Showing 129001 words to 132000 words out of 159340 words
ba ta ba dom
in ina ji a raina na yi mata wani abun ba sai domin yi masa kara tun da shi babba ne kuma bai kamata na watsa masa ƙasa a ido ba.
Sannan ya sha ta layi tsakanin Bahijja da Ma'u ya ce kar ta ƙara zuwa gidan nan bai hana su ha
ɗ
u can dangin mijinta ba amma
in aka sake jin wata mgana ta bullo ba za su hana ni na
ɗ
au matakin da ya kamata ba.
"Nima Kawu ka fa
ɗ
a mata kar ta ƙara shiga harkan gidana da matana. Ba Saudatu ba Sadiya ba. Ta kama girmanta a matsayinta na yayata su kuma su girmamata a matsayinta n
a yayar mijinsu."
In ji Yalla
ɓ
ai.
"Fakat"
Kawu Abba ya fa
ɗ
a, Kawu Sa'adu ya ce gaskiya kar ya ji kar ya ƙara gani.
Har Anty Maimuna itama an ce kowacce ta ji da kanta ba ruwansu da matan ƙannensu. Mazan su ne dolen su su tsaya a kansu.
Itama Gim
biya Yalla
ɓ
ai ya ce ya yi mata tsakani da Anty Bahijja bai ce ya raba su ba amma ta sani su yi zumumcin su kawai in har wani munafunci ya sake fitowa sai ta raina kanta da sauri ta ce ba za a ƙara ba.
Kafin a tashi Kaawu Abba ya gyara zama ya na fa
ɗ
in"
"Na so sai mun gama daidaitawa da Marwa kafin na kawo mganar amma tunda maganar ta yo kutse, shi kenan ni na ga
ɗ
iyar Yayar Sadiya ina so ga Tafidan nan shi ya rakani gidansu na nemi izini ko Sadiyan ba ta sani ba, ina so kowa da ke nan ya shaida nan da l
okaci ka
ɗ
an zan tura maganata domin a yi maganar aure. Wanda bai so abin ba ya yi shurun sa kar ma ya saka albarka tunda da saka albarkarshi da rashin sakawan duk
ɗ
aya ne ni a wajena."
Kawu Sa'adu ya ce duk lamarin bai kai haka ba. Abu dai ya riga ya
faru a yi haƙuri a tari gaba tun da sun ba da haƙuri sun ce ba za su ƙara ba.
To a yi musu afuwa.
Da haka taron ya tashi, ban ko tsayawa ba na ce zan koma gida Yalla
ɓ
ai ya ba ni ku
ɗ
in adai-daita muka fita tare da su Hauwa suna ta cewa Anty Bahijja ta sha
kunya, da ga ita har Gimbiyar ni dai ban ce komai ba. Duk da na
ɗ
an ji sanyi da Yalla
ɓ
ai ya tsaya min amma ba a biyani ba tunda ba a bar ni na kai hukuma ba.
Gidana na koma amma na kira Ya Aina na fa
ɗ
a mata, na ce an yi muui mgana sun nemi gafara Amma
sun shiga tsakanina da su gaba
ɗ
aya.
"Hakan ma ya yi. Hamza ya ce min ya na hanya ma."
Na ce Allah ya kawo shi lafiya. Tu
ɓ
ewa na yi na fara gyaran gidana da ya yi datti. Bayan na gama
ɗ
ora girki, taliya na yi da miya, kayan miyan ma sai da na kira Yal
la
ɓ
ai ya aiko min da cefanen kayan miya shi na ya yi bilandin na yi miya da kifi.
Da su Jidda suka dawo makaranta suka ganni suna ta murna na sha labari wajen Baby. Jidda na fa
ɗ
in suna ta tambayana Abba ya ce wai na yi tafiya ne ni kaina na ji da
ɗ
i da n
a gansu ashe na yi kewarsu ban sani ba. Da su na yini a gidana suka
ɗ
ebe min kewa sai bayan isha'i Yalla
ɓ
ai ya shigo da kayan marmari da yawa a leda.
*Janafty*
*TKG019019*
Da yake na san Yalla
ɓ
ai ba ya son cin taliya a cewarsa wai ba ta ƙosar dash
i. Shi ya sa sai na dafa masa shinkafa mai karas da kabeji. Mu kuma sai muka ci sauran taliyan da ta rage ni da yara. Kayan marmarin da ya kawo rabi na
ɗ
ibar mana na wanke muka ci, rabi kuma na saka a cikin frizer.
Sai da Yalla
ɓ
ai ya yi wanka ya sauya k
aya zuwa wasu sauƙaƙku na zaman gida sannan ya ci abinci ya na cin abincin ina gefen shi amma da ka ganni za ka fahimci sai a hankali saboda na zama wata shuru shuru kamar wata mara lafiya. Duk da na saka kaya masu kyau amma ban yi kwalliya ba fuskata kaw
ai in ka kalla za ka fahimci damuwa ƙara ƙara tun da har damuwar ta bayyana.
Ya na gama cin abinci bayan na tattara komai na mai da kitchen yara kuma na ce su shiga ciki su kwanta. Nan na bar Yalla
ɓ
ai a falo ya kunna kallo ni kuma sai na shiga ciki tiol
et na fara shiga na kama ruwa sannan na fito na yi shirin kwanciya. Har na ma kwanta na rufe ƙafafuna zuwa saman cikina da bargo na kuma rage hasken
ɗ
akin sannan can na ji shigowar Yalla
ɓ
ai shima kayan jikinsa ya cire ya saka na barci sannan ya biyo ni kan
gadon.
A bayana ya kwanto ya na mai riƙo hannuwana da na har
ɗ
e ƙirjina da su, ya fara
ɗ
an shafawa ka
ɗ
an ka
ɗ
an lokaci
ɗ
aya ya na kiran sunana.
"Sadiya ta."
"Uhm"
Na amsa a cikin maƙoshina, sai da ya
ɗ
an yi jim kafin ya cigaba da fa
ɗ
in" Ki yi haƙ
uri kin ji ko?
Sai na gya
ɗ
a masa kai ba tare da na yi magana ba. Haƙurin kam tabbas zan yi amma ba na jin zan iya mantawa da abin da suka yi min har gaban abada kuwa.
"Ki yafe musu. Musamman ma Daughter ta yi nadama sosai kuma ta fa
ɗ
a zugan Anty Bahijj
a ne sai she
ɗ
an ya yi tasiri a kanta."
Ita ce she
ɗ
aniyar kanta na fa
ɗ
a a cikin raina a fili ko numfashi kawai na fesar ba tare da na sake yin wata mgana ba.
"Ki yi haƙuri ki manta komai don Allah"
Nan ma shuru na yi sai ya leƙo fuskata lokaci
ɗ
aya y
a na fa
ɗ
in" Kin ji ko?
Sai na ka
ɗ
a kaina kafin na ce" Na ji. Ya wuce."
"Ba irin wannan wucewan ba. Ina so ki yafe musu sannan ki manta da komai kar ki ce za ki riƙe su a cikin ranki. Sannan kar ki ce za ki daina zumunci da su. Sun zama dole a garemu Sa
diya. Daugther matata ce Anty Bahijja kuma yayata ce ita ta saki nono na kama. Kin ga ke ma sun zama dolen ki, ina so ki cire abin a ranki in kun ha
ɗ
u ki mu'amalance su kamar yadda kika saba."
Kawai sai na yi shuru ina sauraran Yalla
ɓ
ai. Haba ai maciji
sau
ɗ
aya ya ke saran mumini ya yi hankali. Shi a tunanin shi zan ƙara sakar musu ne! Har abada ai sun yi min hankali sannan na yi karatun duniya na ƙara shiga taitayina.
"Ba ki ce komai ba?
Ya sake tambayata sai na gyara kwanciyata ka
ɗ
an duk da har
lokacin bai bar jikina ba sannan bai sake ni ba.
"Ban yi maka alƙwarin zan cigaba da mu'amala da su kamar baya ba. Sai dai na yi maka alƙwarin zan manta komai a hankali ba da gaggawa ba."
"Me ya sa?
Sai da na
ɗ
ago na kalle shi ta hasken da ya ke
shigowa ta window
ɗ
in bedroom
ɗ
in mu. Sannan na koma na kwantar da kaina a saman filo ina fa
ɗ
in .
"Saboda sun yi min hankali. A kan su na ƙara sanin karatun duniya. Ka yi haƙuri amma ba zan iya sake sakin jiki da su ba."
Ya bu
ɗ
e baki zai yi magana n
a yi saurin tare shi.
"Kar ka matsa min Yalla
ɓ
ai. Wataƙila a hankali in na manta na iya kallon su a matsayin kallon da na ke yi musu a baya. Shi ya sa na ce kar ka matsa min don Allah."
Sai ya yi shuru bai ƙara magana ba. Sai dai ya karkato ni ina fu
skantar shi, sumbatar goshina ya fara har ya gangaro saman bakina ya fara sumbatata. Duk da ba na cikin mood
ɗ
in amma ban ture tayin shi ba. Sai nima na tallafe shi muka samar ma junanmu natsuwa ba mu wani da
ɗ
e kamar yadda muka saba ba daga shi har ni
ɗ
in
ba mu da wani karsashi da baƙatuwa shi ya sa lamarin bai yi mana armashi kamar yadda muka saba ba. A daran muka tsarkake jikin mu, shi ya rigani barci ni kam na da
ɗ
e ban yi barci ba sai wajajen biyu saura na dare na samu barci ya kwashe ni.
Washega
ri kuma daman Asabar ne. Ina idar da sallar asuba na fara azkar kenan barci ya
ɗ
auke ni a nan saman darduma Yalla
ɓ
ai ne ma ya tashe ni ina layi na haye gado. Ba ni ta shi ba sai da wayar Ya Hamza ta tashe ni. Sai bayan mun gama wayar ne na duba agogon way
ata na ga har sha
ɗ
aya saura na safe ai sai na diro daga kan gado na fita can falo yara na iske ba su nan sun tafi hadda. Sai Yalla
ɓ
ai ka
ɗ
ai ne a gidan ya na aiki a system
ɗ
in shi.
"Ina kwana."
Na fa
ɗ
a lokacin da na shiga falon shi na gan shi zaune
ya na aiki.
"Kin tashi lafiya?
Ya fa
ɗ
a ya na mai
ɗ
agowa ya na kallona.
Sai na jinjina masa kai. Ban tambaye shi yara ba saboda na san sun tafi hadda ne.
Na juya zan bar falon na ji shi ya na ce min." Tea suka sha sai ƙwai da Jidda ta soya musu s
uka ci suka tafi makaranta."
Sai na gya
ɗ
a kaina daga nan kitchen
ɗ
in na shiga wato aikin na manya ne an yi kaca kaca da kitchen
ɗ
in da jiya na gama wahalan gyarawa. Haushi duk ya kamani mu ma tea
ɗ
in na sake dafa mana sai na fere mana doya muka sha dashi.
Na so na
ɗ
an gasa mana buredi sai kuma na fasa ganin rana ta yi, muna cikin karyawa na ce ma Yalla
ɓ
ai ina son zan je Ɗorayi.
"Ki shirya in zan fita sai na sauke ki kafin na wuce office"
Yadda bai tambayeni me zan je ba, nima ban fa
ɗ
a masa ba saboda
na san ya san ba zai wuce maaganar Ma'u ba.
Muna gamawa Yalla
ɓ
ai ya fara yin wanka ni kuma sai na
ɗ
an tsaya na gyara kitchen ga himilin wanke wanke. Saude ba ta nan fa ta tafi garin su ni kaina ban san ta tafi ba sai daga baya. Na yi ta fa
ɗ
a da cewa ana t
sakar makaranta ai ba a tafiya, ita kuma Balaraba sai ta ce wai auren
ɗ
iyar ƙanin babansu ake yi Sauden ta matsa sai ta je. Ni dai fata na kar su je can su yi mata aure tun da can ƙauye sokoto ne garin baban na su.
Wanke wanke kawai na yi sauran ayyuka
n na ce in Jidda sun dawo ta
ɗ
an gyara gidan. Yalla
ɓ
ai na son tafiya tun da ana ta kiran shi ya yi baƙi. Mun bar gida wajen sha
ɗ
aya da rabi na rana ya kai ni
ɗ
orayi bai ko shiga ba ya wuce.
Na je na iske Ya Hamza da Gwaggo a falon Alhajinmu ne suna hi
ra nima sai na bi ayarin su. Bayan mun gaisa da Alhaji da Gwaggo ne na juya ina gaida Ya Hamza ina tambayan shi ya wajen su Khaleesat?
"Duk suna nan lafiya. Sun ce a gaishe ku."
Mun
ɗ
an yi hira sama sama a kan sanyin da ake yi a can zaria. Sai ya kal
leni kafin ya ce" Jiya an yi zama a can gidan Baban su Jiddan?
Sai na gya
ɗ
a masa kai kafin na fara bashi labarin abin da ya faru. Gwaggo na gefe ta na ji ita da Alhajinmu.
"Ka ji ko Alhaji.? Ma'u she
ɗ
aniya ce. Ta ha
ɗ
a husuma ta na neman wargaza zaman l
afiya a gidan auran Sadiya."
Ya Hamza ya fa
ɗ
a cikin
ɓ
acin rai ganin haka ya sa na kalli Alhajinmu shi da Gwaggo da suka yi shuru sun kasa mgana na ce" To ita da ta ce ma Anty Bahijja a yi hankali da ni. Ina shige shigen malamai zan iya yin komai domin n
a ga bayan cikin Amaryan Yalla
ɓ
ai."
Gwaggo ta saka salati tana tafa hannu.
"Kai Ma'u ta yi asara. Ta kuma ba ni mamaki. Wallahi tun da na ji abin da ya faru na kasa suƙuni kawai mamaki na ke yi me kika yi ma Asma'u da zafi haka da ta nemi tozarki haka Sa
diya?
"Me kuwa na yi mata Gwaggo? Na fa
ɗ
a muku tun a baya kan fasa auranta da Ya Hamza ne daman ta ce na jira zan gani. Kuma ta da
ɗ
e ta na yi min shige da fice yanzu dai burinta ya cika akaina ta yi min sharri ta kuma yi sa'a na tozarta."
"Za ta ko c
i ubanta. Har Baaba sai an kira ta zo domin a kawo ƙarshen makircinta."
Ya Hamza ya fa
ɗ
a cikin jin haushi Gwaggo ta ce haka ya kamata a matseta sai ta fa
ɗ
i dalilinta na aikata abin da ta aikata. Alhajinmu na zaune amma ƙala bai ce ba sai ka
ɗ
a kai kawai
ya ke yi lamarin ya gama ba shi mamaki. Muna cikin magana da Ya Hamza Alhajinmu ya kira sunana na amsa ina mai kallon shi.
"Ki fa
ɗ
a min tun farko yadda lamarin ya faru."
Na gyara zama na sake fa
ɗ
a musu duk abin da ya faru har zuwa gidan Ma'u da na yi
na ja ta da fa
ɗ
a sai da na fa
ɗ
a saboda ban ga abin
ɓ
oyewa ba ni ai ban ma samu yadda na ke so ba, da na samu da tuni ta na gadon asibiti.
" Daman ba tun yanzu ba. Na da
ɗ
e ina jin wasu labaraina a bakin Yayar mijina Alhajinmu. Ban ta
ɓ
a
ɗ
aga maganar ba sab
oda ko na
ɗ
aga sai a ce ni ce ke da fitina tun da Alhaji ka ce in ban yi zumunci da Ma'u ba za ka yi fushi da ni ya sa na kauda komai ina zumunci da ita to ashe ita babban burinta na tozarta. Ta tozarta zuru'an Mama ni kuma ta yi min ƙazafin ina ƙokarin zu
bar da cikin Amaryan Yalla
ɓ
ai. Alhaji ka yi haƙuri amma ina jin lokacin da zan datse zumuncin da ke tsakanina da Ma'u ya yi. Kuma na tabbata kaima ba za ka ce don me ba, domin matuƙar cin zarafi Ma'u ta gama yi min shi anan duniya."
Gwaggo ta nisa amma
ba ta yi magana ba. Ya Hamza ko ya ce gaskiya ne babu amfanin yin zumunci da wanda ke neman ya tozarta ka.
Ya kalli Alhajinmu ya na sake fa
ɗ
in" Alhajinmu mataki za ka
ɗ
auka domin bayan Sadiya har kai yar iskar yarinyar nan ta ci ma mutumci."
Alhajinmu
kai kawai ya girgiza ba taree da ya yi magana ba.
"Ga ma labarin Marwa. Ƙanin Nene ya ganta gidana ya ce ya na so. Wallahi Babansu Jidda ya raka shi wajen Babansu Marwa ya neme ni izini ya na zuwa wajenta domin su dai-dai ta daman ya ce sai sun gama yar
da da juna zai kai mganar ga manya. Amma Ya Murja na samun labari ta je ta fa
ɗ
a ma Ma'u ita kuma munafuka ta kwashe ta fa
ɗ
a ma Anty Bahijja. A ranar da abin ya faru har ta na ce min ban isa ba yadda na asirci Yalla
ɓ
ai ne na ke so na tusa ma Kawun su
ɗ
iyar
Yayata shima a asirce shi sai yadda aka yi da shi tun da mu yan na gada ne ba haya ba."
Gwaggo ta ƙara saka salati ta na fa
ɗ
in" Na ga duniya ni Maimuna. Me Ma'u ta ke so ta zama ne! Ko na ce ta zama ma?
Ya Hamza ya yi wani kayci kafin ya ce" Ni fa dama
n tuni na san za a rina. Tun a baya ta fi kowa kalkalin mgana da tsara zence. Ta ko gama ma kanta aiki sai ta gane ba ta da wayau"
Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce" Tabbas Ma'u ta yi kuskure. Kuma ya zama wajibi a nuna mata kuskurenta."
"Tabbas."
Gwaggo ta fa
ɗ
a daga gani itama ranta duk ya gama
ɓ
aci.
"Hamza kira min Hasiya mu yi mgana."
Alhajinmu ya fa
ɗ
a ya na kallon Ya Hamza nan ta ke ko ya doka ma Baaba kira. A handfree Ya Hamza ya saka wayar bayan sun gaisa sai Alhajinmu ya ce ta zo gobe in da
sarari ya na son ganinta kawai sai itama ta ce.
"Daman ko ba ka kirani ba Ya Sule ni zan kira ka. Kana da labarin Sadiya ta je har gida ta daki Ma'u? Me ta yi mata? Ko na ce me