Showing 183001 words to 184731 words out of 184731 words
gidansu khadija
Baban khadija ya tarbesu da farin ciki ya shimfida musu taburma suka zauna aka gaisa sosai
Daddy ne yafada
mishi abinda yake tafe dasu ya nuna mishi alhaji hashim shine baban yaron da auri khadija
Sosai baban khadija yanuna farin cikin sa yace to inbanda abinka muhammed ai khadija yarka ce dagacen ma dasaiku bashi basai kun
zo neman izina ba khadija zatama jininku dama mu baki daya munzama yan uwan juna ba komai nabashi Khadija
Sosai su daddy sukayi farin ciki daddy yace za'a hada bikin dana hajara , Baban khadija yace bashida damuwa hakan ya
yi nan suka mishi sallama sukayo gidan basuko zauna fa suka juya zuwa kano
Suna zuwa gida bayan yahuta yafadawa su mommy komai itama ameera yakira yafada mata yadda sukayi
Ameera da daddy yafada mata har sujjadar g
odiya ga Allah Allah tayi ,shidai ameer kallon ta yayi yana jin yadda sonta da kaunarta ya mamaye dukkan sassan jikinsa , shima yataya farin ciki
Alhaji hashim na zuwa gida shima yafadawa mom din aliyu sosai tacika da
farin ciki itada aliyu
Yaune jamila tagama wanka ameera da fatima sukazo daukarta basu jimaba aka hada musu kayansu suka tafo gida baba direba yakawosu gida
Ameera da fatima suka tayata gyaran gida jamila ta shirya
kayansu ko ina suka gyara tsaf tukun suka mata sallama kowa yashiga part din sa
Akwana a tashi yau ne bikin su hajara
Ameera ce tafito da wani kofi a hannunta tana hade rai ta nufi dakin da amare suke
Ka
llon su tayi tace kunsandai bana wasa da yaro ko to kowacce ta amsa tashanye tinkafin na kira inna tazo
Da sauri khadija ta amsa tace nidai zansha aminiya ta basai kin kira inna ba ta kafa maganin abaki ta shanye tas
Wurgawa Hajara harara ameera tayi tace uwar yan taurin kai ki karba kisha anjima za'a yi diner so kike ana miki shiri wanda bazaiyi kyau ba
Kamar hajara zatayi kuka ta amsa tana runtse ido tashanye ta mikawa am
eera kofin , murmishi ameera tayi tace ko kufa wannan fa gata nake muku amma kuna min wulakanci irin na amare , dariya sukayi tukun tafita ta rufo musu kofar
Da misalin karfe 2:00 pm na ranar asabar aka daura auren *haja
ra ahmed da muhammed usama sai na khadija hambali da aliyu alhaji hashim* akan sadaki naira dubu dari biyu biyu , sosai anguwar tacika da mutane
Anan aka fadawa yan gidan an daura auren hajara ko kuka takama yi , ita
kuma khadija tagumi tayi tana kallon ta tace kefa garace hajara maimakon kiyi addu'a sai kike kuka
Hajara tace kukan farin ciki ne nakeyi ,Khadija tace kinga ni banyi kukanba
Hajara tace zakiyi aiba sosai kukayiba sh
iyasa bakiyi kukaba
Shuru khadija tayi tana jin maganar hajara
Da yamma aka shirya amare sunsha ado ga kyau kamar kasacesu ka gudu , fitowa sukayi a aka soma daukar kawayen amarya
Ni kuma ina tsaye ina dube
dube naga wata mota zan shiga sai naga tawagar *fans din ameer da ameera* ansha anko kowacce takashe nan aka shiga mota sai wajan diner
Sai kusan magarib aka tashi kowa yayo gida
Washe gari akayi walima da da da
re aka kai amare gidansu nasiha sosai aka musu tukun kowacce aka barta da mijinta (to hajara da khadija Allah yabada zaman lfy)
Bayan biki ameera da ameer hadda su umma duka dai family sukaje garinsu inna sosai ameera
taga canji duk sun musulinta anyi masallaci da
islamiya kowa kagani a garin abin burgewa hakan yakara faranta ran ameera da family ta
Kwana su goma tukun suka dawo gida aka cigaba da rayuwa mai dadi
BAYAN SHEKAR
A GOMA SHA BIYAR
Wata na gano tana saurin fitowa daga wani part da bulala a hannun ta tana bin wata karamar yarinya
Ita kuma yarinya taki tsayawa sai gudu takeyi
Shigowa akayi da gidan ya tifo da sauri ya t
areta ta dauke yace haba wifey wai ummin nawace zaki daka har kika sauri haka kuna tsare , hararar shi tayi tana fadin dama aikai kake daure mata gindi tana rashin ji to bazan daukaba
Tajuya tashiga ciki binta yayi
a falo yasameta tana kwashe kayan wasan data tara
Sunkuyawa yayi suka kwashe kafin yazauna yace mamana mai kikawa mommy naki
Yarinyar tace daddy wannan abun ne fa na zubar shine zata dakeni
Shafa kanta yayi
yace to shikenan kidena kinji ,da to ta amsa yace ina yayanki yake tace yana gidan granny dukansu dai kadai ce banje ba ,Ameer yace to jekiyi wasa zanyi wanka idan nadawo saimuje cen din ko
Tana fadin ameer ya ja
nyo ameera jikinsa yace duk fushin ne wifey na kefa yanzu kinzama babba kidena fushi
Dukan wasa takai mishi tace amma ai duk girmana a wajan ka ni yarinya ce
Kuncinta yaja yace hakane baby na muje kiyimin wanka
ko , tasukayi , sukayi daki zan shiga ameer yace koma ki huta maman nusy
Nace to
Tammat bihamdulillah anan na kawo karshen littafin *ameer da ameera* Allah yasa muyi anfani da darasin dake cikinsa , kuskuren dan
a yi Allah ka yafemin
Shin acikin wannan littafin wani guri yafi baki dariya
Wani waje yafi burgeki
Wani waje yafi baki haushi
Wani waje yafi baki tuasayi
Ina jiran amsar ku fans
ππΌππΌππΌππΌ
Muhadu daku a sabon novel dina mai sunan *hafsat*
*Takuce har kullin maman nusaiba
β
π»
*
*Nan zan tsaya*