Showing 63001 words to 66000 words out of 159340 words
ta rika zagina ta yada min mgana na ƙarishe da cew
a" Ina da ta cewa ne Amina? Ƴar'uwata ce ta ba da ni fa, shi ya sa na ke addu'an Allah ya shiga tsakanina da Ma'u duk mugun nufin ta ya koma kanta."
"Amin in sha Allahu."
Amina ta fa
ɗ
a lokaci
ɗ
aya ta na cigaba da fa
ɗ
in" Ita fa abin da ya faru na rash
in auran Ya Hamza ne ta riƙe a ranta shi ya sa ta ke jin haushin ki Ya Sadiya."
"Sai dai ko ta mutu amma Ya Hamza ya yi mata nisa. Kuma wallahi tallahi ba na nadaman abin da na yi har nan da gaban Abada Amina"
Na fa
ɗ
a ina mai jadadda mganata sannan na ƙa
ra da cewa" Ba ki lura ƙawarta Shema na ta ya ta ba. Ita kuma shegiya ta ki auru ai duk wanda ya ce tunkunyar wani ba za ta tafasa ba ina mai tabbatar miki da na shi ko
ɗ
umi ba za ta yi ba. Kuma ko alaqarsu da Ma'u hali ne ya zo
ɗ
aya amma in kin lura Ma'u
ta fita wayau ita kuma har da kwa
ɗ
ayi gani ta ke yi Ma'un na ba ta duniya ita kuma saboda mijinta na da ku
ɗ
i sai ta riƙa yi ma Shema'un abu kamar ita ce uwarta."
Na ƙarishe fa
ɗ
a ina mai kallon Amina wacce ta jinjina kai kafin ta ce" Kwarai kuwa. Kamar r
aƙumi da alaqarsa haka Ma'u ke jan Shema."
Ƙ
wafa na yi kafin na ce" Gungun munafukai ai sai munafuncin su ya ci su in sha Allahu." Nan muka cigaba da hira har muka gangaro kan Ya Murja na ce ai ita wannan na da
ɗ
e da sanin yadda ta
ɗ
auki Ma'u ba haka ta
ɗ
a
uke mu ba, sannan kuma da ƙwa
ɗ
ayin itama, wani cewa halina ne ba ta so duk mgana ce amma jiya ta
ɗ
an samu muhallin afuwa acikin zuciyata a karon farko da ta gano Ma'u ba ta kyauta ba.
Sannan Ya Abubakar ma sai a hankali. Shima raƙumin ne sai abin da ya
ga an karkata acan ya ke. Har neman fitan hayyacinsa ya ke yi in dai akan lamarin Ma'u ne.
Amina ta bushe da dariya kafin ta ce" Tsohuwar zuma ce Ya Sadiya "
Nima ina taya ta dariyan na ce" Shi ya sa wani lokacin na ke yi masa uzuri."
Mun da
ɗ
e muna hira
har aka kira sallar isha'i sannan ta fita ta ce min za ta je falo ta yi kallo nima na ce in na idar da sallah zan fito.
Una ko idarwa na fito na iske suna kallon wani indian Movie a Bolloywood Kuchi kuchi hota hae. Ina son film
ɗ
in tuni na zauna muna k
allo har da Saude da Jidda Baby ta kwanta ita da Sultana
ɗ
iyar Amina ƙarama, muna cikin kallon Amina ta je ta
ɗ
umamo mana Tuwo muna ci muna ƙona hannu sannan muna kallo bayan mun gama muka kora da lemu da ruwa, mune har 11pm har sai da aka gama film
ɗ
in na
n sannan muka tashi har Jidda ba ta yi barci ba sai da a ka gama sannan muka kora su
ɗ
aki, ni na tsaya na rage hasken duka
ɗ
akunan na duba ko'ina sannan na je na kwanta na iske Amina ta yi shirin barci ta na kwance suna waya da mijinta sai na ba su waje na
shiga Tiolet na kama ruwa na yi brush, ko da na fito sun gama wayar sai nima na yi shirin kwanciya na saka kayan barci muka kwanta, mun
ɗ
an fara hira ba da
ɗ
e barci ya
ɗ
aukeni ban ƙara sanin kaina ba sai hu
ɗ
un asuba sannan na tashi na
ɗ
auro alwala na yi na
filfilu, sai da a ka fara kiran sallar farko sanman na fita na ta da su Jidda. Dakyar na idar da sallar asuba saboda barci na cin idona na haye gado ba ni na tashi ba sai tara na safe.
Na iske gida ƙal an gyara ko'ina ya na tashin kamshi har sun karyawa
Amina ta shirya sai tafiya Ɗorayi ita da Saude. Ina zama a saman kujera a falon su Jidda na ce" Ke Amina da sassafen nan? Kamar ana koran ki?
Amina na gyara
ɗ
aurin
ɗ
ankwalinta ta ce" Yau fa zan koma kaduna Ya Sadiya gwara na je na gaida su Alhaji na
ɗ
an
zauna zuwa azahar haka."
"To tare da Dattin za ku koma?
Sai ta gya
ɗ
a min kai, ya na iya duk da ba na son tafiyarta haka nan na yi shuru ina laifi an yi min kwana uku. Ni da yara sai rakiya har bakin get muna
ɗ
aga musu Hannu Saude dai gobe ma za ta da
wo. Sai ga shi mun dawo cikin gida mun yi tsuru ni da su. Zama kawai na yi a falo ina nazarin rayuwa. Yanzu yau kwanan Yalla
ɓ
ai biyu ya na cikin garin nan amma ba ya tare da mu sai na ji kwalla sun kawo min amma na yi saurin mayarwa. Tea na ce Jidda ta ha
ɗ
o min na ci da Dankalin da Amina ta soya da safe. Su daman sum yi wankansu ni ce bayan na gama na tashi na yo wanka yau ma
ɗ
in sabuwat atamfa ta na saka, ban zauna a
ɗ
aki ba fito wajen su Jidda saboda su
ɗ
e
ɓ
e min kewa. Baby ta
ɗ
auke mana hankali da rawan d
rama
ɗ
in da suka yi a makaranta ni da Jidda muna ta dariya.
Haka muka yinin mu ka
ɗ
ai a gida sai can bayan La'asar Musbahu ya zo ya ce min Yalla
ɓ
ai ne ya ce ya zo ya duba mu ina mirmiahi na ce" To me zai same mu? Ai dole ma mu saba tunda haka tafiyar za
ta miƙa."
Ban tambaye shi ba da bakinsa ya ke fa
ɗ
a min Yalla
ɓ
ai bai fito Office ba kwana biyu a raina na ce ya fito ya na can ya na cin amarcin sa, ya
ɗ
an da
ɗ
e tunda har sai da ya tsaya ya ci abincin da na yi. Da zai tafi Baby sai ta fara rigiman wai it
a sai ya kaita wajen Abba da Anty Gimbiya tun jiya ta fara min riginan Ina Abba na ce mata ya na gidan Anty Gimbiya ta
ce sai ta je na ce ba yanzu ba, to jiyan ban biye mata ba sai yau ne bayan Tafiyan Musbahu yarinyar nan ta kafa min kuka da rigiman ita s
ai an kaita wajen Abba da Anty Gimbiya.
Yarinyar nan har da zan shiga salla sai da na yi ma ta jan ido akan ta tashi a saman cafet
ɗ
in ta je ta yi salla amma ba ta ji ba. Har na idar da sallah na fito ta na wajen ta na min kukan banza ba tare da na yi m
ata mgana ba na koma
ɗ
aki na
ɗ
auko bulalar injin ce wacce na ke dukansu ne, ƙarama ce ma wannan
ɗ
ayar babban Yalla
ɓ
ai ya dauke ta wai ba ta dukan mutane ba ne kamar zan doke dabbobi.
Ta na kwancen nan ta na rigima sai dai ta ji saukan bulala tuni ta far
a ihu tun tana kiran Abba sai ta koma Umma ki yi hakuri Ya Jidda Ya jidda. Ta na kuka ta na majina karshenta dai Jiddan ta ƙwace ta, ta na ba ni hakuri.
"Don Allah Umma ki yi haƙuri."
Kwafa na yi kafin na ce"ka ji min yarinya mara mutumci kawai da ma
ngariban nan ki
ɗ
aga min hankali! A'a ba gidan Anty Gimbiya ba saura gidan Sarki."
Raina a bace na koma
ɗ
aki ina magana ni ka
ɗ
ai.
"Mata duk ta bi ta gama min da ƴaƴa. Ina dalili."
Wayata da ta kwana ma a kashe ban san ko uban na su ma yau ya tuna da su
ya neme ni ba. Sai ga shi can ajuma na koma na ganta har ta yi barci a raina na ce ashe ma iskanci ne irin na yara, Jidda ma da wuri ta kwanta ranar amma ni na
ɗ
an dade ina kallo saboda ma kar na kwana ni ka
ɗ
ai na yi tunani na ce Jidda ta zo
ɗ
akina mu kwan
a ni kuma na
ɗ
auki Baby na kaita bedroom
ɗ
ina na kwantar.
Ranar tare da yara muka yi barcin mu har da su makara domin sai shidda na safe muka farka. Qur'ani na riƙe shi kuma ya kawo min salama da kwanciyar hankali a kwanakin da Yalla
ɓ
ai ya yi a gidan w
ata mace ko na ce wata matar ta sa bayan ni, sai a ranar na kunna wayata na kikkira mutane na yi musu ban gajiya Amina ma ta ce jiyan da suka isa gida ta yi ta kirana a kashe haka ma Farida ta ce itama ni dai na ce su yi hakuri wayar ce ta mutu ba chaji ba
n sani ba.
Ina lissafe da yau kwanan Yalla
ɓ
ai uku kenan a gidan Gimbiya na
ɗ
an ji ba da
ɗ
i da na kunna wayata ban ga saƙon shi ba amma dai ina ji a jikina ya kira ni wayar ce bai samu ba. Ko bai sanar da ni ba na san kwanakin bazawara kwana uku ne yau Ya
lla
ɓ
ai zai dawo gidana shi ya sa da yamma na dumama sauran kazar da na siya wajen Hajiya Surayya Halin yau, na ci tare da tsumi karfe bakwai da wani abu na yamma Yalla
ɓ
ai ya kira ni lokacin ma ina kan darduma ina lazimi ne bayan na idar da sallar mangariba
.
Ban
ɗ
auka a lokacin ba sai da ta katse sannan ba da
ɗ
ewa ya ƙara kira sannan na
ɗ
auka cikin sanyin murya lokaci
ɗ
aya da sallama a bakina.
Sai ya amsa min daga can bangaren shima a sanyayen, tambayar ya kuke? Ya yara na ce lafiya lau daga nan shuru muk
a yi dukkanmu na wani lokaci.
"Me ya faru jiya da yau wayarki a kashe."
"Ta mutu ba chaji ne ban sani ba."
Domin kar ma ya kawo tambayar ba wuta ne? Shi ya sa na ce ban san ta mutun ba.
"Ok. Yanzu ba da
ɗ
ewa za mu taho nan gida tare da Daugther"
Haka na ji ya fa
ɗ
a sai da na dan yi jim kafin na samu damar magana ya cigaba da fa
ɗ
in" ina so zan yi magana da ku gaba
ɗ
aya."
Sai da sauke ajiyar zuciya sanna na amsa masa da cewa.
"Shike nan sai kun ƙariso."
Da ga haka muka yi sallama ban tash
i ba sai da na gama lazimina na yi salatin Annabi na shafa sannan na miƙe na ninke darduman na
ɗ
ora saman gado daman na yi wanka na saka riga da wando. Ban kuma jin zan iya sauya shigata turaren wuta na
ɗ
auka na fita falo na saka Jidda ta kunna Burner gid
an ya dan yi kamshi Baby kuma na baje a falo ta ba je littafinta na drowing ta na ta zane zane kuma ta na bin shi da kala a baya in na gani sai na hana ta Yallabai ya ce na kyaleta na sani ko ita ce za ta ga je shi? Tun daga lokacin na saka mata ido daga k
arshe ma katon drawing ya siya mata mai kama da littafi da pensira na zane da clours ya na zane ni, in akwai makaranta ban barin ta yi amma yanzu da suka samu hutu ba na hana ta.
Muna zaune a falon gaba
ɗ
ayan mu mu ka ji shigowar Motar Yallabai gidan da
ƙ
aran rufe get, tun da karfe ne dole in an bu
ɗ
e ko an rufe sai mun ji kara. Jidda ta daka tsalle ta mike ta na fa
ɗ
in" Baby Abba ne."
Daga ita har Baby a guje suka fice baby ta yi falati da kayan zanen ta suka fice da gudu suna kiran oyoyo Abba, na ji bu
ɗ
e
kofar falon da yadda yaran suka na
ɗ
e shi da muryan shi ya na fa
ɗ
in.
"Oyoyo My princess. I miss u."
Ina zaune a in da na ke na kasa tashi. Haka kurum sai na ji gabana na fa
ɗ
uwa ras! Kamar kuma sai na ji kamar wani tsoro tsoro na shiga ta.
Yau ne fa
zan hada ido da kishiya? Kishiyar da mijina ya kwana da ita har uku. Ƙilama akwanakin nan ta samu ciki.
"Auzubillahi minal she
ɗ
anir rajim"
Haka na fa
ɗ
a da sauri domin koran she
ɗ
an
ɗ
in da ya ziyarce ni.
*Janafty*
*TKG*
*Assalamu alaikum!*
*Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.*
*Karku manta b
amu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku
hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin fa
ɗ
ak
arwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.*
*Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.*
*Ku biya ku
ɗ
inku ta wannan a
susun Kamar haka
👇🏻
*
For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account
👇🏻
7087809778
Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704.
*Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntu
ɓ
eni ta wannan line
ɗ
in 0816
7768704.*
10.
Ina zaune ne amma na kasa tashi domin sai na ke jin gaba
ɗ
aya ilahirin jikina na rawa. To in ma na tashi wa zan je tarowa? Kishiya ko miji? Kawai sai na yi zama na amma fa zuciyata bugawa ta ke yi da sauri da sauri cikin lokaci ƙalilan h
ankalina ya tashi ina neman fita hayyacina saboda wani iri abu na ke ji yana ta so min daga ƙasan zuciyata.
Kishi masifa ne, zai iya haifar ma da mata lalura mai karfin da nan ta ke za a iya kai su emergency a yi tunanin ciwon ya da
ɗ
e a jikinsu ne ba a sa
ni ba alhalin kishi mai saka ma zuciya ciwo nan take ba tare da mutum ya sani ba.
Idanuwana suna kallon ƙofar falon suka shigo, shi ya bu
ɗ
e mata kofar ta fara shigowa hannunta na riƙe da na hannun Baby. Sai shi ya biyo bayan su, shima hannunsa na riƙe
da na Jidda. Gimbiya fara ce sosai doguwa domin har ta
ɗ
an fini tsawo sannan tana da jikin murjewa kyakyawa ce domin hancin ta har baka. Sanye ta ke da atamfa mai kalan orange shi ya sa mayafin da ke jikinta ma kalan shi kenan, shi kuma Yalla
ɓ
ai an cakare
cikin ƙananun kaya har da zanzaro. Dukkansu fuskarsu tana fitar da wani annuri ne. Annurin da ka na ganin shi za ka san na farinciki ne wanda zuciya ke samu ta hanyar gangan jiki.
Duk ina zaune ne na ƙare musu kallo, ina ganin za mu ha
ɗ
a ido da su na yi
saurin
ɗ
auke kaina ina jin zuciyata na ƙara tsananta bugawa. Ina jinjina ma matan da ake yi musu kishiya sannan a ha
ɗ
a su zama da su a gida
ɗ
aya. Wallahi in ni ce ba zan iya ba, domin na tabbata wata rana zan iya ha
ɗ
iyan zuciya na mutu saboda baƙin ciki.
Da na so na tashi na tarbe ta amma daga baya kawai sai na fasa sai ma gyara zaman da na yi daga in da na ke zaune na ce.
"Sannun ku da zuwa."
Na fa
ɗ
a ina ƙara gayyato mirmishi a saman fuskata.
Ita ta amsa amma a hankali shi ne na ji amsar ta shi da
ƙarfi yaran na maƙale da su, shi ya nuna ma Gimbiya kujeran da za ta zauna na zaman mutum biyu, ta isa ta zauna Baby ta haye jikinta shi kuma sai ya durkusa a gabana lokaci
ɗ
aya ya na mai riƙe duka hannayena cikin tafukan hannunsa
so ya ke mu ha
ɗ
a ido, ni
kuma na ki bashi damar haka sai ma Juyawa da na yi ina kallon Jidda da ta zauna gefen Gimbiya sai mirmishi suke yi daga ita har Baby umh yara ai ba ku san dawan garin ba.
"Jidda kawo ma Antyn ta ku ruwa da lemu mana."
"To Umma."
Ta fa
ɗ
a da saurin
ta sannan ta ta shi ta nufi kitchen
ɗ
in.
"Kalle ni mana Sadiya ta."
Ya fa
ɗ
a ya na leƙa fuskata sai na yi fuska ma maze na kalle shi ta ƙasan idanuwana. Haushi fa ya ke ba ni, hannayena ma da ya riƙe ji na ke yi kamar na ƙwace, domin haskowa na ke yi
da wa
ɗ
anan hannayen na shi fa ya riƙe Gimbiya da su, shi