Showing 168001 words to 171000 words out of 184731 words
shareef yayi farin ciki da matar mlm ranar suna aka sakawa yaron ,Ahmad sunan mlm ne
Malam yayi farin ciki da takwaran d
a aka mishi dan haka koda yaushe yana wajanshi bacci kawai ke rabasu
Bayan shekara uku nasake haihuwa wani namiji yaci sunan muhammed , shima ansha biki sosai bayan wata shekara hudu nasake haifo namiji yaci sunan
Abubakar sadeeq ,, amma ake kiransa da , Abubakar ko ace sadeeq amma Abubakar din yafi karfi
Bayan haihuwar abubakar da shekara biyu na haifi mace ,, nasha murna dan sai wannan lokacin na haifi mace , nan na saka ma
ta sunan ma wato mufeeda , tin daga kanta haihuwa ta tsaya min
Haka muke rayuwar mu amma fadana yana nan yanzu nazama yar gari duk wanda ya tabamin mufeeda sai anyi fada dani sosai kowa na garin yagane halina
Ahmed yana da shekara goma mlm ya rasu shida matar dalilin wata tafiya sukabar yaransu mata biyu sadiya da nana
Mukaci gaba da zaman mu dukanku a wajena kuka taso
Haka muke rayuwar har kowa ya girma a cik
in ku
Da kuka girma dagin matar mlm suka dauke su sadiya
Banso hakan ba amma ba yadda na iya suka tafi
Da suka girma bayan kun gama karatu aka aurawa Ahmed sadiya abubakar ya auri nana
Hakan yayimi
n dadi sosai Muhammad kuma ya auri fadila diyar abokin baffan ku
Wannan shine tarishinmu nida baffan ku
Inna ta kalli maman anty karima tace kanwata ,, bayan muntafi wani hali kuka shiga
Maman anty karima tac
e ,zan fada muku amma muje muyi salla mudawo aci abinci tukun
Nan kowa yatashi yatafi salla
Ameera ko bataso ta tashiba so take taji yadda kakan su daddy yayi lokacin daya kori su inna,,, amma akace sai anjima
*Nima nace bari naje na huta kafin sudawo*
[30/10, 19:24] MRS. MU'UTASIM: *
🌟
𝘼𝙈𝙀𝙀𝙍
𝘿𝘼
𝘼𝙈𝙀𝙀𝙍𝘼
🌟
*
*
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮
𝙖𝙣𝙙
𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜
𝙗𝙮
*
*
𝙈𝙖𝙢𝙖𝙣
𝙣𝙪𝙨𝙖𝙞𝙗𝙖
*
💫💫
*
🅙
︎
ARUMAI
🅦
︎
WRITERS
🅐
︎
SSO
CIATION
📚🖊
️
*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
💪
*_
*
💫
(
🅙
︎
.
🅦
︎
.
🅐
︎
)
💫
*
𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧
𝐬𝐡𝐚𝐟𝐢𝐧
𝐧𝐚
𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮𝐤𝐚𝐫
𝐠𝐚𝐫𝐞𝐤𝐢
𝐚𝐝𝐝𝐚𝐧𝐚
🥰🥰
💃🏼💃🏼
𝐧𝐢𝐤𝐚𝐝𝐚𝐢
𝐛𝐚𝐝𝐚
𝐤𝐨𝐰𝐚
𝐛𝐚
:::ummu amsad
𝐤𝐢𝐣𝐢
𝐝𝐚𝐝𝐢𝐧𝐤𝐢
𝐝𝐚
𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧
𝐟𝐚𝐠𝐞
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*87—88*
Suna tash
i daga falon kowa ya nufi inda masaukinsa yake ameera ta nufi dakin su ita da ameer ta kyer take tafiya saboda ciwon da jikinta har wani jiri takeji saboda yayan nata jiya bai bari tayi bacci ba shiyasa yake take
dafe kai
Suna shiga ameer ya rikota yana shinhina wuyar ta da gashinta wanda yasha gyara sosai
Ganin yana neman zufe mata jib din rigarta tayi sauri rike hannun shi tace , yaya cikani salla fa
Idonshi a rufe
yace wifey yunwa nakeji fa jiyama ban goshiba
Kura mishi ido tayi wani tausayin shine yakama ta amma ta danne dan itadai ko ba zata koma wajan jin karashen labarin su inna ba tofa bazai yiyuba ta kuma hayeta saboda
ko ina na jikinta ciwo yake mata
Tace yaya please kayi hakuri wllh duk jikina ciwo yakeyi kasan bayana kamar zai fita bazan iya daukar nauyinka koda na yadda bazaka samu abinda kakeso ba kayi hakuri kuma kaga za
mu ida jin labarin su mama dan haka kabari sai dare kafin lokacin nayi bacci na ware
Rungume ta yayi yace shikenan na hakura muje muyi salla idan angama jin labarin saikiyi bacci
Tashi sukayi toilet suka nufa da
yin alwala bayan sun gama salla suka sauko
Kowa yadawo nan baba laraba ta gabatar musu da abinci mazan suka tafi dakin baki matan ko suka zauna a falo nan aka soma cin abinci
Ikram karama ce ta tashi daga bac
ci , waigawa tayi ko ina taga ba muhammed aikuwa ta soma kuka iya karfinta
Da sauri suka juya ameera tace kai wllh yarinyar anyi ja'ira wllh fice kibamu waje duk kin damemu da ihun kuka tafiyar wajan uban naki
Fatima tace to ke ina ruwanki ,, yar iya bata tafiya nandin gidankine , bare amata gori kema tafi gidanki
Hajara tace kedai bari wai hadda ta tafi to bata zuwa zonan ikram
Ikram ko nufar hajara tayi tana fadin
daddy mommy daddy
Dariya sukayi mommy tace wannan yarinyar tayo gadon uwarta wllh
Mama tace da alama kuwa
Umma tace tashi hajara ki kaita wajanshi wannan ba shuru zatayi ba inbata Ganshi ba
Mike
wa hajara tayi tana fadin to umma nan ta dauketa suka nufi dakin baki
Takusa isa shima muhammed ya fito dan yana tunanin kar ikram ta tashi take nemanshi yasan halin rigimar ta
Karo suka kusanyi da hajara ta ts
aya tace a tureni zakayi
Zaro ido yayi sai kuma yayi murmishi yace banganki bane yar kanwata
Ikram na ganinshi ta soma dariya tana daddy daddy
Hannu yamika mata yace yar kanwata dama yanzu nake tunanin kintas
hi ashe hakane
Mika mishi ita hajara tayi tace yanzufa da anty ameera ta zaneta kamar zata daketa
Da sauri yace tab yar mommy din ce zata daka lalle data ga police a gidanta dan bamai tabamin kanwa ta
Murmishi
tamishi tace to shikenan nina tafi
Muhammed yace am sai kuma yayi shuru
Hajara tace magana kakeyi ne ,, da sauri yace a a ba komai nan tayi gaba abinta
Muhammed yace kash maiyasa ban fada mata ba ,amma ba komai
wani lokacin zan fada
Ameer ne yafito yace to yar mommy harta tashi daga bacci ne
Muhammed yace eh yanzu hajara takawota wajena
Ameer yace lalle wannan anyo gadon su yar inna ,,,dariya sukayi tukun sauran suka
fito nan aka nufi falo
Matan ma sungama cin abinci har an gyara wajan tsaf
Zama kowa yayi aka nutsu ana sauraron mama maryam
Mama ta gyara murya tace ,, lokacin da papa ya koreku munsha kuka sosai nida
yan uwana sosai muka shiga damuwa maman mu tafi sati a hospital tana kwance ba lafiya
Maman yohun itama haka abin yadameta kowa na family mu yashiga damuwa harma su papa da daddy haka suka shiga damuwa
Sosai
granny mu tayiwa papa fada tace akan me zai kore ku ba gyara a kori headmaster din ba yakoma garinsu amma yanzu anyi biyu babu ba ku din ba headmaster din duk kowa baya garin
Haka muka kasance muna jin kewarku ma
man mu ko abin ciwo yazame mata sosai ciwon zuciya yakama maman mu
Maman su papa ko ita kawai dena magana ma tayi saidai take ta kallon mutane ko mai za'a mata na farin ciki to baza tayi dariya ba abin yayi ta
damun su papa da daddy kullin ina bata labaran dariya amma abun ba sauki haka mukaci gaba da rayuwa me cike da k'unci
BABAN SHEKARA BIYU
Wata rana su papa da daddy suka tafi legos domin yin wani taro , nasu na
manya
Kwana biyu basu dawo ba sosai abin yabawa maman mu mamaki ganin basu taba irin wannan abun ba
Muna gida munyi jugum jugum sai aka sanar wani nason ganin maman mu awaje fita mukayi tare
Tashin hankalin
da muka shiga alokacin da mukaga gawar papa da daddy a kwance jini yanata kwarara a jikin su
Da gudu mukayi inda suke bude fuskar su papa maman mu tayi tana kuka sai jijjiga papa takeyi
Maman su yohun ne tazo i
tama aguje tana kiran sunan mijinta kafin wani lokaci gidanmu yacika da mutanen garin kowa kukan mutuwar su papa sukeyi saboda sune manya garin ragamar komai a wajansu take
Shiyasa suke ganinsu kamar iyayensu , haka
munaji muna gani aka dauke, su papa aka binnesu
Sosai muka sake shiga damuwa mutuwar iyayenmu maza sai kowa yayi sanyi har mutanen garin
Bayan wata daya da mutuwar su papa aka rasa wadda zai gajesu ganin ga p
apa da banju sai akace su zasu maye gurbindu tinda su zama samari a lokacin
Haka kuwa akayi
Bayan cikar su papa shekara daya da mutuwa aka radasu , mai sunan papa shine ya maye gurbin papa banju ya maye gurbin d
addy
Mutanen garin sukace dole suyi aure tinda an basu mulki
Hakan kuwa akayi dama muna soyayya da papa banju kuwa , lokacin bashida budurwa , sai wani dattijon garin namu yace ya bashi diyarshi ,,ai kuwa su maman
mu sunji dadi sosai sukayi godiya har ya gida sukaje godiya
Aka saka ranar bikinmu sati biyu kadai kacal saboda bikin na gaggawa ne shiyasa aka saka sati biyu kacal
Banju da farko kin yarda yayi da auren ya
rinyar da aka bashi
Jin haka papa ya yaringa kwantar mishi da hankali yana nuna mishi idan sukayi aure zai so ta da haka aka shawo kanshi ya amince
Sati biyu nayi aka daura aurensu a majami'ar garin akayi sha
gali sosai harna kwana goma
Bayan biki aka kaimu gidanmu a lokacin gida daya aka bamu
Sosai nakejin dadin zama da kutta saboda tana hankali ga biyayya ta daukeni kamar yayar ta nima