Showing 12001 words to 15000 words out of 295116 words
Sameer ya shiga mota ya fito ya nufi Malam Wanda har ya Fara t
afiya, sai Kuma yaja ya tsaya Yana jiran karasowar Sameer din.
Dan risinawa yayi Yana fadin "ko za'a samu Wanda ze rakani na Kara dubo jikin wannan yarinyar?"
Wani kallon kasan ido Mahmud ya bashi dashi "Wai yarinya".
"To! To! Masha Allah ai sai kuje da Ma
hmud din da Habibu kuga jikin, ai wannan tunani ne Mai kyau.Nima na shiga da safe gurin Alhajin naji yata kwana".
Har cikin harabar gidan Sameer ya shiga da motar, Abdul Hakeem Habib ya Kira kafin su shigo ma ya fito Nan Harabar gidan Yana jiransu.
Shi yay
i musu jagora zuwa falon Abban, yayi murna sosai da ganinsu sun gaisa sosai sun masa godiya sosai da karamcin da yayi musu, yaji dadi sosai Dan har ya ringa tsokanar Sameer Yana fadar "wato tunda kazo gabatar da aikinku ban sake ganin kafarka ba a gidan
Nan sai yau dana baku Mata ko? Dan na lura baka da aminin daya wuce Mahmud a garin nan. Masha Allah, Malam ya fada min duk Fadi tashin ku akan lamarin Allah ya saka da Alkhairi yabar zumunci".
Suka Amma da "Amin ya Rabbi".
Mahmud Alhajin ya kalla Yana fa
din "kayi hakuri fa Mahmud munyi maka nauyin kuka".
Kai ya gairgiza Yana fadin "ko daya wallahi ba komai nagode, Allah ya saka da Alkhairi ya Kara lafiya Nisan kwana Mai albarka"
"Allahumma Amin. Allah yayi Albarka, ya baku zaman lafiya ya baku zuru'a Mai
Albarka, sai ayi ta hakuri da lamarin Mata fa. Abdul Hakeem ku shiga ciki su gaisa da Iyayen nasu".
Wannan shine shigar Mahmud na biyu gidan, na farko lokacin da magaji yayi accident da mashin suka shigo shida Abdul Hakeem da Hamza ya duba shi a dakin Am
mah, dan ma lokacin ba kowa a gidan sunje gaisuwar mutuwa.
Directly dakin Hajiya Mama Abdul ya nufa dasu, Zilai Mai musu wanke wanke ce tayi zuruf ta shiga dakin Ammah.
Tana fadin "Ammah Ina Jin fa ga mijin Zahara'u Nan sun shiga dakin Mama shida Abdul Ha
keem da wasu inaga abokansa ne".
Ta juya ta fita.
Gyalen Inna maimuna Ammar ta dauka dake kusa da ita ta yafa a jikinta.
Da sallama Abdul Hakeem din ya shigo Yana fadin Bismillah ku shigo Mana, a nan kan carpet a kasa suka zauna suna gaishe dasu Ammar t
are da tambayar Mai jikin.
Abdul Hakeem ne yace " Inna mijin Zahra ne da ubangidansa suka shigo duba ta shi yau ze wuce shine yace a rako shi ya Kara dubata da jikin nata".
"Kai Masha Allah an gode madallah Allah ya saka da Alkhairi ya maida ka gida lafiy
a". Inna maimuna ta fada sannan ta kara da cewa "to waye angon nawa Dan nice ta karfe ita wannan Farafarar ba wani abun azo a gani zata iya ba ni kuwa ko banza na tuka maka tuwon dawa da man shanu ko ba haka ba?" Ta tambaye shi tana kallonsu.
Duk dariya s
ukayi Amma shi gogan Dan murmushi yayi kadan Yana basarwa.
Abdul Hakeem ne ya nuna Mahmud Yana cewa.
"Ga angon naki nan nagama kamar kunyarki yakeji"
"A'a! Masha Allah tubarakallah Mai gidan nawa wanke hannu daka taba ne, kaga dago ka kalleni ni Kaka ce k
ada kaji wata kunya ta".
Kara sadda Kai yayi shifa duk jinsa yake wani iri Wai shine a zaune a dakin surukai Ashe da gaske ana jin kunyar shi wallahi da ji yake kawai fada ake ba wani nauyin da akeji Saida ya same shi yanzu yake gaskata hakan.
A kaikaice A
mmah ta kalleshi "Masha Allah" ta fada a zuciyar ta, ita bataga wata makusa ba a tare dashi Kuma idan ba idon tane yake Mata gizo ba sai taga duk cikin Wanda zasu auri Zahrar a baya bataga Mai nagarat wannan yaron ba.
Albarka da nasiha dai ya Sha ta gurin
Inna maimuna.
A haka suka fito daga dakin har suka fito compound din Abdul Hakeem Bai fito ba sai duba agogo Sameer keyi Yana mita.
"Nifa bana son nayi Rana a tafiyar Nan gaskiya, Naga alamar kuma neman kuke kusa nayi yamma ma".
Kafin Mahmud ya bashi ams
a Abdul Hakeem din ya fito da sauri da key a hannunsa Yana fadin "kuyi hakuri key din ne ba'a gani ba da wuri ku karaso ciki kafin Zahrar ta fito ku gaisa".
Mahmud ne yace "Kai haba da an kyaketa ta huta ita da Bata da lafiyar kirki".
Karamin falo ne da k
ujeru masu kyau sosai da kayan kallon alama an tana deshi ne saboda Yara Mata na gidan da Kuma dai dai kun Baki.
Bayan fitar Abdul Hakeem, Sameer ya kalli Mahmud.
"Dan Allah my man yaushe idonka ya koyi kunya? Naga sai wani sadda Kai kake, nifa lamarinka y
a Fara bani tsoro na rasa wace alkibla ka kalla kazo garin mutane ka Mike kafa kana wata irin rayuwa a takure nace zan dauki mataki ka aje min sharadi, da kasan bazan it's tsallakewa ba, yanzu Kuma Rana tsaka a tarko aure Kai kadai kamar marar gata sai wal
agigi kake alhalin kana da madafa".
Tsaki yayi " kana da matsala wallahi ko me zance fada maka bazaka Gane ba, amma idan lokaci yayi zaka fashinmta,yanzu duk bayanin da zanyi maka ba fashinmta zakayi ba, kawai mu bar maganar kawaai"
Kanshin turaren ne ya
alamta musu zuwanta. sallama tayi cikin siririyar muryarta.
Sameer ne ya amsa Mata sallamar a zahiri Dan shi Dan gogan a saman lebensa ta amsa sallamar. Sameer din ne ya Dan Mike Yana fadar.
"Masha Allah jiki yayi sauki kam, "Bismillah". Yana nuna Mata kuj
erar gefen Mahmud. Kai ta dangirgiza Masa tana dan murmushi kasa kasa.
A Nan kan carpet ta zauna daga gefe tana gaishe da su a jimlace.
"Lafiya kalau"
Sameer ya amsa Yana fadin "ya jikin naki?"
"Alhamdulillahi" ta amsa masa.
Sai Kuma duk sukayi shiru, g
anin lokaci Yana qurewa Sameer ya Mike tare da kallon Zahra Yana fadin " To madam bako zeyi halinsa Allah ya bada zaman lafiya. Amma fa sai kina hakuri da halinsa gaskiya ba kirki ya cika ba Ina son idan na dawo Naga canji na zahiri a tare dashi, sunan Sa
meer Sa'ad koko, zeyi miki cikakken bayanin koni waye a gurinsa Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a mai..albarka Allah yasa next year by now muna bkin suna"
Da sauri Mahmud ya kalli Sameer a zuciyarsa Yana fadin "Allah ya shiryeka Sam baka girma".
A han
kali tace " Mun gode kwarai Allah ya tsare ya kiyaye hanya".
"Amin" ya amsa Yana kallon Mahmud.
"Ni zan wuce saina sake shigowa ayi kokarin ganin aikin Nan ya kammalu".
Ya fada Yana nufar kofar fita.
Sai lokacin Mahmud din yayi magana "pls ka jirani minti
biyar Dan Allah".
"Idan ya wuce haka Kam...."
Ya fice ba tare daya karasa fada ba.
Tunda Sameer din ya fita take wasa da karamin zoben da yake hannunta. Bata dagon kalle shi ba shi Kuma Bai tofa tasa ba amman idonsa Yana kanta, Kare Mata kallo yake Yana
fadar "Masha Allah tabarakakkahu ahasanil kaliqin".
Tsam ya taso daga inda yake ya sauko kasa inda take zaune.
"Ya jikin naki?".
Ta tsinkayi maganarsa kusa da ita daf Sam bataga lokacin daya taso ba.
Cikin daburcewa saboda kusancin nasu yayi matukar yawa
ji tayi kamar ma iskar gurin ta tsaya sai munfashinsa take shaqa kawai.
A mamakance taga yasa hannunsa ya dago fuskarta suka hada Ido hudu dashi. Da sauri ta runtse idanunta zuciyarta na wata irin bugawa.
"Bude idon Kona Baki mamaki".
Marmar ta Fara da
idon tana budewa a hankali Amma taki kallon nasa idon.
"Ya jikin?".
Ya Kara maiamaitawa, a hankali ta bude bakinta tace "da sauki"
Gamshin Lister mint ne ya daki fuskarsa. Banda Yana daf da ita ba yanda za'ayi yaji abinda ta fada.
"Allah ya Kara lafiya".
"Ameen"
Ta fada.
Hannunsa ya cire daga fuskarta yana Dan furzar da iska daga bikinsa ya Mike tsaye, a hankali ta sauke wani numfashi.
A bazata taji yace "bani wayarki"
Ba musu ta Mika masa, aljihu taga ya saka Yana fadin "ki shiga gida ki kwanta kiyi barci
sosai kada ki yawaita hayaniya ki samu hutu sosai, zan tambayi magaji idan bakya hutawa yanda ya kamata ni Ina da inda zan kaiki ki samu isolation, tashi muje ki shiga gida ana jirana".
Saida ta shige ciki kafin ya juya ya nufi gurin da Sameer da Abdul Ha
keem suke suna Hira.
Lokacin data shiga dakin ta Samu Aunty Hasana dasu sajida sunzo har da yaran duka.
Da guda ta karasa cikin suka rungume juna da Sajida Nan da Nan sai hawaye itama sajidar kukan ta fara.
Ammah ce tace "Naga abinda ya isheni meye haka
zaku tasa mutane a gaba Kuna kuka, to kukan maganin me ze muku aikin Gama ai ya Riga ya Gama Saida hakuri da addu'a kawai".
Uwar dakin Ammah suka shige.
Magaji ne yayi sallama ya shigo da manyan ledoji guda biyu niqi-niqi da kaya Auntyn Hasan na tambayar"d
aga Ina?"
Ya fice da sauran Yana fadin "ina zuwa Aunty"
Wata ledar ya shigo da ita Yana fadar"kayan dubiya ne aka kawo Mata" ledar daya kawo daga karshen ya bude rafar 'yan dari bibiyu hura biyu ya dauko daga saman kayan, Aunty Hasana ya
Mikawa yana fad
ar "gashi nan inji abokin mijinta Wanda suka shigo dashi dazu".
Godiya su Inna maimuna sukayi tayi kamar Yana nan a gurin suna ta Saka albarka.
********* Bayan tafiyar Sameer can gurin aikin gidan suka wuce, ba karamin mamaki Habib yayi ba har ya kasa
hakuri ya tambayi Bilyaminu lokacin Mahmud Yana ciki. "Dan Allah wane irin kudi gayen Nan ya bada haka Nan da Nan gidan ya juye ya Zama kamar daukowa akayi daga wata kasar".
"Wallahi Nima bazance ga abinda ake kashewa ba, iya kudin aiki Dana abinci kawai
suke a hannuna, bakaga wash bakin fuska ba su biyu?'
"Eh nagansu"
Habib ya fada. "To ai tun jiya sukazo da komai na aikin bakaga Nata'ala ba shima lebura ya koma kaga ai da malam shi yasa a Kira saboda 'yan gyare gyaren amman da masu iyawar sukazo shima ya
ronsu ya koma".
Ya fada Yana dariya.
"Wallahi Bilya sai a kyaleka Kai kowama sai ka tab'a".
"Gaskiyar kenan ni wallahi burgeni ma yayi tunda baiyi zuciya ba ya tafi, ko banza nasan Yana lure da koma Dan gyaran nasa aikin".
*****A bedroom din ammah Zahra
ce da Sajida suke tattaunawa akan abinda ya faru,sunyi iya nasu hasashen amma sun kasa gano bakin zare Sajida ce tace "nifa Zahra Ina hasashen wani Abu akan lamarin ki"
"Kamar me kenan?"
Dan Jim tayi kafin tace "Anya ba asiri ake yiwa duk wani Wanda yazo d
a niyyar aurenki ba? Ki tsaya kiyi nazarin abun Mana ko mafarkan da kike yi duk lokacin da maganar aurenki ta taso abin dubawa ne"
Dan murmushi Zahrar tayi "kin jiki kema bestie wane irin asiri Kuma,ana zaune lafiya to waye har ze bata lokacinsa da kudins
a gurin yi min wani Abu kawai daga Allah ne kinsan kowa da yanda Allah make jarabtarsa ni tawace tazo a haka".
"Eh na yarda daga Allah ne bana inkari Amma akwai sanadi, inaga gobe ma zan wuce duk da nacewa Umma sai Wednesday Amma na fasa wallahi Rimi zanje
gurin Baban Umma na fada Masa ai kinsan shi farin sani Kuma zeyi duk abinda ya kamata tunda ke wani lokacin kanki ba Maths".
Kwarkwar tayi da ido Dan Allah Saji kada ki tafi ki Bari a Gama komai saiki tafin".
Wani kallo tayiwa Zahra "tafiya dole na tafi
Amma zan dawo kwana kusa in Sha Allah, kinsan Zama da Baffa yasa Ina Gane wasu abubuwan tunda Yana fadw min ire -iren abubuwan da suka shafi sihiri Kinga yace min duk wani ciwon da yake da lokaci misali ace kullun sai dare mutun yake kasa barci kinsan da m
atsala, ko ace mace duk ranar girkinta Bata da lafiya ko duk ranar girkinta tana zubar da jini amma idan ta Gama aikin shike nan sai ya dauke babu, ko kamar taki matsalar sai an saka Miki ranar aure sai ana gaf da biki abun yake lalacewa, Kika sani ko Abba
n naku ma ya Fara irin wannan tunanin ne yasa ya yanke wanna hukuncin cikin sirri ki tsaya kiyi tunani Mana"
Sosai magungunan Sajida sun sakata a tunanin da Bata tabayi ba.
Sauke zazzafan numfashi tayi tana fadin "Allah ya kyauta ni duk kin sakani a tunani
wallahi"
Haba "Bestie ai kinsan ruwa baya tsami a banza me ake nema a gurin mace Allah Bai Baki ba Amma sai an Yi abu kama-kama ya lalace zance da muka Dade munayj da Aunty Hasana kenan jiya Kuma ta bain go ahead na naje na faduwa Baffan rimin, tace ma z
ata fadawa Ammah, ma".
Kiran da Aunty Hasana tayi wa Sajida ne ya katse musu tattaunawar, ta tashi ta fita.
Washe gari duk bakin Ammah suka tafi, Inna maimuna kadai suka Bari sai Amarya taje dakinta zata koma gida.
Part din da bakin suka zauna Ammah tasa
su Zilai suka gyara sosai tunda Daman nasu Zahra ne, kafin yamma gurin yayi tas kamar ba'ayi wata dabdala a cikinsa ba.
Bayan sallar insha'i zahra da Sajida suka koma part din.
Suna zaune a kan gado Autan Ammah musaddiq ya shigo dakin da sallama hannunsa
rike da leda fara Mai kyau ya mikowa Zahra yana fadin "gashi Aunty inji wannan na gidan Baba Malam din yace a kawo Miki Kuma yana duba ki, Kinga Nima ya bani".
Ya Mika nata 1 k din dake hannunsa.".
"To angode madallah".
Ledar Sajida ta dauka ta bude way
a ta gani sabuwa kar a ciki.
"Wow gaskiya ba karya ke! Irin wannan babbar harka haka, Dan Allah Yi min bayani naji yace wannan na gidan Baba malam din waye ko angon namu ne da ake Raina mana ya Fara tsula Mana abun arziki haka?".
Baki ta Zahra ta zunbura.
"Nace Masa Ina bukatar sabuwar waya ne da zai kawo min, ni wallahi a mayar Masa".
Ta fada tana kokarin amsar ledar faga hannun sajidar.
"Ke tsaya da Allah yi min bayani yanda zan gane, Ina taking wayar naji kina wata magana".
"Tana gurinsa tun safe ya k
arba ni bansan abinda zeyi da ita ba, ya dai ce na bashi kawai ni kuma na bashin shine Kuma maimakon ya bani tawa shine ya Aiko min da wannan".
Musaddiq Sajida ta kalla 'kai auta maza kaje kace tace ta gode Allah ya Kara nudi"
Sai da ya fita sannna ta ju
yo gurin Zahra. "Amman wallahi kin bani mamaki Allah ya tarfawa garinki nono ki nemi ki Bata rawarki da tsalle to kici gaba har ki nuna b'araka a gaban 'yan uba, Koda wasa kara ki Kara ba'a yiwa miji haka ko bakaso Abu baka nunawa a gabansa, kika san da Y
aya yayi sawo Miki danya faranta Miki Rai Amma Zaki wani kwasale shi kice a mayar Masa kina son tun yanzu ki kashe Masa Gwiwa ko".
π
β€
οΈ
AUREN HUCE HAUSHI
π
β€
οΈ
JINJINA TA MUSAMMAN GA MALAMAN MAKARANTA ALLAH YAYI JAGORA YA QARA BASIRA DA JURIYAR SAUKEN NAUYI
N DA AKA DORA MUKU NA AMANAR YARA QANANA
π«π«π«π«πππ
β
οΈ
β¨β¨β¨β¨β¨β¨β¨β¨β¨β¨
This page is deducted to you Families of late Alhaji Isah Musa Bakin kasuwa kazaure jigawa state.
π·
PAGE SEVEN
π·
_______Mika tayi tana salatin ma'aiki s a.w.w sannan ta Zoro kafafunta k
asa, tunda ta farka tasan tabbas karfe biyu tayi na sulsulin dare har ya zamar Mata jiki. Dubanta ta kai inda Sajida ke kwance barcinta take sadidan cikin kwanciya hankali, sai taji Ina ma ita ce haka, wasu hawayen ne suka ciko idanunta a hankali tace "Ya
Rabbi ga baiwarka Mai rauna ka jibinci lamarina dan Isar Manzon Allah s a.w.w. kada ka barni da iyawata ka iya min da iyawarka kada ka Bari makiya su yi min dariya ka bani rinjaye ka dorani akan duk Wanda yake son Hawa kaina".
Ta Mike tsam ta nufi toilet
din cikin dakin sai Kuma ta fito saboda shaf ta manta kafin su kwanta taga famfon ya dauke Kuma da alama ba'a kunna layinsu na tanki ba. Cikin rashin tsoro ta bude kofar ta fita zuwa bayan part din Mama don ta kunno ruwan, gurin ta dosa gadan gadan sai Ku
ma tayi turus, magana take jiyowa daga wurin da sauri ta koma baya dan bata San abinda zata gani ba. Tana tsuma ita fa duk da Bata da tsoro amma tana tsoron ganin abinda yafi karfin idonta ko Kuma wani mugun abun.
Dole tayi hakurin yin sallar a koma ta kwa
nta tana ta sake-sake har kusan Asuba, ba Kuma taji motsin wani na tada hankali ba.
Saida Sajida ta tashe ta lokacin har an Fara sallah a masallacin gidan nasu.
A gurguje tayo alwala da alama Sajida ce ta shigo da ruwan.
Bayan sunyi sallah zaman Azkar suka
yi har lokacin da gari yayi shahhh alamar wayewa, sannan suka koma suka kwanta. Dukkan su ba barci suke ba, Zahra ce ta danyi tsaki kadan ta tashi zaune.
Kallonta Sajida tayi.
"Yaya Bestie akwai damuwa ne?"
Dan juyowa zahrar tayi tana kallon sajidar tana
Kara wani tsakin "nifa wallahi na fada Miki tsoron mutumin nan nakeji tun ranar Dana Fara ganinsa a gidan Baba malam nake Jin wata irin shakkarsa. Dan Allah a haka zamu rayu bana ko son kallon idanunsa? Kinsan wani tarin abin haushin jiya fa hannu yasa ya
dago fuskata Wai dole saina bude idona na