Showing 105001 words to 108000 words out of 159340 words

Chapter 36 - Turken Gida Complete

/>
.

An cika

ɗ

akin ana ta hira shi ne ma muka ji Anty Bahijja na waya da Hajiyar Tafida ana mganar wanda za a samo daga rano zai zauna tare da Gimbiya amma kamar ba a samu ba kowa na da iyalai da abin yi, bayan ta gama wayar ta kalli Anty Maimuna ta na fa

ɗ

in" Kin ji ita kanta Baaba Asma'un da na hango ba ta da lafiya.'

"Topha. Ba dai a samu mai zuwa ya zauna da itan ba kenan?

"Ba a samu ba kam."

"To ta koma wajen Nene kawai ta zauna ba shike nan ba."

Anty Bahijja ta ce" Nima haka na ce da farko

to kin san halin Tafida da taurin kai ya ce wai Nene na fama da kanta itama. Kuma na kawo hujjan ga su Maman farko ga iya ai duk za su kula da ita ya ce a'a a samo wacce za ta zauna da ita."

"Wallahi kuwa. To da ya ce bai yarda ba yanzu da ba a samu mai

zaman ba ya zai yi?

"Shi dai ya sani. Abin haushin ma ita Mimisco ta goya masa baya. Shi fa shegen nuna iko ne da shi."

Ni dai ina gefe in jin su ban tofa ba daga karshe ma ni da Hauwa muka fara tafiya salla tun da ana ta kiran sallar azahar Munnira

ba ta yi ta na hutu shi ya sa ba ta biyo mu ba. Bayan ma mun idar da sallar mun zauna a wajen cikin asibitin muna ta hira da Hauwa. Ta na gaya min ba in da labarin cikin Gimbiya bai za ga ba na ce ai ya za ga tun da su Anty Bahijja na raye.

"Ji fa suke

yi kamar Tafida bai ta

ɓ

a haihuwa ba sai yanzu."

Ina murmishin takaici kafin na ce" Bai ta

ɓ

a ba mana. Ni ai bare ce saboda haka ƴaƴana ma bare ne. Ita kuma ta su ce haka ma ƴaƴan da za ta haifa ma kin ga ai na su ne."

Hauwa ta rike baki kafin ta ce" La

lle kam"

Ban ƙara mgana ba amma ina ƙokarin danne wani abu dake ta so min a ƙasan zuciyata.

Bayan mun koma

ɗ

akin har dai lokacin Anty Bahijja na ta buge bugen waya amma ba a dace ba. To kowa na da abin yi wata mata ce za ta yarda a

ɗ

aukota a zaunar da

ita waje

ɗ

aya sama da wata

ɗ

aya tun da na ji Halima na fa

ɗ

in likita ya ce bedrest za ta yi na sati biyar ko botiki ba a yarda ta

ɗ

auka ba ai neman mai zaman akwai wahala Yalla

ɓ

ai kuma ba mace ba ne ballatana su ce ya zauna ya kula da ita dole dai ƙanwar na

ƙ

i wata macen za su nema. Har muka baro asibitin gabda mangariba ba a dace ba ina jin Anty Maimuna har Nene ta kira ta na fa

ɗ

a mata ba a samu mai zama ba kowa suka kira sai ya ce ga uzurin shi kila Nenen ta ce a dawo da Gimbiyar wajenta sai na ji ta na cew

a.

"To Nene Tafidan ya hana. Sai dai ki yi masa mgana ƙila ke ya saurare ki."

Daga karshe na ji ta na cewa to shikenan.

Mun rabu da su Hauwa a bakin asibiti na hau adaidaita zuwa gida ban san abin da ya faru ba, can bayan isha'i Yalla

ɓ

ai ya na dawow

a wanka kawai ya yi ko abinci bai ci ya ce mu je

ɗ

aki zai yi magana da ni, ina falo ne ma ina koya ma Baby aikin da aka ba ta a makaranta da na ce ma ya bari mu gani sai gani na yi ya ƙariso ya kama hannuna ya mikar da ni tsaye ya kuma nufi har korido ya n

a fa

ɗ

in.

"Ƙarisa mata aikin Jidda."

"To Abba."

Ta fa

ɗ

a cikin sanyin ta damam ta na gefe itama ta na yin nata.

"Mene ne ya faru Yalla

ɓ

ai?

Na fa

ɗ

a ina biye da shi a baya bai direni ko'ina ba sai da muka shiga cikin bedroom

ɗ

in mu, kan gado ya

zaunar da ni tun da na ga ya jawo stool

ɗ

in madubi ya zauna na san akwai mgana ko wani abu ya faru.

"Mene ne ya faru Yalla

ɓ

ai? Ka fara ba ni tsoro."

Na fa

ɗ

a ina kallon shi ganin kamar ba ya cikin natsuwarsa.

"Sadiya."

"Na'am me ya faru?

Na a

msa shi a gaggauce sai ya sauke ajiyar zuciya ya riƙe hannayena duka biyu tun da na ga haka jikina ya ba ni cutavta Yalla

ɓ

ai zai yi tun da na ga wannan ladabin na shi.

"Me kake so?

Na katse mishi tunani sai ya

ɗ

ago yana kallona kafin ya ce" Alfarma z

an ƙara roƙa a wajen ki."

"Ina jin ka"

"Kin san ina sonki ko Sadiya ta?

"Na san wannan ka tafi kai tsaye? Me kake son na yi maka?

"Izinin ki na ke nema."

"Izini kuma? Izinin me?

Na fa

ɗ

a cikin ƙanƙance ido ina kallon Yalla

ɓ

ai.

"Ina so Daughte

t ta dawo gidan nan da zama"

Sai na zaro ido ina kallon shi cikin mamakin kalaman shi.

"Nufina na

ɗ

an lokaci saboda kin san dai na fa

ɗ

a miki dokar likita ko? To ba a samu wacce za ta je gidanta domin ta zauna da ita ba. An ce ta koma wajen Nene ni ku

ma na ce a'a Nene ma ba ta da lafiya sai na yi tunanin duk duniya bayan iyayena ba ni da kamarki. Za ki kula da Daugther a gaban idona haka kuma za ki kulata da ita a bayan ido na shi ya sa na yanke shawaran za ta dawo nan gidan ta zauna tare damu har ta f

ita daga dokar likitoci."

Har ya gama mgana kallon shi na ke yi cikin mamaki. To yanzu kuma abin da ke shirin tunkaro ni kenab? Gimbiya a gidana? Ban ta

ɓ

a tunanin haka ba shi ya sa na zama kawai ina kallon Yalla

ɓ

ai na kasa mgana."

"Ki yi magana mana

Sadiya."

Ya fa

ɗ

a ya na matse hannayena cikin na shi.

"Me kake so na ce? Ka na so na ce a'a ne?

Na fa

ɗ

a ina kallon shi sai ya yi saurin girgiza kai kafin ya samu zarafin mgana na tare shi da cewa" Na ce a'a mutane su je su ce kai da gidan ka na han

a ka yin abin da kake so?

"Ba haka ba ne. Haƙƙin ki ne na sanar da ke. Kuma muhimmanci ki ne ya sa na ce ta zo gidan ki ta zauna tare damu."

Kallon shi kawai na ke yi na ma kasa mgana saboda mamaki.

"Aiki zan riƙa yi ma matarka Yalla

ɓ

ai?

"Aiki

kuma? Haba wani irin aiki kuma? Ko ni da na gina gidan nan da sunan ki na gina shi saboda haka duk wacce za ta zo ta zauna alfarman ki za ta ci. Ita Daugther rigar alfarman da kika yi min za ta shiga ciki amma in har kin ce a'a shike nan ba ni da zabi sai

ta koma Rano kawai."

"Ka san zan iya cewa a'a me ya sa ka kawo mini mganar?

"Na san ma ba za ki ce Aa

ɗ

in ba ne shi ya sa."

Shuru kawai na yi ban yi mgana ba, uhm ni fa namiji ya daina mamaki ya zo ya na yaudarata da mgana yanzu na ce ban yarda ba

magana ta fita a gari a ce na hana ta zama a gidan mijinta gida ba na uwata ba kuma ba na ubana ba. Gidan shi ne ya na da damar da ko kare ya kawo ya sauke ba zan yi magana ba. Abu

ɗ

aya ne ba zan

ɗ

auka cin zarafi da wulakanci. Sai na kalle shi na ga shima

ni ya ke kallo ya na jiran ya ji me zan ce.

"Shike nan bakomai ai gidan ka ne itama gidanta ne."

Na fa

ɗ

a ina danne wani abu daga ƙasan zuciya.

Rumgumeni ya yi daga zaunan ya na fa

ɗ

in" Na gode Abar ƙaunata"

Kallon shi kawai na yi ba tare da na yi m

asa mgana ba.

"Amma ina da mgana."

Sai ya

ɗ

ago ya na kallona ni kuma sai na gyara zama ina fa

ɗ

in" Ta zo ta zauna ban damu ko yau ko gobe ko sai ta shekara ko kuma anan

ɗ

in ma zata zauna gaba

ɗ

aya ba. Ai gidan ka ne itama tana da iko da shi saboda haka

ba ni da hurumin na ce wani abu akan haka, abu

ɗ

aya ne ba zan

ɗ

auka ba a zo har gidana a ce za a ci min mutumci, in hakan ya faru ba zan yi shuru ka san halina ba ni da hakuri matukar aka ta

ɓ

a min mutumcina."

"In sha Allahu ba abin da zai faru. Daughte

r tana girmamaki ina da tabbacin ba abin da zai faru."

"To wai kar ma ya farun ne na yi mgana ka ce na cika cewa an yi min kaza."

"Ba zai faru ba in sha Allahu."..

Ya fa

ɗ

a ya na min mirmishi. Hannuna na zare a na shi kafin na miƙe ina fa

ɗ

in" Wani

ɗ

aki za mu sauke ta?

"Wanda kika ce Madam"

Sai na kalle shi kafin na ce" Ko

ɗ

akin nan nawa na baƙi? Tun da kusa ne da namu."

"Ba matsala?

"Babu mana."

"To shike nan a yi haka

ɗ

in."

Sai na jinJina kai kafin na ce bari in na gama da yara sai na shi

ga na dan ƙara gyara

ɗ

akin

Sai ya riƙo hannuna na juyo ina kallon shi. Shima ya na kallona har ya na wani sauke ido.

"Na gode Abar ƙaunata"

"Yalla

ɓ

ai ni kuma yaushe na koma Abar ƙaunar ka kuma?

Ya na mirmishi ya miƙe ya rumgumeni ya na fa

ɗ

in" Tun

a ranar farko da na fara

ɗ

ora idanuwana a kan na san cewa tabbas ke

ɗ

in Abar ƙaunar Yusuf ne."

Ni dai ina ta dariyan yaudaran Yalla

ɓ

ai saboda na yarda da zaman matarshi a gidana shi ne zai zaunar da ni ya na min ruwan kalamai. Kai jama' a Maza na abin da

suke so ranar kusan raba dare muka yi muna hira da Yalla

ɓ

ai da na yi magana jikinsa na rawa saboda wata macen sai na ke tunanin in da na yi boren ban yarda ba ya na gaba gaba wajen ci min mutumci ko ba a yau

ɗ

in nan ba nan gaba sai ya yi min gori kuma dan

gin sa su ji labari su tsine min.

Da safe ya ke fa

ɗ

a min sun yi waya da Gimbiyar an yi ma sallama saboda haka yanzu daga nan asibitin zai je ya

ɗ

auko su. Na ce to ni kuma zan

ɗ

an kara gyara

ɗ

akin. Wanka ya yi muka karya tare su Jidda sun tafi Tahfeez da

wuri tun da jiya ba su je ba. Ɗan gyara gidan na yi na saka turare daman

ɗ

akin da Gimbiyar za ta zauna tun jiya na gama gyara shi daman kuma a gyare ya ke sai dai ƙura.

Karfe sha

ɗ

aya da wani abu na safe na ji ƙaran bu

ɗ

e get da shigowar mota. Ban fita

ba domin ba zan iya zuwa tarban kishiya ba ai na yi iya abin da zan iya yi. Ina falon yara suka shigo Gimbiya ne da Anty Bahijjja sai Maman farko Yalla

ɓ

ai daga baya ya shigo

ɗ

auke da kayan su. Na kar

ɓ

e su faram faram kamar yadda na saba na yi musu kuma jag

ora har

ɗ

akin da zata sauka Maman farko na ta yi min sannu da godiya ina amsawa na je na kawo musu ruwa suka ce sun ƙoshi fita na yi na ba su waje Yalla

ɓ

ai bai zauna ba ya fice tare da Maman farko da zai maida ta gida ita dai na rakata har haraba sai bayan

tafiyar su ne na dawo cikin gida na yi zamana a falo can ba da

ɗ

ewa sai ga Anty Bahijja ta fito ta kalleni daga sama har ƙasa kafin ta ce.

"Wai ashe kin ji haushin hana Gimbiya shan faten nan da kika yo mata ranar a asibiti Sadiya ?

Na kalleta ban yi

mata mgana ba sai ta cigaba da fa

ɗ

in" Ni ban san kin ji haushi ni fa har a zuciyata ba da wata munafa na yi ba kawai sai ga shi kin turo Tafida ya zo ya na min fa

ɗ

a tun da an taba uwarsa ba."

"Ni ban turo shi ba."

Na fa

ɗ

a ina kauda kaina gefe sai ta

basar kafin ta ce" Koma da mene ne ni ban ce haka domin na ci zarafin ki. gwara ma ki daina jin haushina."

Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba to me zan ce? In yi magana ta ce na zageta ko na yo mata rashin kunya..

Ta gama zagayen gidan ta koma ciki b

a da

ɗ

ewa sai ga Naja'atu ta zo kamar kayan Gimbiyar ta je ta kwaso mata. Wajen uku na rana suka tafi lokacin har na gama abinci amma ba su tsaya sun ci ba

Anty Bahijja har ta na ƙara jadaddamin likita ya ce ko botiki kar Gimbiya ta

ɗ

aga ta rika cin wake d

a abinci mai allayahu, hutu kawai ta ke bukata kuma shi za ta yi, na ji tsoron Allah tun da dai Tafida ya na ce sai an kawo ta gidana na kula da ita sosai

Mamaki bar bar ni na yi mgana ba har suka fice daga gidan. Na saki a tsaki a fili na ce" Tun da ni

na yi mata cikin ba.' ko kuma ni mahaifata ba ta ta

ɓ

a

ɗ

aukan cikin ba."

Daman ni na san za a rina an saci zanin mahaukaciya ko ita Gimbiya ba ta munana min ba irin su Anty Bahijja yan kanzagi ai za su munana min.

Zuciyata na kai nesa na riƙa shiga ina d

uba Gimbiya ba saboda Anty Bahijja ba sai saboda Allah da kuma Yalla

ɓ

ai. Na samu bayan ta ci abiinci ta sha mgani sai ta kwanta barci sai bayan la'asar ta tashi ta yi salla.

Saboda ita na yi mana Tuwon semo da miyar kuka mai naman rago tun da ta ce min

ta na so. Da yamma da su Jidda suka dawo makaranta ya sa sai ga ta fito falo ma muna ta hira da ita. Sai dare Yalla

ɓ

ai ya dawo yadda ya ganmu tare ya sa bakin sa ya ƙi rufuwa sai washe haƙora ya ke yi ina lura da shi. Kamar magungunanta akwai na barci ta n

a sha ta ce min za ta shiga ta kwanta sai na ce ma Yalla

ɓ

ai ya je wajenta ya kwana saboda makirci har ya na ce min.

"Ba matsala."

"Babu."

Na amsa masa a takaice saboda ni nasan can ya ke son ya ce zai kwana kunya ce ta hana shi mgana. Ina gidan a

gaban idanuwana Yalla

ɓ

ai ya shige da Gimbiya

ɗ

aki suka sakayo ƙofa sai da na yi kuka karshenta dai Jidda da Baby na

ɗ

auko zuwa

ɗ

aki na suka taya ni kwana amma ji na ke yi kamar ba zan iya ba. Muna gida

ɗ

aya kusa da

ɗ

akin juna amma Yalla

ɓ

ai ba ya tare da ni

ya na tare da wata matar ba ni ba, lalle mata suna ƙokari matan da ake yi musu kishiya suna zama da su a gida

ɗ

aya ya tabbata za a kira su Jarumai.

*Janafty*

*TKG016*

Tun dawowar Gimbiya gidana na ke ta ganin ikon Allah a wajen Yalla

ɓ

ai da dangin

shi, su rawan ƙafa shima rawan ƙafa, ni dai ina gefe ina ganin komai kamar al'amara kamar mafarki. A ce yau wai a gaban idanuwana Yalla

ɓ

ai ke ririta wata macen ba ni ba, kuma a cikin gidana ƴan'uwansa ke zarya saboda wata ba ni ba. Rayuwa kenan abin da ya

baka dariya wata rana shi zai koma ya na ba ka tsoro.

Anty Bahijja ku san kullum sai ta zo gidan nan sai ka ce ni

ɗ

in zan cutar da Gimbiyar ne. Kuma in ta zo ta riƙa bibiya kenan me Gimbiya ta ci? Kar a riƙa ba ta abincin da ba ta so kar a riƙa tashin

ta daga barci in ta kwanta daga ta ce wannan sai ta ce wannan, ni dai ba na wahalar da kaina wajen mgana, saboda duk abin da zan fa

ɗ

a ba shi zai sa komai ya koma yadda ya ke a baya ba shi ya sa kawai na kawo ido na saka musu daga shi har ƴan'uwan na shi.

Abu

ɗ

aya na ke yi shi ne ina girki sannan in zan dafa na kan shiga na ji ra'ayinta in ma na dafa abin da ba ta so in har ta ce min ga abin da ta ke so ina dafa mata ba zai gagare ni ba. Don Allah na ke yi don kuma ita da Yalla

ɓ

ai sannan in ya fita ina sh

iga na duba ta in na ji ta shuru saboda kar wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login