Showing 21001 words to 24000 words out of 182667 words

Chapter 8 - AMEEENATOU COMPLETE

Unknown   

30 Aug 2026

27

a hankali ahankali dan samun nutsuwan zuciyarsa.

Yana gama dubawa ya Nemi doctor din da kusan komai

na case dinta na hannunsa suka fara tattaunawa Yana sake masa bayani da Baki tareda shawarwarin yanda zasu ci gaba da lallaba jikin nata Dan har lokacin Bata iya komai da kanta kuzarinta Bai dawo ba na iya motsa jikinta da kanta.

Ya dauki lokaci me tsa

yi Yana wayan kafin ya gama,

Yana ajiye wayarsa akan table din gabansa dago idanuwansa yayi ya Kalli agogon gabansa ya duba time.

Karfe goma Sha biyu NE da Mintina arbain da shida Dan haka ajiyan zuciya me sanyi kadai ya sauke tareda miqewa ya natsensa

ya fice daga office din tareda rufewa ya nufi block A din Yana sake Dan duba time a agogon Dake daure a hannunsa.

A natse ya isa dakin batareda ya Hadu da kowaba ga Wani tsit da gurin yayi baka Jin motsin komai bayan na iskan Daren Dake kadawa..

Bud

e dakin yayi a natse sbd kada motsi me girma ya tashe ta idan bacci takeyi ya shiga dakin idanuwansa akan gadonta datake can qurya ta dunqule guri Daya tareda qanqame jikinta idanuwanta a rufe hakama ta fita rufan da yayi mata da alama awannin alluran sun

qarasa cikewa a cikin Daren ta sake ta tinda ta samu kuzarin motsawa harta hade jikinta guri Daya ta nannade haka.

Takowa yayi a nutsuwansa tako yaushe ya iso bakin gadon tareda dago fararen idanuwansa ya zuba mata su a hankali kaman mara lafiya Yana ka

llan fuskanta datake fayau kaman ta baby,

If zai Tina Asalin kamanninta daidai sune na ranar Daya fara yi mata kallan seconds a Nasarawa sai kuma ranar daurin aurenta da Haroon a cikin

adonta na jiran zama matarsa batareda sanin ranar ne ranar barinsa d

uniyanba.

Dauke idanuwansa yayi a hankali tareda matsowa ya Kai hannuwansa duka biyu ya ja abin rufan ya sake rufeta tareda kama kanta ahankali ya mayar mata akan pillow Yana qin kallan fuskanta sbd kusan da sukai sosai.

Hannunsa ya Saka a aljihunsa

ya Ciro Wani turarensa me shegiyar tsada da kama duk abinda ya tabasa ko kusantarsa ya nufi jikinta ahankali ya fesa mata tareda Kai hannunsa ya Bude tafin hannuwanta masu taushi ya fesa mata a ciki.

Yana gama rufeta da gyara mata kan nata karfe Daya da

minti Daya na bugawa Dan haka ya juya a fice tareda rufe kofan ya fesa turaren a handle na kofan shiga dakin ya juya ya fice daga block din gaba daya.

Yana iso office Kai tsaye bedroom din ciki ya wuce yana zaunawa kan single couch din dakin Yana Dan r

ife idanuwansa Dan kansa ma ke sarawa.

Karfe biyun dare daidai block A ya dauki qarar Wani firgitaccen ihun Ameenatou me firgitarwa da tashin hankali me girman gaske Dan kuwa ihun duk Wanda ya jisa mummunan faduwa gabansa yakeyi..

Sister Ashley da wa

su nurses biyu ne suka fara fitowa a rikice hankalinsu a tashe harma da tsoro suka nufo block din.

Dr JEEY ma dayake zaune Daram a office dinsa Yana jiran Daman shedawa da kansa abinda yake faruwa a block din na Abinda yake tayarda ciwonta da baa saniba

.

A kunnuwansa amon ihun da Shirun dare ya debo ya kawo masa ya sauka,

A Karo na Babu adadi ya dago idanuwansa ya duba time Taga karfe biyu da Mintina biyar,

Amon ihun ne me karfi ya sake shiga kunnuwansa Dan haka Kai tsaye ya miqe batareda ya tsa

ya komai ba ya nufi kofa ya fice zuwa dakin.

Koda ya Isa su sister Ashley da sauran nurses sunata kokarin Riqeta Amma kwata kwata ta haukace gaba Daya ihun takeyi jikinta na Wani irin rawa da jijjiga sbd firgata.

Yana shigowa Kai tsaye gurinta ya nuf

a din idanuwansa akan wuyan rigarta Daya cakuda ba kaman yanda ya San ya barsa ba Dan kallan dayayi mata Babu abinda Bai riqe yanda ya barsa ba Dan haka Koda ya Isa idanuwansa tini suka sauya take da wani irin zafi da bacin ran Daya Saka Bai tsaya komai ba

Yana isa hannuwansa biyu yakai ya kamota gabaki dayanta tareda girgiza ya ambaci sunanta a Karo na farko rayuwansa.

Bata Jin komai Bata gane komai bayan ihun da rawan da jikinta keyi Dan haka duka abin ya sake rikicewa hakama sister Ashley Kai tsaye it

ama idanuwanta suka Kai wuyan rigar Ameenatou din Da botiran gaban rigar na sama kaman biyu sun fice.

Mummunan faduwa gabanta yayi da sauri ta matsa tana cewa kowa ya fice daga dakin Dr JEEY din da ita datake nurse dinta zasu shawo kanta sbd ganin mutan

en ke sake haukatar da kanta.

Shigowan nurse Fahat ne da sauri Yana bayyanarda damuwansa da tambayar jikin ne ya Saka Sister Ashley dakatar dashi tana cewa anason a rage ne sbd duka kowa yasan Taron mutane a gabanta shine babban matsalan ciwonta.

Mur

yan nurse Fahat ne ya Saka ihun Ameenatou din da rawan jikinta tsananta tana kokarin kwacewa daga riqon JEEY din Wanda shigowan nurse Fahat ya bankado masa da qamshin turaren Daya fesa Dan Hakan.

Sakin Ameenatou din yayi ya dakatar da nurse Fahat din da

ga ficewa ya nufosa sedai duk takunsa daga Isa garesa qamshin qaruwan masa a hanci yakeyi.

Nurse Fahat da Shima yake a matiqar tsarge sbd qamshin dayake tashi a jikin nasa na Ameenatou din Daya rasa wane turaren ne wannan sabo sister Ashley tayi mata am

fani dashi ayau Daya kasa barin jikinsa Kuma har uniform ya sauya da sauri shine dalilin dadewansa Bai iso na Amma har lokacin tafukan hannuwansa da jikinsa qamshin yake tayarwa sosai.

A daidai lokacin da Dr JEEY din ya iso gaban Fahat din zuciyarsa ta

gama cika da wata irin wutar zafin da Baya buqatan qarin bayani sbd qamshin dayake tashi sosai a jikin Fahat din su sister Ashley ma dukkaninsu tsayawa sukai suna kallan abinda zai faru din Dan kallo Daya zakaiwa Dr JEEY kaga yayi Wani ja duk farinsa ya ko

ma ja kaman Wanda aka ajiye cikin Rana.

"Meya kawoka bangaren patients da dare?

Meye abinda ya Sakaka zuwa Nan dakin???

Wannan tambayar ya Saka kowa dawo da kallansa kan Fahat da sauri musamman sister Ashley data Kalli kayansa tasan ba sune a jikins

a ba koda suka Hadu dashi zasu taho dakin Yana cewa bara ya dauko allura da maganinta ya biyosu.

Sisters din biyu ma kusan a take suka lura da Hakan Dan Koda suka gansa a yanzu yanzun Nan fararen kayansu ne a jikinsa Amma a yanzu ya sauyo zuwa green Wan

da suke sakawa idan zasuwa patients wanka da sauransu.

Rikicewa Fahat din yayi Yana kallan Jamaal din yace

"Dr JEEY,ni Kuma?

Ban taba zuwa........

Qarar Marin Daya saukan masa ne ya Saka su sister Ashley firgicewa suna ja da Baya cikin tashin han

kali.

Fahat dinma daukewa jinsa yayi harma da lafiyar ganinsa Dan wasu taurari yaga suna masa yawo ya dago da sauri ya Kalli Dr JEEY din Wanda ya sake jeho masa tambayar meya kawosa Nan din.

Ihun da Ameenatou keyi tana yaga kayan jikinta da jikin nat

a ma ya Saka sister Ashley rungumeta da sauri jikinta itama Yana rawa Dan shock din da suke kokarin samun kansu a ciki da abinda yake Neman tabbata.

Wayar Dake aljihunsa ya fidda Kai tsaye Kira daya yayiwa siddeeq Dake jiran Kiran ya kashe Yana qin kall

an fahat din dake gaban nasa hannuwansa wata irin rawa sukeyi a boye sbd jinin jikinsa Dake kunar dayake Jin idan baiyi karfin halin riqe kansa ba zai iya aikata kisa a gurin.

Nurses da sauran duk Wanda yake dakin ficewa yayi sedai ko gama ficewa basuyi

ba siddeeq ya iso asibitin tareda team din da zasu Basu tabbacin komai tukuna ya nunawa Fahat din jinin MAM SEELAH ne ke yawo a jikinsa shugaban Ashalawa na yanzu gaba dayanta.

Ameenatou data kasa tsayuwa ta dawo daidai Siddeeq ya juyo batareda ya kalle

ta ba sbd yanayin jikinta da kayanta dasuka fara yagewa yace sister Ashley ta fita da ita tukuna.

Manyan asibitin da sauran doctors Dake cikin asibitin cikin Daren tini suka iso Babu Bata lokaci aka dauki tprint din jikin kofar dakin Da rigarta da akace

sister Ashley ta kawo tini ta cirota ta bawa siddeeq ya kawo dayake ana cewa ta fita da ita tsoron Kaita Wani dakin tayi sbd yanayin datake cikin sai Kai tsaye ta nufi office din Dr JEEY din da ita Siddeeq ya Bude mata suka shige ya rufe.

##MAMUH

#SEELA

HS

#DR JAMAAL MAM SEELAH

#AMEENATOU OMAR JADEN SEELAH

[5/18, 12:28 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*

#ZafafaBiyar

70

A gida ranar JEEY ya wuni wayansa a kashe batareda ya koma asibiti ba ya huta sosai sai yamma sosai bayan la'asar ya shirya da kansa ya

ja motansa yau cikin ash Armani's ya nufi asibitin.

Koda ya shigo asibitin office dinsa ya nufa Kai tsaye Saida yayi wasu ayyukan kafin ya fito sallan magrib Yana fitowa magrib Kai tsaye dakinta ya nufa.

Duk inda ya wuce ya Hadu da ma'aikata ko nurse

s cikin girmamawa ake gaidasa tareda masa barka da shigowa cikin turanci sbd da yawa Basu sani ba ko Yanajin Hausa ko Wani yaran.

Da Kai yake amsawa kawai a natse batareda ya Bude bakiba sai thank you data kama bakinsa Dan ko gaidasa Kai Saiya ce Maka t

hank you.

Dakin ya iso ya tsaya a natse tareda zare hannuwansa Dake cikin aljihun wandonsa tareda Dan sauke numfashi me sanyi da nutsuwa a boye Dan baisan Menene zai faru ayau din idan ta gansa ba duk da yasan saita sake kwana Daya kafin alluran ya sake

ta ta dawo daidai.

Sister Ashley ce ta Bude dakin zata fito zuciyarta cikeda tsananin farin ciki da Kwanciyar hankalin samun dawo da itan da Akai block din hakama Siddeeq ya sanar da ita Dr JEEY SEELAH mijin Ameenatou ne da igiyoyin

aurensa uku suke kan

ta batareda ita kanta tasan ba shine Haroon twin dinsa ba daya rasu Dan haka ya sake bata tabbacin kulawa da Ameenatou da kuma tabbatarda ciwon Ameenatou Bai bari ko Bada hanya ko Daya da zata bayyanarwa da kowa wannan sirrin hakama a yanxu da jeey din yak

e nan ta ninka kulawan datake wa Ameenatoun sbd inshallah suna Saka ran sauki da lafiyanta zasu iya dawowa kowanne lokaci sbd daga yanzu Babu me qara yi mata kowace irin alluran.

Wannan maganar ta Saka zuciyar sister Ashley wankewa daga dukkanin damuwa

akan Ameenatou tareda Jin farin ciki me tsananin gaske harma da fara tinanin daga Nan zuwa wata Daya da alluran keyi ta warware daga jikinka gaba Daya Ameenatou zata iya dawowa daidai idan har ba sake mata alluran akaiba gashi siddeeq ya bata tabbacin baza

a sake mata Hakan ba,

Ko siddeeq din Bai fada ba a yanzu da Dr JEEY yake asibitin a matsayin kaman sabon shugaba Dan labarin tafiyar Dr Dee yagama yaduwa tasan Babu abinda zai sake Ameenatou dinta inshallah.

Cak tayi saurin dakatawa tareda Dan komawa

Baya a natse sbd batai tinanin da tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacin ba a kofan dakin Amma Tino shi waye din ya sakata sauke numfashi a boye cikin girmamawa tace

"Barka da zuwa Dr"

Qamshinsa ne ya cike mata iskan kofan dakin Yana kutsawa ciki

n dakin tareda faduwa ko Ina cikin sanyi da nutsuwa sanyin ke shiga har hancin Ameenatou din Dake kwance idanuwanta a rufe Amma ba baccin takeyi ba.

Da tattausan muryansa me nutsuwa ya amsa da "yawwa,thank you"

Shigowa dakin yayi Yana Maida hannuwans

a aljihun wandonsa idanuwansa akan inda Ameenatou din take kwance shiru cikin wasu cotton Riga da wandon bacci marasa nauyi kalan blue me haske.

Ahankali ta Bude idanuwanta ta zuba masa su gabaki dayansu suna Wani irin narkewa da cikowa da Hawaye masu s

anyi da suka gangaro mata gefen fuska a hankali sbd azaban datake Ji a zuciyarta na cinta da jininta na rashin kuzarin zuwa garesa.

Sister Ashley sanyi jikinta yayi idanuwanta itama na cikowa da Hawaye masu sanyin tausayin Ameenatou din Dan kuwa a cikin

idanuwanta daga ita har shi JEEY din suna iya hango tsagwaron zallan so da tsananin kaunar datake masa a matsayin Haroon batareda tasan Haroon dinma gaba daya baya duniyarba ya tafi inda har abada idan ba a mafarki ba bazasu taba sake haduwa ba.

Sister

Ashley Bata taba sanin mara hankali na iya son Abu da gasken gaske kauna mara sirki me karfin gaske irin Hakan ba,

Da cikin cikakkiyar kuzarinta take tabbas tasan Babu abinda zai hanata nufar Dr JEEY din ta kasa rabuwa dashi Dan Haka ciwo da radadin Ha

kan yake bayyane a fuskanta suna kallo sedai Babu yanda zatai mata Dan kuwa Alamu sun nuna Ameenatou din ba lallai ta samu kwatankwacin son da Haroon yayi mata daga Dr JEEY din ba,

Sunkuyar da Kai sister Ashley tayi batareda ta Kalli kallan da Dr JEEY d

in kewa Ameenatou ba batareda ya qyafta ko idanuwansa ba Dan kuwa ayau fuskan Dad Omar dinsa yake kallo a baby face dinta tareda fuskan Haroon duk a lokaci Daya hakama innocence dinta na hanasa Tantance da kamannin wa zai kalleta a cikinsu.

Shiru dakin

yayi itama Ameenatou din har lokacin idanuwanta dasuke a lausashe akansa suke ga bacci na cinta Amma ta kasa rufe idanuwanta sbd kada ta rufe ya tafi ya barta.

Sister Ashley data lura da Hakan ta qaraso ahankali ta ranqwafo ta Dora hannunta akan lallaus

an fatan fuskanta ta shafa a hankali tana Ambatar sunanta da cewa

"My sweet girl zatayi bacci ko??

Ahankali cikin wahalallen karfin hali ta tilastawa jikinta motsawa ta girgiza Kai so Daya har lokacin idanuwanta na kansa wasu hawayen na gangaro mata.

Daga shi har sister Ashley sun San ba qaramin karfin hali da azaba ta daure Tasha ba gurin tilastawa jikinta motsawan sbd sanin azaba da karfin alluran Dan haka sister Ashley tayi saurin tsayar mata da Kai tana share mata hawayenta da tissue cikeda kul

awa da tausayawa tace

"Kinason Dr kada ya tafi right??

Lumshe idanuwansa dake sake tsiyayo Hawaye tayi tana kallansa zuciyarta na narkewa.

Lumshe idanuwansa da suka sauya yayi Yana dauke kallansa daga fuskanta dayake ganin mutanen Nan biyu a ciki

ya Tako a hankali ya iso har bakin gadon Yana rasa abinda zai fada,

Sister Ashley na ganin Hakan ta silale gefe tana Satan kallansa sai daukan ido yakeyi komai nasa class ne dashi hatta shirunshi Wani iri dashi.

Hannunta dayane yake motsawa ahankali

alaman son take ta motsa bayan Hakan bame yiyuwan bane,

Saukan hannunsa ahankali kan nata din ya Saka sister Ashley sake ajiyan zuciya me sanyi a boye sbd tinda ya shigo din hawayen Ameenatou ya Sakata Jin kaman ta janyosa takai gaban Ameenatou din ta D

ora hannunta akanta ko yarinyar zata Jin sanyi.

Ita kanta Ameenatou din idanuwanta ta rufe a hankali tareda budesu akan fuskansa daya kallanta cikin murya mara sauti sosai ya Bude Baki yace

"An Bata dinner??

Matsowa sister Ashley tayi tana kallan

Ameenatou din tace

"Tasha tea Wanda idan tana cikin wannan alluran dole iya tea dinne yake shiga tinda bakin bazata iya budesa ba bare hadiyewa da kyau"

"Any damuwa?fever or something??

Girgiza Kai sister Ashley tayi tana cewa

"No,sedai ciwont

a da daddare Yana tashi sosai fiyeda yanda ka Gani jiyan wasu lokutan Kuma dai Bata Hakan sai tsakan dare" ta qarasa maganar tana gudun fadan abinda Bata tabbatar ba.

Akwai sauran bayani a maganarta idan yaji qarashen sautin daidai Dan haka ya dago zai

juyo ga mamakinsa da nata hannunsa Dake kan na Ameenatou din ta riqe na yatsinta biyu cikin kuzari.

Kasa juyowa yayi sbd idanuwansa da suka Dan rage budewa ya Kalli sister Ashley data dauke kallanta kan hannun nasu yace

"Akwai abinda kike tinanin Yan

a kawo Hakan?

Menene yake Saka ciwon nata tashi Kai tsaye?

Dagowa tayi ta kallesa kadan tana cewa

"Bata taba yadda kowa ya rabeta ko ya kusanto gurinta idan ba ni ba sai Sir siddeeq sai doctors wainda Suma duk suka taho sai ciwon ya tashi,

Bata tab

a yadda da kusancin kowa ba Hakan shine ke tayar da ciwonta sosai kum......

Idanuwansa Daya dago ya zuba mata gaba Daya ya Sakata kasa qarasa maganar.

"Akwai Wanda yake zuwa ne dayake Saka ciwon tashi cikin dare?

Akwai staff Da aka taba bawa Daman k

wana a cikin patients ne

A can baya tana Hakan?

Tana firgita ne cikin baccin dayake tayar da ciwon?

Ina buqatan amsa Daya Kai tsaye game da Hakan."

Rikicewa sister Ashley ke Neman yi da maganarsa Dan tasan illan fadan abinda Bata tabbatar ba musamman

a asibiti Dan zai iya kawo babban matsala da zata iya kawo illa me girma ga likitoci da kaf ma'aikatan Dake cikin asibitin Dan haka ta dago zatai magana Amma kallan dayake cikin idanuwansa ya Sakata Neman rikicewa tace

"No acan Baya Bata Hakan and Bata

firgita cikin bacci and Babu staff dayake da Daman kwana a cikin patients Koda likita ne Amma Kuma duka staffs sunsan password na shigowa kowanne room and babu security cameras a dakunan patients,

To Nima dai bansan Menene asalin abinda yake Sakata wanna

n halin ba."

Shiru yayi Baice komaiba Bai Kuma sake kallanta ba yace

"Yanzu time yayi na tafiyanki kenan?

Babu wani abu datake buqata daga Nan har safe?

"Yes doctor"

"Ok,Zaki iya tafiya."

Daukan wayarta tayi ta juya ta fice daga dakin tared

a jan kofar ta nufi dakunansu na nurses tana fatan Allah yasa yauma Dr JEEY din ya tafi da Ameenatou din office dinsa Dan ita dai hankalinta Sam Sam ya kasa Kwanciya Kuma Bata zargin kowa Amma dai tana zargin akwai Wanda yake shiga gurin Ameenatou din koda

i da sunan sata ko Wani abin daban.

Bayan ficewan sister Ashley ya dauki mintina a tsaye batareda ya juyoba Yana tinanin dayake Neman nauyaya kansa kafin ya sauke numfashi me sanyi da nutsuwa tukuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login