Showing 132001 words to 135000 words out of 184731 words
ta warke, yeee zamu tafi gida yau
Murmishi ameera tayi ganin , sun shigo yaran su hu
du,, kowa sai mommy yake cewa ,,,hannu tabude musu nan sukayo kanta,, suna rungume ta,,,,, beauty tace sannu mommy
Kallon ameera tayi shesuka bata tausayi yandda suka lafewa ajikin ta,, tace,, to kutashi muje gida kunji
yaran albarka, ,, mikewa sukayi tasauko,, koya kama hannun ta, tana tsallen murna
Doctor aisha ce tashigo tace to ,she gidako " Allah yakiyaye gaba, ikram tasaki hannun ameera ta kama na doctor aisha,,
Murmishi ta
yi tace,, a a ikram ko mutafi gidana dake,, hannu ta daga, tana fadin umbo,, mommy, ,dariya tayi tace wai ameera wannan bagwariyar,, yar taki mai take cewa,
Kallon su ameera tayi, tace idan tace umbo,,, wato tana nufin ki
dauketa, idan kuma tace aiya , to ku zauna take nufi,, idan tace, mamo kuma bacci take nufi kai wani yaren nata nima ,, kasa ganewa nakeyi idan tanayi ", saidai in tana nunamin da hannu zam gane abinci take nufi
Dar
iya sukayi su duka,, Umar yace ai akwai yaruka akan ikram wani abun intana jagalgwawa ,, sai ka kasa gane ina ta dosa ,
Doctor aisha tace,, gaskiya naga alama zo mutafi ,,gidana nan ta dauketa ", ita kuwa sai murna takeyi
, antafi da ita,,,suma tafiya gida sukayi
Ikram ce zaune a falo,, yauma aikin tunanin ameera takeyi,, abu kamar wasa ameera har tayi shekara biyu da rabi ,, da bata yanzu a ina take
Su ameer da ameera ne suka s
higo
Jikinta suka fada
firgigit tadawo daga,, tunanin tace harkun dawo,, ina daddyn ku yake
Ameer ne yace mom " daddy yace mushigo shiya koma ,wai meeting gareshi,
Tace to muje namuku wanka nan sukayi daki
A
meera ce,, kwance cikin dare sai juya kanta takeyi, tana yatsina fuska, kamar mai ciwon,, junnu a razane ta farka " har jike tayi sharkab,, kamar an zuba mata ruwa, , addu'a ta ringa yi,, , yashafa,, tanason komawa bacci amma y
a gagareta " tana tunano abinda tagani a mafarkin ta.....
*ko meye ameera tagani a mafarki oho*
*thank you my fans ina godiya da addu'o'i ku agareni Allah yabar kauna*
[30/10, 17:51] MRS. MU'UTASIM: *
🌟
AMEER DA AMEERA
🌟
*
*STORY AND WRITER*
*BY*
*MAMAN NUSAIBA CE
✍
️
*
💫💫
*
🅙
︎
ARUMAI
🅦
︎
WRITERS
🅐
︎
SSOCIATION
📚🖊
️
*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantar
wa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
💪
*_
*
💫
(
🅙
︎
.
🅦
︎
.
🅐
︎
)
💫
*
*73—74*
Tagumi ameera tayi tana tunano abinda tagani a mafarkin nata ,, anty karima ce tagani wasu mutane najanta ,,
tana kiran sunan ameera kizo ki ceceni kada kibari sutafi dani " please ameera....ta fada da karfi
Da gudu ameera tabisu harta kama anty karima zasu gudu wani daga cikinsu ya bige ta akai nan tafadi,, ihu anty karim
a keyi saboda ganin abuge ameera tana jijjiga,, ta nan sukazo suka dauke anty karima " wani daki suka sakata,,, ajiyar zuciya tasauke bayan tadawo daga tunanin mafarkin data yi sosai jikinta yayi sanyi tashi tayi tashiga toile
t , tayo alwala nan ta soma jero nafila
Umar ma , yadda ameera tayi mafarkin shima haka yayi,, da sauri yadiro daga kan gadon yana safa da marwa ,, shi yakasa gane wannan dakin acikin gidan bauta a wani waje yake
babu inda bai sani ba gidan bauta amma wannan dakin baisan shiba kai dasake lokaci yayi da zai je gidan bauta yaduba lungu da sako saiya gano wannan dakin ,, yaga ko karima na ciki ganin hakan ba mafita bane yasa shi
tashi yayo alwala yasoma nafila ,, yanakai kukansa wajan Allah daya bayyana mishi matar shi ya kareta aduk inda take
Su bilal abin nema yasamu sai nan nan ake da jamila ita har mamaki ma yake bata in yanayin wani
abun, ,, da wuri yake dawowa daga wajan aiki yazo " yayi tawa cikin jamila magana wai yana magana da babyn shi
Dariya jamila keyi duk lokacin daya soma wannan abun
Yauma suna zaune ya kara kunnanshi ajikin cikin
, dagowa yayi yace habibty wllh baby yana motsi ,, yasan babanshi na kusa dashi
Kallon shi tayi tana murmishi tace, eh nima naji yana motsi " kasan dani zaiyi kama bada kaiba
Harara ya aika mata yace, tab wllh
baki isaba dani zaiyo kama yarinya ,, nasha wahalar samar dashi amma kice dake zaiyi kama, ninefa nafi yin aiki wajan samunsa
Dariya sosai jamila tayi tace habiby wannan maganar haka bakajin kunya,, to naji yayi kama da
kai shikenan
Murmishi yayi yace ai dole ma kibar min maganar insha Allah dani zaiyi kama
Tace ameen
Shafa cikin yayi yace waida watan shi nawa cikin nan
Bakwai ta bashi amsa
Yace kai ashe nakusa zama dad
dy wllh Allah yamiki albarka habibty Allah yasaukeki lfy
Tace ameen habiby. ,,Fatima kuwa haihuwa ko yai ko gobe insha Allah
Bilal yace eh wllh bakiga yadda cikin ya keretaba idan kika ganta abin tausayi ,, kai Allah y
asakawa iyayenmu da Alkhairi ,, Jamila tace ameen ya Allah ,nan sukaci gaba da hirarsu ta masoya
Fatima ce tafito , tana tafiya da kyer anass ne ya taimaka mata,, ta zauna ahankali
Kallon ta yake cike da tausa
yi yana matukar tausaya mata ,, yadda cikin ya hanata komai amma duk da haka,, bata hanashi hakkin sa " gaskiya yana jinjina wa fatima kukan tane yadawo dashi da sauri yarike ta yace yadai
Kwantar da kanta, tayi a
kafadar shi tace sweetheart
Juyowa yayi yana kallon ta yace na'am meke miki ciwo ne
Kwabe fuska tayi tace , cikin nan yahanani zama irin nakowa, ko bacci ban iyayi na kirki ,ga bayana namin mugun ciwo ,, dana fadawa
mom cemin tayi
wai idan mace ' ta kusan haihuwa haka take fama da wannan ciwon bayan " har ta haihu ,, nidai wllh nagaji da ciwo nan please ka amsa nima nahuta,, kona sati biyu ne kayi sweetheart yana kai karshen maganar
tana dagowa daga kafadarshi
Danne dariyar shi yayi tana rarrashin ta,, har bacci yayi gaba da ita yace fatima rigima kenan inbanda abinki ina maza ke daukar ciki, ai sai mata Allah Allah yasaukeki lfy,, nan yaringa mats
a mata kafafunta dasukayi,, kumburi yana murmishi,, yakusa zama daddy
Alhamdulillah yau ameera takoma islamiya,, kuma taji dadi makotansun nan suma suna zuwa sosai , lokacin da aka ce musu an doki ameera ,, mai gidan s
aida yakai reported wajan sanda amma aka kasa gano mutumin " haka suka hakura amma yace duk lokacin da suka ganoshi, su fada mishi ' shiyasa yau da umar yace musu zatazo suke ta murna
Assalam alaikum ameera tace lokacin
datazo bakin kofar shiga
Amin wa'alaikum salam suka amsa mata matan da sauri sukayo wajan ameera ' suna nuna farin cikin su da ganinta
Murmishi tayi tace, kuna lfy daiko ,, a tare suka amsa mata da lfy lau,, ya saukin naki
'' Ameera tace Alhamdulillah,, nan suka zauna aka kama karatu
Bayan antashi kowa yatafi gida,, Ameera ta dauko jakarta, har taje bakin kofa saita dawo,, wajan muhammed
Kallon ta muhammed yayi , yace kanwata yadai
,,, ko kewar ikram kike ne
Yar dariya tayi,,tace tab kewa fa aiko shekara zatayi bazanyi kewarta ba haba yarinya sai rashin jin tsiya
Murmishi yayi yace to shikenan kibamu ita kyauta " dama bamuda mace agidanmu , shikenan
Ameera tace to nabaku ai inda ikram ce gata gaku, asha zama lfy
Tace am dama inason muyi wata magana ne
Muhammed yace ina jinki kanwata
Numfashi ameera taja tace wllh yayana wani mafarki nayi mai ban ts
oro kuma nakasa samun nutsuwa
Muhammed yace subhanallah to mai kikagani acikin mafarkin naki kanwata
Tuni har ameera tasoma kuka tace matar yaya umar nagani acikin wani hali tana kirana amma wasu suka bugeni nafadi
nakasa manta abinne
Muhammed yace ban ganeba ameera dama umar yana da mata shin dama su abubakar sadeeq da mufeeda ba ke kika haifesuba ,, kaina fa yakulle kanwata kiyimin bayani ta yadda zan gane
Ciki kuka amee
ra tace,, yayana niba matar sa bace bakaga sai wannan shekarar suka musulinta ba su din kaddarar rayuwa tane,, shiyasa Allah yajefoni cikinsu bansan suba anty karima kadai nasani itama a mafarki nake ganin ta sau daya n
aganta afili sanye da kayan likitoci
Zama muhammed yayi yana dafe kai yace to kanwata " kince su kaddarar rayuwar kine to kuma naga su abubakar suna tsananin kama dake " babu wanda zaice bakece mamansu " ba duk da
ana samun masu kamanni amma basuda,, hadin dangi haka Allah yakeyinsu kama daya " amma naga shakuwar da kukayi da yaran abin yana bani mamaki ,, kanwata shin ke wacece daga ina kikazo nan " da ciki ajikinki ina baban yaran
da kika haifa please kiyimin bayani
Share hawaye tayi " tace hakane yaya muhammed nima abin yana bani mamaki sosai yadda muke kama da yaran har mamansu , ita munfi kama sosai.
Nan tabashi tarishin rayuwar ta da y
adda akayi aurenta da lokacin da anty karima " take zuwar mata a mafarki, da kalaman datake mata har zuwa rabuwar dasukayi ita da ameer din ta da yadda " tayi luzing din memory dinta " har zuwa yanzu tana saka kuka mai ta
ba zuciya " saboda ta tuna yadda ameer ke sonta na riritata kamar jaririya da kulawar shi,, amma yanzu gashi kaddarar rayuwa ta rabasu.
Tace ninasan yanzu sun dauka na mutu kawai yanzu shekara biyu da rabi ,,kenan rabona da
family na
Baki da hanci muhammed yasaki yana kallon ameera " da tagama bashi tarishin wannan rikitaccen,, lamarin ,share zufar dake karyo mishi yayi yace kai amma kanwata na tausaya miki " insha Allah kinkusa