Showing 171001 words to 174000 words out of 184731 words
na dauketa kamar kanwata sabo
da banida yar uwa ,
Haka muke zuwa gidan su maman mu anan muke yini sosai sukejin dadin hadin kanmu
Auren da wata biyar kutta tasamu ciki aikuwa munsha murna sosai ba kamar ni dan ina son yara
Kutta takusa h
aihuwa surukar mu ta mutu wato maman su yohun munyi jimami sosai kafin mudawo nomal
Su papa ko sosai suke kawo mana cigaba a garin mu hakan yayiwa mutanen garin dadi sosai
Ranar asabar kutta ta haifi danta
namiji ai kamar na maidashi cikina saboda tsananin son danakewa yaron
Sosai nake kuda da ita komai ninake mata dan ko mamanta saidai ta kallemu nida ita kuma tanajin dadin zaman mu
Ranar suna aka sakawa yaron
suna joshow ,,sunan yayimin dadi sosai
Bayan suna aka ce za'a tafi kutta aikuwa na haukace musu nace bansan zancen ba , na ringa kuka nace babu inda zataje ta barni ni kadai ba sosai nake kuka
Gaban maman ta
na zauna ina kama kafar ta nace tabarmin kutta zan kula da ita
Kallona tayi sai taga nabata tausayi tayi murmishi tace shikenan ta bari
Aikuwa da sauri naje na dauki joshow na goya na kama hannun kutta nace mu
je part dina acen zata zauna
Dariya suke min ganin nazama kamar wata zararriya maman mu tace a su ingozi badai son yara ba ,,,ficewa nayi na bansu ban kula suba
Haka naci gaba da kula dasu kutta da joshow ,
komai ninake mata
Banju da papa ko ba karamin dadi sukaji ba yadda nake kula da yaron da soyayyar danake nuna musu
Haka mukaci gaba da rayuwar mu mai dadi har kutta tayi wata uku tukun na mata lalle kitso duk
mata saboda na iya sosai , na gyarata tukun papa yayo mata siyayya tashirya nida papa muka kaita part dinta ,muyi yar hira tukun muma muka dawo gidanmu
Kullin joshow na hannu na ina lalenshi , har yakai shekara da
ya da rabi , nina yaye shi yadawo wajena gaba daya , saboda lokacin banju aka kira daga kasar America donyin wani aiki haka suka hada kayansu muka kaisu legos nan muka jirginsu ya sauka ,
Sallama mukayi muna kuka
nida kutta su papa na mana dariya
Jirgi yasoma kira nan muka rabu sai tafiya sukayi jirginsu ya daga zuwa America , nan muka dawo gida cike da kewarsu
Naci gaba da kula da joshow wasa wasa su banju suka
shafe shekara uku a America sau daya suka zo ganin gida amma muna waya dasu
Da suka shirya dawowa nan banju ya kira papa yace zasu dawo gida gaba daya gashinan jirginsu zai tashi zuwa legos
Murna nasoma nace za
nbi papa legos yace a a namusu girki kawai nan yatafi ni kuma nayi girki na gyara joshow
Papa na xuwa legos ya zauna jiran jirgin su banju yazo ,,, abu kamar wasa har yamma ba su zoba abin yabashi mamaki
Yana
zaune nan yaji ana magana a spika da sauri ya nutsu dan yaji mai ake cewa nan mai magana yasoma da fadin
𝗝𝗶𝗿𝗴𝗶𝗻
𝗱𝗮𝘆𝗮
𝘁𝗮𝗳𝗼
𝗱𝗮𝗴𝗮
𝗮𝗺𝗲𝗿𝗶𝗰𝗮
𝘇𝘂𝘄𝗮
𝗹𝗲𝗴𝗼𝘀
𝘆𝗮𝘆𝗶
𝗮𝗰𝗰𝗶𝗱𝗲𝗻𝘁
𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲𝗻
𝗰𝗶𝗸
𝗶
𝗱𝗮
𝘆𝗮𝘄𝗼𝗻𝘀𝘂
𝘀𝘂𝗻
𝗺𝘂𝘁𝘂
𝘄𝗮𝘀𝘂
𝗴𝗮𝘀𝘂𝗻𝗮𝗻
𝗮𝗰𝗶𝗸𝗶
𝗮𝗻𝗮
𝗱𝘂𝗯𝗮𝘀𝘂
𝗱𝗮𝗻
𝘀𝘂𝗻
𝘀𝘂𝗺𝗮
A razane papa ya mike yanufi inda aka fada wajan gawawwakin ya ke budewa yana dubawa ,cen yaga gawar banju
da sauri yamatso yana fadin kanina dubawa yayi baiga kutta ba
Wajan masu jinya yanufa yana dubawa nan yaganta tana kuka an nade mata kai da bandej da gudu yayo wajan ta
Tana ganin shi ta sauko tace ina banju kas
a mata magana yayi sai ya kama hannun ta suka fito nan yakaita inda gawarshi take
Tana yin arba da shi yamutu nan ta yanke jiki ta fadi sumanmiya papa kusan haukacewa yayi saida ya dauko ruwa yazufa mata ta farfado
, tana kuka sosai wani doctor yaxo yace kuna da wanda ya mutune papa yanuna mishi kanin sa
Daukar shi yayi agadon nan suka fito aka sakashi a mato ya saka mutta da kyer yake dravin saboda zafin da zuciya take mishi
Allah ne kadai yakawosu gida
Suna shiga gida aguje na taresu ina oyoyo kanwata ga kanina ,turas nayi ganin kutta ta nufoni tana kuka sosai
Abin yabani mamaki sosai kasa daurewa nayi nace kutta lfy kike kuka ,
ai murna zakiyi da kuka dawo gida lfy
Papa ne yafito shima kukan yake sosai
Hankali na yatashi ganin suna min kuka kuma bamai min magana nima na ringa yin kuka bamai rarrashin wani
Papa ne yayi karfi hali ya
dena yace ingozi banju ya mutu accident sukayi na jirgi sai itace bata mutu ba
A zabure nake kallon shi da dauri na bude motar nan na ganshi a shimfide
Ihu na kurma ina shikenan family mu sai karewa sukeyi ya
nzu kaka da maman mu ne suka rage mana
Aikuwa yan unguwa suka shigo dan ganin mai nakewa kuka ,mugun ganin da sukayi suma nan suka ringa kuka
Kama kutta nayi muka shiga ciki akayi majami'a da banju cen suka
binneshi
Maman mu naji mutuwar banju ciwonta na zuciya ya tashi itama tace ga garinku nan
Wannan lokacin hauka ma nayi nida kutta har kullemu ake a daki saboda da gudu muke fita kamar sabbin shiga hauka ,,haka m
uke
Bayan sati daya na zauna saiga kutta da joshow suka shiga zama sukayi na share hawayen fuskar ta ina kallon su
Kutta tace haba yakamata kidena kukan nan ya isa haka
Kallon ta nayi sosai kafin nace taya bazan
yi kuka ba kutta yanzu fa kaka kadai ta ragemin duk duniya sai ita duk suntafi sun barni
Rungume juna mukayi muna kuka
Haka mukaci gaba da rayuwa ba dadi amma har yanzu ban haihu ba , ban damu ba saboda maman
mu tace itama tadau shekaru bata haihuba shiyasa ban damu ba
Joshow saida yacika shekara 12years tukun nasamu ciki ,, aikuwa sosai muke murna zamu karu
Kutta ke aikin komai ta hanani koda daukar cop ne nakai kit
chen haka nake zama na nida joshow idan yadawo daga school
Wata rana na haihu ya' mace zo kuga murna wajan papa sosai yake farin ciki harmu da kaka
Papa yace asa mata sunan mama na ,nace a a yasa duk wanda
yakeso
Papa sai yace to asa mata jenifer sunan kaka aikuwa kaka hadda kukan ta jin taji takwara
Haka mukaci gaba da kula da yaranmu jenifer da joshow
Jenifer shekara ta daya da rabi na haifi kaninta daga nan ha
ihuwar ta tsaya , nan suka zama su uku sosai muke kula dasu
Bayan wata shida kaka itama ta mutu munyi jimami kafin mudawo nomal
Haka muke tare har yaran suka kai aure muka hada jenifer da joshow aure ganin s
una son junansu
*WANNAN SHINE ABINDA YA FARU LOKACIN DA KUKA. BAR GARIN DAJI*
Inna ko kuka take sosai tace Allah sarki papa na su mamana duk sun rasu ashe
Mama tace eh yaya maryame sunfa rasu sai gashi dalili
n jikar mu ta hada familyn masha Allah kuma mundazama musulmai Alhamdulillah zamuce
Daddy da abba da ubbu suka amsa da ameen gaskiya munji dadin haduwar wannan family ashe batan ameera alkhairi garemu masha Allah
Muh
ammed ne ya mike yace to daddy zan tafi gida ga ikram nan bayan kwana biyu zanzo daukar ta
Daddy yace baka tsayawa akira la'asar da yamma sanyin marece saika tafi
Murmishi muhammed yayi yace a a zanje gida nay
i wanka ne ko wanka banyiba nazo to zan wuce
Inna tace dan kan uba shiyasa ashe nakejin falon yana tsami ashe kaine kazami , shiyasa ka kasa samun matar aure , yowama zai auri miji kazami ,saidai irinka kalle ka k
amar wani dodo duk kayi baki kamar kayi birgima a toka tana banka mishi harara
Dariya sukayi yan falon ameer yace kai inna ke yanzu wannan ranar ma bazaki hakura da masifar nanva koda yake anyo gado ai , yana ruf
e baki
Inna ta hannu biyu aka ta innalillahi wa inna ilaihin raju'un Allah ameeru yau ni kake zaki shikenan yanzu Muhammadu kana ganinshi yake zagina , tana goge fuska da sharen zaninta
Daddy yace yi hakuri ai yau bam
ai rabani dashi dukan kawo wuka zanmiki tinda ya tabaki , da hancin sa kamar karas irin na naki
Inna tace kaima kaci bindin ubanka , nice mai hancin kamar karas to wllh na kare zama daku agidan ai Alhamdulillah t
inda Allah yakawo min dangina , saimu koma asalina cen nazauna ana gama bikin fauziya da safiyanu zan tafi ,,badai ni kukewa baa ba zaku ga hukuncin dazan yanke
Abbu ne yace yi hakuri inna bafa haka yake nufiba kiy
i hakuri innar ameera
Murmishi tayi tace kunci darajar ameera , saida tafi amma na fasa zanje dai ziyara
Muhammed yasake cewa to sai anjima mommy natafi nayason hajara ta rakashi amma yana jin kunya
Mommy tace
to kabar mana ikram anan yace to gatanan ,
Harya kai bakin kofa ikram ta waiwayo