawa idanuwanta kasawa sukai ahakan ta maidasu akan Hafiz tana kalla,
Rawa jikinta yafara yi ahankali Yana qaruwa hakama
ta kasa ko kyafta idanuwanta daga kansu.
Babbah ne ya taso da sauri ya tsaya gabanta cikin rawar murya da Mummunan karyewa da zuciyarsa keyi ya Bude Baki yace
"Budurwan Babbah??,
Babbanki ne,tareda Hafiz dinki
Ga Kuma dadanki......
Katsesa tayi
cikin rawar da hannuwanta ke qarawa da Bude Baki cikin Wani sauti mara fita sosai ta furta
"Babbah,Babbah,
Ameenatou tanada Babbah,
Ameenatou tanason Babbah,
Ameenatou na son babbah...."
Wata shegiyar ajiyar zuciya su Dr ibrahim suka sauke gabaki
dayansu a fili sbd tashin hankalinsu Daya fada lokaci Daya da jin kalamanta Dan kuwa shikenan ba matsalan tafiya da ita Dan Daman tashin hankalin da zaa zuba sukaiwa tsit cikin zufan tashin hankali.
Sake jero ajiyan zuciya md keyi Yana share zufa hakama
Dr Charles,
Dr ibrahim