Showing 150001 words to 153000 words out of 184731 words
razane yadago jin muryar da bazai taba ,, mantawa ba juyo da ita yayi , kawai ya rungume ta sosai yana fadin Alhamdulillah , Alhamdulillah , Alhamdulillah
Allah abin godiya ,
Inna tace kai ameeru ,, bakada hankali ka rungume matar mutane kana ,, cewa Alhamdulillah , ko kasha giya ne
Dagota yayi ya juyo sa fuskar ta ta yadda zasu ganta idan yacire niqaf din , cire
niqaf din yayi ,,yana dariya hade da kuka yace ,Inna kin ganta wife na ce tadawo garemu dama ,, nace ba mutuwa tayi ba
Da sauri ,inna yayo wajansu tana kuka sosai tace allahu akbar ,, yarinya ta dama kina raye
bamu sani ba , Ameera ina kike duk wannan tsayin, lokacin ,, sakin ameer tayi ta rungume inna ,, suna kukan farin ciki ,, abin tausayi
Sakin inna tayi taje wajan daddy ta rungume shi tana kuka ,, tace daddy kun dau
ka na mutu ko , ,, rungume daddy yayi yana share hawaye ,, yace daughter ,, ai bamu yadda kin mutu , ba kawai , dai mun barwa Allah komai ne
Sakin daddy tayi ,,tazo wajan mommy ta rungume ,, kuka mommy tasa sosai
tana fadin Alhamdulillah ,, Allah mungode maka daka dawo mana da yar garemu
Sakin mommy tayi da gudu hajara tazo ta rungume ameera ,,, tana kukan itama tace anty ameera ta ,, dama nasan yar uwata baki mutu ba kina
nan " a raye Alhamdulillah
Ameera ta gaskiya ne kanwata gani ,, nadawo ahlina
Sakin hajara tayi taje ta rungume Fatima da fauziya a dare ,, sosai fatima ke kuka
Tace yar uwa ta dama kina raye ashe kai A
lhamdulillah Allah nagode maka ,,
Maman anty karima ko , Inna ce tajuyo aikuwa da karfi tace maryame ,,, da sauri inna ta kalli inda aka kirata ,,, cike da al'ajabi tace , ingozi
Maman anty karima da sauri taz
o ta rungume inna nan sabon kuka yatashi mama sai shafa inna takeyi tana fadin ,, yar uwa ta dama kina raye ashe nayi kuka harna gaji ,,da zubar da hawayen rashinki
Dagota inna tayi tace ingozi ina nan a ra
ye ashe kema kina nan suka sake rungume juna suna kuka
Nan fa kallon yakoma kansu ,, Fatima ce takasa hakuri tace inna wannan din yar uwanki ce ,, naga kuna kama sosai
Dagowa inna tayi tana share hawaye tace
" eh wannan labarine mai tsayi yar uwa ta ce uwa daya uba daya
Baban anty ma ganin yasashi zumar tsaye sai cen , yadawo daga hankalin yace maryame ,, ina shareef , ina dan uwana
Da sauri inna ta kalle shi ta
ce papa , kaine
Baban karima yace eh maryame nine ,, yanzu duk mun cenja wannan sunan sunana, Usman ugozi kuwa,, sunanki gare ta ina shareef maryame,,
Share hawaye inna ,tayi tace ai ya dade ta rasuwa tin ameera t
ana yar shekara uku ya ,rasu ,, kullin zancen shi papa da gaye , harya mutu
Mama ce ta matso kusan Usman tace ,,wai usman kana nufin shareef ,dan uwanku ,, shine mijin maryame , kuma kakan ameera
Jinjina kai
yayi yace sosai makuwa ,,
Su daddy kam abin al'ajabi ,, da mamaki da komai sukewa su inna
Daddy yace , wai ina kina nufin kice mana wannan duka dangin mune da , naki dana " baffa ne
Inna ta bace majina tac
e , eh muhammadu wannan sune ahalinmu nida bananku
Sai alokacin ameer ya kalli doctor aisha da suma ,, suke kallon ikon Allah ,, Ameer yace a a kakata wai dama harda ku akazo
Muhammed yace eh tare mukazo " ashe k
aine mijin na ameera ,, a lokacin dazaka dawo kano kana tafiya sukazo " da alokacin zaku hadu
Doctor aisha tace kai masha Allah dama ameera matarka ce
Murmishi ameer yayi yace eh kakata kowa ya zauna tukun
Zaz
zanawa , sukayi farima tace wai ameera ,, ina cikin da kika tafi dashi
Kallon Fatima ameera tayi , sai kuma tayi murmishi ,,ta dago da muhammed,, ta kama hannun ikram tace ,, wannan sune ckin dana tafi dashi " yan bi
yu na haifa , sunan daddy da sunan momsy na ,, garesu
Ai kafin kowa ya taba su ameer , ya yace kuzo nan yaran albarka , Ikram dama ita so take yace tazo da dan gudun su suka nufi ameer
Saukowa yayi daga kan k
ujerar , y durkusa ,, bude musu hannu yayi suka shige jikin sa,, Ikram tace daddy cike da murna ameer yace na'am my daughter ,, na ashe dai ,, ke jinina ce shiyasa ganin farko " kika makale min , nima kamar na sace ta
naji ,a lokacin ashe jinina ce
Doctor aisha tace ,, haba koda naji fa yarinya daga ganinka ,,taki yarda ku rabu ashe ita dumin babanta taji
Sakinsu yayi yace kuje mommy na kiranku ,, wajan mommy muhammed ,, yayi
yana dariya ganin suma dariyar sukeyi , Ikram ko tana jikin ameer , ko matsi batayi ba " itadai ,daga anjima tace daddy shikuwa ,, Ameer yabiye mata sai yaketa amsawa
Daukar muhammed mommy tayi , tana fadin mai g
ida oyoyo ,,nan kowa yayi ta daukarshi ,, Ikram kuwa ko kallon inda suke bata yiba ,, tayi kwanciyar ta , jikin babanta ,, duk wanda yace zo ikram "" bata fuska takeyi tace daddy ta dago ta kalli ameer ,, shafa kanta
yake yace daughter ,,kwanta abinki " idan kika huta sun ganki
Hajara ko murna kamar tayi rawa haka takeji sai rungume ,ameera takeyi tana shafa fuskar ta
Murmishi ameera tayi tace , to mage ashe dai baki dena s
on jiki ba ,, yar dariya hajara tayi tace ,ai kinfini ingaya miki ,
Doctor aisha ce ta kalli ikram tace babyn mommy zo mutafi mana kinsan anbani rikonki " tin kina jaririya to yanzu munzo gun babanki ban saniba kozai
banike
Murmishi ameer yayi , yace ai indai nine " bakida matsala ,,dago da ikram yayi yace daughter , maza jeki wajan kaka ,
Kallon shi tayi zatayi kuka muhammed ,, yace babyn mommy ,,zo nan juyowa tayi,, ganin
muhammed ne yasa ta sauka daga kan ameer ta tafi inda muhammed yake,, tace daddy , daukarta yayi yace kinga mommy na kallon ki maza jeki wajan ta , mikawa doctor aisha hannu tayi " daukar tayi ta rungume tana shafa kanta
har bacci ya dauketa ,
Baba laraba ce tashigo gidan ,da sallama daga,, kasuwa take ,niki niki da kaya ganin falon cike da mutane,, tace sannunku baki , ,, dagowa tayi zata wuce bazata ga ", da sauri ajiye kayan hannun
ta ,, tace hajiya koda gizon ne dana saba yi ameera nake gani ", mommy tace babu gizo itace
Wulli baba laraba tayi da c, kayan hannun ta ta nufi ,Ameer tana kuka ,,, itama ameera mikewa " ta taro baba laraba ,
rungume ta sosai
Baba laraba tace ya'ta kece ashe , ba gizo bane ashe zan sake, ganinki yar lelen ameer ' waiyo Allah Alhamdulillah ,
Share hawaye ameera tayi , tace nice baba laraba " gani nadawo gareku ba mutuwa
nayi ba ,,, ina raye
Sakinta baba laraba tayi, tana dariya sosai najin dadin dawowar " Ameera cikinsu ,, mommy tace baba laraba ki mana girki dayawa ga hajara ,nan zata tayaki da fauziya " Baba laraba tace to hajiy
a nan tayi kitchen din don , daura girkin
Daddy ne ya kalli ,, Inna yace inna ashe dai ameera tana wajan danginta ,, to amma daughter ya akayi suka tsince ki , keda kukayi accident ,a kan hanyar ku ta zuwa nan
Zama ameera ta gyara , tace daddy lokacin da motar mu , tashiga dajin dake gefen titi , kawai gangara wa nake ina daga kwance , wata bishiya " na buga daga bansan inda nake ba, ashe lokacin dana buga kaina ciki
n wani kogin dake " gindin bishiyar na fada yayi ta tafiya dani har kogin su yaya umar na bayan gari " anan ya tsinceni ,,,da farko sun dauka ni anty karima ce " saboda na manta komai na rayuwa ta na baya , shiyasa sa
ida " nadawo haiyacina , tukun nace bani bace karima ,, nan ta kwashe labarin komai tabasu har cututtukan datashayi ,, da sokar ta da akayi da wuka " da mutanen garin da sunfi rabi duk sun musulinta ,
Su mommy sai kuk
a ,, suke jin abubuwan da ameera ta fuskanta , amma Alhamdulillah tinda har mutanen garin sun musulinta , kadan ne basu musulinta ba
Sake rungume ta , Inna tayi tace Alhamdulillah jikata Allah yakara daukaka musulin
ci akan kafirci , ashe kece hasken ahalina , Allahu akbar Allah mai girma Allah Allah yakarawa annabi daraja s.a.w. ,,,, yan falon sukace ameen
Mommy tace inna zamuso ,, kibamu tarishin ku na rayuwar ku dakukayi a bay
a kuma ya akayi kuka baro garinku kuka dawo jahar katsina ,,da zama
Zama inna ta gyara tace , kozan baku labarina ,, sai kowa yazo dan kowa yaji ni da babanku suwaye mu
Da sallama tashigo falon ,,hijab din
a hannu har dan kwalinta ,, tana fadin babyn momsy baby ina kike
Kowa kallon ta yake cike da tausayin yadda take kuke
Da gudu ameera , ta nufi ikram tana " fadin waiyo momsy na ,, momsy na rungume juna sukayi
ikram ta