Showing 105001 words to 108000 words out of 184731 words

Chapter 36 - AMIR DA AMIRA complete

27 Aug 2026

52

fita waje domin tacewa,, su mama ", Ameera bazata iya haihuwa da kanta ba sai an bata c.s. nan tafito waje tana tunkarar wajansu mas

Da sauri sukayo wajan ta suna daha baki wajan fadin ,

doctor ya jikin nata ta haihu '

Numfasawa,,, Doctor din tayi tace a a gaskiya bazata iya haihuwa da kanta ba sai an mata c.s . Dan yaran sun girma a cikinta

Da sauri joshow yace in akayi c.s din babu

abinda zai faru

Doctor tace gaskiya ban saniba muje kasa,, hannu saboda tana jin jiki

Har sun juya zasu tafi wata nosee , tafito da sauri tace ma kizo sauri baby yatafo

Da gudu gudu doctor din tayo

room din " ta rufe kofar

Joshow kam ya tsorata sosai sai,, kashe kunne yakeyi " yaji kukan baby

A cikin room din kuwa ameera tana hada sauran kafinta tana kiran sunan Allah ya kawo mata dauki

Dai

dai lokacin kuma umma,, tagama nafila tana addu'a wa ameera Allah ya kareta ya taimake ta aduk halin da take ciki ta shafa fatiha

Suma su ameer da hajara a lokacin suna mata addu'a hajara hadda kukan ta suka s

hafa fatiha

A lokacin kuma ameera ta haifo danta qato dashi tana haifoshi aka , daukeshi " suka bawa wata nosee ta gyara shi

Wani sabon ciwon ya zowa" Ameera wannan karan da karfi a jikinta tana addu'a s

una fadin ta yi nishi

Da karfi tayi nishi sai ga yarta mace ta fado suka dauke itama aka gyara ta

Su mama na daga waje sukejin kukan baby's murna suka kama yi sosai suna jiran a fito musu da baby's

din

Saida aka gyara ameera,, suka mata wanka sosai suka gasata " saboda taji dadin jikinta,, kafin suka gyara wajan tsam kamar " baa yi wani ,, abu ba a wajan " nan suka fiddo ameera da yaran ta

Da sauri

joshow ya karaso " wajansu mika mishi babyn akayi aka bawa mama daya , nan akayi gaba da ameera zuwa,, dakin hutu

Kukan baby's dinne ya tashi su marus da beauty ,, aikuwa suna hada ido da baby's din,, da gudu

kowa yayi wajan daya suna dariya

Marus yace yauwa,, naji dadi mommy ta haifo min brother ,, mai kama dani

Beauty ma tace,, nima kaga sister na sai nake mata kwalliya , mai kyau nima mai kama dani

Kallon baby's din mama da joshow sukayi " suna ta al'ajabin wannan kamanni,, haka

Joshow ya kalli macen yana kura mata ido babu abinda yaraba ta da jenifer har farar fatar,, kamar jenifer ce tayi kaki yana shaf

a fuskar babyn , yace beautiful ,, kina kamar jenifer na

Mama , ma kallon su tayi tace kamar ma ,, harta baci sosai suke kamanni da jenifer

Wata nosee ce tafito,, daga inda aka kai ameera nan sukayi wajan

ta sukace doctor zamu iya ganinta", tace eh kushiga ta kusa tashima nan suka nufi dakin

A kwance ", suka sameta karasawa sukayi beauty zata tasheta, joshow yace no kibari zata farka ne nan tayi baya ta zauna sun

a jiran tashin ameera

Baa fi minti goma ba " tasoma motsa hannun ta mama,, tadawo kusa da ita , ta rike hannun ta

Bude idon ta tayi akan mama, tana kallon kowa

Murmishi ta wa su marus nan sukayo

wajan ta suna fadin mommy sannu kintashi saimu tafi gida,, ko

Mama ta taimaka mata " ta zauna tana kallon su

Joshow ma murmishi yakewa ameera ganin yaran data haifo amma lfy lau take

Mama ta mike

ta hado mata tea mai zafi ta matso kusan ameera tace,, amshi kisha wannan kinji daughter ,, zakiji " dadin jikinki ma muso ta amsa tashanye duka sai zufa take hadawa"

Joshow ne yakaro wa A.C. karfi dan taji sanyi

sosai

Yaran mama ta mika mata,, suna jin hannun mahaifiyar su suka tashi , nan suka soma kuka kallon ameera keyi,, itama tana hawayen , tana ganin yadda namijin ke kama da ameer rai da rai

Su mama kam

mamaki ne yakamasu, ganin tana kuka

Mama tace daughter lfy daiko kike kuka keda, zakiyi farin ciki da samun kyawawan diya haka gasu , kamar ba twins ba

Ameera tace mama kuna da ruwan zam zam ne

Mam

a tace a kasuwa dai naga suna siyarwa masu irin addinin ki

Ameera tace a kira min doctor din

Nan joshow yafita kiran doctor babu bata lokaci suka shigo tare,

Ameera ta kalli matar ta mika mata hann

u alamar ta karaso ,, matsowa tayi ameera tace,, anty kina da waya

Doctor din tace eh tace please bani zan duba wani abu ne

Ba muso ta bata

Nan ameera ta tubuta sunan zamzam nan yafito gasu nan a j

ere kafin ta kuma rubuta dabino nanma,,, yafito ta nuna mata tace tana son akawo,, mata su

Doctor din tace muna dashi anan kafin tace amma ke Muslim ce

Ameera tace eh ni musulma, ce inason bawa wa

nnan yaran kafin susha nono

Doctor din tace nima Muslim ce har mijina da yarana bari,, na kira yarona yazo dasu saiya " rada musu suna ya misu kiran salla

Cikin jin dadi ameera ta rungume doctor tace than

k you nagode sosai

Nan doctor ta kira yaronta yazo dasu aka bashi yaran

Kiran salla ya fara musu a ko wani kunen kafin ya tauna dabinon nan ya diga musu " a baki aikuwa suka tsotse tas dan yunwa suke

ji " kafin yabasu zamzam din sukasha

Dagowa yayi yana murmishi yace wani suna za'a saka musu

Ameera tace macen inason a kasa ,, mata ikram

Namiji sai kuma tace ya sunan ka kai

Yace ni sunana Muh

ammed

Ameera tace to kasa mishi Muhammed sunanka,, dama sunan kakansu ne

Cike da farin ciki yace to sister godiya nake nan ya rada musu nan , Muhammed da ikram yana jin dadi an mishi takwara,

Su kuwa

su mama kallon ikon Allah sukeyi dama idan musulmi ya haihu haka ake saka suna ,, lalle kam musulinci da ban yake

Doctor din tace kina da waya kibani nember ki

Ameera tace eh amma yana gida kawo nasa miki

nember ,, idan na je gida zanga kiran

Mika mata tayi " sata mata kafin ta mike sukabar dakin

Mama ta matso kusan ameera tace daughter haka ake saka suna idan mai addinin ku ya haihu

Murmishi ameera

tayi tace haka akeyi mama

Mama tace mu sai anje wajan abin bauta ankai yaron , yayi kwana biyu acen ana mishi addu'a tukun sai asa mishi suna

Da mamaki ameera ke kallon mama tace tab lalle kuna, wahalar

da kanku mama

Sallama aka basu suka yo gida

Haka aka yita hidima da ameera da yaran ta sosai takajin dadi ,, ganin yadda dangin joshow dana anty karima suke kaunar yara

Gasu lafiyayyu masha Allah

da kuzarinsu gwanin burgewa , a haka har akayi suna

Joshow ya tambayi ameera yaya akeyin sunan a garinsu nan tafada mishi komai ,, ya nemo Muhammed ,, suka kai kayan suna gidan su Muhammed su uku suka yi fatihar s

unan twins , kafin joshow yadawo gida

Kayan baby's kam ameera tashasu sosai dangi ko kawo kyautar,, shi ta kaya ko kudi

Su ameera baki yaki rufuwa tana jin dadi sai ta kuma yi tunani wai wannan a cikin ba

re ne take,, ake mata wannan hidimar ,, to inda a wajan dangin tane ya zai kasance " girgiza kai tayi ta maida hawayen ta,, tana fadin ke zuciya ki nutsuwa " wannan ameera bata da,,, bace kizama " jaruma dan akwai aiki ja

agaban ki,

Cikin wannan satin, Ameer cikin farin ciki yake duk inda yayi sai murmishi ita kanta hajara , taji tana cikin,, farin ciki sai godiya sukewa Allah ameer kam "dayaje wajan mlm Ahmed har,, kudi yaringa ya

rabawa mutane,, sosai sukaji dadin ganinshi haka

Dan kullin cikin damuwa yake shiyasa suka tayashi farin ciki duk da basusan meyasaka shi farin ciki

Mom ma taga ameer na farin cikin hankalin ta yasoma kwanciy

a ganin dan nata na cikin fara'a

Suna zaune da daddy da mom daddy yace gobe zaije kauye, saboda a saka ranar bikin hajara da ameer sai an saka zasu fada mishi nan mom tayi na'am da shawarar da daddy ya yan

ke

Raju, ne shida shugaban nasa,, suna tsafinsu " so sukeyi a daren nan su aikawa ameera bakaken aljanu su zuke mata jini daga baya kuma su dauketa " su maidata irin na anty karima ",

Sai hado kan aljanun su

ke suna fada musu yadda zasu kamar yadda sukabi suka dauka na anty karima ana gama musu jawabi nan suka bace,, sai gidan su joshow

Ameera na zaune tana bawa ikram nono ganin gilmawar,, wani bakin abu tayi

Bata ankare ba taji kamar an tsikara mata allura ,, runtse ido tayi tana fadin la'ilaha ilallahu Muhammad (S.A.W)

Da sauri joshow yakaraso inda take kafin yazo harta kai kasa da karfi yace ,Ameeraaaaa......

*i

na godiya da karfafamin gwiwa dakuke da addu'o'i ku agareni Allah yabar kauna masoya ina yinku over*

[28/10, 14:23] MRS. MU'UTASIM: *

🌟

AMEER DA AMEERA

🌟

*

*RUBUTAWA DA TSARAWA*

*MAMAN NUSAIBA CE





*

💫💫

*

🅙



ARUMAI

🅦



WRITERS

🅐



SSOCIATION

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login