Showing 138001 words to 141000 words out of 184731 words
ido y
ayi ganin mace aciki , saboda sanyin akwatin ta sandare , da kankara , ahankali yace umar leko kagani
Da sauri yaleka , da sauri yake cewa it...it..ita...itace , karima ce maza mu fiddo ta
Ameera ta matso jin abind
a, Umar yake nan ta leka dafe kirji tayi ganin anty karima , fadi take,, anty karima
Muhammed yace , dasu babu lokaci maza mutafi musamu " mufita daga wannan wajan nan , suka fito daga gidan kasar
Ahankali yanzu m
a suke tafiya har sukabar majami'ar , nan suka yi wajan motarsu " aka saka karima abaya , umar ya zaune kusanta
Muhammed da ameera agaba nan sukayi gidan su muhammed
Yanzu fatima tana samun sauki sosai , ga baby
girl din masha Allah , lafiyayya da ita " Inna kuwa koda yaushe tana rungume ' da baby din ta hana kowa dauka , komai ita kewa babyn ,,
Ameer ne da hajara sukazo hospital din suka shiga cikin dakin, da fatima ke
ciki da sallama suka shiga ciki , Inna ce ta amsa musu ,,Fatima na kan gado tana cin wuton dawa da miyar kubewa,, yasha man shanu sai kamshi yakeyi
Hajara tayi wajan inna take kawo babyn mugani inna
Harara t
a aikawa hajara tace , to ke taya ma kika iya rike jariri abaki kije ki , targada musu yarinya
Bata fuskar hajara tayi tace kai inna hadda cin fuska a alamar na yau , kuma kike cewa ban iya rike jariri ba kokin
manta ni nayi renon, Ibrahim shine, kikemin gori
Inna tace bazan bayar badai " koma meye futsararriya,, kawai kitashi kiban waje kona make ki,
Ameer yace haba inna kibata " mana tagani tasa mata albarka
Inna tace kai kuyi tafiyar ku wajan aikinku " karku damemu dan banza, to ance baza'a bataba
Hajara kamar zatayi kuka tace please yaya kace , tabani naganta , Ameer yace zo nan kyaleta idan anty ikram tazo saiki g
anta tashi mutafi , office ,mikewa tayi tana kunbura baki nan suka fita
Tinda su muhammed suka dauko karima, mommy sa yakira tana bacci ,, dauka tayi ganin danta ne yasa ta tashi da sauri
Tace hello , son lfy
kake kirana sa asubar nan
Muhammed yace mommy kitashi , zamuzo nida umar da ameera , kice abude mana kofa
Mommy tace to to saikun zo , tana ajiye wayar fita tayi tana " cewa mai gadinsu ,idan anyi Hon ya bude
kofa,, ya amsa mata da to nan takoma gida
Doctor aisha mamaki take, to kodai wani abu yafaru da safiyar nan muhammed yake gidan su ameera , bata gama tunanin ba taji shigowarsu
Da sauri tasa hijab ta fita t
ana tsaye har suka fito
Baya suka bude nan suka fito da karima da mamaki take kallon su
Wajan ta sukayo ameera tace please momma ba lokaci muje ki duba mana ita
Bunsu tayi ciki kamar rakumi da akala , a
falo suka shimfide ta ,
Ruwa yasoma diga daga jikin alamar kankarar tasoma narkewa , Muhammed ya kalle ta yace mommy ki dubata mugani tana da rai
Kayan aikin ta ta dauko tashiga auna karima tajima tana aunaw
a , kafin ta dago tace tana da rai zuciyar ta na mugawa ,,amma tana mugatar " karin numfashi saboda nata yamata kadan , kuma dole sai an ringa gasa mata jikinta da ruwa mai zafi sosai saboda kankarar jikinta, ta fita
kozata samu damar motsawa da kanta
Muhammed yace to ,mommy muje hospital din , karmuyi jinkiri , kayanta ta hada , umar yadauki karima nan suka shiga mota sai hospital din mommy
Suna karasawa , doctor aisha tashiga o
ffice dinta,, ta saka kayan aiki tukun tafito ,, nosee nabinta abaya
Karin numfashi aka sakawa karima shima da kyer aka samu aka saka mata saboda duk ilahirin jikinta yayi tauri ,
Umar ko yama rasa mai zaiyi shid
a , ameera ,, kuka ameera tayi rusa kamar ance karima ta rasu ,, Umar na bata baki akan tayi shuru amma kamar kara mata karfin kukan yake,, haka ya hakura yazuba mata ido
Cen kuma saiya kira mama , ringing daya ta da
uka , dama tana kokarin kiransa ne saigashi ya kirata dan taleka dakinsa sai, Abubakar tagani na ameera kuma sai muhammed , yana bacci nida mufeeda
Mama tace hello umar wai ina kuka tafine na leka banga ameera ba
kaima banganka , ba sai yara suna bacci
Ajiyar zuciya yasauke yace mama ki kira , maman karima dukkanku , kuzo hospital din doctor aisha , idan kukazo zakuji komai
Cike da tashin hankali ,Mama tace na shiga uku
hallau wani abunne yasamu ameera din
Umar yace no ba ita bace kudaizo nan ya kashe wayar yana kallon ameera da har yanzu take kuka abinta
Ameera ko kukan farin ciki ne takeyi, saboda tacikawa karima burinta ga
shi kuma sun fiddo ta daga cikin inda aka boyeta ,, shiyasa take kukan farin ciki saboda ,, takusa komawa wajan mijinta da danginta , duk wani nauyin da zuciyar ta kemata kullin yau tana kukan , yana fita , tana haka su ma
ma sukazo
Doctor Aisha ce tafito kallon muhammed tayi tace son , kaje gida ka wanki ikram saikuzo idan kunyi break , , ya amsa da to nan yatafi baima ,, tsaya sun gaisa da su mama ba , ta tafi
Doctor aisha ta
ce, zaku iya ganin ta kafin asoma shirye shiyen mata aikin nan da sati biyu ,
Ameera na ganin mama da sauri ta fada jikin ta tana kuka ,, Mama tace wai lfy kike kuma shi kuma sai murmishi yake " ku fada mana
Dagowa ameera tayi tace mama mun samo anty karima ,
Kallon mama tayi da sauri tace ke ameera bana son wasa " kinsan me mike cewa kuwa
Cikin kuka ameera tace , eh mama kuzo muje kugani , nan suka nufi dakin da
aka kai karima,
Cike da mamaki suke kallon karima da take kamar gawa a kwance , maman ta ta karasa wajan da take tana kallon ta tace tabbas wannan karima ce " wannan kayan dashi ajikinta , akace ta mutu kowa
Umar ne yamusu bayanin komai da dakota da abinda doctor aisha tafada
Mama tace Alhamdulillah Allah mungode maka ,sai ta kalli ameera wanda take share hawaye , tace lalle ameera ke haske ce agaremu,, alkairan ki yana daya
wa " agaremu Allah yasaka miki da alkhairi yadda kikayi sanadiyar, fitar damu daga duhu Allah yarabaki da duhun kabari, Allah yamiki albarka
Ameera tace ameen mama , nima ai yarki ce , yanzu dai mubari , muga tashin an
tyna
Nazeer ma kukan yake share hawayen sa yayi yana murmishi ,, yace kaji masu anty to sannu ko
Harara ameera ta banka mishi tace ,eh anji din tuzuru kawai
Dariya sukayi , Nazeer yace oho dai yarinya ai nim
a zanyi auren na huta da gorin dakike min ,,, nan suka fita daga dakin
Yau ne ake bikin ,sunan babyn fatima , sosai aka cika gidan maman anass da dangin mommy hadda yan kauye sunzo
Umma tacewa khadija tabiyosu
, amma tace bazata zoba tin babu ameera , haka ta hakura ta kyaleta
Yarinya taci sunan mommy fadila za ana kiranta da ,Iman , masha Allah anyi suna abin burgewa, anyi taro lfy , (*cen* *nagano* *fans din ameer da ameera
* *musamman* *ma* *mrs*. *Sadeeq *wato kawas
💃🏻
da ,Queen farida su asna maman sudes ,dadai sauran fans kowa na cashewa*)
Haka akayi taro lfy kowa yatafi gidanshi , aka bar mai jego da baby iman ,mama tacewa anass fatima
gida zataje wanka
Aikuwa takafe shi babu inda za'a kai mishi mata ta tsare gida yahana , ganin abun da anass yake gaske ne yasa mama hade rai
Tace anass ,, jin takira sunanshi ful yasan babu wasa , saiya zau
na
Kallon shi tayi tace wannan tafiyar dole, Fatima taje gidansu wanka haihuwar fari haka akeyi tin asali,, kai dan kaine shugaban marassa kunya kace , bazata tafiba " naji kara fadin bazata tafiba saika hadu da fushin
a , haba yaran zamani sai shegen rashin kunya tana, rankwashin sa aka
Dafe kanshi yayi yace ,washh mama wllh akwai ciwo sosai ,, shikenan naji sutafi
Inna dake jinsu tin dazun tace,, ka anaru kake ko anu , to
ka kiyaye wllh " in banda ma ku futsararru ne,, hadda cewa bazata jeba " ni yanzu saina hada maka jini da majina dan butar uwa kake wani sunne kai kamar tsohon munafiki,,, kai nifa baa kawomin reni ko rashin kunya yanzu
saina
saita maka hanya " dan kwal uba , uwar taka na maka magana , kana tankawa, yo inbanda ma karfina yadan ragu da tuni na dauki sandar nan " na mammake ka da , ai dakai da ameeru ,,duk tafiyarku daya,,, dogayen banza
kawai masu hankalin,, rakuma duk wanda yake rashin kunya acikin ku , dukanku zan bubbuge ja'irai ,, tana kai karshen maganar tana , gyara daurin dan kwalinta ,, ta turoshi gaba
Mama na dariya tace yauwa inna , ai gya
ra ki mana maganin su wllh basuda kunya
Anass ma dariyar yake yace yi hakuri inna nadena ,, kutafi
Inna na aika mishi kallon tara saura kwata tace, kobaka fadaba tafiya zamuyi dan kan uba ,baki kamar tukunyar dad
dawa,
Dariya sukayi mama tace inna , kyaleshi muje muhada kayan , nan suka shiga dakin fatima,, aka hada kayan suka fito dan tuni direba yazo