Showing 180001 words to 183000 words out of 295116 words

Chapter 61 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

dinta ta wuce ta nufi kitchen inda ta samu Alawiyya tana aiki.

"Ina Ammah?".

Zahra ta tambayeta.

"Tana bangaren Abba zata dauko sakon Daya turo a daukar masa, tan

a Nan Ammah ta shigo da takardu ta mikawa Alawiyya ta kaiwa malam Bala driver.

. lokacin da suka fito zahra nata zabgawa Ammah magiyar da besan kota mecece ba, zahra Ammah ta kalla.

"Ya haka Baki bashi abincin bane?".

Dan narke fuska tayi.

"Ni ai bansan na

waye ba, a Nan na gani kawai na dauka Baki zakiyi".

Harara Ammah ta zabga mata.

"Amma ke bansan yaushe Zaki nutsu ba wallahi to maza Zuba Masa shida zeyi tafiya".

"A'a Ammah zamu tafi dashi can kada na makara".

Mahmud ya fada Yana kokarin tashi.

"To shike

nan Bari Alawiyya ta Kai muku mota, maza fada Mata ta dauko basket ta Zuba".

Kitchen din zahra ta koma, Ammah Kuma ta fuskanci Mahmud dake fadin.

"Zamu tafi Ammah kiyi min addu'a".

Sai taji yaron ya Kara shiga ranta duk Inda ya fito ya samu uwa ta gari, c

ikin nuna kauna tace Masa.

"Ubangiji yayi Albarka ya taimaka ya kaiku lafiya ya bada abinda akaje nema".

" Allahumma Amin, nagode".

Ya tashi yayi waje, Yana fita zahra ta matso kusa da Ammah.

"Yanzu Ammah ki rokar min ko sati Daya ya Bari nayi Amma kika Ki

ya shikenan".

"Kina son na Zama uwar banza kenan? yaron Nan bansan abinda ya gano ba tunda harya iya tunkarata da irin maganar Daya fada min kije kawai ki yiwa mijinki biyayya idan anjima da magariba magaji ze kawo zilan sai ku zauna, kije Yana jiranki kad

a ya kosa".

Tare suka fito da Alawiyya data dauko Abinci.

Tunda suka dauki hanya yake amsa waya da alama da likita yake magana a yanayin yanda ta fuskanta.

Lokacin da suka shiga gidan wani daban ta gani ba zayyan ba sai safwan tunda shi tasan shi a kano.

Gurin motar suka karaso, da sauri safwan ya bude masa ya fito.

Dayan ya duba yace.

"Naseer ka kula da gidan Nan kafin zayyan ya dawo idan an Jima wani yaro ze kawo wata mata, daga su ban amince wani ya shigo gidan nan ba har zayyan ya dawo, sannan ya juya

gurin safwan ka Zama ready Zan fito Nan da ten minutes in Sha Allah".

"To suka amsa sannan suka koma Inda suke.

Dayan side din mahmud ya koma ya bude Mata ta fito a yangace Yana nazarce da ita ba haka taso ba so tayi a ajeta a can ta Zama nama shi Kuma abi

nda bazeyi tolerating ba kenan.

Ta baya yabi da ita tayi mamakin ganin kofar kenan ginin dai sak irin na Kano ne, suna wuce idanun jama'a ta dauketa cak Bai direta a ko Ina ba sai bedroom dinsu ya ajeta, wata irin soyayya ya kwada Mata Mai wuyar mantawa ta

re sukayi wanka shaf-shaf suka suka shirya da kyar ta matsa Masa yaci abincin, Yana mak'ale da ita suka fito, cikin motar suka shiga tare a Nan ma saida yayi son ransa kafin ya barta ta fito.

Saida ta juya ta Fara tafiya sannan safwan ya taso, fitowa mahmu

d din yayi.

"Precious...."

Ya fada Yana Jan sunan.

Cak ta tsaya Amma Bata juyo ba Dan idanunta fal da hawaye ji take Kamar ta bishi su tafi Batasan tayi mugun sabo dashi Kamar haka ba sai yanzu da zeyi Mata nisa, Saida ta shanye hawayen sannan ta juyo, wan

i kiss yayi Mata blowing dinsa sannan yace.

"I missed you my previous, I really missed you".

"And me too...." Ta fada tana shigewa ciki.

Jikinsa ba karamin sanyi yayi ba a haka suka fice daga gidan.

,

Mahmud Basu shiga Kano ba sai kusan magariba sultan r

oad suka nufa, Saida ya huta yayi wanka sannan ya kirawo Sameer ya fada Masa ya shigo yazo ya sameshi a sultan road, ta Tarauni suka biya suka sai musu fruits sannan suka wuce can court road din.

*AUREN HUCE HAUSHI*

MAMAN FATEEMAH.

08055362975

____

My

WhatsApp number

09061432330

Page 61.

.............Ana Kiran sallar insha'i suka shiga unguwar, a masallaci suka tsaya sukayi sallah, su Kuma su Habib a masallacin kusa da gidan sukayi sallah, gurin Mai gadi suka zauna suna Hira Abu daya ya ringa bawa

Habib mamaki yanda Mai gadin ke yiwa Abubakar wasu maganganun dake nuna da sanayya a tsakaninsu Koda ba Mai yawa bace sai dai shi Abubakar din Yana waskewa ya basar dashi, suna cikin wata hirar da tayi matukar bawa Habib mamaki ne sukaji Horn din mota dag

a waje da sauri Mai gadin ya tashi yana fadin.

"Ga Oga nan da kansa, gaskiya ba karamin matsayi bawan Allahn nan ke dashi a gurin yallabai ba, yaushe Rabon da wani ya ganshi sai irin ku Abubakar 'yan gaban goshinsa".

Ya fada yana nufar gate din cikin azam

a, ya bude kofar motar ta kunno kai ciki.

Mai gadin ne ya Fara jera Masa kirari yana fadar.

"Allah ya taimaketa barka da sauka fari Mai farar aniya! Allah ya Kare maka mutuwar zuciya kaga Wanda yayi gadon arziki uwa da uba. Ubangiji ya Kara maka daukaka da

daraja, baya Mai goya marayu kaga Dan sakwkwatan Asalin jikan zabarmawan Niger ubangiji ya Kara maka daukaka da arziki Mai Albarka, ya tsone idon maqiya da mahassada a kanka, jikan Hajiya Inna Mai abin mamaki"..

Haka ya biyo motar Yana zabga Masa kirar

i, in da sabo Mahmud ya saba da halin malam sule tamkar maroki haka yake.

Abubakar da Habib ma tasowa sukayi suka nufosu, Amma fa zuciyar Habib fal mamaki, to me hakan ke nufi? be Kara shiga rudani ba Saida yaga Mahmud ya fito ma'aikatan gidan suna nufosu

da sassarfa suna kwasar gaisuwa, shi in ba idanunsa ke fada Masa karya ba sai yaga wannan na tsayen ba Mahmud dinsu bane, Dan totally ya canza a idanunsa Bai gaskata shi bane Saida yayi magana lokacin da hadiman gidan ke kwasar gaisuwa.

A gurguje yake amsa

wa ya nufi bangaren da baba malam din ke ciki,duuuu suka bishi a baya, Koda Wasa Mahmud be yarda sun hada Ido da Habib ba.

Lokacin da suka shiga Malam ya farka Yana sallah, Sauran hadiman juyawa sukayi suka koma dakin ya rage daga su Mahmud sai nurses din

da suke kula da shi. Cikin girmamawa suka gaishe da Su Mahmud din.

Saida Baba malam ya shafa Addu'oinsa sannan ya dubi gefen dasu Mahmud ke tsaye, ganin ya idar da sallar yasa Mahmud matsawa kusa dashi Yana murmushi, shima Baba malam din murmushin karfin

Hali yake mayar Masa, gefen gadon ya zauna kusa dashi sosai ya riko hannunsa.

"Sannu Baba malam, ya jikin naka?".

"Masha Allah. Alhamdulillahi jiki da sauki kam, Allah yayi Albarka".

"Amin ya Rabbi.Allah ya baka lafiya gobe karfe shida da rabi na safe zamu

tafi in Sha Allah".

Dan Jim malam din yayi kafin yace.

"Zuwa Ina Kuma mahmudu?"

Sameer ne ya matso Yana gaishe da baba malam din sannan yayi masa bayanin halin da ake ciki.

Shiru yayi Basu yi zato ba sai ganin hawaye sukayi yana bin gefen idon Baba malam.

Cikin rudewa Mahmud da su Habib suka shiga tambayarsa.

Menene? Ina yake Masa ciwo? Har Daya daga cikin nurses din ya Ciro waya ze Kira doctor Mahmud ya daga Masa hannu alamun ya jira.

"Babu komai, me zance muku yaran Nan Ubangiji yayi Albarka, ya biyaku

da Aljanna madaukakiya"

"Allahumma Amin,Allah ya baka lafiya".

Daga nan yaja Bakinsa yayi shiru, Suma babu Wanda ya Kara cewa komai.

Key din motar Sameer ya mikawa Abubakar yace.

"kuje ku shigo da Kaya".

Nurses din Sameer ne ya tambayi nurses din ko akwai

abinda suke bukata? Sukace masu babu duk abinda ake bukata daga Nan zuwa safe akwai shi.

Ledoji ne manya suka shigo dasu, da Ido baba malam ya bisu kawai har suka aje, shi tun ganin gidan da aka kawo shi da irin yanda aka dauko Masa manyan likitoci suka

zo suka zauna zaman jiran zuwansa da irin yanda yaji Wani Yana fadiwa abokin aikinsa yana Abuja DANGE ya katse Masa tafiyarsa dole ya dawo duba patient dinsa, ga ma'aikatan jinya an aje su duba shi,yasan abun bana Wasa bane, da abinda Allah s.w.a ke nufi

da kawo wannan yaron cikin rayuwarsa ya Dade Yana mamakin halayyarsa da yanda yake mu'mala da jama'a zuwan gurin tamkar kofar arziki aka bude musu taimako da tallafi Kota ina, a she ubangiji ya sallad'o wata kaddarar da tafi karfin tunaninsa shi wannan ya

ron ze zaman sanadin tallafawa rayuwarsa, Hamdala kadai ta kamace shi, a zuciyarsa ya dunga maimaita ta, ya Kara girmama girman ubangiji, wato duk abinda Allah s w.a yayi akwai hikima a cikinsa sai wani abun ya faru kasan wani connection din yafi gaban kar

amin tunanin mutum.

Mahmud Bai bar gurin Baba malam ba Saida ya matsa din yaci Naman kazo yasha fruits sosai, misalin goma da rabi suka fice daga gidan Muhmud be koma Nasarawa ba Nan Bawo road Sameer ya ajeshi, bayan sameer ya wuce ya dade Yana ta kokarin

ya samun visa zahra abin yaci tura, duk Wanda yake tunanin zasuyi masa aikin duk ya rasa su, abin ya bashi matukar mamaki Dan wannan shine first time da irin haka ta faru dashi, dole ya hakura ya sakawa sarautar Allah Ido besan abinda Allah yake nufi da H

ana samuwar visar ta taba.

Su Habib ma sunso kwana a gurin Baba malam, Anna kememe nurses din suka Hana sukace aikin da aka biyasu makudan kudi suyi kenan,idan yallabai yaji labarin sun Kwana a Nan za'a samu matsala dan ba karamin warning aka kada musu ba,

dole suka hakura suka wuce nasu masauki daura da Inda Baba malam din yake.

Gida ne na Alfarma tamkar gidan want gwamnan komai na Jin dadin rayuwa an tana deshi hatta da suturar sakawa gasu Nan sabbi sai da ka saka Wanda yayi dai dai da kai, Abinci sai Wan

da kake bukata za'a kawo maka tunda suka sauka ake hidima dasu Baga Abinci ba Baga snacks ba Baga drinks ba, komai enough gashi nan, gurin malam sule suka koma sukaci gaba da Hira a Nan Habib yaji shima Ashe Abubakar Dan Sokoto ne.

Saida sukayi Shirin kwan

ciya sannan Habib ya kalli Abubakar.

"Dan Allah ka fada min gaskiya Daman kasan Mahmud ne kafin kaddarar data kawo shi nan Azare? Naji Mai gadi Yana maka wasu maganganun da suka sakani a duhu?".

Dan Jim yayi Yana nazarin maganar Habib, kafin yace.

"kayi h

akuri nayi maka Alkawarin fada maka Amma Dan Allah ba yanzu ba".

Jinjina Kai kawai Habib yayi, alamar gamsuwa, Bai Kara cewa komai ba ya kwanta zuciyarsa fal tambayoyin rab'ab'a wanda bashi da amsarsu.

Mama tun Rana da tayi muguwar kwarewa har dare tana

fama da kanta duk abinda ya kamata, Tasha ta Sha Amma dai Abun yaki Zama dai faint Dan ji take wani Abu ya tsaya Mata a kirji yaki wucewa, da kyar wurin goma na dare ta samu number Aunty Larai ta kirata cikin nuna damuwa ta zayyane Mata komai da yanda taga

Mahmud, da zargin da take yiwa Abba akan Yana da masaniyar ko waye yaron har canzawa da Zahra da Mai aikinsu zilai Saida ta fada mata, bala'i Aunty Larai ta Fara tana zuga Mama dole tayi Abun da zata wargaza rayuwar yarinyar gaba Daya tunda Asabe ta nunaf

rceta ta gudu da wadannan magungunan da aka kawo Wanda da anyi yanda akace da yanzu ba wannan labarin akeyi ba, kudi masu yawa Mama ta turawa Aunty Larai tace tayi duk abina ya kamata, sun Dade suna tattaunawa kafin suyi sallama da alkawarin da safe zata b

azama gurin arnan Kan Dutse.

Aje wayar Mama tayi tana fadin.

"Wallahi Asma'u keda wannan Fara farar yarinyar kun shiga uku, kuda kwanciyar hankali kunyi ban Kwana Ina Raye bazanga bakin ciki ba, wannan yaron ace shine mijin zahra? Wato a baya kallon tsoro

nayi Masa kenan,wallahi sai kwanciyar hankali ta gagare ku, Dan karya malam na Bande ze want ce bega rabuwa ba a cikin aurensu Naga kashin awaki saina rabasu yanda naji niyya saina tagayyara rauwar Zahra babu fashi Dan halak ka fasa".

Ta debo wata ashariya

ta lafta tana kwafa duk idanunta sun firfito saboda bacin Rai ga azabar data Sha ta kwarewa.

* * * * *

Tun bayan tafiyar magaji zahra da Aunty zilai suka shiga kitchen sukayi simple girki, Aunty zilai ce ta mikawa Naseer,Bayan ta dawo ne take fadin.

"Uwar dakina wato lamarin yallabai Yana bani mamaki gashi dai yaro Karami amma fa Naga alamar kowa a Karkashinsa yake,dan oga Sameer na fuskanci a nan ne yake oga amma a waje yaron oga ne". Ta fada tana dariya.

Dan yatsina fuska zahra tayi.

"Nifa na aje l

amarin su a gefe,ita dai ai karya ai fure take Bata 'ya'ya, ni meye nawa tunda Kika min fada a kano na sakawa Raina salama na iya kaina tunda Naga abun nasu ba Mai karewa bane, Kullum da wani sabon salon da Zaki gani a gurinsu basai mitum ya Zuba musu ida

nu ba Randa suka shirya magantuwa sai su magantu".

"Gaskiya dai kam, Nima da farko na shiga razani lokacin da aka Kaimu Kano Amma Dana ji bayani daga bakin Iya Rahane saina fashimci duk Inda mijinki ya fito ba daga Karamin gida ya fito ba,Kuma naji kishin-

kishin din bacin Rai ne ya fito dashi Dan iya ta fada min sai dai tace Bata San takamaimai menene ba itama tsintar zancen tayi mommy da oga Sameer sunayi ta shigo ta kofar kitchen ta baya, abunda nakeso dake uwar dakina duk Inda rayuwa ta kaiki ki Zama Mai

takatsantsan da mutane yanda naji labarin nasa dai sai kin nutsu sosai Dan na fuskanci mijin naki ko a cikin dangain na daban ne shi gaskiya, bare yanda naji iya Rahane na fada sai Wanda ya gani, Kinga dai yanda akayi ta samun akasi akan Aurenki Kuma Bill

ahillazi asirai ne aka dunga yi nasan Allah ne ya nunawa ko waye ma iyakarsa ya Baki miji Daya da daya, wallahi a gaban idona anyi dariya an Kara akan an aura Miki Almajir Qolo Wanda Bai aje ba Bai bada ajiya ba, ance sai aga ta taqamar kyau an Kare a Alma

jiri mane min tsaba".

Ta fada cikin nuna bacin Rai.

"Kai haba Aunty zilai meye na tuna abinda ze Bata Miki Rai, ba gashi ya Zama fast ba, Ni nasan mutum be Isa yayi min abinda babu Shi a cikin kaddarar da Allah s.w.a ya rubuta min ba. Daman haka take kadda

rar sai dai a jahilci irin na mutum yaga abinda yayi ne yayi tasiri,sun manta Alkawarin Allah baya canzawa". Kai Aunty zilai ta jinjina tana fadin.

"Wannan gaskiya ne Allah ya Kara Miki tawakkali da qarfin imani ya doraki a Kan mak'iya da mahassada, yasa w

ata Rana ki Zamar musu kadangaren bakin tulu a barka ka bara ruwa a karka a Kar tulu, Allah ka nuna min ranar da karya zata Kare gaskiya tayi halinta in Sha Allahu sai kin zamar musu ciwon Ido ba yanda za'ayi dake sai hakuri, in Sha sai munga karshe masu h

assada da muna furci".

"Allahumma Amin".

Sun Dade suna hira kafin zahra ta nunawa Aunty zilai wani daki a cikin parlour na biyu daga cikin corridor da yake fitar da mutum waje, daki ne comfortable yaji Turkish bed Mai shegen kyau yasha ubansun bedsheet sai

sanyi A/C da kamshin roomfreshner dake tashi, sallama zahra tayi Mata ta wuce nata bedroom din.

Wanka tayi ta Saka sleeping dress tayi shafa'i da wutiri sannan ta kwanta, lamban tayi a gado, duk kewarsa ta dameta Amma tana Jin nauyin kiransa a wannan loka

cin rabonsu da waya tunda ya kirata yace Yana Dutse, da magariba tayi ta try Bata same shi ba tasan yanayi network duk da tayi marking da wuya a Kira wayarsa Bata shiga ba.

Data ta bude tana duba sakonnin da suka shigo Mata ba tunda ta mayar da master layi

nta Daya Bata dazu.

Reply din sajida ta Fara dubawa, saina Aunty Rukayya data tura mata sallama ta fada Mata itace, sakon karin jajanta rashin lafiyar malam ta turo mata har tana tsokanar ta akan meya Hana balarabiya taje India ta Sami ruwa biyu tunda kyau

ne ke dukan kyau, Emoji na rufe Ido da hannu ta tura Mata.

Ba zato kawai kiransa video call ya shigo, wani Abu taji ya tsirga Mata tsikar jikinta ta tashi, data tuno moment dinsu na dazu.

Dauka tayi tana lumshe sexy eyes dinta.

"My previoussss.."

Ya fada

a hankali, Yana bin fuskarta da kallo gani yayi Kamar Kara Mata kyau akeyi matukar zeyi some hours Bai ganta ba.

Cikin nata salon ta bude idanunta dake Rita Masa lissafi ta saukesu a Kan nasa.

"Yesss.. meu Amorrrr..."

"Ya Salammmm.."

Ya furta a hankali ta

mkar Mai tsoron wani yaji abinda yake fada, da gaske yarinyar Nan so take nayi ta sakin layi a gabanta.

"Cikin muryar data saka zahra a cikin wani yanayi yace.

"Inaga na fasa tafiyar Nan har sai kin samu visa Kona tafi akwai damuwa gaskiya".

Tashi zaune t

ana cire blanket daga jikinta tunda tana jingine da pillow ne a jikin face din gadon, rigar irin transparent din nan ce Mai siririn hannu baqa sai ta Kara haskaka fatar Qirjinta sosai Nan da Nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa.

Cikin shagwabar data Fara zamar M

ata jiki ta Fara fadin.

"Haba dai Dan Allah me Amor... kuje kawai babu Dadi Baba malam ne fa ba Wani ba,! Idan ma kazo to me zanyi maka sai dai fa ka raba hankalinka biyu, Amma idan kuka tafi zakafi samun nutsuwar data Kamata, kaji plsss.. Dan Allah".

Mak

'e kafada yayi tamkar yaron goye Yana Mata wani kallon Daya sakata rufe idonta dole.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login