Showing 33001 words to 36000 words out of 159340 words
dai ta samu saurana.
Kuma na samu natsuwa sosai fiye da tsammani na. Ba tare da ya nuna ya gaji ba na sake shi ya saka hannu zai riƙe ni na ce" Zan ta shi.'
Sai ya taimaka min na miƙe hijabin jikina
duk ya bushe da ruwan hawaye shima miƙewa ya yi ina gani yana juya wuya da hannayena. Sai da na yi dariyan mugunta a raina, ban ce masa komai ba ya ga na fara ta ku zan bar falon sai ya biyo bayana ya na fa
ɗ
in"
"Sadiya ba mu karya ba fa yau"
Sai a l
okacin sai kuma ya na mganar na ji cikina na juyawa sai na juyo muna fuskantar juna kafin na ce" In soya ƙwai mu sha tea."?
Na tambaya cikin sarƙewa muryan. Ya ƙariso gabana ya kuma saka hannunshi ya riƙo hannayena lokaci
ɗ
aya ya na fa
ɗ
in" Za ki iya?
Ko
na kama miki?
Kai kawai na gya
ɗ
a masa alamin zan iya. Amma bai bar ni ba duk in da na bi yana bi na, hijabin jikina ma shi ya cire min tare muka soya ƙwanan ko na ce shi ya ma soya a falon yara muka karya dka da shima bai ja ni da hira ba amma zai kalleni
da kulawa in ya ga na yi shuru na kasa kur
ɓ
an tea
ɗ
in
"Are you ok?
Da kulawa ya ke tambayata amma ga ni na yi ni da ya yi ma kishiya sai na ga kamar tambayar ta renin wayau ne shi ya sa na bi na ha
ɗ
e rai, duk da haka bai ƙyaleni ba bayan mun gama sh
i ya kwashe komai ya kai kitchen ya dawo ya iske ni dafe da kai ya na tambayata na ce kaina ne ya fara ciwo jikinsa na rawa ya je ya kawomin panadol ya
ɓ
allo ya ba ni tare da ruwa na sha ya kuma riƙe ni har bedroom
ɗ
in mu na kwanta na ya rufa ma ƙafafuna b
lanket.
"Ki kwanta ki
ɗ
an huta ina ga kukan da kika yi ne ya sa ka miki ciwon kai."
Ya fa
ɗ
a lokaci
ɗ
aya ya duƙa ya sumbaci goshina. Ya juya zai fita sai na riƙe masa hannu sai ya juyo ya na fa
ɗ
in" Me kike so uhm?
Sai na ce"Ba za ka fita ba ne?
"Ko
zan fita sai zuwa anjuma."
Sai na gya
ɗ
a kai sannan na sakar masa hannu
"Menene ko kina son wani abu ne?
Sai na girgiza masa kai alamun babu, sai ya ƙara dawowa ya duƙa ya sumbaci bakina, har zai tashi na riƙe masa wuyan rigarsa da hannuna guda
ɗ
aya na
ɗ
ago kaina nima na sumbaci bakinsa sannan na sake shi sai kuma da sauri na juya masa baya har ina runtse ido kamar na yi abin kunya na san ya na ta kallona sannan na ji sautin mirmishinsa kafin na ji takunsa da fitarsa lokaci
ɗ
aya ya na fa
ɗ
in.
"Ina son k
i Sadiya ta."
"Ina sonka Yalla
ɓ
ai na."
Na fa
ɗ
a a hankali tare da jin wasu tasowar wasu hawayen amma na danne. Ni fa sai yanzu da kishiya ta fa
ɗ
o kaina na fahimci halin da wa
ɗ
anda kishi ke saka su kashe miji ko su illata kishiya, a da in na ji labari
in ta mamaki ina zaginsu a raina har ina ji ma a tunanina kawai saboda namiji sai mace ta haukace har da kisa. Wato daga ranar da na san Yalla
ɓ
ai ya zama namu ba nawa ba na fara yi musu uzuri da gaske ba sa cikin hayyacinsu. She
ɗ
an na ƙawata zafin kishi, k
a ji kamar ka yi hauka, ka koma kana ganin hotuna kala kala wa
ɗ
anda in ba ka da imani tsab za su iya saka ka aikata abin da za ka dawo kana nadama. Ka koma kana ganin mutane dishi dishi tsabar kishi, zuciyata ta riƙa suya ta na kai ka in da in ka hasaso za
ka ji kamar kowa ma na duniya ya mutu duk a huta. Ni kaina ba domin Allaah da addu'ar da na riƙa yi da dauriya da tuni an ji kanmu ni da Yalla
ɓ
ai tsabar yadda na ke jin haushinsa sai she
ɗ
an ya sarrafa tunanina na yi masa illa.
"Astagafurillah."
Na
furta a fili saboda tunanin da ya giftamin a fili na furta" Ya Allah ka sassautamin wannan zafin kishi. Sannan ka tsare ni da aikata abin da zai jawo min nadama a rayuwata."
Na duba wayata ban gani ba sai na tuna na baro ta can falo sai na koma na kwanta
na runtse ido ina karanto suratul Jumma'a tirya tiryan ina cikin yin karatun barci mai cike da natsuwa ya kwashe ni ban farka ba sai sha biyu da wani abu na rana.
****
Ko da na tashi Yalla
ɓ
ai ya gama komai na aikin gida. Girki ne kawai bai yi ba shi
ma domin zai je office ne ya ce akwai aikin da zai yi, ya fita ya barni a falo yau har haraba na raka shi, ni kaina na yi mamakin ji na sakayau kamar ba ni ba.
Bayan fitansa ba da
ɗ
ewa aka kawo naman rago kilo biyu duk da ma muna da sauran naman salla a
cikin kakide, sannan ga dambun nama bai ƙare ba Musbahu ne ya kawo min tare da kayan miya da kayan lambu. Daga Yalla
ɓ
ai ne, kawai sai na samu kaina da tambayan shi ina Yalla
ɓ
an ya ke.?
"Ya na can office akwai mutanen da ya ke ganawa da su."
Har ya ba
r gidan ina zaune ina tunanin dalilina na tambaya. Me na ke tsoro? Kar ya je wajen Gimbiya? Wata zuciyar ta ce kar ki manta ya aure ta wata rana tare za su kwana a
ɗ
aki
ɗ
aya. Sai na ji hankalina ya tashi amma sai na fara kiran sunan Allah har na samu natsu
wa. A raina na saka jarumta sannan zan
ɗ
auki shawaran Nene zan riƙe Allah domim shi ka
ɗ
ai ne za ba ni ƙwarin gwiwan fuskantar wannan yaƙin da ke gabana.
Wanka na fara yi sannan na shiga kitchen na soya naman nan gaba
ɗ
aya. Kayan miyan ma na yi blanding
ɗ
in su, na tafasa na
ɗ
iba na yi miya sauran na saka a fridge kafin wani lokaci na gama aikina na gyara kitchen
ɗ
in wajen ƙarfe uku na rana ina falon yara lokacin mun gama waya da Balaraba
kenan na ce Saude ta yi zamanta kawai sai gobe sai ga kiran Hauwa a
waya wai gobe ta na nan zuwa na ce Allah ya kawo ta a raina na kuduri niyyar sai na yi ma Hauwa tsinin baki domin ina jin haushin su ita da Munnira.
Ina gida har yamma yara sun dawo daga makaranta har sun ci abinci. Mun yi waya da Yalla
ɓ
ai ya na tambaya
akwai kayan marmari? Na ce sun ƙare sai ya ce gashi nan zuwa zai taho dashi. To bayan mun yi mangariba muna azkar da yara ya sake kirana.
"Sadiya ta."
"Yalla
ɓ
ai."
Na amsa masa a sanyaye.
"Ina Gwammaja yanzu haka bayan na tashi aiki sai na biyo
zan duba Daughter daman ba ta jin da
ɗ
i da safen ma sai da Nene ta ce in na fito na zo na duba ta. To ina sauri ban biyo ba sai yanzu na kuma zo na iske ta ta na ta amai zan kaita asibiti a duba ta yanzu."
Cikin danne abin da ke taso min na ce" Subhanal
lah. Ku je mana a duba ta ka yi mata sannu Allah ya ba ta lafiya."
"Amin Sadiyata. Take care sai na dawo "
Da haka muka yi sallama ban bari na saka tunanin komai ba muka cigaba da azkar din mu bayan mun gama ni na
ɗ
ora da karatun Qur'ani Allah ya cire mi
n lamarin a cikin zuciyata. Kafin Yalla
ɓ
ai ya dawo na sake wanka na yi masa kwalliya sai tara da rabi ya shigo gidan muna tare da su Jidda a falo muna kallon Cartoon ya shigo gidan suka tashi suna masa oyoyo ya tarbe su ni ma na miƙe ina masa sannu da zuwa
ya amsa ya na kallona duk da bai furtamin ba amma na ga jin da
ɗ
i a fuakarsa da muryansa da ya ganni cikin kwalliyata kamar ko yaushe.
Ledan hannunshi na kar
ɓ
a zuwa kitchen na cire kayan marmari a leda na saka a frezer sauram kuma na wanke na yayyaka ma
na a Filet na kawo falon ya na zaune tare da su ya na yi musu hira.
"Ya mai jikin?
Na fa
ɗ
a ina zaman gefen jidda, min jera da shi ya na gefen Jidda Baby kuma na kan jikin shi.
"Ta ji sauƙi. Ulcer an saka mata drip da mganguna."
"Ash. An ba ta g
ado ne?
Na fa
ɗ
a ina kallonshi sai ya kalleni kafin ya ce" No mun dawo gida. Sun ce dai ta riƙa cin abinci ta shan mganuna nan da sati
ɗ
aya sai ta koma ta ga likita."
"Allah ya ba ta lafiya."
Ya amsa da Amin Baby sarkin mgana ta fara tambatyan waye b
a lafiya?
Shi kuma sai ya ce musu Anty Gimbiya ce da ya ke yaran suna son ta daga Jidda har Baby suka fara ma sa magiyan gobe ya kai su suke su duba ta sai ya fara cewa akwai makaranta su bari weekend su sai suje.
Ina gefe na ce" Ya yi nisa. Ko da dadda
re gobe haka Yalla
ɓ
ai?
Na fa
ɗ
a ina kallon shi, sai na ga ya kalleni kafin ya ce" To shike nan sai mu je
ɗ
in."
Suna jin haka suka fara murna. Nan muka bar su da shan su kankana ni da shi muka shiga ciki sai da ya yi wanka sannan na ha
ɗ
a masa tea na kawo
masa abinci tare muka ci tunda ni daman ban ci ba tuni su Jidda suna
ɗ
aki sun kwanta muna ci muna
ɗ
an ta
ɓ
a hira ya ce min jibi Jumma'a zai shiga Kaduna domin ya duba aikin nan na ce Allah ya nuna mana.
Bayan mun gama ya ta ya ni muka kwashe komai zuwa k
itchen, muka kakkashe hasken
ɗ
akunan da falo sannan muka koma
ɗ
aki muka yi shirin kwanciya yau dai ban hana shi kaina ba na saki jiki mun farantama juna, muna riƙe da juna cikin yanayi na ma'aurata sai wayarsa ta yi ƙara alamun shigar saƙo sai bayan mun na
tsa har ma mun yi wankan tsarki ya duba ashe cikon ku
ɗ
in aikin da ya yi na gina tiolets da wasu azuzuwaa makaranttun gwammatin kano na tuntuni n a ka turo masa.
Sai ya kamani ya rumgumeni ya na fa
ɗ
a mini. Sai na riƙe shi nima ina mai ta ya sa farinciki.
A zahirin gaskiya ku
ɗ
in nan ba su iya zuwa lokacin da ya dace ba. a can baya ne na yi zumu
ɗ
in zuwansu amma yanzu sai na ji ba na musu zumu
ɗ
i ko na so ko ban so wannan ku
ɗ
in da su za a yi shirye shiryen tariyan Gimbiya. Ana nufin kishiyar da za a kawo min
wataƙila a nan wataƙila a wani gidan na dabam.
*Janafty*
*TKG*
06.
FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nige
ria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622
Yalla
ɓ
ai fa miliyoyi sun dira a cikin account
ɗ
in sa na banki ba zama. Tun safe ya fita ya ma riga yara fita saboda sauri, bayan kuma tun asuban fari ya fara wa
ye waye da mutane bakinsa ya kasa shuru. Ni fa tun a farkon auran mu tun ina mamakin halin Yalla
ɓ
ai har ya zame min jiki, in ya yi wani abin na daina ganin sa a sabo a wajena.
Tun da na san shi, shi ne mutun ƙwara
ɗ
ayan da zan ce na sani mai bayyana ya sa
mu ku
ɗ
i a duniya. Kowa sai ya sani daman kuma tun kafin ku
ɗ
i su zo zai ta yi ma jama'a alƙwari da cewa in an biya shi ku
ɗ
in aikin sa na kaza zai baka kaza, a farkon auranmu na ga lamarin na shi wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara, tu ina yi masa mga
na har na gaji na kama kaina domin na tabbatar da halin shi ne, ba zai iya dainawa ba.
Ni dai kafin ya fita sai da na yi masa maganar kar ya je ya yi ta facaka da kuda
ɗ
en nan ya rage sauran basukan mutane da suke kansa. Sai ya ce min zai rage daman na
Kawu Abba ne mai yawa zai biya shi sai na Tariq da ya kar
ɓ
a a wannan aikin na kaduna amma shi ba zai biya shi sai an biya shi na kadunan. Sai yaran shi da zai cika ma ku
ɗ
in aikin da suke yi rabi ya ba su, wasu ma bai ba su komai ba saboda ba kuda
ɗ
e a hann
un shi. Ya
fita da cewa office zai je amma tunda ya na da ku
ɗ
i sai in da mansa kuma ya ƙare ya bar ni ni ka
ɗ
ai a gida tun da su Jidda sun tafi makaranta suma.
Bayan fitan shi ba da
ɗ
ewa ya kira wayata ya na fa
ɗ
a min na rubuta list
ɗ
in duk abin da muke bu
ƙ
ata a gida na kayan abinci da sauran kayan amfanin mu ni da yara, sai na amsa masa da to, bayan mun gama wayar na tashi na shiga Kitchen ina duba abin da babu. Sai da na gama gani sannan na koma
ɗ
aki na rubuta a cikin wayata kayan amfanin mu kuma ni da ya
ra sabulun wanka ne na su, sai nawa wanda na siya wajen Lame ya kawo gangara. Sai su man wanke kai da maclean sai izel da klin muna da komai su ka
ɗ
ai ne suka yi ƙasa, sannan a raina na ce zan tuna masa da ku
ɗ
in makarantar yara domin wannan term
ɗ
in ne ƙars
he, in suka yi hutu suka koma akwai biyan ku
ɗ
in makaranta. Test ma Jidda ta ce min suke yi sun kusa hutun kirisimet na ƙarshen shekara.
Allah ya sa ma ya yi dubara lokacin da zai biya a second term ya biya gaba
ɗ
aya na season
ɗ
in.
Sanin Saude na makaran
ta sai in ta dawo ne in ta na da lokaci ma ta ke zuwa. A ranakun makaranta zuwanta ya koma sau hu
ɗ
u ne kawai a sati. Alhamis da jumma'a sai weekend na san yau za ta zo amma sai wajen biyu na rana, kuma ga shi Hauwa ta ce min za ta zo sai ban kwanta ba na m
iƙe na yi aikin gidana da kaina ban bari wani tunani ya ziyarce ni ba, karatun Qur'ani na saka a wayata ina ta ji, kuma ina bi da bakina ko kafin goma na safe na gama komai gidana sai kamshin turaren wuta ya ke yi, haraban gidan ne na ga ya yi datti sai na
bar shi da cewa in Saude ta zo sai ta share ta gyara wajen. Wanka na yi na shirya cikin wani leshi na mai sauƙakƙan nauyi, ina falon yara ina hutawa wayata na hannuna ina danne danne, yanzu sai na yini na kwana ban bu
ɗ
e data ba, ba na so na ga ma abin da
zai
ɓ
ata min rai ko ya
ɗ
aga min hankali shi ya sa na kama kaina.
Ina nan zaune, ba kallo na ke yi ba saboda sun
ɗ
auke wuta yau tun safe ba su dawo da shi ba. Ina ta mamakin ma rashin dawo da shin da ba su yi ba, saboda in suka
ɗ
auke in ta da
ɗ
e ba su da
wo dashi ba awa
ɗ
aya amma yau sama da awanni uku ba wutar. Karatun Qur'anin na cigaba ji a wayata ina kuma zaune na kishigi
ɗ
a a saman kujera a sannu sannu ina bin karatun, idanuwana a lumshe suke sai na ji karatun ya tsaya wayar ta fara vibration alamun an
a kirana, a kasalance na
ɗ
an tashi daga saman kujeran da na ke zaune, ina mai bu
ɗ
e idanuwana da suka yi min nauyi, domin sai na ji kamar barci barci ma na ke ji, hannu na saka na jawo wayar ina duba mai kiran nawa saboda kafin na
ɗ
auki wayar kiran ya katse
.
"Yaya Aina ce."
Da sauri na bi bayan kiran. Bayan ta
ɗ
auka mun gaisa ta na min tsiya da cewa"Uwargida ran gida. Ko kina barci ne?
Ina
ɗ
an mirmishi kamar ta na ganina kafin na ce"Barci kuma Ya Aina? Na tashi tun safe."
Yara ta tambaya na ce suna m
akaranta, Yalla
ɓ
ai kuma da za ta tambaye shi sai da ta yi dariya kafin ta ce" Ina Yalla
ɓ
ai Ango? Dariya na saka mai sauti kafin na ce" Ya na nan lafiya. Sai