Showing 237001 words to 240000 words out of 295116 words
akan aure, sai gashi Ashe wani hanin ga Allah baiwa ne, wa ya taba zaton yaron Nan wani ne ko Dan wani? Ba Karamin toshe kunnu
wa Abban Yara yayi ba lokacin da ake Kan ganiyar maganar ana ta ruruta wutar ya aura Mata Almajiri Wanda ba'a San asalinsa ba Dan ba 'yarsa bace Amma ace duk yanda take da kyau da cikar halitta ta Kare a kolo fakiri marar madafa, to gashi hakuri Mai tarar
da arziki yau ga Zahra ta Zama farin wata Sha kallo, ga lefen da ba'a taba kwatanta kawo Mata Koda kwata dinsa ba, yanzu haka wancen lefen suna Nan a daki to ga Kuma wannan Sha kumdum din.
Wurin Abbanta Aunty Hasana ta rakata yayi Mata Nasiha sosai ya Kar
a jaddada Mata mashimmancin biyayyar Aure.
Kafin karfe Sha Daya gidan ya dinke da jama'a abin har yaso ya bawa Ammah mamaki to ita dai Hajiya kaltume ta dankawa I. V din da Ammi ta aiko dasu na mutanen Ammah ita dai kawai tasan ta Debi shida ta bawa maman
mujiba tace ta aikwa makota Koda Wanda zasuje kada abun ya Zama na tsegumi.
Zahra ma nata mujiba ta debarwa tace ta bawa kawayensu Amma kadan zata bawa ita kunya ma takeji Ace Wai za'ayi wani Abu kuma na bikinta, daga baya kenan Wai sadaka da bazawara.
Ta
bawa magaji ya kaiwa Amatu da Aunty safiya sai wasu Kuma ta bawa sauran malaman duk da tasan abune Mai wahala suje tunda ko a Nan basuje ba tunda sukaji labarin ance mijin Almajiri ne.
Zahra na dakin Ammah su Inna suna karayi Mata nasihar zanmantakewar aur
e tana ta sharbar kuka, ficewa Ammah tayi Dan itama daf take da sakin nata kukan.
Tun dare Ammi ta Kira Ammah ta fada Mata akwai tickets na mutum goma a Nan hannun wani a Bauchi Wanda zasu rako Zahra dakinta, Sameer Yana Nan shine ze musu komai ze shigo su
wuce sauran mutanen Kuma motoci sun taho.
Har Cikin jirgi Abbanta ya kaita ya zaunar da ita kusa da Inna mainuna da Hajiya kaltume, Yana fadin.
"Hajiya gata Nan a mikata hannun Alhaji Muhammadu ace masa ga Amanar 'yata Nan kafin nazo da kaina,Allah ya sa
ukeku lafiya uwata ayi ta hakuri kinji".
Kai kawai ta iya gyada Masa ya juya ya wuce tabe baki mama tayi wadda ta kafa sai taje sokoton ita ta warke abinda yaso ya kawo sabani kenan da Abba sai da Ammah ta shiga tsakani tace ya barta tunda tace zata iya.
K
arfe Daya da kwata jirginsu Zahra ya sauka a sokoto,wani irin Abu Zahra taji ya tsirga Mata gata a sokoto karo na biyu a cikin girma da mutumci kamar ko wace Mace da ake aurowa daga gaban iyayenta sai yanzu ta Kara fahimtar manufar Ammi na rabata da gidan
tun ba'a Farga da ita ba,wato wannan martabar take nemar Mata kenan.
A Hankali take sakkowa daga steps din jirgin sanye da rigar material Mai azabar kyau da sari fari tasan Mai ratsin flowers coffee kalar material din Aunty Hasana na biye da ita a baya.
Ya
na tsaye daga gefe shida Tajuddeen ta ringa saukowa wata ni'ima yaji tana saukar Masa, ya yarda ya amince ta zamar Masa wani bangaren jikinsa ganinta kadai ya saka masa nutsuwa Yana binta da Ido har suka karasa gurin motocin da aka tanada Dan daukarta.
Tam
bayar duniya Tajuddeen yayi Masa akan me Suke jira a airport Amma yayi Masa Shiru.
Sai da suka wuce sannan Sameer ya Karaso Yana fadin.
"Ina Ina zamu nufa ne Wai?".
Wani smile yayi Wanda Kama gani kasan Yana Cikin nishadi.
"Gidan uwar gida za'a kaita mana
ta kwashi albarka, sannan ku kaita gurin Ammin na fadawa Shatu komai kuje Dan Allah Naga idanu sunyi yawa a kanta".
"Shegen sama kace wannan model din itace kayo kamu, Wai Dan Allah yaushe ka Sami lokacin mace yanda nasanka baka da lokacin kowa saina sabga
rka, Amma India ce ko?".
"Bafulatanar Adamawa ce?".
Ya fada a takaice yayi gaba inda Naseer yake zaman jiransu, da sauri Tajuddeen yabi bayansa.
Su Zahra na dosar inda masu tarbarsu suke Aishat ta taho da sauri tana rike da Afnan Wanda suka dauki wanka ga
yu dai yaci gidansu a gurin, rungumo Zahra tayi tana fadin.
"Amincin Allah da Rahamarsa su sauka a gareki sister Fateemah Zahra. Allah ya albarkaci Aurenku da zuri'a masu Albarka, barka da shigowa DANGE FAMILY you're welcome".
Afnan ce ta Fara zillo tana r
injayowa gurin Zahra, wato ta ganeta.
Hannu Zahra tasa ta karbi Afnan din daga hannun Aunty Aishat din, Hajiya kaltume da Inna maimuna suka nufi ubansun motar da za'a dauki Zahrar wadda sabuwa ce Zahrar ce farkon shigarta bayan direban Daya tukota.
Tun a a
irport Mama ta Fara Raina kanta yanda taga Mata 'yan gayu na gani kasheni Wai duk masu tarbar Zahra ne, ga wata yarinya Kuma da suka rungume juna itama wanke hannu ka taba ga Kuma yanda taga wata farar mace nata kaffa kaffa da Zahrar.
Mama Bata Kara Raina
kanta ba sai da suka shigo gidan Hajiya Inna inda taji wasu Mata na fadin.
"Wallahi soyayyar Hajiya Inna da mahmud tana burgeni sosai kiga fa Saida ya Fara cewa a kawota gurin kakarsa kafin a kaita gurin mahaifiyarsa".
Wata ashariya Mama ta lafta a Cikin z
uciyarta tana karewa gidan kallo me kalaman wadannan matan ke nufi? Gidan kakarsa wannan din? Ai jikinta har tsuma yake ta nufi kofar shiga da sauri so take taga zahiri Nan gidan tsohuwa ne, to Ina ga gidan iyayensa da Kuma nasa? Wato maganar malam na Band
e ta tabbata da yace wannan yaron yafi ko wane namiji daya taba kwatanta Yana sonta karfin arziki saita dauki maganarsa shifcin gizo yaso ya nuna Mata hanyar da za'a dakile abun duk da yace shi baiga saki a tattare da ita ba.
Wato abinda ya gano Mata kenan
tayi kunnen uwar shegu da maganarsa, ga abinda Asabe tayi Mata ta tabbata da an aiwatar da abin nan da yanzu wata kila Daya daga Cikin yaranta ne Dan aikin anyi shi da niyyar Zahrar ta bijiere ne taki mahmud fir har Abbansu yaji haushi ya Kara bashi madad
inta da Daya daga Cikin yaran nata, sai kuma Asabe tayi batan dabo Wanda har yau ko labarin Wanda ya ganta Mama Bataji ba.
Parlour ne na Alfarma tamkar wata fada Dan a tsakanin shekaran jiya da jiya Saida aka canza komai na parlourn tun Inna na mita harta
hakura dan tasan ba fasawa za"ayi ba Cikin barkwanci Hajiya Inna da jama'arta suka tarbi amarya da danginta, an Sha dariya Dan Hajiya Inna cewa tayi.
"Haba da walakin goro a miya shi yasa ya tubure mini Yana faman rantsuwar baze dawo ba saiya Nemo ki duk i
nda kike a duniyar Nan ya kawo mini ke har gida a ranar da ze bar gidan Nan, Ashe da abinda ya gano, tofa ko yaya ne dai nice ta karfen Kinga ai niya Fara kawowa ke ko?".
Inna maimuna ce tayi 'yar dariyar barkwanci Yana fadin.
"Ai Hajiya duk abinda lauje y
a yayo ciyawa ce, Kai da Kaya Kuma duk mallakar wuya ne, ga Zahra Nan taki ce tunda mahmud nake ne"
Dariya Hajiya innar tayi tana fadin.
"Ato gara na fada Mata kada taga Yana kawo min abu Mai maiko tace ya fifitani akanta."
Akayi dariya dai, duk Mama na z
aune kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ba wani karsashi ko daya ga rashin dadin jiki karfin Hali kawai takeyi Amma lafiyar dai sai a hankali.
Nan cikin part din Aunty Aishat tayiwa Zahrar da Aunty Hasana masauki kusa da bedroom dinsa na part din jiya
aka hada dakin komai sabo ne, laffayar Zahra ta cire ta kwanta kusa da diyarta da take ta Wasa da kafafuwa tana dagasu sama da gani tana Cikin farin ciki. Saida Aishat ta fice sannan Aunty Hasana ta dubi Zahra.
"Wacece wannan? Naga Suma matukar Kama da mah
mud sai dai ita farace sosai".
"Twins sister dinsa ce kamar keda Ya Hassan".
"Kai! Kice Suma irin mu ne? Ke twins sun sakaki a tsakiya kema Allah ya Baki irin mu".
Ta fada tana murmushi.
Kwal-kwal Zahra tayi tana kallon Auntyn tata.
"Ke! Wai lafiyarki kuw
a? kamar wata sabuwar Amarya sai wani rarraba idanu kikeyi tunda muka shigo garin Nan Naga kin kasa samun nutsuwa".
Hannaun Auntyn ta riko ta janyo ta kusa da ita kamar tana tsoron wani yaji abinda zata fada.
"Wallahi Aunty tsoronsa nakeji nasan no way out
a nan".
"Ban fahimta ba tsoron sa kamar Yaya? wani Abu yakeyi da kike gudun ya cutar da ke ko menene?".
Runtse idanu tayi sai hawaye, sharrrr..
"Aunty wallahi I am afraid about sex.."
Wani shock Auntyn ta shiga tana ayyana.
Babbar magana! Jarimi wato duk
tsawon wannan lokacin kallonta yakeyi kenan Saida ya kawowa iyayensa ita sannan ze nemi hakkinsa duk yanda akayi da dalilinta na wannan shiga rudun.
Amma a zahiri sai ta dake taja hannunta suka zauna a gefen gadon.
"Haba Zahra me kike son Zama ne?wa kikaga
aure ya kashe da zaki tashi hankalinki a banza, ai wallahi samun yaro irinsa a zamanin Nan sai an tona, ke idan kina da lassafi ko tari kin Bari ya kubce miki akan duk abinda yake bukata a gurinki ai wallahi yayi rawar gani, kada naji kada na gani ke ba g
odewa Allah Zaki ba, ki duba kiga inda ya fito da yanda Allah yayi masa nasibi a rayuwrsa tunda kananun shekaru da fitinannene da Allah kadai yasan adadin yaran daya Bata Amma yasan ke tasa ce malak malak ya iya kauda Miki Kai irin haka ai cewa nake zaki b
a marad'a kunya yayi yanda yakeso dake, Naga alamar sai anyi Miki shiri na musamman idan haka zakiyi wallahi kwana kadan ze lafto miki kishiya kina gani ta shiga gabanki ta kwace miki fada duk kuwa irin son da yake Miki idan baya samun gamsuwa a gurinki ze
ji kin fice Masa daga rai ki nutsu tun dare Bai Miki ba Ashe ganin kitse nake yiwa rogo Ashe ba jaruma bace ke ai sai ki Bari kiji Yaya Abun yake kafin ki yanke masa hukunci, Ina ganinki kin Kai matsayin da Zaki yiwa wata wannan karatun Ashe biri boko ce a
i Wallahi shima da nasa laifin har yaushe ze wani saka miki idanu kiyi yanda kike so'.
Knocking din kofar da akeyi ya saka Aunty Hasana dakatawa da fadan da take yiwa Zahra ta Dan matsa tana fadin.
"Bismillah shigo".
Aunty Aishat ce a gaba wasu 'yan mata
n buzaye farare tas suna biye da ita dauke da manyan basket dauke da kayan abinci.
Suka gaishe da Aunty Hasana sannan suka gaishe da Zahra.
Aunty Aishar ce ta gabatar da Zahra a gurin yaran sannan Suma ta gabatar dasu ga Zahra Radeeya da mardiyya 'ya'yan M
ummy badai'a ne wadda sukaje Azare tare matan uncle Ishaq .
Zahra ta nuna farin cikinta Sosai taso su zauna sukace Ammi tace su koma yanzu.
Abinci Aunty Aishat ta zuba musu tare da sauran abubwan da aka kawo sai da Aunty Hasana ta ce ta Bari ina zasu Kai
wannan abincin sannan ta bari.
Sai yamma Zahra ta sake wanka Aishat tazo da Mai yin makeup tayi Mata light ta kawo Mata wata irin Riga da Alkyabba Fara sol ta saka sai tayi wani irin kyau, Mai makeup din sai zuzuta Zahra take tana fadin.
"Masha Allah. Wall
ahi ban taba yiwa amaryar da kwalliyar ta ta tafi da imanina ba sai a kanki".
Murshinta Mai ban sha'awa Zahra tayi sai akayi dace Aishat ta dauketa hoto sai tayi wani irin kyau Wanda dole ka kalleta ka Kara, sai Kuma ta Fara daukarta video, tana gamawa tay
i review dinsa taga komai yayi ta hada da hotunan ta turawa mahmud.
Mota ta dauki Hajiya Inna da Zahra kadai ta nufi gidan Su mahmud dake Kan titin Garba duba.
Masha Allah gidan ya dauki haramin Dan mutum motocin a tare suka shigo su mummy Badi'a dasu Aunt
y Surayya su suka tarbi amarya har cikin master parlourn Ammi wadda Tasha gayu kamar ba gobe an tarbi Zahra da iyayenta tamkar Dade duniya Ammi Bata taba ganin Zahra ba sai yau har gurin da Hajja take zaune su mummy Badi'a suka kai Zahra Aunty Surayya na f
adin .
"Hajja ga kishiyarki Nan tazo ta gaisheki"
Hannu tasa ta bude fuskar Zahra.
"Masha Allah sannu yarinya kinji. Allah yayi Albarka ya kade fitina ya hada Arzikinku".
"Allahumma Amin"
Aka amsa, sannan taci gaba da fadin. "saifa kinyi hakuri da halin mi
jin namu dan miskili ne ga dukan Mata idan Zaki iya to idan Kuma kin barmana nida Kawata Hajiya Inna to yanda dai Kika yanke muna saurarenki".
Anyi dariyar kalaman Hajja sosai Aishat ce tace.
"Haba Hajja duk kishin ne haka? kinsan ko ana dara fidda uwa ak
ayi Mai dukan wannan sai ruwan sama shima sai idan ta tsaya Kice dai kina kishi tafi ku komai".
Gaishe da Hajjar Zahra tayi sannan suka karasa gurin Ammi itama saka Mata albaka tayi, sanna ta cewa mummy Badi'a su kaita dakinta.
Muzanta iya muzanta Mama tay
i Dan sai taji Daman batazo ba Dan ko suturar azo a gani Bata zo dasu ba tunda Bata taba kawo hakan zata riski dangin mijinna Zahra ba, sai taga zahiri Ashe ita karyar banza takeyi mijinta Mai kudi Saida tazo taga zahirin inda kude ke magana da kansu Dan y
anda aka tsara gidajen da abinda aka zuba kadai ya Isa ka yankewa kanka hikunci,dan Nan guri ne tamkar baza'a mutu ba.
Sai kusan magariba 'yan Azare suka samu isowa, part din sameera matar Abbie da suka rabu aka gyarawa Baki, aka saukesu ba Karamin mamaki
Mama tayi ba ganin harfa Hameeda a cikinsu.
Aunty Hasana ma dakin baki na kusa da Aishat aka bude musu suda su Inna maimuna.
Da wuri suka kwanta duk da ba wata tafiya sukayi Mai tsawo ba tunda a jirji sukazo.
Wurin Sha Daya mahmud ya kirawo Aishat Yana ta
mbayar ta Ina Zahra?
"Tana dakin Ammi fa ni Kuma Ina kasa".
"Dan Allah ki fito min da ita wani Abu Zan fada Mata na Kira wayarta a rufe".
"Kaima kasan wasa ne naje nace ta fito sai dai ka Kira mummy Badi'a ka fada Mata sai naje na taho maka da ita tunda ba
zaka iya hakurin goben ba, ni na rasa wane kinibibin ne yasa ka haramtawa kanka abunda Allah ya halasta maka Saida aski yazo gaban goshi Kuma zaka tuburewa mutane kawai ai saura kiris dai kowa ya huta, sai kuje can ku karata a hanyar karaye".
"Afuwan Aunty
na Kece fa kika rudani wallahi, da kinsan bazaki kawo min ita kamar yanda kikayi min alkawari da Baki turo min hotunan Nan ba gashi kin
Sak."
Kit ta yanke Kiran taga alama nema yake ya saki layi Kuma gara a tattara a Mika masa ita a wuce gurin, taji suna
maganar wani taron yini fa da momin kano tace ta dauki mauyin yinsa.
Tashi Aishat din tayi ta nufi sama tana hawa ta Fara jiyo muryar su batool daga dakin da Zahrar take, Dan knocking tayi kafin ta turata ta shiga.
"Wai ku menene haka kikeyi? Ku barta ta h
uta kunsan nisan tafiyar da tayi kuwa da kuka tasa ta gaba da surutu Kuna ma duba time kuwa?".
Tashi sukayi sun Kai su shida suka fice.
Shigowa tayi ciki tana sakin murmushi tana fadin.
"Nazo a bani sirrin Nima Sweet heart ya ringa rikice min kamar yanda H
ussein yake rikicewa ko a gaban waye idanunsa rufewa sukeyi, sai ki ringa kula dashi yanda baze ringa sakin layi ba kada ku raba Hali a gaban Ammi yasa kiji kunya".
Hannu Zahra tasa ta rufe idanunta tana fadin.
"Kai Aunty Dan Allah ki daina fadar haka Ni w
allahi ba ruwana fa".
"Na sani shine baya iya jure kiyi nesa dashi yanzu ma fa shine yake nemanki a can part dinsa na Cikin gjdan Nan Wai na Kai Masa ke Yana jiranki".
Wani kwalalo sexy eyes dinta tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta.
"Dan Allah Aun
ty Aishat ki rufa min asiri wallahi bazan iya fita ba, me zanyi masa Kice Masa nayi barci Dan Allah".
Idonta ya cicciko da hawaye.
"Shikenan kada kiyi kuka Hajiya shagwaba ki Adana abinki tunda Mai lallashin baya Nan".
Dan murmushi a tayi a kunya ce tana k
auda kai.
Ficewa Aishat tayi tana saka wayarta a Airplane mode.
*
Da safe sosai gidan ya kacame da Baki kowa sai sabgar gabansa yakeyi, Zahra na daki tun bayan da tayi sallah ta shiga ta gaishe da Ammy da Hajja wadda a Nan ta kwana tunda Allah yayi Mata la
fiyar kafa daraf take hawa sama.
Daki ta koma duk da Hajja taso ta zauna suyi Hira, tana kwance tana chart da dasu Aneesa wadda suka nufo sokoton ita dasu Fatima da Khadija.
Sajeeda Kuma sai karfe flight din is karfe biyu zata biyo zuwa sokoto, Jin alamun
bude kofa yasa Zahra dago Kai Aunty Rukayya ce da Fateeha suka shigo, da wani uban tsalle Zahra ta tashi ta fada jikin Aunty Rukayya tana fadin.
"Daman Kuna Nan Aunty Rukayya? Sannunku da zuwa"..
Ta Mika hannu ta karbi Akram.
"Wallahi muna Nan Amarya ai
harda mutuniyar dasu mommy".."
"Kai haba dai harda Hajiyata kuka dauko ga nisa".
"To ya za'ayi tace biki na farar kaza Wai balbela ba gayya ce ba, haka fa ta fada min".
Anan suka baje tare sukayi break fast da ita, kafin Azzahar gida ya gama cika an yiwa Z
ahra makeup na garari, ana haramar tafiya gurin walima su Ummee da Aunty Nauwarah da mommy Haneefa suka sauka Mahmud da Kansa ya dauko baikinsa dan ya cewa Ummee zuwansa ne bana Zahra ba, Su Ammy