Showing 171001 words to 174000 words out of 295116 words
muje na duba shi".
"Ok, shikenan ku shiga Allah ya bashi lafiya".
Ammah ta fada ta wu
ce main kitchen dinsu sata dauko wasu abubuwan tunda Alawiyya Bata Nan ta aiketa gidan Hajiya kaltume.
Nan suka bar Mama sororo da tarin kunya wato amsa aka Bata a kaikaice.
Jiki ba kwari ta koma part dinta.
Su zahra suna shiga Musaddiq ya mika Mata Jakart
a Yana fadin. Kai Adda kike yarda Jakarki da kudi da yawa Kuma a ciki".
Kansa ta shafa tana fadin "Ni bani da wasu kudi a ciki, Wai Ina zaka Naga kana Bata rai?"
"Ba Ammah bace ta bada kyautar biscuits dina da chocolates da suka rage ba a kaiwa jikar Haji
ya kaltume data aiki Aunty Alawiyya Ni Kuma Ina son All butter Kuma babu a Nan kusa sai naje store Kuma Zazzabi nakeyi".
"Ah gaskiya ba'ayi daidai ba, kayi hakuri na bude opay sai na yiwa magaji transfer saiya sawo maka"
"Kai! Adda ki duba da kudi fa a jak
ar sosai".
Budewa tayi taga da gaske yakeyi to tana tunani lokacin da tayi barci ya Zuba matasu.
Jeka kirawo Amadun gidansu Aunty mujiba yaje ya sawo maka".
Ya fice Yana tsallen murna.
Ammah ce ta shigo da wasu ledoji a hannunta, da sauri zahra ta tashi t
a karba tayi kitchen dasu, da Ido Ammar ta bita 'yar tata ta cika Masha Allah ta cicciko kamar me karamin ciki Amma idan tayi la'akari da duka yaushe suka bar garin a halin ciwo ai ko cikin ne be Isa ya nuna Kansa haka ba, kawai samun hutun Zama guri Daya
ne.
Kusa Ammar ta zauna data dawo.
"Ki daina saka turare haka duk kamshinsa ya kashe min nawa na freshner da turaren wuta".
"Wallahi Ammah Wanda nake sakawa ne na saka, yanzu Dan Allah Ammah inata rokonki jki taimaka ki saka Baki ya maidoni gida Amman Kika
qiya, nasan badan rashin lafiyar Baba malam ba bazezo Dani garin Nan ba".
Dan murmushi Ammar tayi Tana K'are Mata kallo.
"Meyake Miki da kike son barin kusa dashi ki dawo Nan kina ganin hakan shiya fiye Miki? Ashe har yanzu Baki da wayo kada na qara Jin m
agana makamanciyar wannan daga bakinki,duk inda mijinki ya saka Qafa ki maida taki duk inda yace ki zauna ki zauna".
"To Ammah,amma fa Kinga mahaukatan gidajen da yake kaini wallahi Sunfi Qarfin kwakwalwata Dan Allah ki taimaka kiyi min gata ki tambaye shi
ya fada Miki gaskiya waye shi Kuma daga Ina yazo Kuma meye sana'arsa wallahi Ammah tsoro lamuransa suke bani. Fuska biyu gare shi wallahi ko suturar da yake sakawa a can ba irinta yake sakawa a Nan ba ki agogunansa fa Rolex ne, Kuma duk gidan daya kaini b
abu abinda babu hatta suturar da Zan saka da akwaita idan zamu shekara bazan nemi suturar sakawa ba shima haka, ban fada Miki ba harfa gidan Nan garin Saida na tarar da mahaukatan kayan sakawa a can".
Wayar dake jakar ta aka Kira abinda ya katse Mata zubar
da takeyi kenan.
Tunda ta dauko wayar Ammah ke jinjina Kai da duk abinda zahra ke fada ta dauke shi rashin son Zama da Mahmud ne ke dawainiya da ita Amma ganin iPhone 16 plus yasa jikinta yayi sanyi wayar wajen 1. 46 a gurin zahra? Dole tasan waye 'yarta
take aure ko kowa be mata wannan aikin ba ita zata yiwa kanta saboda akwai bukatar sanin waye shi, tunda zilai ma korafinta kenan akan gidan daya saka aka kaisu da Kuma yanda ake kawo Mata kudi ace shiya bada a Bata bayan sutura tace an Bata kusan kala gom
a babu na banza tace wasu ma Bata taba zaton sata samesu ko a Jace ba an Bata sabbin su.
Jin Mahmud ne yasa zahra Dan kallon Amma taga ko hankalinta Yana kanta sai taga ta Mike ta nufi kitchen ajiyar zuciya ta sauke Dan wasu kalamai yake fada Mata Wanda su
ka girmi shekarunta kamar bashi bane ya kwana zulumin lalurar Baba malam, wato yazo ya ganshi ya samu 'yar nutsuwa ze ishetq da wannan maganganun nasa masu nauyi a kwakwalwarta.
"Kina jina?"
"Uhmmm ina ji, Dan Allah kayi min Alfarma na kwana gurin Ammah wa
llahi nayi kewarta sosai".
Abinda kunnuwan Ammah suka jiyo Mata kenan tazo fitowa.
Jinjina Kai tayi tana ayyana bazaki mayar Dani sakaran uwa ba kibi mijinki can ku karata".
Ya koma taci gaba da abinda takeyi Daman fitowa tayi taji idan zataci fattira wadd
a aka yiwa Imam be Kai ga tashi ba taji ana neman mayar da ita shashasha ta barta ta kwana a Nan mijinta na can rakube kamar gwauro.
Mama ce a daki tana ta faman Kai kawo da waya a hannu ganin zahra ya daga Mata hankali ba kadan ba, a fill ta Fara fadin.
"Jar uba wallahi baze yuwu ba wannan ce matar Almajirin? Da sake wallahi Alhaji munafuttarta yayi yasan ko waye ya dauko agola ya bawa ga 'ya'yansa na cikinsa be Basu ba, wato ni za'a yiwa lullubin biri ko? Wai Ina Kika shiga ne Asabe! Naje gidan,na tura
babu ke babu mahaifiyarki na Kira wayarki Bata aiki Kuma mahadin cimma burina Yana hannunki tunda Kika karbo ban Kara jin ko labarin Wanda ya ganki ba"
Ita kadai a daki tana ta buga sambatu kamar sabon kamu, Aunty Ladi ta Kira akace Mata wayar a rufe tak
e jefar da wayar tayi Kan gado tana buga tsaki tana fadin. Wallahil da sake dole nayi Wani Abu yau ba sai gobe ba".
_AUREN HUCE HAUSHI_
08055362975
* MAMAN FATEEMAH*
Page 59
.......... Abincin kawai Ammah ta zubowa zahra ta fito mata dashi, l
okaci Ahmad din yazo zahra ta bashi kudin da za'a sawowa Auta kayan kwalam, Ammah ce ta tsawatar Jin yawan abinda za'a sawo.
"Ki Bari a sawo masa kawai Ammah ba sai ya rinqa zuwa makaranta dasu ba tunda yace nasa kinyi kyauta dasu"
Tana Ciro kudin magaji
ya shigo da manyan ledoji a hannu Yana fadin.
"Ina Ammah Bari kiga Aunty zilai yanda ta zama inaga supplement Tasha ta Zama haka naga alama harda bleaching takeyi Kinga yanda ta ...
Bai karasa ba yaja birki Yana ware idanu.
"Kam bala'i! Wannan yarinyar ya
ushe kikazo? Gaskiya kinci Amana koki nemeni duk amincin dake tsakaninmu dake har kizo garin nan ki mike kafa kiyi awanni Baki bada cigita ba,wato kin Zama DONE ko? yanzu na baro mijinki a Asibiti shima ya wani zama Jan wuya,da gani Yana Gane garin Dan ba
haka yabar garin Nan ba, ku fad'i gaskiya dai ko kun danne Kan dollars din America na qungiyoyin da kuke yiwa aiki?".
Pillown kujera karami zahra ta jefa Masa daga inda take zaune.
"Allah ya shirye ka magaji, Kai Kullum baka girma, shi yasa nafi son Zama d
a Ya Imam wallahi saboda komai nasa gentle yake yinsa, amma Kai kamar rikon kauye,gaskiya da a kauye akayi ka da anga tabargaza, Wai nice yarinya ka tafi ka nemi yarinya ni yanzu yayarka ce dole kace min Adda, sauran amsar Kuma sai mun kebe Zan baka ita".
Dariya ya dauka Yana tafa hannu.
"Very good, inye yaushe kikayi Baki irin haka? Da sake wallahi Nima azo ayi maganar manya auren nan zanyi, kuga yarinya ta zanzare tayi bulbul sai magana fal cikinta".
"Magaji! Magaji! Wallahi ka fice kada na Bata maka Rai
yanzu, daga zuwanka zaka damu mutane, ka Dade bakayi auren ba mutumin musawa".
Hannuwa ya hade irin yanda indiyawa sukeyi.
"Sorry Ammah idan na fita dawa zatayi Hira ki Bari mu Dan cukusa kadan dan Allah".
Sallamar zilai ce ta katsewa Ammah hanzari abinda
zata fada.
"Lah! Aunty zilai har kun karaso? Sannu da hanya".
Zahra ta fada, tana kallon magajin.
Yara ne suka shigo da Kaya suka sauke suna gaishe da Ammah, sannan suka gaishe da zahra.
Da sauri magaji ya fita Yana Fadar.
"Ina Zuwa ya fice.
Wasu kayan y
a dauko, zahra na ganinsu ta gane Wanda Zayyan ya aje a gidan dake BAWO ROAD ne, sai yanzu taga Ashe kilishi ne dasu dabino da cukui sai tarkacen kayan zaki dasu BAMA.
Sauran Kuma suna cikin ledoji.
Gurin da Ammah ke zaune Zilai ta karasa ta tsuguna tana f
adin.
"Sannu da gida Ammah mun sameku lafiya? Ashe Kuma Baba malam haka tsautsayi ya sameshi, Allah ya bashi lafiya, Kuma nagode Ammah Allah ya jikan mahaifa ya yiwa zuri'a Albarka a tayani godiya gurin yallabai nagode, nagode".
Sai hawaye.
"Ikon Allah! k
u kuma da 'yan kuka kuke shigowa garin? itama mutuniyar da kukan ta shigo min, amma na fashimci kukan Dadi kukayi gaku nan kun zama wanke hannu ka taba".
Yar dariya zilai tayi tana goge hawaye.
"Wallahi Ammah duk yanda Zan fada Miki karamcin da akayi min N
i kaina baze misaltu ba Kinga waccan jakar wallahi duk suturu ne babu ta karamin kudi a ciki Kinga yauma abinda oga Sameer ya bani".
Ta dauko envelope brown ta dora a gefen kujera inda Ammar ke zaune.
"Tab Aunty zilai kice shagalinku kuke a kanon kun nink
e mu a nan, da gaske Ammah wannan yarinyar ma kukan tayi Miki?".
"Innalillahi! Magiya fice Dan Allah".
" Kiyi hakuri Ammah, Amman fa ba inda zani nabar wannan sabgar Arzikin Kinga fa".
Ya fada yana nuna kayan dake zube a tsakiyar parlourn.
"Allah ya shirya
"
"Amin" suka fada, gurin zilan Ammah ta juya.
"Lafiya kalau muke, wallahi kuwa Haka Allah ya kawo wannan kaddarar sai fatan Allah ya bashi lafiya, ki dauke abunki an gode madallah".
Harta yunkura zata tashi ta koma tana fadin.
"Ga kayan tsara Nan inji oga
Sameer yace a kawo Niger sukaje aiki".
* * *
Baba malam bashi ya farka ba sai kusan hudu da 'yan mintina, lokacin Mahmud ne kadai a dakin Shima ya rigasu fitowa daga masallacin ne, da sauri ya taso ya karasa kusa dashi.
"Sannu Baba ya jikin?"
Mahmud ya
fada Yana rik'e hannun malam Daya Miko Masa.
"Alhamdulillahi Ala kulli halin, duk abinda Ubangiji ya yiwa bawa akwai hikima a cikinsa, Kuma bawa baya wuce K'addararsa sai dai neman sauki,Haka Allah ya hukunta tun ran gini tun ran Zane rubutaccen al'amarine
baya canzuwa,ita kaddara haka take sai dai fatan Allah ya bani juriyar da dangana, inaga iyakar takawar kenan wadda akayi a baya na gode da kokarin ku naji jiya kaima bakayi barci ba, Allah yayi muku Albarka ya saka muku da mafificin Alkhairinsa, ka shigo
cikin rayuwarmu ka zamar Mana fitar data haske Mana duhu, Ina hadaka da girman Allah kayi hakuri bisa abinda akayi maka ka koma ga mahaifanka nasan ba manta garinku kayi ba na dai kyaleka ne saboda halin bacin ran da nake ganinka a ciki,naso idan ka dawo
na sakaka a gaba muje ga iyayenka kodan halin damuwa da nake ganin mahaifiyarka a ciki, gata da matsakaitan shekaru sai a tausaya Mata, Mahmuda ba'a fushi da iyaye kaji, sun 'yan lallabone, to sai ga kaddarar data sameni Kuma lallai naso yin wannan Alkhair
n Amma bamu San abinda Ubangiji ke nufi da hakan ba shi Allah s.w.a baya da sabon aiki".
Tunda Baba malam ya Fara magana Mahmud ya sadda Kansa kasa Bai dago ba Saida yaji ya saka aya a maganarsa, amma fa maganar ta doki zuciyarsa ba kadan ba.
A hankali Mah
mud ya dago idanunsa Wanda sukayi jajur badan Yana namijin duniya ba da kuka ze fasa kamar mace, hannun Baba malam ya Kara rik'ewa cikin nasa.
"Baba ka daina fadar haka in Sha Allah saika cigaba da taka kafafunka Kuma niyyarka ta Alkhairi saika idata da iz
inin Allah in dai akwai inda suke magance matsala irin taka da Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w sai an kaika, daman Nima nayi tunanin fada maka asalina idan na shigo garin sai Kuma wannan ibtila'in ya faru, kayi hakuri Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne, ya
nzu ka kwantar da hankalinka ka cire damuwa in Sha Allah zaka warke, ai sunce ba wata damuwa Mai yawa bace bayan ne ya Dan bugu, harma oga sameer yazo ya gana da likitocin bansan dai yanda suyi ba, sai ya shigo muji yanda za'ayi"
Habib da Sameer ne suka s
higo tare da zugar dattawan unguwa masu zuwa dubiya tun safe Dan mutum be yanke ba tafe suke maza da Mata, Dan ma iya Abu na gida tunda tazo da safe taga jikin ta Fara koke koke Habib ya mayar da ita gida.
Sun Jima suna Masa Addu'ar samun lafiya sannan suk
a tafi tare da ajje Masa kudi masu Dan kauri.
Mahmud da Habib suka Kai shi toilet suka taimaka Masa yayi alwala suka dawo dashi suka kwantar yayi ramuwar sallar da ake binsa.
* * * * *
Tunda Mama taga shigowar zilai da yanda taga zilan ma ta koma,
sai hankalinta ya qara duguzuma ya tashi, nan da nan ta shige toilet dinta dole ta nemo malam na Bande.
Cikin sa'a ringing Daya ya dauka Yana fadin.
"Idan kin Kira ta baci kenan, yaya ake ciki!?"
Babu Bata lokaci ta Fara bayanin.
"Malam da matsala sosai D
an komai nema yake ya cukude, da Alama Alhaji munafutta yayi ance an bawa yarinyar nan Almajiri Qolo,amma wallahi kaga yanda ta koma kamar matar shugaban Qasa, ko Mai aikin mu da suka tafi tare ta Zama abin kallo duka a cikin 'yan satiitka Dan Allah ayi wa
ni Abu kada bakin cikin su ya kasheni, malam ga Kuma na nemi Asabe na rasa duk komai Yana neman lalace min".
Wata dariyar marasa nutsuwa yayi duk da yawan shekarunsa Yana fadin.
"Ai daman na fada muku ayi duk yanda za'ayi ta turara turaren wutar nan sai ku
kayi sake kayan suka fada a hannun yaron mijinta, sannan Kuma Kika kasa hakuri mu karkare Kika canza guri, wannan shiya rusa duka ayyukanki na baya,maganar Asabe Kuma bana Jin zaku Kara haduwa da ita nan kusa dan naga tayi nisa sosai da nan din, naga alama
r kamar korarta akayi daga garin saboda Wani asirinki Daya tuno ban dai fashimci abunba sosai gaskiya amma Yana da nasaba da ita wannan yarinyar gaskiya sai dai itama kanta yarinyar Bata sani ba".
Karkarwa jikinta ya dauka ta Fara hada jibi.
"Dan Allah mal
am ka taimaka mini kada maganar nan ta fito har abada, kayi duk yanda zakayi ita kanta Asaben a dauke Mata hankalinta daga garin dama jahar Baki Daya. ko nawa ne Zan baka fatana kada asirin ya tuno, ita Kuma kayi abinda zakayi kada ya Kara marmarin Zama da
ita har abada yanda ya kawota ya tafi ya barta a nan kada ya Kara tunawa da ko sunanta dama garin gaba daya".
"Ki kwantar da hankalinki, Naga tafiya Mai nisa da zeyi Kuma gaskiya banganta a kusa dashi ba, zata zauna Dan Zama kam Amma Kamar yanda nasha fad
a Miki Banga rabuwa a cikin aurensu ba in dai shine ze saketa to bangani ba".
"Zan turo maka da sako ayi duk abinda ya Kamata kawai".
Ta fada tana sauke wayar daga kunnenta, iska Mai zafi ta buso daga bakinta tana fadin.
"Haba biri yayi Kama da mutum shi y
asa na nemi Asabe na rasa kaura wambai tayi batan dabo, to waye ya Kamata har malam yace asiri ya tuno kenan wayarta ma ankwace tare da sauran sakonnin da zata kawo min, Kuma sakon farkon ma hannun yaron mijinta ya fada".
Ta maimaita yaron mijinta yafi sa
u biyar.
"Me hakan ke nufi kenan? Ina ga ko cikin yaran makarantar ne, amma a cikinsu waye ze budewa Asabe Ido har ya iya koreta daga garin irin haka afujajan da gaggawa?".
Haka ta zauna tana faman kullawa da kwancewa babu Mai Bata amsa.
Abincin kusan kal
a uku Ammah ta saka Alawiyya tayi tunda itama ba laifi Ammah ta horata, zilai ce ta shiga ta tayata duk da Ammah tace ta huta ita da ta dauko hanya, Amma Sam taqi Zama ta shiga sukayi tare, a manyan warmers aka Zuba abinci, magaji Ammah ta Kira yazo ya Kai
Asibitin.
Zahra bacin da Bata samu ba jiya ta shige bedroom din Ammah tayi kwanciyar ta daga ita sai vest da Wani wando skintight ta saka wata hula Mai budedden Baki ta zubo da gashinta baya ta Fara barci hankalinta kwance.
Sai da Ammah ta Gama sallamar m
agaji ta shigo dakin, tsayawa tayi tana Qarewa zahra kallo, yanda ta ganta komai nata ya kara cikowa kirjinta da kasanta suka ciko sai zuciyarta ta shiga kokonton anya babu yaron ciki a jikinta kuwa? duk da bangaren ta ne da yake abin anzo Kan 'yarta ne s
ai ta samu confused.
Abinda zata dauka ta dauka ta fice daga dakin.
Sai kusan magariba zahra ta farka, wanka tayi ta shirya ciki rigar Atampha royal blue da ratsin Baki Mai manyan ganye, dinkin yaso ya matseta daga kirji abinda ya Bata mamaki ke nan dan ka
sa fitowa tayi Saida ta rufa da gyale sannan ta iya fitowa, sabanin da rigar har Dan yawa tayi Mata daga wurin breast cup din.
Su Aunty zilai ta samu suna gyara parlourn, Zama tayi tana tana musu sannu, Alawiyya ce tace.
"Aunty zahra a Zuba miki Abinci?".
Dan yamutsa fuska tayi.
"A'a bana Jin yunwa duk cikin ma bana jin Dadinsa, ki hado min salad kawai ya isheni sai ki hado min da fruits salad ya isa".
"To Bari naje na hado miki" .
Ta fada tana barin gurin.
"Aunty zilai Ina Ammah ne naji shiru ba motsinta?"
.
"Tana sabon part din Abba na bayan Nan kinsan Ammar mu Bata daukar raini ta dawo da Abba nan ta raba musu turaka ita da Mama, kinsan halin Mama har Saida takai hakurin Ammah karshe ta yiwa part din can yaji ta nuna sai dai a raba ko Kuma ta hakura ta bar
mata mijin duka shine ya dawo sabon nan".
Baki zahra ta rike tana kallon Aunty zilai.