Showing 165001 words to 168000 words out of 184731 words
har mukayi itama
tace saboda tashiga musulinci iyayen ta suka koreta daga Enugu cen ne garinsu , tace ku inane garinku
Shareef yace mu a cikin daji muke sosai sunan garinmu mai daji saboda bamuda makotan gari shiyasa suna saka mish
i suna mai daji ,
Ma tace to ku kwantar da hankalin ku nice maman ku kunji muje mu kwanta
Nan muka tashi kowa yanufo daki muka kwanta
Sosai mukejin dadin zama da ma dinmu dan da haka muke kiranta ma
Shareef yasamu ma yakai mata kudinsa yace yanason soma sana'a yagaji da zama haka gashi bashida takardun sa na school dasaiya nemi aiki ma to babu su
Ma tayi murna sosai daya zo mata da wannan shawarar shago
tabude mishi ta kara mishi kari ya ringa siyar da kayan masarufi hakan ba karamin dadi mukajiba
Ni kuma kullin ina gida idan nagaji da zaman gidan naje wajan ma na tayata siyar da abinci , taso ta maidani mak
aranta amma na nace mata kawai zanke tayata siyar da abinci ,, haka ta hakura ta kyaleni , naci gaba da siyar mata da abinci dan yanzu komai ni nakeyi kuma muna kara samun sabbin costumes hakan ba karamin dadi yayi
wa ma ba she saka mana albarka takeyi mu kuma muna jin dadin zama da ita
Wani lokacin nakanyi kukan rabuwata da ahalina ,, idan natunasu sainayi ta kuka ina tunanin ashe iyaye zasu iya rabuwa da diyansu akan wani
ra'ayin banza da wofi ,, shesu zabi gunki akan mu yaransu ,, ganin ina neman sakawa kaina damuwa yasa nayi watsi da tunanin su papa nace , insha Allah bazan sake tunani akan su papa ba ,, tinda ba kaunar mu sukeyi ba
harda zasu zabi wani abu akanmu
Haka mukaci gaba da rayuwa a wajan ma sosai shareef yake samun kudi , hakan yasa yabude account bank na soma tara kudi
Ma tace ya tara kudi yasiyo min kayan lefe sai yakawo
sadaki a daura mana aure
Shareef yaji dadi sosai nan yakara kaiminsa yana tara kudi
Ranar da muka cika shekara a wajan ma shareef yahadamin lefe yakawo kudin sadakina dubu talatin , sosai ma tayi farin ciki nan
,,ya kaiwa wani malamin anguwar mu sadakin aka daura mana aure nida shareef
Ranar munyi farin ciki sosai marar musaltuwa ma ta gaiyato kawayenta da abokan kasuwancin ta tace ,, tana yiwa yaranta biki
Sosai mutane ke
mamaki to ina tasamu yara bayan sun jima da sanin batada kowa ita kadai take
Wata kawar ta ta tambayeta mu suwaye ,, sai ma tace ai mu yaranta ne da haka sukabar maganar
Bayan ansha biki , ma da kanta tak
aine dakin shareef ,ta hadamu tamana nasiha mai ratsa zuciya tukun ta tafi
Tana fita shareef ya matso kusana yace maryam kinga ikon Allah ko ashe iyayenmu bazata ga aurenmu ba ,, Allah Allah yasaka wa ma da gidan aljan
na
Na amsa da ameen nan mukayi sallar miga godiya ga Allah daya mallaka ,, mana juna tukun muka kwanta
Haka mukaci gaba da rayuwar mu mai cike da farin ciki da jin dadi ,
Wata rana wadda bazan taba manta
wa ba a cikin tarishin rayuwar mu ,,,,wani mutum yazo wajan ma yaci abinci ,, amma yahana ta kudi
Aikuwa ma tace batasan ,zancen ba kullin saiyazo yaci abinci amma saiya gudu yau tace bai isaba saiya biyata kudinta
Ganin tana neman tara mishi jama'a ya kwance rigarsa ta tafi aguje
Ma tace kaci wuta bal bal nan tadawo kan abincin ta taci gaba da siyar wa
Bayan mundawo gida mun kwanta cen cikin dare aka diro mana
ta katanga ,, bamu ankara ba mukaji muryan ma tana basu hakuri
Da gudu tayo dakinmu tana huce ta dauko card din bankinta ,, ta jefowa shareef tace maza kubi wannan kofar tabaya ku tsere banason su tabaku ,, ninas
an kwanana yakare tana kuka
Da sauri muka rungume ta muna kuka nace ma ina zamuje kece uwarmu kece ubanmu yanzu idan muka barki ina zamuje ,, kawai muma su kashemu
Da sauri ta dagomu ta kalle mu tace wannan car
d dinane na banki idan kun tashi kuje kucire kudin duka dama bamai yawa bane na dauko jiya , tana fadin haka ta turamu ta wani kofa mai lungu ta kullemu
Haka munaji muna gani suka kashe ma dan kurma ihu shareef
yarufemun baki yana matseni ajikinsa ,, saida suka tafi tukun muka fito daga inda ma ta tura mu
Ina ganinta cikin jini na fadi sumanmiya sosai hankalin shareef yatashi ganin wannan mugun aiki
Baiyi wata wataba
ya kira nember police ya fada musu yan fashi sunzo gidanmu sun kashe mana mahaifiya
Yana kashewa ya dauko ruwa yazuba min ,, bayan na farfado , naringa kuka sainaje zan taba ma ,,sai shareef yace karna taba ta , idan
akaga shatin hannu na zaace nina kasheta ,, inajin hakan na hakura
Police suka kira shareef wacce anguwa suke nan yatura musu address din gidan ,,babu mata lokaci suka karaso
Inda ma take suka nufa nan aka s
oma bincike munsha tambaya dan wani ma cewa yayi mune muka akshe ta
Sosai naji tsoro saida akaga babu shatin hannun mu ajikinta tukun suka yadda bamu bane ,muka kashe ma ,, ga kukan da mukeyi nan akayi station damu
Gari na wayewa aka kai ma gidanta na gaskiya nayi kuka tamkar ruwan idona zai kare kullin ina dakinta ina kuka ,
Anyi ta bincike amma ankasa gano wannan yan fashin hakan yasa shareef yace kawai abar magana
r Allah zai isar mana
Kullin ina cikin damuwa da kuka duk na rame nafita hayyacina ,,haka yasa shima yashiga damuwar halin danake ciki
Ganin yashiga damuwa saina rage tawa ina danne ta haka mukaci gaba da ray
uwa agidan ma har Allah ya azirtamu da samun ciki sosai mukayi murna ,
Shareef ko kullin hirarshi babyn dake cikina hakan ba karamin dadi yaminba muma zamu karu nace idan na haifi mace zan saka mata sunan ma ,
Shareef yace to nan mukaci gaba da renon cikin
Cikina yanada wata biyar cikin dare wannan yan fashin suka sake dawowa gidanmu
Inda ma ta boyemu nan muka shiga muka kulle daga ciki kamar ba kowa
Shigowa dak
inmu sukayi sunata dibe dibe
Daya daga cikinsu yace oga nan gidan fa ba mutane nafada maka
Ogan yace injiwa akwai yaran ta shiyasa taki bamu kudin ta duka kila sun tafi wani wajan mukoma falo mujira zuwansu ,,
nan suka koma falo suka zauna kamar sun samu gidansu
Shareef yafito yadauko wayarshi yakoma inda nake ina kyerma rikeni yayi ya kiran police ,, yace inda suka kashe ma sunzo zasu kashemu nan sukace gasunan zuwa
Babu jimawa saiga kiransu yashigo wayar shareef , sukace kada mufito zasu shigo ahankali shesu kamasu ,, mukace to nan ya kashe wayar
Muna nan cen sai muji ana harbe harben bindigu sosai na tsorata , bayan wan
i lokaci muka ji shuru bude kofar dakinmu dan sandan yayi ya kira wayar shareef ,, nan muka fito yana rike dani
Barayin ankamasu nan nayi arba da wannan wanda sukayi fada da ma da sauri nace shine azzalimi ya ka
shemin mahaifiya ta dama kullin saiyazo yaci abinci yahanata kudi nan nabasu labarin fadansu ,, aka tasa keyarsu zuwa mota ,,ni kuma aka kaini asibiti saboda tsoron dana ji
Wasa wasa saida nayi sati a asibiti , ina
jinya nice harda karin jini
Bayan an sallamemu ne ,, mukaje zaman kotu saida akayi sati ana shari'a tukun aka gama yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbi
Sosai mukaji dadin wannan hukuncin ,, bayan mun fito m
ukaje mukawa loyanmu godiya shareef yabiyashi kudinsa amma yaki karba ,, yace ma tana da kima a wajan sa dan haka bazai amshi kudinmu ba nan muka mishi godiya zamu tafi
Yace am shareef dazakuji shawara ta dakun s
iyar da gidan nan kubarma garin gaba daya saboda ,,wannan mutanen suna da diya zasu iya koma muku
Godiya muka sake mishi nan muka dawo gida
Bayan kwana biyu muka samu malamin anguwar mu muka cemishi zamu siya
r da gidan , shima yace zai tashine yakoma kauyensu nan mukace zamu bishi cen kauyensu
Sosai yaji dadi yace muje inda ake siyar da gidaje , nan suka tafi da shareef ni kuma nakoma gida
Bayan kwana uku aka si
yar da gidan million daya saboda wulakanci a haka ma wai mai siyan yace sai an rage mishi ,, mlm yace sam kawai yasiya ahaka , tukun yabda milion daya
Haka muka tattara kayanmu na siyarwa muka siyar wanda zamu i
ya dauka muka dauko nan muka hau mutar katsina
Musha tafiya sosai nagaji kafin azo katsina tinda sassafe muke tafiya har dare tukun mukazo katsina
Shareef yakama bama dakin biyu a hotel din garin muka kwana
Da safe yabiya kudin mukaci abinci tukun muka kama hayar k'ankara babu dadewa mukaje garin mai kyau da tsari
Gidan malam Ahmed muka je matarshi ta tarbemu da murna ,,sosai ta nuna mana karamci ,hakan yamana dad
i harda malam kanshi
Ana mukaci gaba da renon cikin jikina har na haifi namiji sosai