Showing 159001 words to 162000 words out of 184731 words

Chapter 54 - AMIR DA AMIRA complete

27 Aug 2026

23

yaga kayan yara tofa saiya siyo yakawo

Idan yazo gida sai anisha tayi ta fada tana cewa , yacika gida da kayan yara wannan ma sun isa

Ida anisha ta fadi haka ka

mar ta kara zuga " papa ne danshi farin cikin da yakeji da kaunar babyn a ganinshi babu abinda bazai siya mata ba saidai inbai zoba , kasuwa ,, koda a kasar wajene saiya sanya an kawo mishi

Anisha ta kasance masifa

ffiyar mace ,, amma tana da dadin kai bata iya rike mutum a rai koda kuwa yabata mata rai , idan mutum ya bata mata rai takan rufeshi da masifa bata barin bashi ko daya ,, shiyasa papa yake lallaba ta , idan yamata l

efi ko har zukewa take tace kawai suba hamata iska itada papa

Shi kuwa papa idan ta fadi hakan saidai yayi ta dariya , ita kuma ita taga haka sai tayi ta fada , ko tace zata bar mishi gidan ,in yaki tanka mata t

ana fada

Sai tagama sai ya zaunar da ita yabata ruwa mai sanyi saboda zufar da take hadawa intasha , sai yace kinsan idan kina yin wannan fadan mugun burgeni kike wani sishirtaccen kyau kike kamar yar shabakwai haka

kike koma gaskiya ina sonki

Idan papa ya fada mata haka sai tayi ta dariya daga nan ,,shesu shirya haka suke rayuwar mai tsabta

Wata lahadi anisha ta tashi da nakuda , nan sukayi asibiti tasha wahala kafin

ta haifi yarta mace kyakkyawa ,, kamar babanta

Ana fitowa da babyn papa ya masa shida baban yohun har shima yohun din da mamanshi , sosai sukayi murna ,, na samun karuwa , tinda yohu yaga babyn din nan ya dauki so

n duniya ya daura mata ,, a hospital din ma shi ya rungume ta har aka fito da anisha zuwa dakin hutu

Kwanan anisha daya aka sallamesu ,, suka koma gida ,sosai ake taya papa da anisha murna kullin gidan , nasu a cik

e yake da dangi sosai , duk da cika mutanen dake gidan amma yohun yana makale da jaririyar nan baya zuwa nan da nan ko yan , barka ma insunzo baya bari abasu sai yace , bazai bada sister dinshi ba a tafin mishi a ita



Idan yafadi haka saidai anisha da mamansa su mishi dariya a haka har aka zo suna ,

Papa yace a saka mata maryame wato dai ,sunan mahaifiyar , annabii isa a.s.m.wanda ake kira da jesius ,saboda su papa littafin

suke aiki dashi da kuma balbu gunkinsu ,

Haka aka saka mata sunan maryame wanda musulmai , suke Kira da (nana maryam , ko maryama) ba kowa bace wannan jaririyar nice , wannan yaron kuma shine baffan ku ,

Ameera

na dariya tace iyee ashe inna gado mukayi granny din su daddy akwai fada

Inna tace ai bakiji komai ba kiyi shuru na gama

Inna tacigaba da fadin

Tin wannan lokacin yohun shike kula da maryame ,, sosai

yake sonta hakan kuwa ba karamin dadi yawa su papa ba ,

Maryame nada shekara daya maman yohun ta haihu shima namiji ne ansha murna sosai shima , amma yohun yace shifa bazai koma gidansu ba anan, zai zauna ,, ba

bansa yace , shikenan duka ai dayane,, aka kawo masa kayansa duka sosai anisha tayi murnan barin mata yohun da akayi ,, nan taci gaba da kula dasu

Bayan maryame takai shekara uku , anisha itama sake haifan wata mace ,

aka saka mata suna ingozi wato maman karima

Haka suka tashi cikin so da kaunar iyayensu kamar yaran mutum daya haka suke

Yohun ya takura akan shifa saiyakai , Maryame sa school haka tasa papa yace ya saka

maryame a school , hakan yayiwa yohun dadi ,,dan dama kullin idan yazo school sai kajun yana da kanwa ahima yar uwanshi mai kyau ce idan yafadi haka sai sumishi dariya , banza yakeyi dasu , yace to saiya kawota ,shiy

asa ya nace sai ansaka maryame a school

A tare suke zuwa ,shi yake mata wanka ya shirya ta , Anisha batada damuwa da shirin su zuwa school shi yake shiryasu su tafi abinsu , shakuwa sosai tashiga tsakanin maryame d

a yohun , kamar ciki daya suka fito ba kowa na school din bane yasan ba, yaya da kanwa bane maryame da yohun ,,haka suke rayuwar su yohun nabawa maryame kulawa ta musammen

Bayan wani lokacin maman yohun tasake

haifan wani namijin aka saka mishi suna papa wato sunan ma haifina ,, yanzu mun kasance mu biyar ne maza uku mata biyu

Hakan yasa ingozi ta koma wajan maman yohun nan muka dawo mu biyu a wajan anisha mahaifiya

ta

Haka mukaci gaba da rayuwa har muka girma alokacin yohun nada 25years ni kuma ina da 18years , banju dana 17years , ingozi nada 15years papa shine karamin mu yanada shekara 12years , haka muke kanmu a had

e sosai iyayenmu ke jin dadi ,, idan za'ayi taron wajan abin bauta yohun ne agaba ,tare dani duk inda yake nima ina nan ,,haka yasa sosai mai tsananin gaske tashiga tsakanin mu nida yohun

Alokacin nima nayo gadon ma

ma tace anisha bana barin bashi,, kullin muna fada a school akwai wata wadda tace tanason yohun , aikuwa abin yabata min rai ,,dama yar ajinmu ce , dan haka na kudurta araina sainayi maganin ta ,, baa tabani bama inayi

bare aka shiga gonata ai abin nema yasamu ,, nan na kira ingozi na fada mata ,, itama dake tana da fadan sosai taringa cika tana batsewa ,,saidai fa duk fadan ingozi batakai ni ba ,, ni har nafice maman mu ma a mas

ifar fada

Mutanen gari sukance wanda ya auri maryame ya auri bala'i idan mutum yafada min haka toko yaro yaje gaban uwarsa saina bishi na, mishi duka ", idan kuma daidai nine sai mu yini muna dambe bana gajiya

I

ngozi nazuwa muka nufi haryar da yarinyar take zuwa , muka zauna zaman jiranta tazo muyi mata duka ,, cen sagata tazo

Saida ta nufi wajan wani lungu na hanyar gidansu muka tare ta

Cike da masifa nace ke dan

ubanki , ni zaki kalla kice wai kinason yohun ,, ni sa' arki kice ko kinga ina wasa dakene

Yarinyar tace oho so dai ina sonshi ,, kuma ko mutuwa zakiyi saina aureshi

Jin haka yasa ingozi balla mata wani

zazzafan mari har biyu tace ke yar uwan tawa kike fadawa magana to yau zanga mai kwatarki ,,,a wannan wajan

Da sauri ta dago tanason ramawa ,, nima nakara mata biyu ai tuni ta gigice , nan tayo kan ingozi dambe a

ka kama ,, batasan munfi karfinta ba ,, nan muka mata duka har suma tayi amma bamu dena ,, dukanta ba dan alokacin raina daci nakejinsa idan ban karya mata kafa ba ,, saida mukagaji dan kanmu tukun muka barta mukayi harya

gida

A hanya ne muka hadu da baban yarinyar ,, bamu kalleshi ba muka fice ,, sai kawai yace ku wannan mafadatan yaran , kuzo nan dan ubanku marar kunya

Wani bakin ciki ne yarufeni jin anzagi ubana ,,idan ana

son ganin zallar masifata to azagi papa nan ko kwana ,zaayi ana fada to bazan bari ba ,, dawowa mukayi kamar wasu na Allah ,, muna sumkuyar dakai mukace gamu

Kallon mu yayi yace , ku bakuda kunya ko kuna ganin

mutane bazzaku ce good morning ba saiku wuce ,gaba koda yake ai dama gidanku ba tarbiya ce daku ba sargantattu , , ne ku

Ingozi ta yunkuro zata mishi rashin kunya na rike hannun ta ,, kaina a kasa nace kayi hakuri

baba zamu gyara

Harara ya banka mana yace ta ina zaku gyara kuda kuka taso gidan rashin tarbiya nan yajuya tafice ,

Da sauri nacewa ingozi maza dauko mana duwatsu daidai jifa da gudu tayi gefen hanya ta

kwaso dayawa bayanshi mukabi , ganin munkusan kamoshi ,, aikuwa kuma soma jifanshi ba saurarawa

Yana tafiya kawai yaji ana mishi ruwan duwatsu ,, yana juyowa ingozi ta aika mishi jifa sai a goshinsa wani a bakinsa

, nan da nan wajan yafashe , muna ganin yadda hakan muka gudu , Gida ingozi tashiga gidansu nima nashiga namu

Kamar babu abinda mukayi haka kowa tashiga gida ,, ina zuwa nasamu yohun yayi tagumi,,,da sauri na kara

sa cikin dakinsa na zauna a kusanshi tabashi nayi

Da sauri ya juyo yana ganin nice da sauri ya rungume ne yana sauke ajiyar zuciya ,, kamar wanda yaci kuka

Dagowa nayi nace yohun yamafaru kake wannan ajiyar zu

ciya ,, ko wani yabata maka rai naje na rama maka ne

Girgiza kai yayi yace naje school dinku daukarki banganki ba ance kintafo gida , nazo banga kowa ba mama ta tafi wajan biki sai ni daya a gida ,, banason naje g

idansu papa duk shesu dameka da surutu

Murmishi nayi nace to ai gani nadawo ,, gidan wata kawata naje " sai yanzu nadawo

Mikar dani yayi yace ,, zomuje kici abinci kiyi wanka saimu kwanta nan muka fita ,

Abinci naci nan mukayi wanka ,, sai bacci

Baban budurwar ,, yohun ko da kyer ya kai gida yana dafe da goshi da baki , nan yasamu wani tashin hankalin ,, sosai abin yabashi haushi jin , wai su maryame

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login