Showing 27001 words to 30000 words out of 295116 words
baiwa Hameedar.
Ba
sifi sati biyu da dawowa ba jarabarsu ta fito ta Federal inda Zahra ta samu F.G.G.C KAZAURE yayin da Sulaiman ya samu F.G.C DAURA, Hameeda F.G.C AZARE. Salma ce kawai bata samu ba a cikinsu.
Sunyi murna Kuma sunyi bakin cikin rashin samun makaranta daya du
k an watsa su Abban Kuma da ya Hassan sunce kowa ya tafi inda ya samu, ita Hameeda Bata da damuwa tana gida, su Kuma duka 'ya'yan Ammah duk sun fita waje danma hanyarsu daya sai an aje Zahra a karasa da Sulaiman.
Ranar da zasu tafi sun Sha kuka haka suka
dauko hanya malam Bala da Ya Hassan ne suka kaisu.
Lokacin da aka Kai Zahra an tashi daga aji, wasu Yara House master dinsu ya kira da wata prefect yasa su Kai Zahra room din 'yan j.s one.
A cikin yaran da suka Taya Zahra daukar kayane wata yarinya tace Ma
ta "sister kizo ki zauna a kwana ta tunda ni daya ce saman gadona ba kowa".
Kai kawai zahra ta gyada Mata tana ta sauke ajiyar zuciya.
Ita ta taimkawa Zahra ta shirya komai a locker dinta, Saida ta Bari zahra ta HUCE daga kukan da tsaha sannan tace Mata "n
i sunana Sajida Musa ni 'yar kano ce unguwar Gwammaja kefa ya sunanki?".
Nan Zahra ta fada Mata komai nata tun daga Nan suke tare har suka Zama aminai komai nasu ya Zama daya banbanci su kawai Sajida na A Zahra na C.
Haka sukaci gaba da rayuwa a makarantar
gasu Kuma Yara masu kwazo barin zahra ga kyau ga ilimi Nan da Nan tayi suna a makarantar kafin hutu tayi popular sosai a makarantar, idan kace 'yar larabawa kowa ya santa ba Kuma Dan Babu irin jiinsin nata ba A'a farin jini ne daga Allah.
Lokacin da akayi
hutu Zahra ba karamar murna tayi ba Kuma cikin ikon Allah da wuri malam Bala yazo lokacin har ya dauko Sulaiman.
Bayan Azahar kadan suka shiga Azare sunyi murna sosai da ganin mutanen gida Dan Sulaiman har da kuka, Nan su Hameeda suka saka gaba suna tsok
ana.
Haka suka cigaba da karatunsu cikin amincin Allah, lokacin da sukazo hutun third term ne akayi auren Aunty Hasana aka kaita Jos, Ya Hassan Kuma Daman Yana karatunsa a Rasha.
Kowa inda yake yacigaba da karatunsa Salmace Allah ya taikata ta samu shiga F
GC AZAREN itama a ss1.
A haka aka dunga juyawa har suka Gama secondary School dinsu suka dawo gida.
Dawowarsu ba dadewa Allah ya yiwa Nanna rasuwa rashin daya taba Abbansu sosai.
Dan ya Dade Yana fama da damuwa tunda a rayuwa da ita ya tashi baisan dadin u
ba namiji ba itace komai nasa.
Ganin abin nasa Yana neman yayi yawa yasa Abokinsa bakon malamin daya sauka Nan daura gidan Nanna da almajiransa dududu Bai zaifi sa'an Alhajin ba malam Bubar ya dukufa yi Masa addu'a tare da saka Yara kanana suna Masa addu'
a, cikin ikon Allah sai komai ya daidaita.
Ranar wata laraba zahra ta shirya zata raka Hameeda duba Qawarta meenal gidan Dan majalissarsu Mai wakiltar su majalissar Jaha, wani material ta saka Mai ruwan sararin samaniya yayi matukar karbar jikinta haka di
nki ma ya Dace da material din, simple makeup tayi ta saka turarenta Amber oud new edition na kamfanin Al haramaini.
Tunda ta fito Mama ke Mata wani irin kallo Wanda har saida ta rinqa Jin ta takura kafin Hameedar ta fito.
A kasa suka taka suna Hira har su
laje gidan,sun Dan jima suna Hira da marara lafiyar kasancewar breast lump ne aka cire Mata ba wani serious case bane.
Lokacin da zasu tafi suka Kara komawa gurin mamanta sukayi Mata sallama suna zaune ne da a falonta kafin meenal din tayi Mata magana ta f
ito. Wani handsome guy ne ya shigo falon da sallama ya Dan jefa car key dinsa sama, kana ganinsa kasan hutu ya Kama jikinsa.
Ciki ya shigo lokacin da Suke amsa masa sallamarsa kujera two seaters ya zauna a Kai wadda ke facing dinsu Hameedar.
Gaishe shi suk
ayi su Duke ya amsa Yana cewa "Hameeda daman kina Nan na Dade ban ganki ba gaskiya Ina ga tun kafin na tafi Colombia fa".
Dan rausayar da Kai tayi tana fadar "wallahi Kam Ya Sahal an jima Kam kune dai bakwa ganuwa Kuna uwa duniya kunyi shiru Kum barmu da z
afin Kasarmu".
Ta fada tana dariya.
Dai dai lokacin mommyn su meenal din ta fito kallon Sahal tayi tana fadar Kai Kuma haka mukayi da Kai?"
Kaisa ya Dan Sosa da key din hannunsa Yana fadi "Iam so sorry Mom kada ki damu yanzu zanje na kawo Miki in Sha Alla
h."
Ya fada Yana mikewa da nufin tafiya Meenal tayi tsagal tana fadin "Dan Allah Ya Sahal ka tafi dasu tunda cikin garin kayi.
Suka yiwa mommy sallama da godiya suka fito da leda Mai Dan girma a hannun Meenal wadda mommyn ta Basu.
Har kofar gida ya kawos
u suna tsayawa ya kalli Hameeda Yana fadar "Dan Allah ki bani aron sister din take Mana Kona ten minutes ne Mana".
Dan murmushi tayi tana fadar.
"Ka Fara yiwa Abban mu magana dai haka Naga anayi"
Ita dai Zahra ciki ta wuce Dan Kamar a kan.kaya take duk ya
takura Mata da wani irin kallo har a cikin mota ma saita mirror yayi sitinta tunda Hameeda ce ta zauna a seat din gaba tana Masa Hira Amman gaba daya hankalinsa yana kan Zahra.
Ita dai zahra Bata San yanda suka Kare ba taga dai Lokacin da Hameedar ta shigo
ta wuce dakin su.
Bayan kwana biyu da zuwa gidansu Meenal da yamma su zahra sun tafi islamiyya ne baki sukazo gurin Alhaji Jafar, ya sansu farin sani daya kanin Dan majalissar su ne dayan Kuma kanin Babansu.
Yayi mamakin ganinsu Saida suka gaisa ne suka
bijiro da abinda ya kawo su na yiwa yaron gurin Dan uwansu Sahal kidiba yaga yarinyar gurinsa Yana so. Shine mahaifansa ya turosu ya gabatar da maganar Yana neman izininsa na Fara zuwa gurinta Shira.
Alhajin yaji Dadi sosai na yanda suka zo suka memi izini
nsa duk da Daman sharadinsa kenan, ya Kuma nemi Jin wacece daga cikin yaran suka gada Masa zahra ce, nan ya amince musu da addu'ar Allah ya hada kawunan su.
Tun daga lokacin Sahal ya Fara zuwa gurin Zahra cikin ikon Allah tayi na'am dashi Basu Dade sosai b
a sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a unguwar yasan irin soyayyar da sahal yakewa zahra kusan Kullum da yamma Yana nan makale da ita, a haka har manya suka shiga maganar aka tsaida lokaci wata shida inda zasu tafi Colombia
inda yake hada masters dinsa ita kuma zata Fara nata degree din.
Anyi lefe na garari Wanda ya dauki Baki fiye da tunanin Mai tunani, an kashe kudi Kamar ba'a San zafinsu ba.
Lokacin da bikin ya rage baifi saura wata biyu ba sai lamarin ya Fara canzawa kwat
a -kwata Sahal ya rage zuwa gurin Zahra haka ma sai a kwana a wuni Bai kirata ba, duk wani zazzari da yake na bikin su events din da yake ta faman damun zahra da maganar duk ya daina Kai tafi-tafi sai ayi kwana uku hudu har sati Bai kirata ba, da farkon a
bin tana kiransa taji ko lafiya a yanayin yanda yake amsa Mata wayar saita hakura da Kiran nasa, tun Ammah na zuba ido har ta samu Zahra a wani dare ta tsareta da tambayar ko wani Abu ya hadata da Sahal ne? Ta Bata tabbacin ba abinda ya hadasu sai dai ta f
ada Mata yanda suka ringa yi dashi a kwanaki idan ta Kira shi.
Addu'a Ammah ta Bata tace ta ringa yi itama zataci gaba da yi, Mata sannan ta umarceta da kada ta Kara kiransa a wayar ta zuba ido kawai.
Duk abinda Ammah take na shirye-shiryen Baki Bata fasa
ba, tayi waya mutanan Jordan ma sunce suna Nan tafe Amma a daure a turo Zahra Kamar saura wata data bikin.
Ba'afi sati daya da waya da kakanninta na uwa ba sakon kayan dakinta ya sauka Nigeria daga Istanbul kayan da suka gigita Mama Dan ba kayan Wasa ban
e set din gado har hudu kujeru set uku bayan electronics kuwa wasu har ba'a San amfaninsu ba sai dai idan an duba manual din.
Alhaji Jafar yayi fada Kamar ya Ari Baki lokacin daya Kira Abbie akan danme zasuyi Masa haka toshi meye amfaninsa da bazasu Bari y
ayi Mata kayan dakin ba.
Hakuri Abbien ya shiga bashi akan su basuyi Dan su Bata Masa raiba, sunga abinda ya kamata suyiwa diyar Najwa kenan.
Ammah da Mama Alhaji Jafar ya Kira ya fada musu tunda an Riga an yiwa zahra kayan dakin da duk abinda ya kamata to
ga fifty million Nan ya baiwa Zahra idan komai ya nutsa saita Fara business na abinda take son sayarwa sannan ya Bata shanu biyar.
Kuka Ammah ta saka saboda Dadi ta rasa bakin da zatayi Masa godiya, yanda take dawainya da wannan marainiyar Allah Bai taba
gajiyawa ba.
Mama ce ta Ari bakinta tana ta yiwa Abban godiya da saka Albarka sai faman dariya tace bakinta yaki rufuwa, tun Ammah na ganin dariyar farin ciki ce har ta Fara wani tunani na daban, Nan da Nan ta Kori shaidan akan abinda zuciya ke sawwala Mat
a.
Lokaci na Kara tafiya daukewar ma'amala na Kara yawaita a tsakanin Sahal da zahra, yanzu ta Kai kwata-kwata sun daina waya dashi, ana saura kwana talatin da hudu a Fara biki Wanda yayi daidai da saura kwana uku zahra da Hameeda da Abdul Hakeem su tafi
Istanbul. Dan direct gurin kanwar Ummeen Hanifa zasu tafi daga baya su Ummeen sun samesu a can, idan an Gama komai su rankato Nigeria Dan da gaske Ummee ta shiryawa bikin sosai.
Washe gari, tunda gari ya waje Mama ke Kai kawo tsakar gida duk da ba aikint
a bane ba Kuma halayyarta bane hakan. Yayin da a bangaren Ammah ta rasa me yake Mata Dadi duk kasala ta baibayeta jinta take Kamar ma zazzabi na neman rufata...
💋
❤
💋
❤
️️
AUREN HUCE HAUSHIN
💋
❤
️
💋
❤
️
🔷
PEGE TEN
🔷
Story
&
Written
By
MAMAN FATIMAH
******Jujjuya littafin project din Ardo yayi, sai Kuma ya mikawa Alhaji Jafar Yana fadin "Duba ka gani Yallabai ni tunda ba ganewa zanyi ba,naji Dadi da Allah yasa aka Gama wannan karatun ba domin na saka auduga na toshe kunnuwa naba da
ba'ayi karatun Nan ba, tunda Wanda yaso auren nata yace in dai zatayi karatun Nan shi ya fasa, shi Kuma Dan uwanta na wajen kanena yace karatu Babu gashi tunda tana ganewa Kuma tana so, kaga yanzu duk gurin nan namu ita me yiwa mutane Allura".
Kallonta Al
haji Jafar ya karayi,sannan ya kalli Ardon Yana fadin.
"Yaushe ta Fara karatun ne na ganta karama amma har ta hada diploma?"
Gyara tsayuwa Ardon yayi Yana fadin "wallahi am tun tana aji hudu na furamare Dan uwanta ta kaita aji daya na sakandire tunda yayi
wani zuwa suka zauna da kannen nasa yaga tana da kokari shine yace Mata idan ta Gama makarantar tana son taci gaba da karatu, shine tace Masa tana son ta Zama malamar asibiti, to tunda sukayi haka ya kudurci aniyar tsayawa akan karatunta shi yasa da akayi
Mata chaaaa akan maganar aure yace Bai Hana ayi maganar aure ba. Amma ya Dora sharadin saidai idan mijin ze barta tayi karatu abinda ya gagara kenan aka fasa Amma duk yan uwanta anyi musu".
"Masha Allah. Allah ya Sanya Albarka, haka ake so a rinka barin Ya
ra Mata suna karatu barin ma na bangaren lafiyar da malaman makaranta, yanzu ba cewa kayi ita ke yiwa mutane allura ba da sauran abubuwa? To da batayi karatun ba da basai an tafi wai gurin an nema ba? Ba komai in Sha Allah zatayi auren ta Kamar kowa".
Ardo
ya amsa da "Allahumma Amin".
Ma'un Alhajin ya kalla "Asma'u kin amince na tafi da project din naki na duba a hankali in yasa said dawo Miki dashi".
Kai ta gyada alamar Eh.
Sunyi sallama da Ardo tawagarsu suka wuce zuwa Yola inda zasu bi jirgi zuwa Abuja.
Wannan shine silar haduwar Alhaji Jafar da Ammah, ya koma maida project da Kuma kafa gwanatinsa cikin ikon Allah suka yarjewa juna.
Lokacin da magana tayi karfi Rabi'a taso tada hankalinta saida Nanna ta taushe ta da kalamai masu kwantar da hankali.
Cikin
kankanin lokaci akayi bikinsu. Amarya ta tare cikin ikon Allah zaman Rabi'a da Asma'u ya kasance Zama Mai tsabta.
Wata uku da auren Asma'u ciki ya bullo duk masoyin Alhaji Jafar ya Taya shi murna sosai a lokacin ne Alhaji Jafar ya biyawa Rabi'a makka kusa
n abinda ya kwantar Mata da hankali kenan Dan ya fada Mata idan take tayi addu'a sosai akan matsalar ta.
A haka rayuwa ta dunga gurguwa har cikin ya Isa haihuwa Ardo dasu Inna maimuna sun so Ma'un to koma gida zaman haihuwa Amma Nanna ta Hana tace meye amf
anin ta ita in dai sai Asma'u ta koma gida.
Cikin ikon Allah a wani dare nakuda ta tasowa Asma'u lokacin Alhajin Yana nan, Nan da Nan suka nufi asibiti wurin karfe biyu da rabi Amma kafin hudu Allah ya dauketa lafiya ta haifi takwaye mace da namiji.
Murna
gurin wannan iyalin ba magana ranar suna yaran aka bar musu sunan su sai dai su Hassan da Hasana aka daka musu.
Kullum yaran suna tsakanin Rabi'a da Asma'u suka rainon 'ya'yansu. Lokacin da aka yayesu a lokacin Allah ya baiwa Rabi'a ciki itama ba'ayi wata
biyu ba Asma'u ma ta Fara laulayi, cikin ikon Allah cikin Rabi'a ya zauna kusan lokaci daya suka haihu Rabi'a haifi Hamza yayin da Asma'u ta haifi Abdul Hakeem.
Bayan haihwar Hamza Rabi'a Bata Kara haihuwa ba Saida Asma'u tayi maza biyu sanan Rabi'a ta hai
fi mace Murjanatu, bayan Murjanatu Rabi'a ta Kara haihuwar Salma sai auta Hameeda ita Kuma Asma'u ta haifi Sulaiman sai auta Musaddiq, zuwa lokacin sunansu ya bace yayin da ake gadawa Hajiya Rabi'a Mama wasu na waje suce Hajiya Mama, Hajiya Asma'u Kuma Amm
ah.
WACECE FATIMAH ZAHRA?
'ya daya tilo ga kanin Ammah shaqiqi Muhammad Sani. Mahaifiyar Zahra Najwa Balarabiyar Jordan ce sun hadu da Muhammad Sani ne lokacin da yaje karatu kasar da farko mutunci suke da Najwa sai daga baya ya juye ya Zama soyayya har
Allah ya nufesu da aure da taimakon wani malaminsu Dan kano Dan kusan ta bagarensa su Ardo wanda suke Kira Baffa ya Sani ya Kuma amince da Malam Muhammad Kabir ya Zama waliyyin Muhammad Sani a can.
Lokacin da Muhammad Sani ya Gama karatu ya zauna a can ya
yi aiki kusan shekara biyu daga baya ya tattaro nasu ya nasu suka dawo Nigeria, lokacin Najwa nada cikin Zahra wata bakwai a lokacin Kuma Ammah na goyon Sulaiman Mama na goyon Hameeda.
A Jimeta Muhammad Sani ya sayi gida saidai suje Mubi kawai suga iyaye
nsa,ba dadewa Najwa ta haifi 'yarta Zahra wadda taci sunan mutum biyu mahaifiyar Najwa da Mahaifiyar su Ammah.
Haihuwar Zahra ba dadewa Muhammad sani ya Sami aiki a Abuja karkashi minstary of internal affairs da taimakon Alhaji Jafar.
Zahra nada wata biyar
wani cikin ya bullo a jikin Najwa Mai wata irin masifar laulayi, Wanda ya tilasta Ammah ta dauke Zahra daga bakin nono.
Lokacin da komai da dai dai ta a gurin aikin nasa ya dauki Najwa suka koma Abuja.
Saida watan haihuwarta ya Kama ya kaita Mubi shi Kuma
ya koma Abuja.
Lokacin data haihuwa iyayenta sunzo Nigeria da kanwarta Nawwara a Karon na biyu Mahaifiyar ta taso tafiya da Zahra Ammah ta dunga magiyar abar Mata ita harda kukanta.
Lokacin da suka Gama wanka Muhammad sani yazo ya tafi dasu tafiyar da ha
r abada Basu dawo ba a hanya sukayi hadari sun bar Jos Basu karasa Abuja ba.
Yan uwa da iyaye sun shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa Ammah tayi Kika Kamar ba gobe,ta rasa Dan uwanta shakiki, ba karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin Ummee kakar Zahra
ta hakura ta barwa Ammah Zahrar.
Tunda daga lokacin Ammah ke baiwa Zahra wata irin kulawa ta musamman sai Kuma shima Mai gidan ya kwallafa ransa akan soyayyar yarinyar abinda ya haddasa tsana Mai tsanani tsakanin Mama da zahra inda ita mamar ke ganin Kama
r nema ne yasa Alhaji ke kaunar Zahra, tana ganin idan Dan tana 'ya mace ne karama ai itama tana da nata kananan 'ya'yan mata Amma baya nuna kulawa akasu Kamar Zahra ko Dan tafisu kyaune tunda Babu inda ta baro uwarta.
Wannan kenan.
Ranar da za'ayi jarab
awar share fagen shiga karamar secondary ta gwamnatin tarayya tun sassafe zu Zahra suka shirya ita da Sulaiman da Hameeda da Salma duk da Salma ta girmesu Amma yawan yi Mata repeating yasa suka taddo ta.
Har sun shiga mota Bala direba na niyyar shiga Zahra
ta bude ta fito da sauri ta nufi cikin gida Sulaiman Yana kiranta tayi banza dashi ta shige da gudu ta karasa dakin Ammah tana fadin "Ammah na manta kayana da Ya Hassan ya kawo min har zamu tafi na tuna".
Daga toilet Ammar ta fito ta nufi bedside locker
ta janyo ta mikowa Zahra ledar tare da fadar "Maza kada ku makara mana".
Kai Zahra ta gyada kafin tace "Ammah ki kara yi Mana addu'a Dan Allah Ina son naci jarabawar saboda Abbana yace idan naci makarantar zemin kyautar wani Abu"
"To naji maza Allah ya bad