Showing 180001 words to 182667 words out of 182667 words
kwanakin gameda mahaifinsa da
yake yawan mafarki Dan haka yasa aka Nemo masa Wani daga asibitin nakasashin da dad dinsa yake ya kirasu Dan yanason Jin Wani Abu gameda Dad dinsa.
Bayanin da Akai masa akan sosai Dad dinsa baida lafiya yayi mugun Nisa ya sakasa Jin rashin nutsuwan zuci
ya idan ba zuwa yayi ya dubosa da kansa ba Dan haka Babu wanda ya sanarwa acan Nigeria suka shirya dawowa.
Yaso Halal dinsa ta zauna anan yaje ya dawo sbd yanason ta haihu a Costa Rica din Amma tace Sam bazata zaunaba zata bisa ta dubo Dad din itama tin
da basusan yaya jikin nasa yakeba.
Siddeeq dai daman shine Mai riqeda ragamar tafiyar musamman daya fahimci akwai damuwa a tattareda Jamaal din Duk yanda yaso boyewa Dan haka suka shirya gabaki dayansu suka dawo.
Ranar da suka dawo Saida suka sauka a
Nigeria akasan da zuwansu aka aika motoci daukansu.
Daga airport jden mansion suka fara nufa inda kowa yake jiransu cikeda farin Ciki da murnan dawowansu.
#MAMUH
[6/6, 11:45 AM] MG: *_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
151
Last chapter
Babbah dayayi
tsananin kewan 'yarsa Yana ganinta kallo daya yayi mata da tsohon Cikinta yaji duka zuciyarsa ta wanke fushinsa na yayewa Yana tsiyayewa musamman daya ga kwanciyar hankalin datake cikinsa da yanda Jamaal kwata kwata ko hannunta baya saki ya Saba duk inda z
asu ko a gaban waye baya iya sake hannunta itama kusan ta Saba din Dan haka ko a gabansu Dad din bataji komaiba Saida tayi Ido biyu da babbanta ta zare hannunta daga nasa ta rungumesa tana ciko Idanuwanta da hawayen kewansa da tsananin kaunarsa.
Dadah m
a Cikin farin Cikin ta rungume yarta tana godewa Allah daya nuna mata wannan ranar ga tsohon Cikinta da Wani irin kyau ya qara mata da lafiya.
Ashley ma tayi Wani irin kyau da fresh ga Cikinta a gabanta sedai ita Kam ba Wani lafiya ne da ita sosai sosai
ba Dan haka lallabata aka fara ana tarairayanta.
Mum dinsa kuwa rumgumesa tayi tana sauke ajiyan zuciya sunfi nawa kafin ya dagota yayi kissing tsakiyar kanta da hannuwanta Yana cewa
"Mum I love you"
"I love you too My love" ta fada tana shafa fu
skansa sbd haske da Wani kyau daya qara ga wata lafiyayyar gashin fuska daya kwanta masa luf daya Tara.
Dad Omar da bayanan suka iso Suna isowa Shima rungumesa yayi Yana fadan yanda yayi kewansu kafin ya sakesa ya rungume yarsa wadda itama kallo daya ya
yi mata yasan tana Cikin amincin Allah da nutsuwan rayuwa tareda kulawa sbd tana barin jikin Dad din hannunta ya koma cikin na mijinta.
Arfat na dawowa school yaga iyayensa tsalle da murna ya ringa Yi Yana fadawa jikinsu musamman ganin Mommah dinsa da a
unt Ashley zasu basa babies masu kyau kamansa sukace.
Kaman zaa hadiyesu dukkaninsu haka aka ringa tarairayansu har zuwa dare suka tattara suka nufi gida.
Koda suka isa masu Aiki sun gama gyara koina bayan qamshi da sanyin AC Babu abinda yake tashi.
Maman fadeela da Ayesha kaman zasuyi me Suma sbd murnan dawowansu Dan haka take gida ya cike tinda sun dawo gashi da Arfat da nanny dinsa aka taho duk da daqyar babbah ya bawa Jamaal din shi Dan yace bazai taba Basu shi din ba ARFAT nasu ne bazai bar jd
en mansion ba.
Dukkaninsu a gajiye suke Dan haka wanka sukai kowa yayi Shirin bacci ya kashe wayoyinsa tareda nata suka shige gadonsu ya rungumeta Yan lumshe Idanuwansa d suke cikeda damuwar dayake boyewa sbd rashin sanin Yaya jikin Dad din nasa da su
ke maimaita masa irin Nisan d yayi Yan buqatan zuwa da gaggawa garesa.
Washe gari Koda suka fito masu Aiki tini suka gama gyare koina tareda cike dining da breakfast dinsu Wanda Saida aka tambaya wanne zasu ci tukuna aka girka verities daban daban.
D
r Aleena ce ta iso gidan sbd tayi kewansu ita Kam Dan haka tare zasuyi breakfast Dan 10 ma ta Dade da wucewa.
Cikin farin Ciki da tsananin kauna da kulawa hankali kwance sukai mata sannu da zuwa tana rungumesa Shima Cikin nutsuwa da sanyi ya rungumeta s
bd gabaki daya ya koma Jamaal dinsa baya Cikin sakewa ko walwala.
Ameenatou ce ta shige jikinta ta rungumeta har zuka zauna kan dining tukuna sukai breakfast cikeda nutsuwa da kwanciyar hankali gabaki dayansu harda su Siddeeq da Ashley da Mum Aleena din
duka Saida ta sake dubasu bayan breakfast din.
Suna gamawa ya shirya white Reiss sweatshirt da wide leg jeans da fcap ya fito.
Siddeeq ma off-white Ralph Lauren polo ce a jikinsa da jeans da farar hular Shima.
Black dolce and Gabbana vshape shade
s ne a fuskan Jamaal daya sake qure fitowan kyau da ajinsa tareda tsadarsa gashi fuskansa a kame take tsaf Babu sakewa ko kadan a Cikinta kana kallansa sai kaji zuciyarka ta narke sbd kwarjini da class.
Kissing lips din halal dinsa yayi tareda sake Dora
mata a goshinta kafin ya Dan rungumeta Yana cewa
"Take care baby"
Gyada masa Kai tayi tana kallan Cikin Idanuwansa itama tace
"I love you,take care too love,
Allah yasa jikin nasa da sauki,
He'll be okay inshallah"
Sake kissing lips dinta ya
yi Yana juyawa gurin Mum dinsa ya rungumeta itama tace masa Allah yasa ba sosai bane jikin na Mam.
Ashley Dake jikin siddeeq janyewa tayi tana zare hannunta daga nasa yayi kissing hannuwanta Shima tukuna suka juya suka fice.
Kai tsaye asibitin da M
am yake suka nufa Babu me cewa komai sai siddeeq daya fara Shirin fitar da Mam din da kawai zasuyi waje duk da Basu ga halinda yake Ciki ba Amma dai hakan shine abinda zaayi din daman komai nasa na hannunsu tin daga Id cards da passport da sauran abubuwans
a masu Mahimmanci.
Suna isa tin daga yanayin asibitin jikin Jamaal ya fara sanyi sbd bayajin zai iya awa ko daya a asibitin sbd cuta zata iya kamasa Dan haka nosemask siddeeq ya dauko musu daga mota suka Saka kafin suka kutsa Kai tsaye inda zaa kaisu da
kin Mam.
Tin kafin su isa dakin hankalin Jamaal ya tashi zuciyarsa tafara tsinkewa sbd ganin balain da suke dosa da sunan dakin da mahaifinsa yake Ciki.
Suna tsayuwa kofar dakin kafin a Bude Wani Azababben wari me Saka ciwon Ciki ya tirniqesu
Sidde
eq ya Kalli Jamaal da sauri sbd shi kansa Jin yayi zuciyarsa na Neman karyewa bare Jamaal din.
Ana budewa kallo daya Jamaal yayiwa Dan qaramin qazamin zanin dayake rufe da Dad dinsa daya koma kaman skeleton sbd rama da azabar Ciwo daya gama cinyesa take
qafafunsa sukai Wani irin mummunan sanyin daya kasa dagasu siddeeq ne yayi karfin halin zuwa har gaban Mam din ya miqa hannunsa ya yaye rufarsa take ya fashe da wani irin Kuka duk jarumtarsa baisan lokacin da kukan ya taho masa ba sbd idan ba ance Maka Ma
m dinne ba bazaka tana cewa shi din bane sbd wannan Yama tashi daga mutum ya koma wata halittar.
JAMAAL da zuciyarsa ta gama karyewa akan mahaifin nasa Shima takowa yayi ya durqusa gabansa.
Qamshinsa ne ya shiga hancin Mam din da Baya iya komai bayan
kallo da Idanuwansa da idan suka kalleka zaka iya firgita sbd tsoro.
Qamshin Jamaal ne daya shiga hancinsa ya sakasa Bude Idonsa daya dayake rage masa ya zubawa fuskan Jamaal din Yana tantance kamannin ran dayafi so a duniya fiyeda komai Kuma duk tsawo
n wannan lokacin Babu wanda yake cikeda kewa da tsananin son Gani kaman Jamaal da 'dansa dayake son Gani ko so daya ne ya tabasa kafin ransa yabar jikinsa.
Jamaal na hada Idanuwansa da mahaifinsa hawayensa gangarowa sukai batareda ya iya riqesuba duk ja
rumtarsa Dan haka hannuwansa na rawa ya Saka batareda qyama ko shakkar komaiba ya dago Dad din ya rungumosa jikinsa Yana rintse Idanuwansa da sukai tsananin ja hawaye na qara saukowa daga cikinsu.
Bai iya cewa komaiba daukansa yayi cak tareda miqewa tsa
ye dashi take suka fito siddeeq kuwa da Shima Idanuwansa suka sauya sbd Kuka sosai shikam yayi.
Da ambulance akai gaggawar barin asibitin da Mam Wanda Bayan hawayen Dake gangarowa daga gefen idonsa Babu abinda yakeyi sai Kuma kallan Jamaal bayason ko ky
aftawa sbd Bai taba tinanin zai sake samun cikar burinsa ba a duniya na ganin Jamaal dayeke tsananin fata kafin barinsa duniya.
Duk halinda yake Bai taba Jin tsana ko zafin 'dan nasa ba sbd ya tabbatarda tsananin son Jamaal shine kaddararsa da jarabawan
sa wadda yake rungume da ita har Lokacin hannu bibbiyu sbd Bai taba Dana sanin sonsaba fiyeda kansa ba har yanzu din.
Qazantar Dake tattare da Mam din wadda ta gama cinye fatarsa da Naman jikinsa ya Saka Saida aka fara tsaftacesa sosai kafin akai dakin
taimakon gaggawa dashi duk da ba a gigice yake ba kawai a Cikin asalin ciwon dayake cinye namansa ahankali yake wanda ruwa kawai da sauran abubuwa sukai masa sbd fita dashi Cikin gaggawa Jamaal din zaiyi.
Zaunawa yayi gaban Dad din lokacinda kowa ya fic
e ya dago jajayen Idanuwansa ya zubawa Dad din wanda Idanuwansa suke rufe Cikin tsananin azabar da shi kadai yake jinta Cikin jikinsa tana cinsa.
Hannu Jamaal ya Dora akan na dad din dayake rufe gabaki dayansa sbd Sam bazaa so kowa ya gansa a hakan ba s
bd ya nade ya koma kaman Dan shekara goma Sha biyar sbd qanqatarsa.
Cikin wata irin murya Dake rawa da tsanani tausayi da kewa ya furta
"Dad Allah ya yafe duka kura kurenka ya dawo da haske rayuwarka da lafiya tareda tuba me tsarki"
Ahankali Mam y
a Bude Idanuwansa ya Kalli Jamaal din Jin adduar da yayi masa har Cikin ransa ya lumshe Ido da sanyi alaman Ameen.
Kafin Jamaal ya sake magana Dad Omar ya shigo dakin Cikin hali na tsananin damuwa da Wani Azababben quncin daya nauyaya zuciyarsa da Kiran
Jamaal din ya samesa akan Mam jikin Mam din sbd duk abinda yake tsakaninsu akwai wata irin kaunar asali tin ta quruciya a tsakaninsu dasukewa junansu.
Kallo daya yayiwa Mam ya kasa qarasowa gurinsa duk manyancinsa Shima Kuka ne ya kufce masa Mai tsanan
in Ciwo da radadin gaske.
Jamaal ma qasa yayi da kansa tareda miqewa daga inda yake ya bawa Dad din guri ya qaraso gurin Dan uwansa ya zauna ya Dora hannunsa akan na Mam tareda sake fashewa da Wani kukan.
Mam da zuciyarsa ta gama mutuwa ahankali ya m
otsa hannunsa ya kama na Omar din dayake Cikin nasa hawaye masu dumi na gangaro masa kaman a mafarki Allah ya basa iKon Bude Baki ahankali ya furta
"Omar idan na rasu Nima ka kaini gefen sauran yan uwanmu ka rufeni"
Omar sake damqe hannun Mam din yay
i Yana kasa cewa komai sai jajir da Idanuwansa sukai yanajin Wani irin nauyi a zuciyarsa gameda Yan uwansa da suka barsa daya bayan daya.
Jamaal Mam din ya kalla kafin ya Kalli Omar ya sake Maida kallansa kan Jamaal ya Bude Baki a wahalance da sauti mar
a fita yace
"Jamaal na yafe Maka komai kada Allah ya kamaka da komai akaina na yafe Maka Allah ya shirya Maka zuri'arka ya musu albarka"
Dago jajayen Idanuwansa Jamaal yayi ya Kalli Dad din nasa Yana kasa cewa komai bayan adduar dayake masa Shima na
allahyya yafe masa.
Omar ma da Mam din ya kasa kallansa ya Nemi gafararsa sbd yasan cun cutatar dashi mafi cutarwa ajiyan zuciya me zafi da qunci ya sauke ya Kalli Mam din ya Bude Baki yace
"Na yafe Maka Mam duka ku dukan Allah ya yafe Muku ya karbi
tubanku Kuma"
Hawaye masu Ciwo ya sake gangaro masa Yana kasa kallan Omar din.
Dr Aleena ce ta shigo dakin sai Ameenatou me tsahon Ciki Dake bayanta sai babbah da dadah tareda Arfat sai Kuma hafiz wanda shine ya kawosu,
Bayan shigowansu maman fade
ela ce da Ayesha da siyam Wanda itama ta warware fes ya dawo tana hannun Dad Omar din kaman yarsa.
Kallansu yayi bayan dayan ciwonsa na tsananta sbd zuciyarsa data kasa daukan kallansu sbd a Cikinsu kaf Babu wanda Bai Raba da masoyansa ba Dan haka Bai i
ya cewa komai bayan ciwonsa dayake Neman rikicewa.
Arfat ya qurawa Idanuwansa Wanda Jamaal ya kamo hannunsa ya kawo masa gabansa tareda kamo hannunsa ya Dora masa Akansa Cikin sanyi murya a shaqe yace
"ARFAT SEELAH"
Wani irin Kuka mara sauti Mam y
a sake Yana riqe Arfat din wadda yake kallansa kafin ahankali ya Bude Baki yace "grandpa" kaman yanda Mommah dinsa ta sanar masa gurin grandpa dinsa zasu.
Wannan kalman ta Saka zuciyar Mam kasa dauka take ya rikice gabaki daya Yana kallansu daya bayan
daya kafin ya tsayar da Idanuwansa akan Jamaal Wanda ya rungumosa jikinsa Dad Omar Yana karanta masa kalman shahada Yana karba kafin rai yayi halinsa agaban kowa take dakin yayi tsit jikin kowa a mace cikeda tsananin tausayin Jamaal Wanda ya rungume Dad di
n nasa da kyau Yana rintse Idanuwansa dake radadi sbd rashin kukan daya kasa fitowa daga cikinsu.
Babu wanda a dakin Cikin mata hawaye Bai zubo masa ba a mazan ma Dad Omar Kuka yakeyi sosai sbd ya koma shi kadai ya rage a Yan uwansa duk sun tafi sun bar
sa Shima Yana fatar idan lokacinsa yayi akaisa kusa da Yan uwansa a rufesa.
****Rasuwar Mam seelah Babu Bata lokaci ta yadu Dan haka Babu Bata lokaci Aka tafi da gawarsa Ashlawa kaman yanda yaso acan Akai janazah dinsa aka rufesa Omar ya zauna gaban k
abarin su hudu a jere yayi kukan da kusan ya sakar masa ciwon kirji,
Jamaal ma yayi kukan daya bawa Ameenatou da mum dinsa tsoro sosai Dan haka Suma sunyi Kukan Wanda yake na tausayinsa Dana tausayin Mam din tareda masa fatar rahamar ubangiji.
Bayan
rasuwarsa da sati uku Ameeenatou ta haihu a hannun Mum Aleena a asibitinsu ta haifowa Jamaal baby girl kyakkyawa wadda tafi Arfat kama da Mum dinsa kaman an tsaga Kara.
Haihuwan ce ta dawo da farin cikinsa daya rasa na lokacin Dan haka sai alokacin kowa
ma ya samu farin Cikin familyn ya dawo sukaita murna cikeda tsananin kaunar Baby Aleena little da aka samu.
Tinda Mam ya rasu lafiya tafara gagarar Dad Omar sbd Saka abin aransa da yayi Dan haka Dr Aleena ta daukesa suka bar qasar sbd treating dinsa da
Kuma kwantar masa da hankali.
Tafiyarsa da Dr Aleena ya Saka kusan duka sauran families dinma biyu suka kwashe gabaki daya suka bisu acan Ashley ta haifi baby boy Wanda aka sakawa Mam seelah little.
Fatmah ma namijin ta Haifa aka Saka masa Omar Shik
uma.
Saida sukai kusan wata hudu acan tukuna suka tattaro suka dawo Cikin kwanciyar hankali da aminci suka Dora sabuwar rayuwa me cikeda kaunar juna da Jin Dadi tareda tarbiyantar da yaransu a Nigeria.
Dad Omar da uncle Ahmed manyanci yazo sosai Dan
haka tini suka ajiye komai zaman Hutu kawai sukeyi sun barwa Yara ragamar komai musamman Hafiz da shine yanzu kusan shugaba a komai na jdens shida Ameenatou da Fatmah wadda ta Jame dasu Ameenatou da Ashley wadda take karatun likita yanzu itama hankali kwan
ce Hutu da nera ta zauna mata.
Jamaal kuwa duk wata martaba da mutuncin sunan SEELAHs ya dawo dashi ya sake daukaka darajarsu xuwa matsayin dayafi na bayan ma Dan haka rayuwa tayi daidai sai hamdala da godiyan Allah yanzu.
#MAMUH
ALHMDLLH
ANAN NA K
AWO KARHEN LABARIN AMEEENATOU WANDA INA ROKON ALLAH YA YAFE MANA KURAKURAI DA LAIFIN DA MUKAI BA DAIDAIBA.
SAI MUN HADU A SABON LITTAFI NA GABA INSHALLAH
INA MIQA GODIYA MAI TSANANI GASKE GA MASOYAN DA SUKAI KOKARIN BINA TIN FARKO HAR QARSHENSA.
ALL
AH YA SAKAWA KOWA DA KHAIRAN
IDAN AKWAI INDA NAYI MANTUWA BAN TABO BA KO TABOWA BA DAIDAIBA KO YANDA YA KAMATA TO AMIN UZURI AJIZANCI JE JA YAR ADAM
ALLAH YA BAR TARE YA QARO MANA HAKURI DA KAUNAR JUNA.
AMEEN YA ALLAH.