Showing 69001 words to 72000 words out of 295116 words

Chapter 24 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

aka Basu Wanda ba shine zabinsu ba su kashe shi su auri wanda suke

so".

Tunda ya Fara Kora bayani Zahra tayi masa kur da ido tana Mai maita.

Kai Sameer ya shiga girgaizawa Yana mamakin wani sabon hali da Mahmud din ya tsira, yaga alama nema yake ta Hana yarinyar Nan sakat.

Ita Kuma tunda ta furta zanci Bata Kara tofa k

o kalma daya ba, sai kawai ta dauki fork ta cako Irish din ta Kai bakinta ta tauna ta hadiye, pepper chicken din ta dauka taci ta dauki kunun Madarar ma ta Sha duk Yana kallon ta shi kuwa Sameer Yi yayi Kamar Allah Bai halicce shi a gurina ba.

Tana gamawa

ta tura kujerar da take Kai baya sannan ta dubi shi ido cikin ido tace.

"Gashi naci idan kana tunanin zan zuba maka poison a abinci kayi kuskure lalacewar tawa Bata Kai haka ba, Idan na kasheka wace riba zanci? wato ka tafi lahira free ko? duk lodin zunuba

n daka dauka niga sakarai na lodawa kaina, to Bari na fad'a maka ba saina aikata zunubi irin haka zan rabu da Kai ba A'a salin alin kowa ze kama gabansa ni da Kai tunda daman masu iya magana na cewa tsintacciyar magen Bata mage nasan komai Daren dadewa zak

a koma inda ka fito".

Ta fad'a Tana wurga masa harara ta wuce ta kyalesu batabi ko takan Sameer da yake fadin "Allah ya huci zuciyar amaryarmu".

Da ido Mahmud yabi Zahra har ta bacewa ganinsa "Wai shi yarinya kamar wannan zata saka shi gaba ta fada Masa so

n ranta amma yayi shiru Yana kallon ta".

Sameer ne ya katse Masa tunanin da yake.

"Dan Allah kada ka koya matsa tsiwa wlh da gani Bata Saba ba, bakaga jikinta har rawa-rawa yake ba".

Ya fad'a Yana kallonsa.

"Jikinta na rawa kenan Kare mata kallo kayi har k

aga jikinta na rawa ni ban gani ba?".

"Subhanallahi! Wace irin magana ce haka wlh ba haka nake nufi ba, Bari naje kawai sai munyi waya".

Ya Mike Yana aje rafar dari biyar guda biyu Yana fadin "A bawa madam ace Mata na wuce tunda ka Hana muyi sallama".

Ya b

iya Kan center table ya dauki keys dinsa yayi gaba tunda yasan ba magana Mahmud ze Masa ba Dan da gaske yazo wuya yanda yanayin fuskarsa ta nuna.

Bayan fitar Sameer, Mahmud kasa ko motsin kirki yayi wai shine tsintacciyar magen? Da gasken gaske maganar ta

dokeshi kwafa yayi Yana fadin zakiga tsintacciyar mage iya ganinki sai kin gane bakin rijiya ba gurin wasan makaho babe".

Ji yayi kwata kwata abincin ya fice masa raga Rai duk yanda yake jin yunwa ture abincin yayi ya Mike ya nufi bedroom dinsa Bai jima b

a ya fito cikin shigar yari filtex fari dinkin boda da farar hula a Kansa Yana baza qamshinsa na Ibada, yayi waje.

Tunda Zahra ta Fadi maganar dake ranta taji zuciyarta wasai, gefen bed dinta ta zauna tana mita.

"Haka kawai saika wani ringa sakarmin magan

a ba control duk abinda yazo bakinka saika fad'a mini, Wai na saka wani Abu girkinma ba saina Kara yo da Kai ba sannan na Zama suspect daman saboda A kashedin Ammah ne yasa nayi, kwana biyu amma kamar na shekara duk ka matsa min ka karbe min waya nayi Shir

u na Zuba maka ido Naga gudun ruwanka, na fita mikawa bawan Allan Nan abinci kace da izininwa? Haka kawai ka zamar min karfen kafa".

Ta fad'a Tana kwafa.

Tunda gari ya waye Ammah Bata zauna ba shirye-shiryen tafiyar Inna maimuna take wadda zata tafi yau,

cikin Shirin fita unguwa Mama ta shigo lokacin Ammar na zubawa innar kilishin da Abba yasa akayi Mata zaunawa tayi tana Fadin "Inna yau zakiyi Mana ta Baki wlh ba dadi".

"Kayya Hajiya Rabi banda abun yazo da sammazi Aida na jima da tafiya gida daga zuwa b

iki na share our na zauna kinsan da Ardo Yana Raye hakan ba zata faru ba yaushe ze Bari".

"Haka ne Kam Allah yayi musu Rahama".

"Amin" su Inna suka amsa.

Leda mamar ta aje kusa da innar tana Fadin.

"Gashi Inna ba yawa Allah ya kiyaye hanya ni fita zanyi

unguwa nasan kafin na dawo kin tafi".

Gdy innar da Ammah sukayi Mata ta tashi tana yiwa innar fatan sauka lafiya.

Sai bayan ta wuce ne innar ke tambayar Ammah ina Hameeda ne Naga tun she jiya da safe bata qara ganinta ba.

"Jiya kina barci tazo Nan Wai ta t

afi Jos gurin yayar mamansu larai".

"To ba laifi hakan ba laifi daman shekaranjiya ne da dare na fita zanje can inda na baza ganyen yandi Dana shanya naji uwar tana surfa Mata zagi ban dai San dalili ba Amma naji ita yayar tata tana Fadin sai kije kiba Zah

ra hakuri Mana tunda kanwar uwarta ce ni dai Nan na barsu Dana dauko shanya ta".

"Allah ya rufa asiri kowa yayi nagari Kansa ya yiwa kuma sharri Dan aike ne duk inda ka tura shi ze dawo, bansan abinda yarinyar Nan ta tsare musu ba, bana raba day biyu da ab

inda sukasa Hameedar tayi inaga daga baya ta gane Bata kyauta ba shine tayi magana uwar ke zaginta".

Sun Dade suna tattaunawa.

Gurin Sha Sha daya da rabi magaji yazo ya dauki Inna maimunar zuwa gidan Zahra.

Zahra na barci Dan batasan lokacin da barci yayi

awon gaba da ita ba, cikin barcin taji alamar bell din kofa ta yunkura ta tashi ta yafa Veil din rigar saman gashinta.

Tana budewa taga Inna maimuna da magaji, jikin innar ta fada kawai sai ta saki kuka Wanda ita kanta bata San kona menene ba.

" Ke matsa

can da Baki rabuwa da shiririta saboda Allah menene abin kuka magidanciya dake, Dan Allah duba min Nan Mai sunan malam wannan ai rashin wayo ne koba haka ba?"

Ta fad'a Tana kallon magaji, duriya yayi Yana fadin "kumfi kusa Inna na bankwana ne tunda Idan K

ika shige wannan lungun Sai baba ta gani, ni Naga ma kinyi Rana gaskiya har yanzu Baki tafi ba".

"Ai a Gombe zanyi kwana biyu gidan Dan aminiyata da nayi rainonsa to nayi Masa Alkawarin zuwa idan zan tafi".

Ita dai Zahra tunda ta kwantar da kanta a cinyar

Inna maimuna Bata Kara dagowa ba, jinta a jikin innar sai takejin wani sauki da nutsuwa suna saukar mata.

Gashin Kanta innar ta Dan shafa inda gashin ya fito tana Fadin shi dai wannan gashin baisan kitso ba Kullum Yana Nan a nannade kamar gammo".

Dan tur

o Baki tayi tana Fadin

"Ya zanyi kinsan ba kitsuwa yake ba ko anyi idan ya Dade kwana biyu ne kawai ga zafi".

"Allah ya kyauta kawai dai 'ya'yan zamani Amma har yaushe za'a yita Zama da Kai haka? Yau Wai uwar taku tace meya samu wayarki ko an Kira Bata shi

ga? tasan ba rashin caji bane tunda ance Kuna da wannan abar Mai amfani da hasken Rana"

Dan Jim Zahra tayi tace ya karbe wayar ai hakan be dace ba, Sai kawai tace.

"Nima bansan meye matsalar ba kawai rufewa tayi taqi kunnuwa".

Magaji ne Wanda yaketa faman

cakular waya dago Yana fadin dauko mugani ko abun minor ne".

"Bata gurina tana gurinsa ban sani ba ko dubawa ze bada ayi".

"Shu wa?"

Ya fad'a da sigar zolaya, banza tayi masa kamar bataji ba.

Tashi daga jikin innar Zahra tayi tana Fadin Bari na dawo wlh mu

rnar ganinki ta mantar Dani ko ruwa ban kawo Miki ba". Tayi gaba innar na Fadin "dawo Zahra'u nida ba bakuwa ba".

Gaba tayi abunta.

Saida ta ciko tray babba da dangin Zaki da sanyi har sauran pepper chicken din ta zubo musu, tunda ta aje innar ke binta da

kallo tana jinjina abin wannan cimakar bata mai Karamin kafin bace ko ance gida tallafin qungiya ya samu har abinci ci susuka dauki nauyin bashi?"

Ita dai shiru tayi Bata tofa ba Amma a kasan zuciyarta da maganganu fal Wanda zasu tattaunawa da 'yarta.

War

e ciki magaji yayi ya kwashi gara har Inna na Masa Dan biki.

Wayarsa Zahra ta barba ta Kira Ammah ta gaisheta itama abinda ta fadawa innar ta fada Mata game da wayar lokacin data sauke wayar harda share 'yan hawayenta, magaji Yana Mata tsiyar shatwabarta t

ayi yawa ita Batasan ta kusa Zama uwa ba,Inna na Taya shi.

Sai da Innar ta Gama sannan ta tambayi Zahra.

"Wai Ina Mai gidan nawa ne banji motsinsa ba tunda nazo?"

Kafin Zahra ta lalubo abin fad'a magaji ya rigata Yana fadin.

"Ai kin baroshi can a unguwar m

u gashi nan suna magana da Ya Abdul Hakeem a kusa da masallaci har suka daga Mana hannu".

"Awoh to ai kasan ban waye dashi ba sai a hankali".

Nasiha Sosai da ban baki Inna maimuna ta Kara yiwa Zahra tare da kara jaddada Mata mashinmancin biyayya ga miji.

K

aya Zahra ta zubawa inna a wata babbar leda harda atamfa dasu turaruka taba Magajin ya rike mata.

******

Tafiya ce miqqqqiya daga Azare zuwa Babban mutum ta Babura jihar jigawa, direban daya dauko Mama da Asabe ya Dan juyo yana kallon Asabe wadd

a ta maida hankali gurin cin doyarta da kwai da suka saya a kanya babba yace ",munzo Babban mutum fa Ina zamuyi kinyi shiru alhalin kece idona tunda wannan ba yanyata bace".

"To na manta wallahi kasan da Dan Habu muke zuwa na zata shine ita dai Mama Bata

cewa komai Dan niqab nema a fuskarta badan ta matsu da son ganin malam na bande din ba da ba yanda za'ayi tayi wannan kasadar Dan yanda ta fadawa Abban Itas/gadau zasu wata dubiya Alhajin yaso Bala direba ya Kaita ta nuna Masa da kawarta matar tshon Ambass

ador zasuyi tafiyar abinda ya Hana Bala direba kaita kenan, hanyar tinkin ta nuna Masa alamar Niger zasu shiga.

"Yanzu ke Asabe a she Niger zamu shiga shi ne kikace min kauyen Babban mutum wlh da bani da takardar ecowas da Saida na zubeku ku nemi wadda zat

a karasa daku kinsan kuwa yanda suke da doka da order?".

Tafiya ce miqqqqiya daga Babban mutum zuwa bande, sun Sami tarba Mai kyau daga yaran malam na ciki suna fitowa su Asabe suka shiga malam din yana zaune akan buzu da wani zabgegen carbi a hannunsa ya

amsa musu sallamar su suka zauna suna gaishe shi.

Asabe ya dago kai kalla.

"Baki fad'awa Hajiya sakona ba?"

"Allah ya taimaki malam na fad'a Mata cewa tayi na kawota gurinka tazo taji Koda yanda za'ayi lamuran ne suke neman canza fasali".

Carbinsa ya Fara

ja yana girgiza Kai yayi hakan kusan say uku kafi ya sauke wani dogon numfashi yana Kara girgiza Kai.

Mama cikin kidimewa ta furta.

"Da matsala ko malam?".

"To da matsalar Amma Abu mafi ban mamaki shi yaron har yanzu bana ganin komai akan Lamarinsa kwata-k

wata sai yau Naga wasu mutane a Kan lamarinsa da Kuma itama yarinyar an tasa ta gaba da dafa'i shiri Kuma na gasken gaske sai dai naga wata tafiya a gaban mijin nata da alama Kuma tafiyar da Alkhairi q a cikinta sai dai idan dauke hankalinsa za'ayi daga ga

rin kwata kwata, idan ya tafi ya kasa ko tunanin garin bare ya dawo, idan ba haka akayi musu ba ba makawa sai kin Zama 'yar kallo a gidan dan duk yaran gidan Mata ba wadda tauraruwarta ta kama kafar tata da gaske haka Allah ya yita da madaukakin Alkhairi".

Zuru Mana tayi ta kasa magana, maganar dai ita kenan Zahra tafi nata 'ya'yan.

"Malam ayi duk abinda ya Kanata inda hali ma ya rattaba Mata saki kafin yabar garin".

""Abinda ban gani ba kenan a cikin auren nasu Dan Idan shi ne ze saketa to inaga sai dai ta

mutu da auren Dan Banga hakan ba a tare dashi,ni a yanda na gani a istiharata ma ya Santa batun a Nan garin naku ba Kuma da soyayyar ta Mai karfi a zuciyarsa wadda har abada baze iya rabuwa da ita ba, ayi dai hakan yanda Idan iyayenta suka gaji da jiran d

awowarsa Bai dawo ba su raba auren da Kansu". Bayanin ya kwantawa da Mama hankali, ya kawo abubuwa ya bata har Wanda za'a hada da tuaren wuta a bawa zahrar Idan harta turara Mahmud ya shaqa shida Azare har abada.

Kudi masu kauri Mama t

✨✨



✨✨





💎

AUREN HUCE HAUSHI

💎





✨✨



✨✨





MAMAN FATEEMAH





PAGE TWENTY FOUR (24)





_____ Tun bayan tafiyarsu Inna da magaji sai gidan ya zamar Mata shiru Bata Dade a parlourn ba ta koma ciki, da taga tunani yana

neman ya dameta saita dauko qur'an dinta ta Fara karatu Saida taji Kiran sallah ta aje taje tayo alwala.

Bayan ta gama sallar ta Haye gado ta Kara A/C tayi kwanciyar ta ba tafi minti talatin da kewnciya ba taji alamar Baki ana Danna bell, tashi tayi

ta nufi kofar da gaske dai bazata samu barcin na kirki ba,Kofar ta bude a hankali su Amatu ita da Aunty safiyya ne guri daya suka zauna a Dr sulaimanu Adamu model school of Hygiene inda tayi service, su Kuma permanent lecturers, rabon ta da Amatu tun ranar

daurin aurenta dan lokacin da zata wuce jama'are garinsu Bata biyo ta gidan Ammah ba daga gidan Aunty Hasana ta wuce kawai. Cikin nuna tsantsar farin ciki Zahra ta rike hannun Amatu tana fadin "wlh nayi fushi Amah Ina nan Ina jama'are? Amma kikaqi dawowa

ni Aunty safiyya zanyi welcoming kawai Amma ke kam dai sai a hankali kawai, Aunty sannu da zuwa". Ta fad'a Tana Basu hanya tare da karbar yaron Aunty safiyya dake hannun Amatun.

"Hakan ma na gode tunda an karbi Auntyn ai shike nan tunda ita ta gari batay

i laifi ba saini da nake can kauyen mu".

Ta fad'a Tana Zama a cikin one seat dake kusa da ita.

"Eh wlh Aunty tana da excuse a gurina tunda nasan Bata Nan taje gida sokoto Amma ke kuwa ko waya fa Baki Kira kinji ya ake ciki ba".

"Kice dai ban Kira ba. Amma

tambayi Sajida kiji na kirata yafi sau ashirin ma ke dince lokacin Kiran baze yuwu ba Sai ki qara narkewa".

Dariya suka saka su duka harda Aunty safiyyar.

"Wlh Amah saina rama kinci bashi, Wai na narke kamar wani danyan tuwo".

"To da mecece? mutuniyar dake

somewa Kikayi fa dif kika dauke wuta".

Kyale Amatu Zahra tayi ta karasa kusa da Aunty safiyya ta zauna ta Dora Shureem a Kan cinyarta tana Fadin.

"Aunty sannu da zuwa Ina yini?"

"Lafiya kalau Amarya ya Amarcin Naga ya barbeki kanwata Masha Allah".

Dan si

nne Kai tayi tana Fadin "Kai Aunty Ina wani Amarci a Nan kawai dai".

"Gulmammiya Kinga yanda kikayi wani mahaukacin kyau kuwa? Ai da gani Amarci ya tabbata a gare ki,wa Zaki kife a baibai yarinya Kar nake kallonki fa".

"Allah ya shiryeki tunda haka Kika za

ma, Bari ki gani".

Ta Mike da Shureem a hannunta ta nufi kitchen, saida ta Zuba musu kayan garar a plate ta dauko musu ruwa da drinks ta dauko plate ta fito tana Fadin "Amah shiga ki dauko dayan Dan Allah".

Sai da suka Gama sannan Zahra tace su shiga suga

gidan, ko Ina suka shiga Fadi suke Masha Allah! a gurin fridge din dake cikin Dan Arc din dake tsakanin kitchen da dining area ne Aunty safiyya ta kasa hakuri Saida ta magantu lokacin data Kai hannu ta bude tana fadar.

"Yau ne ganina na biyu da fridge din

nan naso shi kamar qaddara Amma da aka fad'a Mana kudinsa Saida na Raina kaina"

"Kai haba Aunty bakiyi niyyar saye bane".

Zahra ta fada.

'yar dariya Auntyn tayi. "Bazaki gane ba Idan ci baizo daya ba ai koshi ma baya zuwa daya".

"Haka ne kam Aunty".

Amat

u ta fada, suka nufi bedrooms dinta ko Ina dai maganar daya ce Masha.

Amatu ce ke fadar "Allah ya mayar damu danshinki".

"Amin. Amma Banda kalubale irin nawa, ba Dadi Amah har gobe abun Yana damuna bani da nutsuwa ko Kankani wlh duk lamurana sun tsaya cak

bani da wani karsashi irin na amarya a gidanta, komai ganinsa nake Wai banbarakwai kamar a mafarki haka".

Sai Kuma idanunta ya ciko da hawayen da taketa kokarin kada su zubo.

"Ayya haba Zahra kiyi hakuri Mana, ai zuwa yanzu yaci ace kin hakura da koke-koke

n Nan tunda Mai abkuwa ta abku ai sai hakuri ki rungumi abinda Allah ya Baki ki dangana wata Rana sai labari".

Aunty safiyya ta fad'a.

Parlour suka dawo sukaci gaba da Hira, rabi duk ban Baki ne Aunty safiyyar kewa Zahra da nuna Mata ribar hakuri a cikin

hirar ne Amatu take fadawa Zahra sakon Sajida na tana kiran wayata Amma Koda yaushe switch off.

Dan lumshe ido tayi sannan ta bude tana kallon Amatun.

"Matsala wayar ta samu shi yasa ba'a samuna Amma in Sha Allah soon zan sayi wata, yanzu bani taki na kira

ta".

Wayar Amah ta Mika Mata tana dialing din number ta.

Tana dauka ta Fara mata tsugudidi.

"Yau wacce Rana Amatu ta kirani".

"Assalamu Alaikum ayi sallama Mana bestie".

Ta fad'a tana murmushi.

"Kai!!! wa nakeji haka bestie, haba Dan Allah kin kyauta kenan

ba waya ba wasika kin barni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login