Showing 1 words to 3000 words out of 159340 words
*TKG*
01.
"SADIYA.."
Wannan karon a yanayin yadda ya kira sunana sai da na ji jikina ya amsa da ya sa kaina na ƙasa sai da na
ɗ
ago na kalle shi. Tabbas a cikin idanuwansa na hango kamar hawaye sun cika masa kwarmin idanuwa kuma na hango gajiya da
haƙuri harda kunya a lokaci
ɗ
aya.
"Sadiya.."
Ya sake furtawa cikin wani irin rauni. Raunin da har ina jin sautin fitar shi daga muryansa.
"Sadiya.."
"Ta.."
Ya sake fa
ɗ
a ararrabe daga gani ya kasa sarrafa kanshi halin da ya ke ciki na neman t
ona masa asiri.
Ba na so ko
ɗ
aya na nuna masa na san labarin abin da ke faruwa yadda bai fa
ɗ
a mini ba nima ba zan nuna masa na sani ba. Tabbas na yi dauriya domin a lokaci ji na ke yi kamar na zube a kan kafafuwana tsabar yadda suke rawa. Ina jin wani iri
n nauyin jiki wanda na zuciyata ne ya sakar ma gangar jikina.
Na yi iya ƙokarina kar ya fahimci nima a firgice na ke shi ya sa na gayyato mirmishi wanda ka na ganin shi gwara ma kuka a kan shi saboda ba daga ƙarƙashin zuciyata ya fito ba.
Ina yin mirmi
shin ina kallon fuskar Yalla
ɓ
ai amma sai na ga yau ba na ganin shi da haske a idanuwana sai ya yi mini wani baƙi kamar ba Yusuf
ɗ
ina ba.
"Sadiya ta. Na dawo"
Ya fa
ɗ
a ya na kallona domin tun
ɗ
azu idanuwanshi suna kaina ne. Ni kuma cikin rawan jiki da
na zuciya na bu
ɗ
e baki dakyar ina jin harshena na karkarwa a cikin bakina.
"Na'am"
Murya ta na rawa ina so na daidaita kaina amma wallahi na kasa. Kai jama'a kishi bala'i ne sai yau na sake samun tabbacin haka duk yadda na so a ro jarumta sai na ji n
a kasa ji na ke yi wani abu na min yawo a cikin jinin jikina. Kaina ya yi nauyi gaba
ɗ
aya ji na ke yi kamar zan fa
ɗ
i saboda tsabar gigitar da na ke ciki saboda tashin hankali.
"Na'am Yalla
ɓ
ai n.."
Sai sauran kalamai na suka maƙale a fatar bakina. Na k
asa iya kiransa da yau
ɗ
aya da Yalla
ɓ
ai na. Yau
ɗ
aya da na kalle shi ina jin dukan zuciya da cewa Yalla
ɓ
ai yanzu ba nawa ba ne ni ka
ɗ
ai ya tashi da ga mallakina ni
ɗ
aya ya koma mallakinmu ni da wata. Ashe haka sauran mata da dama suke ji in an yi musu kish
iya? Na
ɗ
auka in Yalla
ɓ
ai zai ƙara aure ba zan wani damu ba ashe ashe kishi ba a yi masa da wasa. Tabbas Ubangiji ne ya hallici mu mata shi kuma ya sanya mana kishi a zukatanmu shi kuma ka
ɗ
ai ya san dalilin shi na haka.
Balle irin auran da Yalla
ɓ
ai ya
yi ban shirya ba. Lamarin ya zo min ne cikin bazata da tsamanin abin da ban ta
ɓ
a tsammani ba. Ban ta
ɓ
a zaton a wannan yanayin ne zan fara raba Yalla
ɓ
ai da wata ba. Ban ta
ɓ
a tunani ko hasashen haka ba.
Takalmin da ke kafata har ya jiƙe da zufa haka wayar
dake hannuna tana maiƙon zufan da ke fita daga jikina
Yalla
ɓ
ai ya fara taku
ɗ
aya, biyu zuwa gare ni da sauri na yi baya a nufina na guje ma ha
ɗ
uwar jikina da na shi domin yau kawai na ji ba na so Yalla
ɓ
ai ya kusantoni. Ƙokarina na yi baya amma jikina y
a ƙi ba ni ha
ɗ
in kai saboda a firgice na ke. Bayan da na yi da sauri ya ja takalmin kafata ya turku
ɗ
e na yi baya zan fa
ɗ
i ban san lokacin da wayar hannuna ta fa
ɗ
i ba, sai na ji Yalla
ɓ
ai ya rike ni gam lokaci
ɗ
aya yana kallona kafin ya ce.
"Lafiyan ki ku
wa?
Ya fa
ɗ
a ya na mai kallona cikin fitan hayyaci na kalle shi sai na ji in na cigaba da kallonsa zan iya fashewa da kuka har na tona asirin zuciyata. Ya ji jikina na rawa ya kuma ya fahimci duk a firgice na ke ba na cikin hayyacina, shi ya na ƙoƙarin
ya ta da ni tsaye ya ra
ɓ
a ni da jikinsa ni kuma hannayen nashi na ke kallo domin sai na ga kamar sun zame min baƙi a cikin idanuwana yau
ɗ
aya kawai sai na ji hannun Yalla
ɓ
ai kamar baƙo a gare ni da ban san lokacin da na yi gefe ina mai kauce ma riƙonsa baa
. Hannun kujera na dafe ina haki sama sama domin na ji tabbas numfashina na cijewa kamar ya na neman ya dawo wuyana.
Yalla
ɓ
ai ya kalleni a tsorace ya sake kallona kafin ya ce" Sadiya? Kina lafiya?
Ya fa
ɗ
a ya na ƙokarin ƙara matsowa kusa da ni da sauri
na yi baya amma kuma ban saki hannun kujeran da ke gefena ba domin in har na yi gangancin saki ba zan iya riƙe kaina ba.
Sadiya ki yi jarumta Sadiya ki daure. Haka na ji wata zuciyar na fa
ɗ
a min da ya sa na yi saurin ƙwato numfashina da karfi na sauke aj
iyar zuciya ina mai kallon wayata da ta fa
ɗ
i a ƙasan Tayels. Yalla
ɓ
ai ya bi in da na ke bi da kallo shi ya duka ya
ɗ
auko min wayar ya riƙe ta a hannun shi.
Kallona ya ke yi yana so ya yi mgana shima bakinsa ya yi masa nauyi kawai sai na miƙa masa hannu y
a saka min wayar lokaci
ɗ
aya yana fa
ɗ
in" Kin tabbata kina lafiya?
Ji na yi kamar in balla masa harara in ko na bu
ɗ
e bakina na tabbata sai na danna masa ashar na katsinawa. Amma sai ban yi haka ba, na sake gayyato mirmishi ina mai
ɗ
aga masa alamun lafiya
ta ƙalau. Ajiyar zuciya na riƙa saukewa a jejjere ina huro iska daga bakina domin na samu natsuwa daga ƙasan raina ina ta mamaita Innalillahi domin Allah ya sake ba ni jarumta.
Cikin ikon Allah na ji na samu natsuwa jikina ya daina rawa. Har na samu da
man sakin hannun kujera na tsayu da kafafuwana. Kallonsa na yi ya na tsaye ya har
ɗ
e hannuwansa a saman kirjinsa ba ni ka
ɗ
ai ba shi kan shi ma a firgicen ya ke sannan ba natsuwa a tare da shi. Ban tsaya sake kallon shi ba na yi karfin halin wucewa
wajen ledojin da ya ijiye na duka na
ɗ
auka ina fa
ɗ
in" Su Jidda sun gaji da jira har sun yi barci."
Na fa
ɗ
a saboda gyara yanayina lokaci
ɗ
aya ina
ɗ
agowa da ledojin ta gabansa na wuce zuwa kan dining na
ɗ
ora ledojin amma ban bu
ɗ
e su ba. Ina so na juyo am
ma ba na so mu sake ha
ɗ
a ido da Yalla
ɓ
ai.
"Ki tashe su mana."
Haka ya fa
ɗ
a a sanyaye sai na juyo ina mirmishi kafin na ce" Sun riga sun yi barci fa? Ƙyale su kawai."
Shi kuma kawai sai ya saki hannayenshi ya wuce kawai zuwa falo ya na mai fa
ɗ
in" Wa
nnan babban rana ce a gare mu bai kamata mu yi murnan ba su a wajen ba."
Ya ƙarishe fa
ɗ
a ya na bu
ɗ
e kofar falon ya shige ni ban bi bayan shi ba ina ta ƙoƙarin yaji da abin da ke taso min. Ina jin sa daga nan ya na kiran sunanayen su Jidda daman ba ta da n
auyin barci. Baby ma ba ta dashi amma ba kamar Jidda ba.
Tsayuwa na neman gagarata ya sa na samu
ɗ
aya daga cikin kujerun falon na zauna ina sauke numfashi. A baya in yi ta ganin laifin matan da mazajensu ke ƙara aure su yi ta hauka sai da ya zo kaina na
fahimci yanayin tabbas kishi ke haukata mata ya kuma sa ka kasa mallakan kanka, ina zaune a in da na zauna ya dawo falon tare da yaran dukkansu ya na riƙe da hannun su. Baby ce sarkin surutu sai fa
ɗ
i ta ke yi.
"Abba yaushe ka dawo?
"Ban da
ɗ
e da dawo
wa ba Baby"
Ya ba ta amsa dai dai suna zama kan kujera mai zaman mutum hu
ɗ
u.
"To ina ka je Abba?
Baby ta fa
ɗ
a tana mai hawa jikinsa ya na shafa kanta ya ce" Na je Rano ne."
Ya
ɗ
ago kenan muka ha
ɗ
a ido da shi sai na yi saurin kauda kai daman ina s
o na ji me zai ce? Tabbas can ya je kuma ya dawo da kyakyawan tsaraba na ce a raina a lokacin da na ji Baby na tambayan shi ya siyo mata tsaraba. Sai ya nuna mata ledojin kan Dining ya na fa
ɗ
in ga tsaranbanta ca.
Daga shi sai Baby suke hiran su ni da Ji
dda kamar ba ma falon ita ta na gefe sai hamma ta ke yi daga gani barcine a idanuwanta ni kuma ina zaune ina fama da turirin zuciya.
"Duk Umma ce ta ha
ɗ
a wannan?
Ya fa
ɗ
a ya na nuna cake
ɗ
in da ke gabansu.
Da sauri Baby ta ce" Umma ce da Yaya Jidda.
Abba ni ma zan ci Cake
ɗ
in"
Ta fa
ɗ
a tana leƙa Cake
ɗ
in . Na ji ya kalleni a cikin jikina ni kuma sai ban juya na kalle shi ba, ina kallon gefe ina ƙokarin sakin fuskata na
nuna komai bai faru ba amma ina jin kamar ba zan iya nuna komai
ɗ
in bai faru ba.
"Sorry Jidda barci ko?
Na ji ya fa
ɗ
a sai na ji ita kuma ta na fa
ɗ
in" A'a Abba."
"To Hammar kuma ta mane ne Jidda?
Ya fa
ɗ
a ta gefen ido na kalle su sai na ga ya na jan hancinta ita kuma tana mirmishi. Yana
ɗ
ago kansa zuwa gare ni na yi saurin
ɗ
auke
kaina kamar ban san suna wajen ba.
Ƙ
ila ya da
ɗ
e yana kallona domin falon ya yi shuru sai karakainan Baby kawai ke tashi a falon ni kuma na yi matukar ƙokarin sassauta fuskata.
"Yaran nan fa na jin barci ta so su mu yi abin da ya kamata su je su kwanta
."
Ya fa
ɗ
a a sanyaye. Ni kuma sai na yi kamar ban ji ba sai na maida kaina can gefe kamar ina kallon Tibi ahalin Tibin ma a kashe ta ke.
"Sadiya"
Shima yau
ɗ
in ya raba ni da wata ni ai ba Sadiyarsa ba ce ni ka
ɗ
ai ya na da gimbiya shi ya sa yau Yal
labai ya ke kirana Sadiya gatsal ta sar ma ya kasa ma minibwannan karan. Ji na yi kamar na fashe da kuka saboda baƙin ciki.
"Sadiya.'
A wannan karon da
ɗ
an karfi ya sake kiran sunana. A sanyaye na kalleshi kuma kallon bai yi yawa ba na yi saurin kaud
a kaina ina ƙoƙarin miƙewa sai na ji duk jikina ya saki. Amma hakanan na miƙe ina ƙokarin dai dai ta kaina ina gani ya na nuna min gefensa na yi kamar ban gani ba na zagaye shi na isa kujera mai zaman mutum biyu dake gefen su na zauna. Ban kalle shi ba sai
na sadda kaina ƙasa ina wasa da zoben azurfan da ke hannuna.
"Sadiya ta."
Sai yanzu? Sai yanzu ne ya gane ni tasa ce kafin ya samu wata. Haka na fa
ɗ
a a raina sai na
ɗ
ago idanuwana da na ji har nauyi sun yi min ina kallon shi, shima fa karfin hali ne
amma kunya da nauyin Sadiya da ya ke ji sun hana shi sakewa.
"Na tambaye ki meke damun ki, kin ce min bakomai."
Ya fa
ɗ
a ya na mai kureni da ido a cikin zuciyarsa kuma na san bugu ta ke yi saboda nima ƙura masa ido na ke yi ina hasashen shike nan yan
zu wai kwana zan riƙa rabawa da wata a kan Yalla
ɓ
ai ko? Shi kenan mun tashi daga Family of 4 mun koma Family of 5 ƙilama kafin a rufe shekara ta haihu za mu hauhawa. Sai na ji kuka na taho min amma na yi saurin kannewa.
"Me ke damun ki? Ko an fa
ɗ
a miki
wani abu ya faru ne?
Shike nan ya fara kama kanshi da kanshi. An ce mara gaskiya ko a cikin ruwa ya ke gumi ya ke yi. Da gangan na kalle shi sai na ga ya daburce yana ƙokarin gyara mganarsa.
"Nufina ko can Ɗorayi su Alhajimmu duk lafiya ko?
Mirm
ishin takaici ya kwace min. Yallabai ya na so ya raina ma kansa ma wayau. Ya na tunanin abin da ya rufe bai fa
ɗ
a min ba ya na ji a ransa zai tabbata a rufe ne ni ban sani ba.
Sai kawai na yi masa wani kallo kafin na ce" Ko
ɗ
aya. Ba abin da ya faru kawai r
aina ne ya
ɓ
aci ba ka dawo da wuri ba alhalin kasan tun karfe nawa muka shirya ni da yara muna zaman jiran ka?
Na fa
ɗ
a hawaye na ciko min a ƙwarmin idanuwana. Ƙura masa ido na yi sai na ga ya sauke ajiyar zuciya irin na samun salama ya na neman
ɗ
auko m
gana na yi saurin tare shi da fa
ɗ
in" Mu yanka cake
ɗ
in ina jin barci.'
Na fa
ɗ
a ina mai kauda kaina saboda ƙokarina na maida hawayena sai ma na ga sun koma da kansu ba tare da na yi yinƙurin maida su ba.
"Sadiya"
Ya sake kiran sunana a zafafe na juya
na kusa na ce ya daina kiran sunana haka tunda ba shi ya ra
ɗ
a min ba amma sai ya yi sauri tare ni da cewa.
"Ta so ki zo nan ki zauna kusa da ni."
Ya fa
ɗ
a ya na nuna min gefensa. Kamar na ce bar ni anan sai kuma ban ce ba na tashi na koma kusa da shi
na zauna amma ban matso kusa da jikinsa ba sai shi ne ya sauke Baby da ke kan jikinsa gefen Jidda sai ya ƙara matsoni ba zato kawai na ji ya sunkuya ya sumbaci kuncina kallonsa na yi bai bani zarafin mgana ba ya yi mirmishi kafin ya ce.
"Ki yi hakuri S
adiya."
Kallonsa na ke yi amma na kasa mgana sai ya ƙara marairaicewa ya na ƙara matso ni a jikina.
"Sorry ba na ce ki yi haƙuri ba? Kin ji ko?
Ya fa
ɗ
a ya na ƙoƙarin saka hannu ya
ɗ
ago ha
ɓ
ata da sauri na kauda kaina ina fa
ɗ
in" Nima ai na ce komai ya w
uce ko?
Sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Yaushe kika ce! Yanzu dai ko?
Ban iya ma yi masa mgana ba ya dame ni kamar na ce ya matsa baya amma na kasa. Shi bai san ni yanzu ba na so ma ina zuwa kusa dashi ba a raina na ke jin duk abin da na ke tunanin ni ka
ɗ
ai ke da shi yanzu ya tashi a mallakina nawa ya koma mallakinmu kuma namu. Ya yi ƙokarin ba ni haƙuri amma kuma ya kasa bayyana uzurin da ya zaunar da shi tun safe sai dare, Me ya sa Yalla
ɓ
ai ya boye min ? Zan hana shi aure ne? Ni a cikin zuciyata na fi j
in zafin munafuntata da ya yi sama da auran shi. Har Ma'u ta na murna ta samu makamin da za ta ya ƙe da shi ni kuma na ce ƙaryanta ba zan ta
ɓ
a bari ta samu wannan damar ba.
Mun yanka Cake amma wannan shekaran Walimar tamu ba cike take da farinciki ba. A
fuskata za ka fahimci ba na cikin farinciki shima kuma haka su Jidda ne kawai ke ta murn. Ko wajen yanka cake
ɗ
in ma hannuna saman na Jidda na
ɗ
ora sai shi ne ya
ɗ
au hannuna nawa ya
ɗ
ora saman wukar
sannan ya kama sai ya ce yaran su
ɗ
ora saman na shi. A h
aka muka yanka cake
ɗ
in kuma wajen ba da wa yarana na fara ba mawa sannan shi na karshe in da a ce zan yi masa kutumar uba wallahi ko kallo bai isheni ba amma hakanan na daure ma zuciyata. Shi ko ni ya fara yankawa ya saka min a baki wanda dakyar na bu
ɗ
e b
akin duk ma ya shafa min a gefem baki ya na ƙokarin ya saka hannu ya goge min na goge da kaina sai ya koma ya na ba ma su Jidda cake
ɗ
in suma suna bashi suna ta dariyan farinciki ina kallonsu a cikin raina ina tunanin shike nan Yalla
ɓ
ai ya yi sanadiyar lal
atamin farincikina na wannan ranar. Daman ya ce zai ba ni suprise lalle na kar
ɓ
i babban suprise da ba zan manta da shi ba a rayuwata ba.
Na gaji so kawai na ke yi na ke
ɓ
e ni ka
ɗ
ai. Shi ya sa kawai na