Showing 78001 words to 81000 words out of 182667 words
gamawa dayake shi ya gama nasa karatun na 2yrs ne yayi tini ya fara aiki da babban ma
tsayin dana Ameenatou dinne yake Kai kafin ta gama duk da matsayi daya zasu hau a kamfanin.
Tareda Arfat ya fita zuwa office sbd yau ba Wani aiki ne dashi sosaiba,
Suna fita Dadah ma ta koma bangarensu har lokacin Babbah Bai tashiba Dan haka a dining
din palonsu ake jere masa nasa abincin Dan Daman can su basa joining Jamaar gidan cin abinci a table musamman idan Omar Yana gari.
*****Karfe biyu ta dawo gida ta tarar da kowa Yana jiranta cikin farin ciki da murnan gamawanta suka fara murna suna taya
ta murna sosai,
Mum Nur ce ta rungumeta tana cewa
"Congrats my girl"
"Thank you Mum Nur"
Didi ma rungumeta tayi cikin farin ciki Da Jin dadi kafin Fatmah ma datake gida ta miqa hannu ta tayata murna fuska a sake.
Daidai lokacin ne Hafiz da A
rfat suka dawo fa gudu yayo gurinta yana nuna mata abinda yake hannunta ta dagasa daqyar sbd yanada nauyi tana kallan Yaya Hafiz Dayake kallanta Yana cewa
"Finally Lady AM budurwan Babbah ta gama karatu, congrats Lady Jden"
Dariya tayi sbd a yanzu du
k lokacinda aka ambaceta da sunan budurwan Babbah farin cikine ya ke rufeta sbd haryanxu duk yanda ta samu sauyin da wayewan ita dai dince budurwan Babbah da haryanxu yake jinta kaman yar jaririya Baya ganin girmanta duk da lafiyayyan jikan data dire masa.
"Yaya Hafiz thank you,Amma ka Tina alkawarinmu right??
Dariya yayi Yana wucewa hanyar dakinsa Dake gefensa shi Daya Yana cewa
"Ban manta ba"
Yana wucewa Kai tsaye palon Babbah ta nufa daidai Yana fitowa zai tafi makarantar tata da kansa su daw
o tare sbd farin cikinsa Baya misaltuwa kaman yanda Omar yake can farin cikinsa a bayyane na ganin wannan Rana.
Hannu Babbah ya miqa mata daidai lokacinda suka Hade a tsakiyar palon fuskansa a washe da farin ciki yayi Wani irin haske Shima ya sauya sosa
i Hutu ya ratsesa daidai gwargwado.
"Budurwata ayau ta zama mace itama ta tashi daga yarinya yar makaranta ko?"
Dariya tayi tana kama hannunsa cikin nata tace
"Babbah ai kullum ni baby ce a gabanka,
Thank you."
Dadah data qaraso ciki itama za
unawa tayi tana kallan yanda Ameenatou din ke narkewa a gabansu kaman dai koyaushe yanda suka Saba abunsu tafara sakawa karatun da rayuwarta albarka harma da Arfat da babusa a zancen.
Bata Wani zauna sosai ba ta miqe ta fita ta haye Samanta inda dakint
a Dana ARFAT ne kadai a saman sai Palo wadatacce sai kofar da zata sadar da ita zuwa palon Dad dinta.
Dayan bangaren saman shine na Uncle Ahmed da matarsa aunt Didi sai dakin Fatmah itama a saman,Hafiz Kuma bangarensa daban.
Komai na Ameenatou da Arf
at a gidan ya banbanta Dana kowa duk da na kowa dinma duniya ce me zaman kanta Dan kuwa kaf gidan baka gane waye Asalin 'dan me gidan waye bare,
Rayuwar Hutu da daula kawai sukeyi da wayewa da zallan ilimi sbd ko Babbah yanzu yana shiga mutane ba laifi
sbd tini yayi abokin hira Wani dattijo Dan boko dayake zaune kasar da yayansa da matarsa yayi retire tini zaune yake a gida Yana hutawa Kuma me kudi sosai Amma kasancewan baida matsala ba ruwansa sosai yake buqatan Abokin hira da tattauna tsufa da lokaci t
ini suka dinke da Babbah dayake a kusa suke Dan Hakan kusan koyaushe suna tare kodai anan gidan can bangaren hutawar Omar ko a gidan shi Alh Al'ameen din.
Bedroom dinta ta Isa Kai tsaye Arfat Yana biye da ita Yana rigimar a cire masa kayansa damunsa s
ukeyi.
Tana shiga bedroom din qamshin turarenta na Rasasi Daya kama dakin da sanyin AC suka buso mata lumshe idanuwanta farare tana qarasawa ciki ta ajiye wayarta dake hannunta sbd handbag dinta tana shigowa sarrah ta karba ta hawo sama da ita.
Kayan
jikinta ta zare ta janyo bathrobe ta wanka ta Saka jikinta gajera fararen dogaye cinyoyinta Dan bayyane ta nufo inda Arfat yake zaune a couch Yana Shan smoothie Daya shigo dashi Yana Sha Yana rigima.
Zaunawa tayi gefensa tana cewa
"My blue eyed cham
p zaqin ya Isa haka zo Mommah tai Maka wanka.,
Karban abinda yake hannunsa tayi ta ajiye kan table tareda zaran tissue ta goge masa bakinsa tana kallan fuskansa cikeda tsananin so da kauna tareda tinani da burinta Daya da a duniya takeson cimmasa fiyeda
komai akan 'danta,
Lokuta da dama ARFAT Yana mata yanayi da Haroon Wanda tinanin hakan kadai Sai Yana bata tsoro da fargaban idan b ciwonta ne ke Neman dawowa ba sbd Babu ta yanda zaayi 'danta yayi kama da Wanda bayama duniyar,
Ta bangaren Daya kuma t
soro da mamakinta shine ta yanda babynta yazo a bature tamkar ba itace ta haifesa ba Kuma Tako ina bata hada jini da turawaba,
Kakanninta na asalin Jadens Kuma da ake fada basu hada jini ba bare tace daga can ta debo jini haihuwar baturen baby.
Babban
burinta a dunuya yanzu shine idan ta tsayu a Kan kujeranta datake Kai yanzu shine neman sister Ashley da Hafiz ya tabbatar mata da ita ce kadai zata iya sanin waye uban cikin sbd a yanda bincikensa yazo itakadaice tasan yanda Ameenatou tayi rayuwa a asibit
in tin daga ranar data shiga har ranar da suka rabu babu abinda ba itace take kulawa dashi ba na Ameenatou.
Basa Nigeria Amma duk wani bincikensu akan Neman sister Ashley Hafiz Yana gudanar dashi daga Nan din batareda sanin kowa ba daga shi sai Ameenato
u din,
Bata San kamannin sister Ashley ba a idanuwanta Amma yanda take samun bayanan da ake samowa da yanda Suke fada mata yanda taso ta ko bayan dawowanta hannunsu batada abin fada sai sunanta ya saka takejin kaunarta da tsananin son ganinta da son san
in waye uban 'danta sanyin idanuwansu.
Sarrah ce ta shigo dakin dauke da Madara me dumi da aka gama hadawa AM din Dan kaidanta ne Shan Madara me dumi kafin cin abinci.
Acikin glass jug ne da cup akan tray ta ajiye kan table tana sake mata barka da da
wowa tana kallan Arfat Dake Kiran sunanta Yana dariya.
"Thank you sarrah
Ki Jira nayi masa wanka kafin na fito kuje dakinsa ki shiryasa Shirin bacci sbd zamuyi bacci kafin yamma kaina yana Dan ciwo.
Toilet ta jasa suka shiga wanda yake a fadade kama
n ba toilet ba sbd tsari da tsafta tareda qamshin dayakeyi,
Komai na amfaninta su toiletries nata na musamman ne gasunan a jere,
Shower gels da toothpaste, mouth wash da face wash da towels na amfaninta duka a tsare suke designers da ordernsu akeyi a
na ganin sun kusa qarewa Ke ciresu a jera mata wasu masu aikinta kenan kuma kusan komai na amfaninta Dana Arfat hakan ne ake masu basa qarewa har karshe ake siyo wasu a dauke waincan a jere sabbin.
Da Asalin original bismd akewa ARFAT amfani Dan haka ak
wai set dinsu a dakinta da toilet dinta Kuma akwai a dakinsa da toilet dinsa Dan haka shi tafara yiwa wanka ta miqowa Sarrah shi daqyar daure da qaramin towel dinsa a jikinsa suka nufi dakinsa dan a shiryasa.
Wanka Tayo a natse tareda alwala ta fito tan
a qamshin Rosella shower gel daureda towel blue sbd gurin wankan Arfat ta jiqa bathrobe din data shiga da ita.
Gaban mirror ta zauna tana goge jikinta ahankali tareda kallan fatar jikinta Dake wani irin daukan idon haske da lafiyayyun gyara datake samu
na luxury life.
Oil na original Neutrogena ta shafa a jikinta na tareda bodyplash masu sanyi ta miqe ta nufi closet ta saka black laced undies kafin ta Saka Doguwan Rigan AnnaBrom black data fitar da kyanta sosai duk da bame adon komai bace sedai kudin
kadai zai iya ciyar da wani gidan n sati biyu.
Veil me kauri ta nada akanta tayi sallan dhuhur tana idarwa Sarrah ta shigo da Arfat a jikinta yayi bacci ta kalli bakinsa da yayi pink alaman yasha Wani abin bayan wankan datai masa Dan haka Sarrah data kw
antar dashi Saida ta goge bakinsa da tissue kafin AM din ta gyara masa kwanciyarsa cikin kayansa ba bacci ta hau gefensa ta kwanta bayan Tasha madaranta sosai.
Sarrah ce ta kashe musu hasken dakin tareda rufewa ta sauka Babu me sake Hawa saman sai sun f
arka sbd kada a tadasu wannan shine kaidan gidan.
#MAMUH#
#AM JDEN
#THE SEELAHS
#JAMAAL MAM SEELAH
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwas
on Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number do
n yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
[5/19, 11:11 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
102
*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan ma
iya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces
and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfa
rma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products
đŸ‘‡
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt
0xVj2vuE8HAGRUL
*******
Ranar da suka isa Miami Kai tsaye Lodge dinsu ta isa shi Kuma hafiz gurin aikin daya kawosu ya nufa Dan yau akwai abinda zai fara.
Wanka tayi tareda saka Riga da wando marasa nauyi tayi sallah takuna ta kwanta Dan hutawa ko w
aya batai da kowaba saita gama hutawa sbd kanta dayake Dan ciwo.
Sai tsakar dare Dad da hafiz suka dawo tareda Uncle Ahmed lokacin tini ankawo mata komai na abinci an jere taci iya abinda zataci tayi brush da wanka ta shirya cikin kayan bacci ta Haye ga
donta tagama wayoyinta tayi bacci abinta.
Da safe dukkaninsu Babu Wanda ya fito baccin safe da hutawa sukai sai after 10 kusan 11 ma tukuna.
Itace tafara fitowa sanyeda wide leg jeans da sweatshirt din Burberry da qaraman hula tana waya dasu arfat da
yake musu rigima sosoi akan rashin Dad da uncle hafiz dinsa da ita mommahn nasa Amma dai ta samu ta lallabasa ya manta da zancen rigiman sunyi fira sosai dasu dadah kafin ta kashe.
Kamshin Dad dinta ne na musamman da Bata taba tantance Wani namijin daya
ke da qamshin nutsuwa irin na Dad dinta ba Dan haka a duk lokacinda ta shaqi qamshin mahaifinta me nutsuwa kamansa sai ta godewa Allah akan yanda yayiwa mahaifinta albarka SBD a duniyarta mutanen datafi so fiyeda rayuwanta dukansu Maza ne su uku,
Babbanta
,Dad dinta da 'danta Arfat.
Omar jaden ma Yana waya a natse ya qarasa fitowa palon ya zauna cikin farar jallabiya data nutsu a jikinsa yana ganin yarsa yayi sallama da wayar a Natse kafin ya ajiye wayar gefensa Yana sake kyakkywan fuskansa ta cika da mu
rmushi da farin cikin ganinta Dan ita kadaice a duniyarsa da idanuwansa suke kalla fuskansa ta yalwatu da sanyin farin ciki da murmushi a take.
Itama farin cikin NE ya mamayeta ta qaraso har gefensa tana cewa
"Dad Ameenatou da Arfat munyi kewanka sos
ai"
Hannu ya miqa mata Yana murmushi ya nuna mata gefensa alaman ta zauna Yana cewa
"Congratulations Lady AM.....
Hannunsa ta kama tana katsesa da cewa
"Dad ban yadda ba bayan baka Nan"
Zaunawa tayi gefensa tana dan narkewa da cigaba da cewa
"Babbah ma Bai je bafa"
Murmushi yayi Yana cewa
"Ayiwa Dad da babbah afuwa to,Amma next time zamu zama a gaba gaba ga duk abinda yazo na budurwan Babbah."
Dadin kalman taji ta kallesa tana yar dariya tana cewa
"Dad ka it's fadan sunan kaima
kenan."
Murmushi yayi Yana kallan wayansa da ake kira,
Bai daga Kiran ba suka shiga zancen business sai ga Uncle Ahmed ya shiga tareda Yaya hafiz daga geamin suke Nan suka zauna ta gaida Uncle Ahmed din tana masa shagwaban Shima Baije graduation nata
ba.
Shima hakurin ya bayar tareda kyautar 10000 dollars as nasa gift din.
Godiya tai masa tana dariya ta Kalli hafiz tana cewa
"Me ma ka bani Kai as gift??
Dariya yayi Yana cewa
"Ohh ni kikewa gatse??
"Eh mana, Dad barazana ma ya ringa mu
n wai aure zaimun Muna komawa Nigeria shine gift Dina imagine"
Dariya dad din yayi Yana cewa
"Eh Kuma ai gift din aure Kam ai Mai girma ne,bare Kila yanada wanda zai bawa ke din kawai a Nigeria,
Ba haka akeyi acan dinba??
"Haka akeyi Dad kawai au
ren sadaka"
Cewan hafiz Yana kallanta da dariya a fuskanta.
Uncle Ahmed cewa yayi
"Ai daughter na ta wuce auren hadi ma bare na sadaka,
Yaya ma ake auren sadakan ne wai??
Ni Banma sani ba wlh"
Dariya sukai dukkaninsu Dad Omar na Tina aurensa da
Aminatunsa mahaifiyar AM din.
Saida suka gama nishadinsu kafin suka nufi table da aka gama gyarawa tsaf da varieties na lafiyayyun abinci da teas kala daban daban Suma.
Zaunawa sukai Breakfast din sunayi a natse kowa na cin nasa abinda yakeda raayi
Cikin nutsuwa da wayewa.
Bayan gamawansu sun jima Suna tattaunawa kafin kowa ya tashi.
AM shiryawa ta sake Yi ta fito Cikin wasu qananun kayan marasa nauyi ta fito suka fita tareda Dad dinta zuwa Wani gurin su kadai.
Basu dawo ba sai dare Dan haka
wanka kawai tayi tayi Shirin kwanciya t kwanta.
Kwanansu biyu Suna hutawa kafin ranar signing din tazo sauran shareholders din ma Dake wasu qasashen sun taho ayau da gobe zaayi an kammala kowa ya koma kasarsa.
10 suka isa Building din Roches Publish
ers/Ltd
Lafiyayyun motaci ne biyu suka iso dasu gurin take securities suka qaraso Dan Bude musu mota,
Jden din da kansa aka fara budewa kafin Lady AM din tukuna dayar motar uncle Ahmed ne da hafiz da Shima ake masa kallan 'dan jden dinne.
Hotunans
u aka aringa dauka Yana jarida har suka shige tana gefen Dad dinta sanyeda Off-white dress na Amhash sai glass na Versace dayake fuskanta da wasu shegun wedges na tomford tayi Wani irin kyau ta fito Lady AM dinta sak hakama handbag din hannunta kudinta kad
ai zai iya siyawa Wani mota hannunta daya Yana riqe Dana Dad dinta hafiz da Ahmed Suna dayan gefen nasa.
A yau Omar jden seelah officially ya sanarwa duniya yarsa 'daya tak dayake da ita shine ya Haifa abarsa da bakinsa ya fada ya Kuma bayyanar da ita t
areda nunawa duniya Dan haka take aka fara daukan hotunanta ana watsawa a labarai da sauran media.
Hakan da yayi ya sake daga matsayi da Sunanta AM jden din Kuma take hankalin wasu da Dama ya tashi sbd dukiyarsa da sukeci Kuma suke jira sunsan tazo kars
he.
A Nigeria ma zancen ya girgixa mutane da Dama sun shiga fargaba,
Alh Mam seelah kuwa a lokacinda yake kallan conference din a Cikin labarai da aka Saka Wani lafiyayyan murmushi ya sake Yana ajiye remote din hannunta gefen Mum atee Dake ta faman s
alati da shock na ganin Ameeenatou din a matsayin Lady AM jdens.
Mam kuwa wannan sanarwan Kai tsaye shine yasan sakon menene Omar din ya isar na bayyanawa duniya 'yarsa daya zabi raba kansa da ita tsawon shekaru Dan bata kariya daga garesu Amma ayau shi
ne da kansa ya kamo hannunta ya bayyanawa duniya ita,
Wannan Sako ne ya isar musu da Shirin fuskantar duk wanda yake jiransa Kuma sakon Kam ya isar Dan kuwa gashinan yanzu Suna ganinta Amma basuma San me zasuyi dinba sedai Kuma Omar abinda Bai saniba sh
ine 'yar tasa CE Kuma bayyanawa duniya ita shi a gurinsa shine Abu mafi farin ciki a garesa yanzu sbd yanda duniya yanzu tasan ita Lady AM jden din asalin 'yar jden dince Kuma magajiyarsa kwaya daya tal to duniya ma zata San sirikar Mam seelah ce qwalli da
ya tal,
Matar zafaffen 'dansa Jamaal seelah wanda Shima ayanzu duniya take takawa dashi a amtsayin seelah din dayafi kowannensu kudin kansa yanzu da Kuma kuruciya hakama babu wanda yasan asalin qasar dayake zaune dindindin a yanzu sbd baama ganinsa sedai
labarinsa.
Zai nunawa Omar komene fuskantar junan da zasuyi to AM sirikarsa ce sai Kuma ta dawo hannunsa hakama aurenta dayake hannunsu mutuwa CE kadai me rabasa Amma mutum dai ko waye yace zai raba auren to kwanakinsa ne suke qarewa.
Wani murmushin
me sanyi ya sake sakewa sbd a shekarun Nan Ya Gina kansa ne a boye tareda kwantarwa da 'dansa kansa Yana bibiyarsa harya samu tausayin uba da 'da a tsakaninsa da Jamaal ya dawo Yana magana da 'dansa a duk lokacinda Jamaal din ya bada daman a samesa a waya
din sbd samunsa Abu ne me wuya,
Jamaal Yana tareda shi Bai yafesa ba hakama ayau Allah ya bayyanar masa da sirikarsa mukullin arziki da cikan burinsa na Tim kafin asan zaa haifesu Dan haka kauna ta musamman yakejin yanaiwa Ameeenatou da kansa.
Omar y
a hutar dashi ta bangarori da Dama Dan haka Babu abinda zai masa sai godiya da wannan conference din daya hada Dan isar da sakonsa.
Wayarsa ya dauka ahankali ya Saka Kiran Jamaal batareda ya tankawa Mum atee Dake gefensa tana fama da shock Dan kuwa itam
a batajin zata taba barin auren 'yar jden ya fita hannunsu duk da Jamaal Bai taba bata daman shiga rayuwarsaba,
Kwata kwata ko ganin idanuwa batai masa Gani nawa ba