Showing 150001 words to 153000 words out of 295116 words
dage Mata girarsa ta dama.
Wani ruwan ida
nunta suka kawo alamun zatayi masa halin.
Bata fuska yayi ya Zama serious din nan.
"Wallahi naga digon hawayenki saina sakaki kukan gaske, kuji min yarinya sai shagwaba, ai Naga kin Fara sallah gara na cire Miki yarintar Nan ko kin nutsu ki fuskanci aurenk
i, dan Naga alamar har yanzu Baki yarda da igiyar aurena ba a kanki tunda na kasa banbance Miki tsakanin Aya da tsakuwa ko?".
Mukus ta hadiye kukan tana qiqqifta Idanu, Jin ya b'aro magana, to a Ina yaga tana sallah har yake fada Mata hakan?.
Kafin ta samu
zarafin magana wayar da take jikinsa ta dauki wani kidan larabawa Mai Dadi.
Dagawa yayi Yana fadin "ok gani Nan Amma ka tabbata komai ya Zama ready kafin na shigo, dan Allah kace mommy ta bani aron Rukayya ta shigo Nan Hausawa Bawo road ta Taya 'yar rigim
ar Nan Zama zuwa yamma, ka Bata address din gidan".
Ya fada yana sauketa daga jikinsa ya Bata light kiss ya manna Mata a saman goshinta Yana fadin "Zan dauki Aron motar ki na fita da ita kinji my previous, anyi min izini?
Kai ta gyada Masa tana fadin.
"All
ah ya tsare".
Harya juya ya nufi hanyar barin parlourn ya dawo ya Mika Mata wayar hannunsa,.
"Kiyi amfani da ita sabon sim ne a ciki Sameer kawai nake Kira da shi kafin a kawo Miki Taki tunda na fadawa yayan mu yau Zan Baki wayarki".
Hannu ta saka ta karb
i wayar iPhone 16 plus ce da sauri ta dago ta kalleshi alamar mamaki fal cike da fuskarta da kallon tuhuma Dan ba da ita tayi ways da Amma ba.
"Ya akayi Kika tsareni da kallo ko batayi miki ba".
Ta bude Baki zatayi magana ya daga mata hannu.
"Bari na dawo
saina amsa tambayoyinki a nutse ai cewa nayi Miki aro bi kyauta ba ko?".
Ya fice da sauri, da alama uzurinsa Mai girma ne, tun bayan fitarasa take juya wayar a hannunta idan ba bataga daidai ba a mbc taga tallarta 1.48 million naira ne kudin ta in Nigerian
Price.
To wai waye shi ne Dan Allah? Duk lokacin da wani Abu irin haka ya gitta a tsakaninsu baya yarda ya tsaya yayi Mata bayanin komai.
Ajeta tayi a gefen da take zaune ta Zuba uban tagumi da hannu biyu tana nazarin wasu abubuwan da take gani tun shigow
ar su Kano abun ya canza salo gaba Daya, ta rasa Wanda zasu tattauna da dashi Aunty Hussina ce to babu waya a hannunta ta mayar da kanta kurma.
Kamar an tsikareta ta Mike ta nufi upstairs da wayar a hannunta tana fadin Bari na Kira bestie musha hurar yaus
he gamo da ita".
Duk yanda zahra taso ta fada Mata wani Abu Daya shafi Mahmud saita kasa fada Mata Kuma da alama Ummansu Bata fada Mata taje gidan ba koda wasa, saima wani abun mamaki da sajidar ta fadawa zahrar cewar Mahmud yace zasuzo har syprus gurinta
tare Amma yace kada ta fada Mata, sun dauki lokaci suna wayar har sajidar ke tsokanar Zahra tana fad'in "ke Kullum canza layi kamar wata marar gaskiy".
Dan nisawa Zahra tayi kafin tace "ki Bari bestie kawai wallahi ba laifina bane shine yake kwace min way
ar Kuma idan ya tashi Kuma ba ita Ze bani ba sai dai ya bani wata, jiya fa da muka fita unguwa ya shiga sahad na Nan zoo road muka hadu da Musbahu bakiga yanda ya yi, ba Banda Allah ya Soni ba da inaga sai yayi min duka ma da Allah yasa nayi tsautsayi mu
nyi magana dashi".
Dariya sajidar tayi tana fadin Namijin duniya kenan Wanda ke kishin iyalinsa, nifa Daman harga Allah musbahun nan ba wani yi min yayi ba, kawai dai baka hana nutum abinda yakeso ne, Amma Ina hadin be hadu ba ko alama wallahi,ban qara san
in haka ba Saida sarkin yaqi ya bayyana".
Ta fada tana kyalkyalewa da dariya.
"Wallahi bestie Baki da kirki ki ringa Jin tsoro Allah, musbahun ne haka? Amma Ina cewa harda ke a masuyi Masa campaign a wancan lokacin"..
"Manta kawai bestie ya zaman past, yan
zu ta Wanda Allah ya zaba Mana mukeyi, yauwa munyi magana da Baffa yace akwai saukar Alqur'ani da ake Miki in Sha Allah babu wani Abu daze sake tasiri a cikin rayuwarki in dai sihiri ne yace kiyi ta Hakuri mijinki Mai jama'a ne".
"Hummm! Bari kawai bestie
nifa mutumin nan tsoro yake bani".
"Tsoro kuma? Kamar Yaya?"
Tsaki tayi kadan.
"Ba Zaki gane ba kwata kwata ba Wanda Kika zani bane wannan wani ne daban, kinsan ya maidoni Kano daga zuwa ganin likata yace nida Azare sai ganin gida, Kuma Kinga wasu mahaukat
an gidaje da yake yawo Dani a cikinsu Kamar baza'a mutu ba wallahi, Kinga wannan wayar dake hannuna yanzu wallahi iPhone 16 plus ce ya bani Wai ga aro kafin ya kawo min tawa. Allah Lamainsa Yana damuna Kuma yaki yayi min bayanin komai sai sabgar gabansa ya
keyi kawai"..
Tunda Zahra ta shiga bayani sajida ke murmushi Dan tasan za'ayi haka Ya Abba ya kirata dazu ya fada mata waye mijin da zahra ta aura kawai ya bada kafa ne wanda shima baisan dalilinsa na yin hakan ba.
"To ke meye naki na sai kin San waye shi
yanzu kiyi Hakuri Mana ai yau da gobe tafi karfin Wasa ba dai Kuna tare ba, ai wata Rana gaskiya zatayi halinta abinda nakeso kiyi kawai ki saka a ranki mijinki ba macucin da ze cutar dake bane, Kuma bata haramtacciyar hanya yake samun kudinsa ba,Kika sani
ko wani mashahurin Dan kasuwa ne Allah ya Baki".
"Kin jiki aikin fa NGOs fa yakeyi Dan dai wata tsohuwa ta fada min wasu maganganu Wanda ta sakani a confusing sosai".
"Ki manta kawai ki fiskanci zahiri tunda gashi gaki bada labari Kuma ai ya Kare keme rea
lity a gabanki,kawai dai ki zama Mai lura da lamarinsa da kyau, kiyi kokarin Kare Masa Sha'awarsa kada ki zama lusara mijinki yaro ne Mai jini a jika Wanda Mata irinsa suke rububi Koda aure ko Kuma ayi shashanci gaskiya sai kin dage in ba haka ba garin kal
lon ruwa kwado yayi Miki kafa".
"Kamar Yaya?"
"Au Baki gane ba to ki ringa bashi hakkinsa Dan Naga alama kamar zakiyi son jiki ta wannan fannin Ni Kuma yanda nake ganinsa ba ragon namiji bane".
"Inna fatahana laka fatahan mubina! Bestie yaushe Kika Zama ha
ka wallahi badan nayi Miki farin sani ba da cewa zanyi kina wata sabgar a bayan fage, to wallahi Ni har yanzu in nan yanda nake shi ba yanda kike tunani yake ba a Nan dai sai nace kinyi failed tunaninki ya kasa.."
Wata irin dariya tayi tana fadin Dan Allah
mu koma video call Naga idanunki su kadai Zan kalla na tantance maganarki"
"Ba zanyi ba sai anjima tunda kin Zama abinda Kika Zama sai neman sauki gaskiya Ya Abdul Hakeem ya gamu da gamonsa a Ido kamar saliha nasan idan Kika shiga gidan sai yayi Dan wuya
tunda Naga alama kina cikin.... Allah dai ya kyauta kawai".
"Kai! Sharrin da zakiyi min kenan shi kenan Zan rama".
Sun dauki lokaci suna Hira har sajidar ke fada Mata Hameeda ta kirata tana kuka akan abunda tayi Mata Wai Mama da Salma ne suka sakata, Bata
gane kuskuren da tayi ba Saida ta dawo gida, abinda yasa suka samu sabani da Salma kenan har ita Hameedar tayi tafiyar ta Jos Saida zasu koma Jigawa sannan ta koma gida.
"Lah ki fada Mata Ni a gurina ya Dade da wucewa wayace lokacin babu a hannuna Dana ki
rata tuntuni Amma idan nayi waya Zan nemeta ai karo Daya masu magana sukace Koda kusa ai yi akeyi, Hameeda tawa ce".
"Kiyi dai taka tsan-tsan da lamarin ta kinsan ance jini yafi ruwa kauri duk rintsi ba zataqi uwarta a kanki ba, ko Zaki Kara karbarta kisan
irin zaman da zakuyi da ita, Ni garama Daya daukoki daga can yayi maganin abubuwa da yawa wata qila Kuma da abinda ya lura dashi yasa ya yanke wannan hukuncin".
Shigowar su Aneesa dakin sun dawo daga lectures yasa suka canza akalar hirar sun gaisa da Zahr
ar suna ta korafin taji dadin aure ta manta dasu ko wayarta ba'a samu saboda tayi nitso cikin kogin soyayya, ita dai saikokarin Kare Kanta takeyi sajida na tayata.
Da haka sukayi sallama.
Aunty Husaina ta Kira itama tayi Mata nata fadar rashin samunta a wa
yar sannan ta Kara dubata da jiki tare da tambayarta yanda sukayi da Asibitin? ta fada Mata fada har yanda sukayi da doctor din, da Kuma maganin da Hajiyar makwarari ta Bata, sannan ta fada Mata abinda yake faruwa da ita a Nan kanon Bata rufe Mata komai b
a, tayi mamaki kwarai sai dai tun farko Daman ta yiwa lamarin sa question mark, tun ganin irin kudin da aka narkar a kankanin lokacin gyaran gidan da aka bashi a nan Azaren.
Kamar hadin Baki itama Aunty Husainar cewa tayi ta Zuba Masa Ido ta Kuma yi masa b
iyayya, sannan sukayi sallama.
Kusan awa Daya da tafiyar Mahmud Zahra taji bell na Kara alamar anyi bako.
Saukowa tayi ta nufi kofar ta bude Aunty Rukayya ta gani a tsaye da basket din abinci a hannunta dayan hannun Kuma da karamar jaka irinta matafiya.
A
UREN HUCE HAUSHI.
(Maman Fateemah)
Page 52
______
Cikin Jin dadi Zahra tayi zarya ta karbi jakar hannun Aunty Rukayya tana fadin. "sannu da zuwa Aunty Ni harna cire rai da naji shiru ga babu Wanda ze tabo min ke a waya tunda number ki tana Kan
waccen wayar". Ta fad'a tana Bata hanyar shiga.
"Wowooo! Masha Allah, gaskiya Ya Mahmud Yana shagwaba ki yarinyar nan, irin wannan babbar harka haka".
Ta fad'a tana karewa parlourn kallo, handbag din dake hannunta ta aje tana fadin Ina zuwa ta juya da saur
i ta koma waje, zahra na tsaye Aunty Rukayyar ta dawo da basket Babba fal Kaya a cikinsa ta shigo.
"Kai Aunty daga ina haka da wadannan Kaya?.
Zama tayi tana Kakabin haduwar gurin. Itama Zahrar zaman tayi kusa da ita.
"Bari kawai wallahi aikin mommy ne, da
man ko Ya Mahmud be kirani ba Mommy zata tasoni takanas ta garin Nan na kawo Miki sakon nan, ai jiya Kuna barin gidan naji ta Kira Hajiya Salima 'yar Sokoto tana Mata wani bayanin dayasa na sulale nabar parlourn".
Ta fada tana dariya.
"Kamar ya Aunty?"
Wat
a dariyar tayi tana fad'in "ji nayi fa tana Kiran a Kara gyara Mata diyarta tasan Shirin wancen yayi sanyi tunda ta fuskanci diyar tata Bata Fara Amarci ba, Kinga kuwa ai Zama Bai ganni ba a gurin, Wai hadi za'ayi Miki bana Wasa ba"..
Hannu zahra ta saka t
a rufe fuskarta wata irin kunya ta rufeta.
"Dan Allah bude idonki ni zakiji kunya? Ni nan Nima zuwa bayi na Dora Miki karatu Naga kin fiye Sanya ba wani abubuwa masu zafi da kikeyi ko wannan shigar batayi min ba, ki zage kina tsula fitinannun shiga wadda Z
aki gigita Masa lissafi, humm wallahi Naga alama bakisanta true colour din ya Mahmud ba".
Da sauri zahra ta bude Ido tayi wuri-wuri tana duban Rukayya.
"Aunty waye shi dan Allah? Dan duniya ne ko?".
Wani sakaran duba Rukayya tayi Mata. "Amma ke wallahi any
i marar wayo, meya hada magana ta da bariki kuma? Allah yayi masa tsari da wannan sabgar, Kinga mubar maganar tunda kin Bata zancen sai wani jikon Kuma".
"Dan Allah Aunty kiyi Hakuri kiyi min bayani, a'a wallahi Naga alama sai an qara gasa Miki bakinki".
T
a fad'a tana janyo basket din gabansu.
Abincin da mommy ta bayar a kawo ta cire suka Kai Kan dining suka dawo wasu food flask ta Ciro guda biyu Daya kazace wadda aka dafa da saiwar Malmo sai kamshin spices ke tashi ga habbahan Nan guda guda a ciki.
Sai day
an wani irin romone na kwai da Albasa da wani Abu a ciki kamar hanta.
Sai Kuma wasu madaidaitan robobi masu kamar girman na swan medium, had'in Zuma ne pure da magunguna,sai wasu Kuma na tsimi da robobin gumbar aya da dabino, a hankali Rukayya ta shiga Yi
Mata bayanin yanda zatayi amfani dasu wata Leda ta Mika Mata wannan Kuma da bayaninsu a cikin kowanne.
Ta karasa tana dariya.
"Wani bayanin sai a takarda ki duba koni ba'a fad'a min ba".
Rufe fuska zahra ta karayi tana fad'in, "nagode Allah ya sakawa mommy
da Alkhairi".
"Allahumma Amin, wato su Mommy ana gyarawa d'a Mata yanda..... Umhh ".
Ta rufe bakinta tana wata dariyar.
Hannu Rukayya tasa ta dauko wayar da zahra ta aje a tsakaninsu ta Fara juyata tana kallon zahra.
"Mrs Dange! Masha Allah yaushe ya gwa
ngwajeki da wannan me zafin?".
Dan warrr tayi da ido tana duban Aunty Rukayyar..
"Ba tawa bace aro ya bani da ya dauke min tawa" .
"Kamar ya?".
Labarin abinda ya faru ta Bata.
" Ke ai gobarar Titi a Jos, ba gashi kin samu waya daga sama ba".
Baki ta bude
tana fad'in. "Kai Aunty Ina Akuya zata da Kayan Cali, wallahi wannan tafi karfina".
"Naki wasa ne yarinya kinsan waye mijinki kuwa Naga alama anyi Miki lillibin biri, bazakiji mutuwar sarki a bakina ba Amma ki zaman very curious a Kan duk wani motsinsa da
lamuransa da kanki Zaki bani labari".
Dan narainarai tayi da ido.
"Wallahi na kasa gane komai a Kansa Kuma an rasa Wanda ze min cikakken karatun da Zan fahimta".
Wayar Aunty Rukayyar ta aje a kusa da Zahrar tana fad'in. "haba Auntyn mu meye na gaggawa y
aushe akayi Daren da shashhsawa zata b'ata ku tafi a yanda aka dauko.tafiyar kamar hakan ze taimaka Miki ki Zuba mulkin da kikeso Kuma tun yanzu ya kamata ki koyar dashi yanda kike son ku rayu, ko Nan gaba sauyin yazo bazezo Miki da wani abin mamaki ba, Ab
u Daya Zan fad'a Miki gidan da kuka sauka a Sultan road mallakin Ya Mahmud ne Dan naji Hajiyar makwarari suna cakusawa da Ya Sameer da tace ta fad'a Miki tsakaninsu da Ya Mahmud din ta fad'a Masa kin tambaya gidan na waye ta fad'a Miki mallakin mijinki ne,
Ina fatan bakiyi maganar dashi ba?"
Kai ta girgiza "a'a, bance Masa komai ba".
"Good, ku tafi a haka, ko a fuska kada ki nuna kinsan wani Abu a Kansa".
"In Sha Allah".
Babbar jakar Nan ta janyo ta bude tsala-tsalan dinkuna ne na materials da laces, sai s
haddoji, fito dasu Rukayya ta Farayi, daukar wata rigar material zahra tayi tana bude dinkin.
"Masha Allah! Kai amma kin iya zaben material ga telar da tayi dinkin kowa yayi yasan takan dinki gaskiya".
"Sun dai yi kyau ko?"
"Tab sosai ma".
Gasu nan naki ne
Ya Mahmud ya bada size yace basai telar tazo ba, Naga alama ko Mata yana kishin su gane Masa jikinki bare maza Kuma".
Zahra taji dadi tayi murna da ganin kayan, Dan ba karya komai classic ne.
Sun Jima suna hira Aunty Rukayya nata guiding din zahra abubuwa
masu amfanin da mahimmanci daya kamata ta rikesu a rayuwar aurenta.
Tare sakaci abincin da mommy ta aiko sannan suka shiga kitchen Zahra taci gaba da gyaran kwakwar data Fara ta bari, a blender ta saka Bata Zuba ruwa ba ta kunna sai tayi kamar an goga ta
juye ta dauko bota da Madara peak powder da condense milk sai salt ta kawowa Rukayya wadda ta tashi zata tayata aikin, Basu dauki dogon lokaci ba suka Gama hadawa suka saka a barking try suka saka a oven.
Suna hira har ya gasu, yayi yawa sosa, kuma yayi ky
au, maganin gurin Hajiyar makwarari zahra ta Zuba a ruwan zafin ta barshi yayi 20 minutes din sai ta tace Tasha. Sama suka haya da kayan sauran kazar zahra ce kawai ta saka a fridge din kitchen tace sai dare zata karasa cinyeta.
Nan ma "Yar kauye Rukayya t
a Zama Dan saita rantse da Allah Bata taba shiga bedroom irin Wanda take ciki ba, tana ganin gidan Nasarawa kamar ta dauka ta gudu dashi, sai Kuma ga wannan Daya dameshi ya shanye abinda wancan ze nunawa wannan girma ne kawai Amma ba abubuwan more rayuwa b
a, Saida Rukayya ta tayar da sallah sannan Zahra ta shige toilet tayi wanka ta dauro alwala, bayan ta Idar da sallar tayi shafa, Rukayya ta takura Mata Saida tayi Mata kwalliya ta zabo Mata rigar material din data dunga dagawa da aka kawo dinkunan, wani i
rin kyau tayi ga farinta sai wani Kara haskawa yakeyi.
Karfe shida sukaji dirin horn din motoci a cikin gidan, da sauri Rukayya ta leka taga Ya Mahmud ne da jama"arsa. Cikin manyan motoci nasa Dana guard dinsa.
Da sauri Rukayya ta juyo gurin da Zahra ke Ad
du'oi.
Tashi na daura Miki dankwali karfin ya Gama ganawa da mutanen da ze gani.
Ba musu ta tashi ta zauna tayi mata dauri irin na Amare ta qara fesheta da turare ta dauki jakar ta tana fadin Bari na sauka kasa nasan yanzu Ya Sameer ze kirani.
Miqewa zahr
a tayi tana fadin "nagode Aunty Rukayya, Allah ya saka da Alkhairi kiyi min godiya.gurin mommy kafin nazo da kaina".
Ledar da Fateeha ta zubo Mata Kaya ta dauko ta zubawa Aunty Rukayya kayyayki dasu turaren Kaya Dana jiki sai sabbin undies da mayuka duk ta
Zuba Mata.
Tare suka sauko kasan direct kitchen Zahra ta wuce ta zubo Mata coconut Cookie da sauran tarkacem su biscuits da chocolates.
Lokacin data fito Aunty Rukayya na amsa waya, a salon yanda take amsawa tasan mutum ne na musamman ake wayar dashi Dan
sai shagwaba da tabara take Zuba masa tamkar wata 'yar baby.
Kayan ta aje a kusa da ita, basu