Showing 159001 words to 159340 words out of 159340 words
/>
ɗ
in sai gani zaune a ƙasan tiolet domin ba zan iya tsayuwa ba, ji na ke yi kamar ba ni da ruwa ba ni da jini, ina amai amma ina ji kamar hanjin cikina za su yo waje, kakari kawai na ke yi ni dai na ji Amina ta bu
ɗ
e ƙofar tiolet ta na ƙara kiran sunana
amma ina kamar a wata duniyan na ke jin ta ,kaina da ya yi min nauyi na jingina da jikin garon Tiolet
ɗ
in ina jin kamar fitsari na bin jikina.
Ya illahi fiteari na ke yi a zaune saboda jikina ya yi mugun sakin da ba zan iya motsa koda
ɗ
an yatsa na ba ne.
"Innalillahi na shiga uku Ya Sadiya."
Na ji ta kamani ta na ƙoƙarin miƙar da ni tsaye amma ina jikina gaba
ɗ
aya ya saki. Idanuwana suna lumshewa amma sai da suka gano min jan abu da na ga ya na zirarowa ta ƙasan kafafuwana. Kamar jini na gani. Ba kama
ba ne jini ne ke bin ƙafafuwana ba fitsari ba ne.
Sai na yi ƙoƙarin tashi ina mai dafe bango Amina na riƙe ni har ta fara murya kamar za ta yi kuka.
"Mun shiga uku Ya Sadiya jini kike zubarwa."
Na ƙara bin ƙafafuwana da kallo jini ne da gaske har
ya gangaro ya
ɓ
ata farin tayels
ɗ
in Tiolet
ɗ
in. Ina ƙoƙarin na tsaya da kafafuwana amma na kasa. Kamar an
ɗ
auke ni daga wannan duniyar haka na ji kamar
ɗ
aukewar iska shuu.! Sai na tafi yaraf na fa
ɗ
a a jikin Amina. Bakina na motsi ina so in yi magana a loka
cin sai komai na duniyar ya tsaya mini cak kamar an zare rai daga gangan jikina.
*Ƙarshen littafi na biyu.*
*ZA MU TAFI HUTUN KWANA BIYU KAFIN MU ƊORA A LITTAFI NA UKU IN SHA ALLAHU.
NA GODE DA JIMARIN BIBIYAR WANNAN LABARIN.
*16. Jan 2025.*
*
Janafty*
.
.