Showing 72001 words to 75000 words out of 182667 words

Chapter 25 - AMEEENATOU COMPLETE

Unknown   

30 Aug 2026

54

Baki tace,

"Cikinta ne muka ga yayi girma

Kuma Babu rashin lafiyar komai"

Kallan Ameenatou din yayi kafin ya Kalli su Babbah yace su Basu gurin Abar Dadah kawai.

Fitowa sukai Babbah kirjinsa na wani irin toshewa,

Hafiz riqesa yayi sbd har lokacin Bai fahimci komai ba.

Zaunar da Babbah y

ayi batareda ya iya cewa komaiba sbd ganin lamarin me girma ne Dan ba qaramin lamari ke Saka Babbah shiga wannan mummunan halin ba.

Zaunawa sukai shiru shiru kowa da abinda zuciyarsa ke sakawa cikin damuwa da fargaba har tsawon mintina kafin aka fito da

su zuwa gurin scanning tareda Dadah wadda bata iya kallansu ba.

Can ma Basu Wani jima sosai ba suka dawo suka shige office din ganin likitan sai gashi Shima daga bayan ya dawo ya shige.

Dadah ce ta fito ta kira su Babbahn ciki.

Tasowa sukai suka s

higa suna kallan Ameenatou Dake zaune duk zazzabi na Neman taso mata sbd bata Saba wahala ba hakama duk an cakuda mata ciki gurin scanning ga yunwa tanaji.

Likitan mamakinsa ya fara bayyanarwa tareda tambayarsu basusan ciki bane da tana dauke da cikin k

usan wata BIYAR Amma ace Basu gane ba.

Fiddo idanuwa Hafiz yayi da sauri cikin tsananin tashin hankali da mamaki me karfi Ya kalli Ameenatou kafin ya Kalli Babbah da Dadah murya na sarkewa yace

"Ciki Kuma?

Cikin haihuwan 'yaya ko me??

Budurwan Babb

ah ake magana kokuwa wata daban??

Kukan da Dadah ta fashe dashi jikinta gabaki Daya Yana daukan rawa ya Saka likitan yin shiru cikin mamaki da tausayinsu Dan alama dai Wani ya lallaba cikin rashin hankalinta yayi mata cikin.

Daqyar Babbah ya iya Bude

Baki da Dan karfin Daya rage masa yace

"Likita kace ciki?Kuma harna wata biyar?"

Ajiyan zuciya Dr ya sauke cikin sanyi kafin ya gyada Kai Yana cewa

"Eh inshallah"

Wani abu me nauyin gaske ne ya danne zuciyar Babbah Wanda ya Saka idanuwansa fa

ra yin duhu Yana dafe kirjinsa.

Hafiz ne yayi karfin halin tare babban shida likita suka fito dashi Dadah kuwa kuka takeyi mara sauti tana share Hawaye.

Mota suka shiga da Babbah suka nufi gida Babu Wanda ya iya magana a cikinsu sbd babu Wanda zuciya

rsa take bugawa daidai ko kadan,

Dadah sbd kuka Koda suka iso idanuwanta sunyi mummunan kumbura,

Hafiz kuwa idanuwansa ne sukai Wani mugun jajir hannuwansa na Dan rawa ya damqe takardan awon cikin datake hannunsa.

A tsakar gidan suka zauna kowa shir

u Babu Wanda ya iya cewa komai har lokacin hakama Babu Wanda yake Gani ko ji daidai.

Wani radadi me tsanani idanuwan Hafiz keyi sbd abinda yake cinsu,

Zuciyarsa radadin Datake yasa har lokacin jikinsa yar rawa yakeyi,

Rintse idanuwansa yayi ya sake

budewa sai kawai ya fashe da wani irin kuka Mai ciwo da radadin zuciya sbd ya kasa riqe abinda yake ji.

Kukansa ya Saka gidan ya sake daukan tsit hakama Babbah hawayen dayake riqewa ne suka gangaro masa Shima zucuyarsa na sake nauyi.

Kuka sosai Hafiz

ke yi dukkanin jikinsa na jijjiga da rawa,

Duk masifar da suka shiga Bai taba kuka irin haka ba sai yau,

Kuka yakeyi sosai kaman ba namiji Mai karfin hali da jarumta ba.

Dukkaninsu kuka sukai Saida idanuwansu sukai jajir Ameenatou na zaune gefe tana

Shan fruits itama jikinta a Sanyaye.

Sun jima a wannan mummunan yanayin kafin Hafiz ya miqe ya dibi ruwa a bucket ya shige toilet.

Wanka da alwala yayo ya fito ya shirya ya wuce masallaci sallan magrib da ake kira.

Babbah kuwa Saida Dadah ta taima

ka masa ya samu yayi alwalan yayi sallan a gida Dan bazai iya fita.

Itama sallan tayi tareda Ameenatou Dake gefenta.

Shiru gidan yai Babu Wanda ke ko dogon motsi,

Saida Akai ishai Hafiz ya dawo gidan ruwa kadai yasha ya shige ya kwanta.

Ameenat

ou din kadai Dadah ta bawa tea Tasha ta shiryata ta kwanta Suma suka shige sbd Babbah tini ya shige sbd lafiyansa datake rawa tini zazzabi me karfi ya rufesa da nauyin kirji me tsanani.

Yanda suka ga Rana haka suka ga Daren Dan Babu Wanda ya samu bacci

ya ziyarci idanuwansa idan ba Babbah da ciwo ya rufesa a cikin Daren Wanda daqyar sukaga safe suka tattarasa zuwa asibiti.

*******Jinyar kusan sati biyu Babbah yayi a asibiti kafin aka sallamosa suka dawo,

Hafiz Shima ciwon ne yake Neman kwantar dashi

Amma yayi karfin zuciya yaqi barin Hakan sbd idan ya kwanta shine bangon gidan Dan komai shike nemowa Dan haka ya sake sakawa kansa karfin hali Amma zucuyarsa bata qara lafiya ba daga ranar da cikin Ameenatou din ya bayyana garesu hakama Babbah lafiya tini

tafara masa rawa gashi sun rufe maganar cikin a tsakaninsu batareda sun tsaya Jan maganar inda cikin ya fitoba sbd cutace ta tabbata an musu mummunan illa,

Idan ma sunje asibitin wahala ce zasusha kudin ma zuwan Lagos a yanzu basuda shi hakama Babbah ha

r abada bazai yadda a nunawa Ameenatou dinsa yatsa ba,.kaman yanda suka reneta Babu Uba Hakan zasu reni abinda zata Haifa Babu Wanda har abada zai San fyade Akai aka samesa matiqar Yana Raye.

Ta bangaren Hafiz ma yabar maganar ne a yanzu Badan yabarta h

ar abada ba Dan kuwa duk Wanda ya keta haddin yar uwarsa bazai sake zaman lafiya ba a rayuwarsa daga ranarda yacika kudinsa na inganta rayuwarsu zuwa Wani matsayin.,,

Bazai taba barin a nuna Yar uwarsa da yatsa akan ta haihu ba sbd duk Wanda yayi Hakan

zai iya komai akansa,

Amma Kuma a yanzu babbar buri da qudurinsa shine Hana Hakan faruwa ta hanyar Saka rayuwarta matsayinsa Babu Wanda ya Isa ko kallo biyu yayiwa abinda ta Haifa da wata manufar.

***********

Abubuwa sun fara yiwa iyalin gidan Babba

h nauyi sbd Babbah da lafiya taqisa Sam Dan haka kullum a yawon Neman lafiyarsa ake asibiti

Hakama Ameenatou ma lafiya nata yin qasa sbd cikin da yanzu da gaske de ya fito tsufa yake yi,

Dadah ce a tsaye gurin hidima da Ameenatou da Babbah shikuma Hafiz

gaba Daya ya koma abin tausayi sbd wahalar nema Dan cinsu da neman lafiyansu harma da sauran abubuwan.

Da kansa shi kadai yakai Ameenatou Akai mata register na awon ciki Yana Kaita duk bayan sati Daya sbd Dadah idan zasu barinta akeyi kulawa Da Babbah i

dan Kuma yaji sauki sai ita takai Ameenatou din awo.

Rayuwa tayiwa Hafiz nauyi sosai Dan Babu abinda yake kalla kaman haihuwan Ameenatou da Baya kaunar ko kadan tazo da matsala,

Hakama Babbah koyaushe maganarsa daya shine Hafiz yayi kokari ya tanadi

komai kada Ameenatou ta haihu da matsala ko buqatan komai.

Duk yanda hafiz yake kokarin ganin samun aiki lamarin ya gagara Dan haka kullum yawon aikin karfi yakeyi shiyasa ba Wani abu yake samu ba duka wahalance yake koyaushe,

Cikin Ameenatou Koda

ya shiga wata 8 Hafiz ya sauya kamanni gabaki Daya sbd azabar rayuwa da wahala tareda nauyin dayake kansa da yayi masa yawa,

Duk zafin Nemansa da yanda yake tinanin samun mafita kafin haihuwan Ameenatou lamarin ya tsaya cak Dan haka kawai ya yankewa kansa

shawarar abinda zai inganta rayuwar Ameenatou dinsu da abinda zata Haifa tareda tsaronsu da samun yancinsu tareda tsayawa su fuskanci komai da kowa kansu a tsaye dan haka batareda sanin kowaba yafara neman hanyar da zai sanar da OMAR JADEN inda suke dan y

asan duk inda yake zuwa yanzu yana can yana nemansu.

A yanzu dai Kam Tako ina dukkaninsu suna buqatansa musamman Ameenatou hakama shi nasa karfin Neman Yana Neman qarewa kaman Wanda Bai taba shiga aji ba,ga babba ma duk da ya samu lafiya yanzu Amma Babu

karfin nema yanzu,ga Dadah ma duk wahala na Neman tsofar da ita,

Babu me farin ciki ko walwala a cikinsu shiyasa haryanxu sun kasa sakewa sosai a cikin mutanen anguwansu koyaushe suna kame a guri Daya.

Koda Ameenatou ta shiga watan haihuwanta ta s

auya sosai tin daga kan lafiyan jikinta harta kanta sbd Takoma shiru shiru sosai ko magana batason yi hakama komai na juyewan kanta kusan ya dawo daidai kawai abinda take kasa tinawa kanta na juyewa wasu lokutan shine shin haroon Yana Ina??

Waye Jamaal a

gurinta hakama waye Haroon??

Hakama kamanninsu na mutum Daya take Gani a idonta Kuma ta kasa tantance Ina kanta yake yanzu Ina ta baro.

Babbah da Dadah daidai gwargwado sunata Shirin haihuwarta Kuma Shima Babbah yanzu Babu abinda yakewa yarsa fata baya

n kyakkyawar rayuwa ingantacciya itada abinda zata Haifa masa Wanda sun Riga sun rungumi kaddara basa fatan ma tsayawa Wani janye janyen Neman uban sbd rufawa Kai asiri.

Ta bangaren Hafiz ya zurfafa Neman hanyar isarwa da Omar Jaden Sako ta duk inda zai

iya Amma rashin kudi ya Hanasa Isa ga wasu hanyoyin da yawa na Isa ga garesa dashi.

Har Abuja yaje so biyu Dan samun isarda sakonsa a companies dinsa Amma kwata kwata ko Daman shiga Bai samu ba bare Isa ga manyan da sune zasu dan iya masa hanyar magana

da Jden din ko Kuma Ahmed hakanan yake kashe kudin mota a banza ya dawo.

#MAMUH#

[5/18, 12:38 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*

#ZafafaBiyar

98

*_AISHA's COLLECTION_*

Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?

Ko kuma kinada jarin amma bakis

an maiya kamata ki fara saidawa ba?

Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, L

aces and shoes at both wholesale and retail..

Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,

ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen

alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...

Join our group to see lot of our amazing products

👇

Location: LAGOS

We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JR

kPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

************

DAWOWA LABARI

Ameenatou tsananin azaba ya Sakata somewa tana kwance kaman Babu Rai a jikinta Babbah ya iso kofar gidan da taxi din Daya samo daidai lokacin Shi Kuma Hafiz Yana kokarin tsayawa wani passenger Daya s

amu zai hau mashin dinsa wayarsa Dake aljihunsa tayi ringing Ya Ciro Yana Dan kare wayar da hannunsa sbd ruwan sama Baya ganin me Kiran sosai.

Bai ga suna ko numbern data kira dinba sbd ruwa Dan haka daukan Kiran kawai yayi tareda dorawa a kunne kafin y

ayi magana Kai tsaye yaji muryan da ko bacci ya tashi zai ganeta ta ambaci sunanta cikin Wani irin nutsuwa da Kamala tareda tsagwaron ilimin Daya ratsashi duk da akwai sauran rashin hayaniyar ciwon da yayi.

Sakin mashin din Hafiz yayi sauran kadan su ki

fe yayi saurin riqe kan mashin din Yana kashewa muryansa na rawa ya amsa da cewa

"Sir Omar Kaine???

Wani kukan da Babu Shiri na farin ciki ya fashe dashi Yana sauka kan mashin din ya koma gefe tareda sunkuyar da kan Yana kuka Mai ratsa zuciya Dan kas

he wayar ma yayi Dan bazai iya kukan a kunnen Omar ba.

Sake Kiransa Omar din yayi sai alokacin yaga numbern Nigeria ce take ya qarasa rudewa kukansa na qaruwa ya amsa.

"Hafiz Address naku kadai zaka tiro yanzu zan sameku aduk inda kuke indai a Nigeri

a ne,

Sbd sakonka da muka samu a shekaran jiya yau dinnan na sauka Ina Nigeria da kaina zan daukeku dukanku mu tafi inda ya kamata."

Hawayen Hafiz qaruwa sukai sbd harya cire tsammanin samowa yar uwarsa kudin da dole zaa buqata.

Hannuwansa har rawa

sukeyi ya rubuta komai ya turawa Omar din tareda share hawayensa ya buga mashin da Dan abinda ya samu na cinikin dayayi ya buga wayar Babbah ya bisu zuwa asibiti.

Yana Isa asibitin ya tararda ance Aiko zaa yiwa Ameenatou din Dan haka hankalinsa yayi mum

munan tashi take damuwansa da radadin zuciyansa suka ninku.

Dadah idanuwanta wata irin bushewa sukai hakama Babbah kowannensu kallo Daya zakai masa ka hango tsagwaron damuwa da qunci tattare dasu.

An samu anbata taimakon gaggawa nakudar ta Dan lafa D

an haka akace su tafi su Nemo kudin aikin kafin dare.

Babu zabin Daya wuce Babbah fita zuwa nema Shima Hafiz fita yayi cikin ruwan saman suka ringa yawon Neman kudi,

Dadah da aka bari kuwa zucuyarta sai tsinkewa takeyi sbd fargaba da tsoro tareda tas

hin hankali.

Duk ruwan saman da akeyi akan Babbah da Hafiz suka qare Dan haka tini Babbah ciwo yafara kokarin rufesa Amma ya danne yaci gaba da yawon daqyar ya hada dubu 7

Shikuwa Hafiz karshe dai guraren 9 na dare mashin din nasa ya siyar ya nufo asi

bitin hankali tashe jikinsa har wani rawa yakeyi sbd tashin hankali,yunwa kishirwa da zazzabin dukan ruwan Daya wuni yanasha.

Shigowansa asibitin yayi daidai da shigowan wata fitinanniyar motar da kaf asibitin Basu taba samun ziyarar Bako Mai irinta ba

ta shigo asibitin tareda parking.

Ahmed ne ya Bude kofar gaba ya fito a natse cikin blue shaddda me tsananin tsada sai kofar Baya da aka Budewa farin kyakkyawan dattijon da kwatjinsa ya cike gurin gabaki Daya.

Babbah ne dayake zaune Yana rawar sanyi

zuciya na cikin qunci yafara ganinsa bakinsa na rawa ya furta "OMAR"

dadah ce ta juya da sauri ta Kalli gurin hakama Hafiz cak ya tsaya daga inda yake tsaye cikin tsananin mamakin Daya Sakasa sakin ledojin hannunsa Yana kallan Omar din zuciyarsa na cika

da dukkanin farin ciki.

Shi kansa Omar dukkaninsu yake kallo yanajin Kauna da tsananin tausayinsu Yana yanka koina nasa yanajin tabbas alkwarin daya daukarwa kansa na bazai sake rabuwa dasu ba har abada Yana sake ratsashi sbd lokaci yayi na ya bayyanaw

a duniya yarsa dasu Babbah a matsayin ahalinsa na jini Dan kuwa Dadah kamar jininsa take tinda kanwar kasim dinsa ce.

Tin kafin ya qaraso gurinsu wata nurse ta fito a masife tana cewa

"Ina iyayen Ameenatou Nuhu Babbah?

Kun shirya kokuwa haryanxu B

aku samo kudinba mu kyaleku duk abinda ya sameta ko babyn laifinku ne,

Idan Kun samo kudin kuje ku biya komai Nan da awa Daya zaa shiga da ita tiyatar."

Juyawa tayi ta shigewanta ciki.

Kasa motsi Omar yayi hakama Ahmed sbd Jin Abinda nurse din ta

fada.

Babbah ne da tashin hankali da masifar tayi masa tareda tsananin ciwon dayaketa dannewa tin dazu suka Fi karfinsa ya yanke jiki ya Fadi a gurin.

Taimakon gaggawa aka fara basa batareda an tsaya zancen komaiba Kuma Ahmed take ya gabatar da komai

suka dauke Ameenatou da cikinta ya Saka Dad dinta kusan yanke jikin Shima Amma ya daure suka kwashesu daga asibitin ko wata asibitin Basu tafi ba ticket kawai suka Siya suka wuce abuja direct dasu Hafiz kawai aka bari ya hado duka sauran takardunsu da abu

buwan buqatansu ya biyo bayansu da tsakar dare Shima ta jirgin.

Suna Isa abuja Kai tsaye wata tsadaddiyar asibiti aka wuce da Ameenatou din wadda ta qarasa gabaicewa sosai,

Duba da yanayinta Babu bata lokaci aka shiga Cs da ita shikuma Babbah dubasa

Akai tareda Kwantar dashi a Wani lafiyayyan daki acan sama Mai komai a tsare kaman ba asibiti ba.

*********

Anyi CS din Ameenatou lafiya an Ciro mata lafiyayyan baturen Babynta Namiji Wanda girmansa kadai zai sake tabbatar maka sa lafiyayye ne.

A hannun Alh Omar jden aka miqa babyn wanda yake kamanni Sak da Ameenatou din sedai haskensa yayi yawan da yazo a bature sosai sbd gashinsa ma ba kaman na babies dinmu bane.

Shiru yayi tareda zubawa babyn idanuwansa jikinsa na sanyi Amma Kuma har cikin

ransa yakejin kaunar babyn tinda ya Riga ya kasance jinin Ameenatou dinsa Dan haka baida zabin Daya wuce ya kaunacesa koma waye ubansa Dan yaji bayanin komai a bakin dadah da Hafiz.

Babbah Yana Dan Jin jikin sosai Dan haka shi hutawa sosai aka barsa yay

i ya samu ya warware.

Ameenatou ma Ko data farfado har lokacin Hawaye ne ke gangarowa daga jajayen idanuwanta da suka kasa komawa daidai Kuma har lokacin ta kasa iya furtawa kowa kalma ko Daya bayan hawayen datake sai Kuma lokacinda aka kawo mata babyn

ta fashe da kuka me sanyi da daci.

Tsananin so da tsanar babyn takeji lokaci Daya sedai son Yana kokarin rinjayar qin shiyasa take Kukan tausayawa kanta da shi kansa babyn tareda babbahnta da Yaya Hafiz dinta da dadanta sbd tasan kaddararta tasu ce su d

ukan me dadi da mara dadi,ta farin ciki data baqin ciki.

Dad Omar ne yayiwa babyn huduba da sunan babbah wato NUHU OMAR JADEN,

Hafiz kuwa Daya karbesa duba da ayau ranar arfa ce sai kawai ya ambacesa da ARFAT.

Ahmed ma addua yayi masa sosai kafin

Kuma yafara kokarin fara binciken asibitin da Ameenatou din tayi zama Dan Gano komai su dauki matakin daya kamata sai Dad Omar din ya dakatar dashi sbd yanason dukkaninsu su fara dawowa daidai tukuna Kuma tinda zasu dawo Nigeria ne kwata kwata da zama wann

an Karan ba gudu ba ja da baya ya shiryawa su Mam tsaf to abari ya dawo din saisu bi komai a yanda yake amma yanzu yana buqatan tafiya dasu Ameenatou din gabaki dayansu saisun huta sun samu sauyin daya kamata tukuna so afara yi musu komai na buqatan tafiya

a cikin satin nan nakeson mu wuce.

***Hakan kuwa Akai a cikin abinda Bai gaza sati biyu ba kafin ma kowa yasan da Yana qasar aka gama musu komai cikin sati na uku suka tattara gabaki dayansu suka bar qasar gabaki Daya zuwa France tin daga Babbah har

Dadah da Hafiz Babu Wanda aka bari tareda Sabon hasken idaniyar dukkaninsu waton baby ARFAT.

Isarsu sosai Mum Noor tareda Aunt Didi sukai mamaki tareda farin ciki Mai tsananin gaske na ganinsu musamman Mum Noor datasan yanda Omar yake azabtuwa da rashin

Ameenatou 'yarsa.

Basuyi mamakin ganin Arfat ba sbd tin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login