Showing 78001 words to 81000 words out of 295116 words
shiya fada Mata wanzuwarsa a falon, a hankali ta dago Kai ta kalleshi "Masha Allah" ta fada a hankali Dan ba lallai yaji ba.
Gurin da take zaune ya Dan tsuguna a gabanta ya Dora Mata laptop din dake hannunsa da wasu takardu da list na sunan mutane
kusan dari da ashirin da biyar daga local government hudu Alkakeri, Jama'are, Zaki da Dass, karkashin makarantun Allo zasuyi step down training a Nan Azaren schedule ne na aikin da payment dinsu.
Ta dago zatayi magana ya Dora Mata yatsa a biki "kiyi kawai
idan na dawo kin tambayeni duk abinda kike bukatar sani bana son nabar garin Nan aikin Nan Bai kammala ba".
Ya Mike fuskarsa ya kawo dad da tata ya Bata light kiss a gefen kumatunta, saina dawo take care". Ya nufi kofar da sauri da key din motar a hannuns
a.
Harya rufe kofar Bata dauke idonta daga gurin ba, ita fa mutumin Nan ya Fara Bata tsoro mutane suna daukarsa wani Abu daban ita Kuma tana ganinsa wani Abu daban.
Ta Dan jima Tana sakawa da kwancewa daga karshe ta watsar da komai ta dauki laptop din t
a shige cikinki bedroom din ta Haye lafiyayyan gadon ta bude ta shiga aikin inda Allah ya taimaketa yaci karfin aikin karasa Masa zatayi.
*******
Lokacin da Mahmud ya fito Ibrahim da wani sulaiman ya Kira ya Basu aikin kula da dakin da Zahra ke ci
ki duk da yasan suna da matakan tsaro sosai Amma hankalinsa Bai kwanta ba sai da ya Kara Mata da nasa, gurin motar ya nufa bayan ya zauna ne ya Ciro wayarsa ya bude ta haka Nan ya shiga CCTV da akayi connecting da wayarsa.
Hotunan ne suka fito rababa na d
akinta yayi zooming qura Mata Ido yayi lokacin data fito daga wanka tana daure da Karamin towel fararen cinyoyinta sunyi wani sambal dasu ta Kai ta kawo Yana kallonta harta gama, tunda ya Fara kallon yake sakin wani Nishi kadan kadan Dan da gaske ta yamuts
a Masa tunani ji yake kamar ya zubar da Alkawarin daya daukarwa kansa a kanta, komawa yayi baya na kofar gate ya dauki hankalinsa ganin wata mota mata sun fito sun dauko wani Abu a Leda sun nufi gate din gidan full screen yayi da gurin da suke ya waye da m
ama amma Asaben
ç
e bai ganeta ba yana kallon duk abinda sukayi har Zuwa lokacin da Asabe tayiwa Mama rad'a a kunne ta Kira Mai gadin ta bashi kudi suka juya
da yanda suke kwasar dariya har da tabawa kamar yara sai abin ya bashi mamaki, meya kawo su gidan
su kadai ga Kuma motar da gani ta commercial ce, girgaiza Kai kawai yana tunanin abinyi.
Da gurin malam ya fara zuwa ya Dan jima tare dashi kafin ya aje Masa Alkhairi yayi Masa sallama, Yana Kara yi Masa addu'ar samun nasara a tafiyar da godiyar Alkhairni
n daya bashi, Habib ne ya Dan kalli Mahmud din bayan sun fito Yana tambayarsa..
"Da gaske baka fad'awa Baba malam ba inda zakun kada fa yaji daga baya yayi fada yace ka tsallake kasa baka fada Masa ba.
Kafadarsa ya dafa.
"Kada ka damu da kaina Zan fada M
asa in sha Alllah".
Tare sukaje gidansu Zahra inda suka Dace suna kokarin yin knocking sai magaji ya fito, daga gani wani gurin zaya yanda yayi Shar dashi.
Gaggaisawa sukayi kafin Magajin yayi musu jagora zuwan gurin Abban nasu. Anan falon ganawa da bak'in
sa suka sameshi, sun gaisa Sosai a Nan Mahmud ya fada masa tafiyar da zeyi, Abban yasa Albarka soshi.
.
✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH
Page 27
_____Dan Jim Mahmud yayi kafin ya Dan mus
kuta kadan ya Kara sadda kansa kasa.
"Abba Dan Allah ko za'a taimaka a bamu Aron daya daga cikin masu aikin Nan Mata su tayata Zama kafin Allah ya dawo damu". Ya fada a ladabce
Dan gyaran murya Abban yayi Yana fadin "Hakan babu laifi kayi tunani Mai k
yau baza'a bar yarinya ita kadai ba gara da babba, ba komai kome kenan da safe za'a turo wadda zata zauna da ita, Allah yayi Albarka ya bada sa'a"
Sun jima suna Hira da Abban har suke fada Masa harkar kayan spares na kayan motocin da zasu ringa saidawa, Al
barka ya sanye musu sannan sukayi Masa sallama, har sun Kai kofa Abban yace Bari ya fadawa Ammah ku shiga ku gaisa, a waya ya kirata ya fada Mata sannan yace su karasa ciki.
A kofar gate na shiga ciki suka samu Musaddiq Yana jiran su, cikin ladabi ya gaish
e su Yana tambayar Mahmud Aunty Zahra, hannunsa Mahmud din ya Kama Yana bashi amsa har suka shiga part din Ammar.
Sallama sukayi tana zaune a parlourn, sallamar ta amsa tana fadin. "Su Habib ne sannunku Bismillah".
Ta fada tana nuna musu gurin Zama.
Basu
zauna a kujerar ba sai suka zauna a Kan carpet.
"Ina yini?"
Suka fada a tare, "lafiya kalau ya wajen malam?"
"Lafiya kalau yace a gaisheku".
"Masha Allah muna amsawa, Allah yayi Albarka, yayi muku jagoranci cikin dukkan lamuranku, ayi ta hakurin Zama da ya
ra".
Ta fada a kunyace Dan har ga Allah tana Jin nauyin yaron da kaunarsa saboda karamcinsa da halin fattako daya nuna lokacin da aka bashi Auren zahra da Rana tsaka ya Kuma sa hannu biyu ya karba.
"Amin na gode ba komai, zahrar tace ma a gaisheku, kuma na
zo ne nayi muku sallama zanyi tafiya ne amma in Sha Allah bazan jima ba, na fadawa Abba a samu wadda zasu zauna tare kafin Allah yasa na dawo".
"Masha Allah. Allah yayi taimako hakan baze gagara ba ko can gida Mubi Sai a samu wadda zatazo su zauna tunda ak
wai yaran sosai ba sai an dauko bare ba tunda yau din ta Zama wata iri Amma kafin tazo sai su Fara Zama da zulai tunda Bata da matsala"
"Godiya muke Allah ya kara sutura" Habib ya fada, suna mikewa har lokacin Autan Ammah Yana jikin Mahmud a zaune. Addu'
a Ammah take musu har suka fito Nan da nan wani rauni ya shigi Mahmud haka tasa Umman take Masa a duk lokacin da ze shiga wurinta bakinta baya gajiyawa da Yi Masa addu'a, duk kewarta sai ta rufe shi, "kaimu gurin Mama mu gaisa".
Mahmud ya cewa autan Ammah.
Part din Mamar suka nufa, Musaddiq ne yayi knocking har sau biyu ba'a bude ba Kuma suna jiyo maganganu da sound din tv.
Habib ne yace "mu tafi Dan Allah yaushe zamu tsaya kamar wasu 'yan maula". Har sun sauka daga steps din balcony din sannan aka bude kof
ar, Asabe ce ganin Autan Ammah da mutane yasa ta fito tana fadin ku shigo Dan Allah wlh bamuji ba sai daga baya Salma ke fadin Kamar taji bugun kofa".
Habib ne yayi farat yayi magana "ai ba komai a gaishe da Hajiyar Daman mujin Zahra ne ya shigo ya gaishe
ta".
Sukayi gaba suka barta a tsaye.
Ciki ta koma jiki ba kwari.
Mama ce ta kalleta.
"Wai su waye Naga kin fita Kuna magana dasu ne Kuma Basu shigo ba?"
Zama tayi kusa da mamar, "sirikin ku ne inda mukaje basa Nan yazo gaishe ki da alama Kuma sauri suke tu
nda sun jima a tsaye ba'a bude ba".
"Wai kina nufin Mahmud mijin Zahra?"
"Shifa sunce a gaishe ki, da alama sauri suke Dan har sun fice.
Baki Salma ta tab'e tana fadin. "saura kiris dai uban kowa ma ya rasa, ba dai kunce kun Kai turaren wutar ba, yanda aka
wayi gari aka ganshi da hakoransa talatin da shida haka za'a wayi gari yayi layar zana inga ta qafafar da ake anyi aure, auren ma Dan jeka nayi ka da ba wani armashi yayi ba, Shima Abba Dan ya ganshi handsome ne ya bashi ai ko banza ance mijin agolar gid
ansa ne".
Dakuwa Mama tayo Mata "Abban naki kike fadawa haka? Nima da farko nayi tunanin ko wani lashi yaga yaron Yana dashi sai da na saka akayi min bincike aka tabbatar min da gidan da kayan da yake sakawa duk Wanda yakewa aiki ne suka kawo Masa Dan wasu
ma ance min wannan yaron shugaban aikin nasu ne ya kawo Masa kwancensu Dan ya rinka fita kunya tunda matar tasa 'yar boko ce, shi Kuma almajiran soro ance min ma iyakarsa secondary ya Dan iya rubutu da karatu ne yasa suka dauke shi aikin nasu, har kike w
ani zaqewa kina sonsa ai da naji haka saina fad'i ba nauyi yo Dan kyau me ake da kyau bako sisi Allah Banda nayi Alkawarin saina Maida Zahra karamar bazawara ba, da barinsa zanyi a garin to idan nayi wannan saken kakanninta zasu iya bashi mahaukatan kudi y
a nemi sana'ar da ze rike musu jika gara dai yayi gaba tazo ta zauna na Dora daga inda na tsaya".
Dariya Salma da Asabe suka kwasa Asaben ce ke fadar "Aikinki Yana kyau uwar dakina ba Wanda ze taba hasaso hakan daga bangaren ki kin kasa kin tsare duk wata
kafa da wani ze fahimci da saka hannunki a lamarin yarinyar nan".
Dariya mamar tayi itama "Au da sokike na ringa nuna adawata a fill ai Ni duk ranar da tazo gidan Nan da bayanin mijin ya gudu sai nafi kowa kuka da tsine masa".
"Sai Maman mu". Salma ta fada
tana kyalkyalewa da dariyar mugunta.
*********
A harabar gidan suka samu Abba Yana yiwa malam Bala direba magana, gurin suka nufa Abban na ganinsu ya nufo inda suke.
"Har kun fito"
"Eh Abba zamu koma"
Suka fada tare, takarda Abban ya mikowa Mahmud.
Hann
u yasa ya karba.
"Gashi Nan ka Kara guzuri Allah ya kaiku lfy ya bada sa'a".
Godiya sukayi Masa sosai har Saida yayi fada.
Tare suka fita da Auta har gurin mota ledoji biyu Mahmud ya dauko daga seat din baya ya mikawa Musaddiq.
"Gashi naka daya na Faruq da
ya tukwaicin ku ne na kawo abinci".
Da murna Auta ya nufi gida Yana fadin "mun gode Uncle".
Cheque din kudi ne masu nauyi Abban ya bawa Mahmud saida abun ya Basu matukar mamaki.
Habib ya mikawa cheque din Yana fadin.
"Ka rike a gurinka kawai a sawo kayan s
hagon Nan dasu a Fara kasuwar tunda Allah ya kawo kawai".
"A'a baza'a yi haka ba ka tafi dasu kayi guzurin Kamar yanda yace idan Allah yasa kun dawo sai asan yanda za'ayin".
"Kayi yanda nace ba wata damuwa acan komai Yi Mana za'ayi to me zanyi dasu? ga Ku
ma abun bukata a gida ba gara ayi ba watakila kafin mu dawo ka koma sari na biyu".
Ya fada Yana murmushi.
Majalissar su sukaje Mahmud yayi musu sallama har salisu Yana zolayarsa akan barin Zahra da zeyi Yana tsakiyar angwancewa. Bai Dade ba ya tafi duk han
lalinsa Yana kanta yasan har ta gaji da jiransa watakila ma tayi barci.
Saida ya biya ya saya musu kaza da apple ya dauki hanya.
Lokacin Sha daya da minti ashirin da bakwai.
A hankali ya bude dakin abin mamaki Zahrar ya gani gurin fridge da glass cup a Ha
nnunta tana Shan wani abu, Sam bataji bude kofar ba saboda tv a kunne take sannan ta bawa kofar baya, Jin kamshin turarensa yasa tayi saurin juyowa lokacin yazo daf da bayanta, juyowar da tayi sai a cikin kirjinsa.
Ledar ya saki qasa yayi Mata kyakykyawan
masauki ya saka hannunsa ya talkafo bayan ta, yasa Bakinsa a dai-dai kunnanta.
"Na dauka kin wuce Kano a barcinki Ashe dai jaruma na aura wadda take iya jiran mijinta komai dare". Ya karasa fada Yana Dan hura Mata iskar Bakinsa a kunnen.
"Dan Allah ka Bari
".
Ta fada tana niyyar janye jikinta shi Kuma ya Hana hakan. Dan kwabe fuska tayi, "ka sakeni toilet zani".
"Ba wani toilet idan Kuma da gaske ne muje na rakaki".
Kai ta gigiza, shafa gefen ribs dinta yayi yaji yanda rigar ta matseta komai yayi tsan-tsan.
Dan sakinta yayi Yana Kare mata kallo daga sama har kasa, Dan sunan dinkin a tsokano fitina kawai, shi a dazu ai be karewa dinkin kallo ba sai yanzu a kausashe ya jefa Mata tambayar.
"Waye telan da yake Miki dinki".
Hannu yasa ba zato ya shafo gaban rigar
da sauri ta saka duka hannuwanta ta tsuguna sai Kuma kasan ya baje. "Ya Salam" ya fada a hankali.
"Kinyi shiru Ina tambayarki".
"Makociyar Aunty Hasana ce take Mana dinki".
Ajiyar zuciya yayi yayi zaton namiji ne yaji ance sune ke gwada Mata idan hakan ta
kasance ai an gama dashi wani ya taba Masa wannan jikin. Tsugunawa yayi ya kamota ya dago jikinsa ya maidata "ki barni naji duminki gobe ya wannan bana kusa dake Ina can na rungumi pillow, so muje muyi hirar yaushe gamo, ko Kuma ban sani ba murna kike kin
a Jin dadin Zan tafi na Baki space ki sake ko?"
Ya fada Yana Wasa da Dan Karamin zoben dake 'yar karamar yatsarta.
"Oya talk kinyi shiru koba haka bane daman ba kince min me naci Kamar maye na tsotseki waya sani ko maye ne ni ko Baki fada ba? Kawai Dan na
koyawa bakinki ladabin magana da miji akan wannan yaron shine na samu lambar maita daga gurinki".
Sexy eyes dinta ta zaro Masa, abinda yake burgeshi yake matukar so kenan yaga ta tsorata.
"Ni nace maka maye? Yaushe akayi hakan Wana fadawa?"
"Abar maganar k
awai sai ranar Dana cinyeki danya Zaki gane Ni maye ne".
"Wlh Ni ban fada ba, Toni Wana na gani da Zan Fadi haka har a Gaya maka, a kwanakin Nan ko waya ban rike ba fa".
"Naji shike Nan zo muje Naga aikin Allah yasa dai yayi kada aiki ya Koma baya"
Ledar t
sarabarsa ya dauka ya jata suka nufi ciki. Gefen gadon ya zauna Yana janyo laptop din gefensa Zahrar na tsaye a dayan gefen.
"Hayo ta Nan ki bude ki nuna min aikin in gani". Ba musu tayi yanda yace Kan cinyarta ya Dora laptop din ya Dan kwanto jikinta yana
ganin aikin har ta Gama nuna Masa, tab'a hannu yayi Yana fadin "inye kice idan Allah ya hure mun na samu sakatariya ta a gida basai na nema a waje ba, yanzu jeki saman fridge akwai plate biyu ki dauko kizo ki Zuba wannan" ya nuna Mata ledar daya shigo da
ita.
Laptop din ta aje kusa dashi ta janyo gyalen da ta yafo zata yafa ya karbe Yana Mata wani kallo.
"Me zakiyi da shi ko akwai Wanda ba muharraminki ba a Nan da Zaki Kama rufe jiki, ok da bana Nan kin aje har Dan kwalin kina watayawa yanzu Kuma na dawo
Zaki wani saka gyale tunda idan na ganki kin dauki zunubi ko?"
Shiru tayi Masa tasan idan ta magantu sai ta Kara laifi, juyawa tayi ta nufi kofa ya bita da idon Yana kistima abubuwa da yawa a zuciyarsa.
Plates din ta dauko ta kawo ta koma ta dauko ruwa rob
a daya da fresh milk tunda taga Kamar yafi son Shanta akan lemo.
"Dauki ki zuba" Nan ma ba musu ta bude kedar Naman wani kanshi ne ya doki hancinta har lokacin Kuma da zafinta, daya ledar ta bude apple din ta Zuba a kai, gyara zama yayi Yana nuna Mata gefe
n shi, Kaita girgaiza.
" Na koshi bana Jin yunwa".
"Naji ai ba abinci bane kizo kici ko nayi Miki dura da gaske nakeyi fa".
Narai narai tayi da ido, Allah bana cin Abu Mai yaji ko maiko da yawa da dare ulcer yake tada min".
Ture plate din yayi gefe ya jany
ota ya zaunar da ita a cinyarsa.
"Me Kika ce? Ulcer as how Kika kamu da ulcer, since when?"
"Bafa wani Abu bane tun Ina secondary ne Amma tunda aka fada min na rage cin wadannan abubuwan more especially da dare idan Zan kwanta saina daina ciwon cikin".
Pla
te din ya ture gefe, "tashi ki Kai fridge ki dawo".
Kallonsa tayi da alamar tambya "to Kai bazakaci ba"
"Ni saboda ke na sawo coffee ko fruit kawai nake Sha a irin wannan time din, ki wanko Mana Apple kawai ya Isa".
Saida ta wanko ta kawo sannan ta dauki
kazar ta Kai fridge din ta dawo.
A Dan nesa dashi ta zauna taga alamar 'ya abun nasa Yau suna kusa.
Matsowa yayi jikinta da plate din Apple din Yana Danna waya da alama kamar Kira yakeyi Apple din ya Mika Mata Yana ci gaba da trying Kiran, sau biyu Yana K
ira ba'a daga ba ya hakura ya aje wayar.
"Labarin ki Zaki bani tun daga primary, secondary Zuwa Yau din Nan da muke tare Kuma ki fada min dalilin da yasa ake fasa aurenki da dukkan Wanda sukaso aurenki laifin na waye? Ok kafin Nan Bari na tambaye ki wani a
bu"
Wata wayar ya Ciro daga aljihun gefen hagu na rigarsa.
Jikinta ya matso sosai Kusan Rabin jikinsa Yana cikin nata ya kanainaye ta CCTV ya kunna ya Mika Mata ya saka fullscreen gurin gate din gidansu ne Mama da Asabe ta gani tun tsayuwar motarsu har zu
wa gurin Mai gadi Saida ta gama ganin komai yace "Daman Kuna abin kirki da Mama ne? Kuma wacece wannan Dan yanzu da Daren Nan da naje yiwa su Ammah sallama naganta a dakin mamar kenan daga Nan can sukayi"
Ya