Showing 21001 words to 24000 words out of 159340 words
da Amin Amin shuru na wani lokaci saboda ya ji falon shuru sai ya
ɗ
an waiwaya ya kalli
ɗ
akin da Gimbiya ta ke kwana ya gansa a kulle sannan ba alamun ta na ciki sai ya juya ya na kallon Nene lokaci
ɗ
aya y
a na fa
ɗ
in" Ke ka
ɗ
ai ce Nene? Daugther ta fita ne?
"E. Ta fita yanzu ba da
ɗ
ewa an kirata daga wajen aikinta."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Ina hanyan zuwa nan ma na kira wayarta ba ta shiga. Ni fa hankalina ya tashi da kiran ki Nene na
ɗ
auka ko ji
kin ne ya tashi."
Sai da ta yi mirmishi kafin ta ce" Ko
ɗ
aya lafiyata ƙalau Tafida."
Sai kuma ta yi shuru shi kuma sai ya bi ta da Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon kwana Nene."
Ta amsa masa da Amin Allah ya sa.
Shuru ya sake biyo baya na tsawon
mintina biyar. Ya na kallon Nene ya ji ko za ta ce wani abu. Amma ya ga ta yi shuru kuma ya san tun da ta kira shi akwai mgana.
Sai ya gyara zama shi ya kauda shurun kafin ya ce" Nene akwai damuwa ne? Ko wani abu kike so na yi miki?
Sai ta kalleshi, ko a
cikin ƴaƴanta Yusufa na dabam ne. Shi ne ya
ɗ
ibo kusan hallayar marigayi mahaifinsu. Shi ne kawai in ta yi shuru ya ke fahimtar ta na buƙatar wani abu amma ta na jin nauyin tambaya.
"Nene ki yi mgana mana. Komai kike so nan duniya zan iya miki shi ko da
ya gagareni zan nemi taimako a wajen wanda zai iya yi mini alfarma domin na faranta miki."
Ya fa
ɗ
a ya na matsowa kusa da ita. Sai ta
ɗ
ago ta kalleshi kafin ya ji ta saka hannayenta duka biyu ta kama duka hannayensa lokaci
ɗ
aya ta na fa
ɗ
in" Alfarma na k
e so na roƙa a wajen ka Tafida. Amma kar ka ji a ranka ko na tursasa ka ne, ina so komai da zai faru ya zama da amincewarka da yardan ka ne."
Cikin mamaki ya kalleta kafin ya ƙara jimƙe hannayenta ya na fa
ɗ
in" Nene ni ne fa Tafida! Umarni kawai za ki ba
ni na cika miki shi ai tsakanin mu ba alfarma Nene."
"Akwai Tafida. Akwai alfarma a tsakanin uwa da
ɗ
anta. Nima yau albarkacin wannan alfarman na ke so na ci a wajen ka Tafida."
Da sauri ya ce" Fa
ɗ
i ko miye Nene, ni ko zan cika mganarki da sunan umarni
ba alfarma ba."
Ta na mai kallonshi hannuwansu sarƙe cikin na juna ta ce" Tafida ka san a shekarun baya da ka kawo mganar auran Sadiya na goya maka baya a lokacin da ƴan'uwanka suka ƙi fahimtar ka ko?
Sai ya gya
ɗ
a mata kai amma gabanshi na fa
ɗ
uwa domin
bai gane in da mganar Nene zai dosa yanzu kuma ba.
"Har ga Allah tun ganin farko da na fara yi ma Sadiya a cikin falon nan nawa a shekarun baya na yaba da hankalinta na kuma san ka yi dacen samun mata tagari. Sadiya ba ta gazamin ba kuma ba ta yi min
komai ba wallahi sai ma tarin alherinta zuwa gareni."
Ta
ɗ
an dakata tana kallonshi kuma shi har ga Allah ya ƙosa ya ji in da mganganun Nene suka dosa.
Ajiyar zuciya Nene ta sauke kafin ta ce" Tun muna ƴan mata ni da Hajiyar Tafida muka yi alƙwarin da
fatan in mun yi aure mun hayayyafa za mu yi ha
ɗ
in auran zumunci a tsakanin y'aƴaƴyanmu domin ƙara karfafa zumuncin da ke tsakanimu, sai ga shi kuma mun auri mazaje abokai, sai amintan mu ya yi girman da mutane ma suna kwatance damu. Tafida tun da na haife
ka na ji a raina kai ne za ka iya cika mini wannan alƙwarin. Zaman ka a Rano a gidansu Gimbiya da shaƙuwar da ke tsakaninku sai muka sakankance za ku dai dai ta kanku har burin mu ya cika kwatsam sai ka zo mini da mganar Sadiya."
Zuwa yanzu kam jikinsa
ya yi sanyi shi ai ba yaro ba ne tuni ya fara fahimtar in da maganganun Nene suka dosa amma bai katse ta ba, gwara ya ji ta har ƙarshe domin ya san a ina za ta dire mganganunta.
Ita kuma kallon shi ta ke yi ta na ƙara nazarta yanayin sa. Amma ko a fuska b
ai nuna mata wata alama da za ta ce mganganunta ba sa yi masa da
ɗ
i ba. Sai kawai ta cigaba da fa
ɗ
in.
"Na so ka da Saudatu Tafida kamar yadda Hajiya itama ta so hakan sosai wanda har sai da ta furta mini tun a wancan lokacin. Amma saboda kai ka kawo Sadi
ya kuma ka nuna ita kake so a lokacin in na ce ka bari za ka bari kuma za ka yi min biyayya ka auri Gimbiya sai dai na yi tunanin na zama azzaluman uwa tunda na hana ka abin da kake so domin ni na wa cikar burin shi ya sa ban ta
ɓ
a yi maka mganar ba na taka
ma su Bahijja burki a kan ƙin auran ka na ce su yi maka fatan alheri, domin ko suma a lokacin da Gimbiyar suke hangenka. Amma suka danne saboda na ce su bar mganar matan mutum ai kabarinsa. A lokacin da mganar auranka ya samu Hajiya ko da ba ta furta ba,
ni na san ba ta ji da
ɗ
i ba amma sai ta yi fatan alheri a gare ku gaba
ɗ
aya.
Na yi ta zura ido na ga ko za ka fahimci Gimbiya na sonka amma sai na ga ba ka nuna wata alama ba, wataƙila ka fahimta amma sai ba ka ba ma hakan muhimmanci ba. Gimbiya ta yi ta
zaman jiranka ta na ture manemanta a yaƙininta cewa wata rana za ka iya fahimtar irin ƙaunar da ta ke yi maka. Amma sai ka kasa fahimtar ta, duk shekarun da ta
ɓ
ata ba ta yi aure ba ta kasa fidda yaƙini be a kanka ne, sai daga baya da ta fahimci ka fahimc
eta kawai dai ra'ayi ne a kanta ba ka dashi sai iyayenta da ƴan'uwanta suka yi mata fa
ɗ
a har ta fidda wannam mijin ta aura sai ga shi cikin hukuncin Allah zaman bai yi tsawo ba ya rasu ya barta. Ta dawo gida ta yi idda ta gama gashi yanzu ta dawo nan waje
na da zama."
Sai Nene ta dakata ta na sauke numfashi har kuma lokacin Hannayenta na hannun Tafida ya damƙe sanyin da jikinsa ya yi ya sa gaba
ɗ
aya ya kasa motsi ya na ji zufan hannun shi na jiƙa tafukan hannayen Nene da ke cikin na shi.
"Yusufa."
Y
usufu wani suna ne da in Nene ta kira shi dashi ya san mgana ce mai muhimmanci. Ba ta kiran sunan shi sai dai ta kira shi da Tafida.
Shi ya sa ya na jin haka ya
ɗ
ago da kansa ya na kallonta cikin dakiya ya amsa mata.
"Na'am Nene"
Ya amsa mata ya na tatt
aro dukan jarumtarsa a gabanta amma a ƙasan zuciyarsa ya yi rauni. Domin hasashen sa bai ta
ɓ
a kawo sa ga wannan bingiren da Nene ta kawo shi yanzu ba.
"Ka ta
ɓ
a fahimtar har yanzu Gimbiya ba ta daina sonka ba? Ko ka ta
ɓ
a lura da cewa har yanzu ba ta cire
tsammani da yaƙini da cewa za ka iya zama na ta ba?
Tambayoyin Nene sun yi masa tsauri da ya kasa cewa komai.. Sannan gashi ta ƙura masa ido ta na jiran amsarsa. In ya ce bai ta
ɓ
a sanin Gimbiya na son shi ba ya yi ƙarya domin tun tana kunya har ta fito
ma da alamomin da suke bayyana cewa ta na son shi, ba ma shi ba har mutanen da ke kusa da su sun fahimci irin soyayya da Gimbiya ta ke yi masa. Da farko shi ma ya
ɗ
auka ya na sonta ne sai da ya ha
ɗ
u da Sadiya anan ne ya fahimci ba so ba ne shakuwa ce kawa
i da ha
ɗ
uwar jini. Sadiya ita ya ji ya na yi ma soyayyar da Ubangiji ya hallita tsakanin mace da namiji. Amma bai ta
ɓ
a ƙin Gimbiya ba, sannan har gobe ta na daga cikin foverite
ɗ
in mutane a wajensa amma bai ta
ɓ
a tunanin ya saka tunanin auran ta a ran shi b
a, ba kuma domin ba zai iya auranta na ta ba sai domin tunanin hakan bai ta
ɓ
a shiga ƙwaƙwalwarsa ba ne.
"Shurun ka na nufin amsarka da E Tafida"
Nene ta katse masa tunani, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Nene ba ni ba duk wanda ke tare da mu zai
iya shaida akwai kyakyawan alaqa tsakanina da Gimbiya. Amma."
Hannu ya ga Nene ta
ɗ
aga mai tana kallonshi kafin ta je fa masa wata tambayar da ta ƙara rikita shi.
"Kana son Saudatu!?
"Za ka iya zaman aure da ita?
Sai ya kasa mgana bakinsa na raw
a ya na so ya yi mgana ya kasa. Tambayoyin suna da girma da tsauri in aka ce ya amsa su nan take kamar ana so ya yi gaggawa ne. A bari ya samu kamar sati
ɗ
aya daga shi sai zuciyarsa ya gani ko za ta iya amsar tambayoyin Nene amma ina Nene ba ta bashi wanna
n damar ba yana ƙokarin mgana ta ƙara tare shi da fa
ɗ
in" Ba buƙatar dogon lokaci ba ne Tafida ka fa
ɗ
amin shin za ka iya auran Saudatu kuma ka yi zaman aure da ita?
"E. Amma Nene.."
"Ka gama min komai Tafida. Na gode da afarman ka. Na gode da biyyarka
. Na gode da kyautatawarka a gareni. Allah ya saka maka da gidan aljannah. Allah ya shirya maka zuru'a ya yi ma rayuwarka da duk abin da ka saka hannu a kai albarka Na gode."
Nene ta fa
ɗ
a ta na zare hannayenta daga cikin na shi sai kuma ta fara sharan ƙw
alla ganin haka sai bakin shi ya mutu Nene na share hawaye ta na ta saka masa albarka da addu'o'in gamawa da duniya lafiya su suka ha
ɗ
u suka ƙara kashe masa baki da zuciya gaba
ɗ
aya.
Ya
ɗ
auka iya mamakin da Nene za ta gama bashi kenan ashe ba shike nan b
a. Umarni ta bashi da cewa ya kira mata Zuwaira da Maimuna da Bahijja suma
su taho gida yanzu tana son mgana da su. Ya
ɗ
auka dai kan mganar da suka gama shi ya ke kiran su da wayarsa amma sai Nene ta kar
ɓ
a ta yi musu mgana Zuwaira(Mimisco) ta fara zuwa tun
da ita ce lokacin da aka kira ta ta na makaranta ta ce ma za su yi meeting ne amma ba ri ta saka a
ɗ
aga zuwa anjuma sai ta taho. Sauran kuma suka ce yanzu za su shirya su taho suma dai hankalinsu ya tashi sun
ɗ
auka jikin Nene ne sai da ta basu tabbacin ka
da su damu ta na lafiya sannan hankalinsu ya kwanta suka ce ga su nan zuwa.
Lokacin da Mimisco ta iso gidan ta
ɗ
an yi mamakin ganin Tafida zaune, amma sai ba ta yi mgana ba ƙila dai ya shigo gidan ne amma dai tana tunanin da akwai dalili acikin kiran na
Nene.
Kalaman da Nene ta furta ma Mimisco ne ya sa
ɗ
an sauran gudun jinin da ke tafiya a jikin Tafida ya tsaya cak!
"Zuwaira Rano na ke so mu je a yau yau
ɗ
in nan."
"Rano kuma Nene! A yau kuma?
Ta fa
ɗ
a ta na kallon Tafida shima ita ya ke kallo
amma ya kasa mgana sai ta maida hankalinta kan Nene ta na fa
ɗ
in" To wani abu ya faru ne a can Nene?
"Ba abin da ya faru sai Alheri. Aure na ke so yau a
ɗ
aura a tsakanin Tafida da Saudatu."
Shi dai sai da ya ji yam! tsigogin jikinsa sun tashi. Numfashi
ya yi sama sannan ya jawo shi ya dawo. Mimisco ko ido ta zaro ta na kallon Nene tana kuma kallon Tafida kafin ta ce"Wata Saudatun kuma Nene? Domin ita sai ta ji ma ta manta wacece Saudatun.
"Gimbiya ta mu."..
"Topha yau shi Tafidan da kan shi ya ce
ya na son ita Gimbiyan! Sannan ya ce a yau ya ke son a
ɗ
aura auran?
Mimisco ta fa
ɗ
a cikin ƙarin mamaki, ta na kuma mai kallon Tafida da ya kasa mgana. Nene ce ta yi mata bayanin komai ta ƙara da cewa" Tunda har ya ce zai iya zaman aure da ita me za mu j
ira Zuwaira! A
ɗ
aura kawai daga baya sai a yi mganar tariyan"
Mimisco ta kasa mgana Tafida ta kalla sai taga itama ya kalleta yanayinsa kawai ta kalla ta fahimci a bazata mganar Nene ta zo masa in kiya ya yi mata ido itama sai ta yi masa alamun ya yi mgan
a mana.
Sai gani suka yi Nene ta miƙe tana fa
ɗ
in" Bari na kira Hajiya na fa
ɗ
a mata muna tafe."
Ta fa
ɗ
a cikin murna wanda har ya bayyana a muryanta.
Mimisco ta yi saurin cewa"Nene dawo ki zauna."
Sai ta juyo ta na kallonsu kafin ta dawo ta zauna ta
na fa
ɗ
in" Me ya faru ne?
Mimisco ta kalli Tafida kafin ta ce" Ka yi mgana da Sadiya ne?
Sai a lokacin ma ya fahimci ƙura ne turƙe a gaban shi bai sani ba, sai ya girgiza kansa kafin ya ce" Yanzu yanzu Nene ta yi min mganar kuma a yanzun ta yanke wannan
hukuncin."
Sai Mimicso ta kalli Nene kafin ta ce" Nene ki yi hakuri ki ba shi dama ya je gida ya yi mgana da matarsa zuwa gobe sai a yi yarda kike so."
Amma Nene ta ce ba ta amince ba, ya kira Sadiya a waya ya fa
ɗ
a mata kuma ai yana da sauran lokaci.
"Waya kuma Nene? Gaskiya bai kyautu ya yi mata waya ba. Sai dai in haka kike so a je a
ɗ
aura
ɗ
in daga baya sai ya yi ma Sadiya bayani."
Nene ta ce hakan za a yi kuma ta san Sadiya za ta fahimcesa. Ba yadda ya iya har Mimisco ba ta so gaggawan ba amma ba
yarda ta iya Nene ta dake har ta Kira Hajiya ta ce suna nan tafe, Bahijja ta fara zuwa daga baya sai Maimuna suna jin ƙudurin Nene suka ha
ɗ
a baki suna ranga
ɗ
a gu
ɗ
a su lamarin ya yi musu da
ɗ
i matuka sannan Nene ta biya su.
Da dai Tafida ya ga da gaske Nene
ta ke sai ya roƙi su Bahijja da don Allah su yi shuru da wannan mganar kar Sadiya ta ji. Ya na so ne in ma za ta fara ji sai daga bakinsa har suka
ɗ
an samu cacan baki da Bahijja domin ta ce bai isa ya hana su nuna farinciki ba.
Sai da Mimisco ta shiga
tsakani ta ce ya na da gaskiya. Za su tarwatsa masa gida ne ai ya na da gaskiya kuma mganar aure ai ba mganar wasa ba ne. Da haka dai suka yi alƙwarin ba za su fidda maganar ba. A lokacin ko awa
ɗ
aya ba su ƙara a Kano ba suka
ɗ
au hanyar Rano da shi da Nene
da Mimisco da Bahijja Maimuna ta koma gidanta.
Suna kuma zuwa Nene ta isar da kudurinta sai da Hajiya ta tashi ta rumgumeta ta na mai nuna farincikinta a gidan Tafidan Rano ƙanin baban Gimbiya aka
ɗ
aura auren Yusuf da Saudatu kan Sadaki naira dubu 100k.
Kuma ba a
ɗ
aura ba sai da shi Waliyin nata ya kira ta a waya ya tambayi izininta tunda bazawara ce kuma addini ya ba ta wannan damar ita kanta a ba za ta ta ji mganar wai ta na son Yusuf? Domin ga waliyanshi sun iso domin nema masa auranta. Da rawan jiki
da na zuciya ta amince, a cikin office
ɗ
in ta bayan Anty Bahijja ta kira ta ta ce an
ɗ
aura auran ta da Tafida sai da ta fa
ɗ
i ta yi sujjudar shukur ta na hawayen farinciki atleast dai yau burinta ya cika tabbas kar bawa ya cire tsammani duk abin da ya ke ra
bon ka ne ko ya hau sama sai ya fa
ɗ
o a kanka. Alhamdulillah.
Bangaren Tafida Kawu Sa'adu ne da su Abba suka kar
ɓ
a masa auran Sadakin kuma Nene ce ta biya da ku
ɗ
inta saboda yadda ta ke son Tafida da Saudatu. Bayan an gama
ɗ
aura aure kuma acan gidan Hajiy
a aka fara
ɗ
ora girki na sadaka, bakinta har kunne ta kira sauran Ƴayanta a waya duk ta sanar da su kafin ka ce kwabo labari ya zaga Rano da kewayenta. Abba shi kan shi ya yi mamakin auran nan cikin gaggawa da Mimisco ya yi mgana ita ce ke yi masa bayanin
yadda lamarin ya fara. Amma Yusuf bai iya ba, domin lamarin kamar a mafarki ya ke gani. Duk roƙon da ya yi musu sai da Bahijja ta
ɗ
ora a status a tunaninta ta cire Sadiya ko ta