Showing 240001 words to 243000 words out of 295116 words
na zaune a parlour sukaga ana shigo da manyan jikunkuna daga
karshe su Ummeen suka shigo Mahmud Yana bayansu shida Aunty Nauwarah, 'yan uwa abokan Wasa sai dan biki suke yiwa mahmud akan yanda yayi kyau Yana baza kamshi, sai walainiyar yake a Cikin Gezner milk colour ga wani daukar ido take kana ganinsa ango sak.
H
ar gurin Su Hajja ya raka Ummee Yana fadin.
"Hajiya Inna ga Ummen Zahra wadda kwana biyu kuke waya da ita".
"Muke waya ko kake Mana tafinta Ni ba iya nata yaren nayi ba itama Bata iya nawa ba,kace Ina musu sannu da zuwa".
Ta fada tana daga musu hannu Hajiy
a ba Ajami.
Cikin yaren larabci ya fada musu sakon barka da zuwa da Hajiya da saura mutanen gurin sukeyi musu.
Gurin Ammi suka Karaso da yake Ammi makarantar English tayi sai abun yazo da sauki sun gaisa sosai dasu kafin a kaisu masaukin su inda sukaci abi
nci sukayi salllolinsu.
Ammi da su mummy Badi'a da Aunty Surayya suka Kara shigowa suka gaisa dasu Ummeen.
Aunty Surayya ce ta fice ta nufi sama lokacin an gama shirya Amarya tsab,ta shiga dakin komai yayi Masha Allah Sai dai mak'iyi.
Hannunta Aunty surayy
a suka fito a hankali suke gangarowa har kasa suna daf da shiga gurin Ummee ta jiyo scent dinsa Dan juyowa tayi shi ta gani Yana tsaye ya harde hannu a kirjinsa ya Zuba Mata Idanu.
Ganin kamar Aunty surayyar zata juyo yasa tayi saurin dauke Kai tayi gaba.
Suna shiga dakin Zahra tayi arba dasu Ummee ai Batasan lokacin data daka wani uban tsalleba ta shige jikin Ummee tana wata irin murmushi Mai dauke da tsantsar farin ciki.
Daya bayan Daya tana shiga jikinsu suna gaisawa.
Anan ta zauna dasu tana ta mamakin W
ai meu amor ne ya fadawa Ummee Amma ita Kullum ta nemesu Bata samu.
Daga Nan Zahra Bata koma sama ba suka wuce gurin walima anci ansha walima ta amsa sunanta anyi wa'azi Mai ratsa zuciya da zaburar da ma'aurata akan hakkokinsu, jiki yayi sanyi sosai Dan an
kwankwashi ko wane bangare, duk iya zarin mutum sai dai yaci ya Bari anyi komai na girma da wadatar arziki, ansha hotuna da Amarya da ango Dan burin kowa yayi hoto da ita 'yan matan dake feleke akan mahmud sun raina kansu Dan sun San mahmud yayi musu f
intinkau da wata irin tazara Mai girma Mai kamar wannan mezeci dasu.
Karfe takwas aka fara Shirin tafiya dinner wadda za'ayi a MABERA EVENT HALL.
Su sajeeda dasu Aneesa su Amatu da Aunty safiya duk sunzo sai suka ringa tuna lokacin da wancen biki ya lalac
e komai ya rikice, Amma yanzu gashi ana kara'i.
Sajeeda ce ta kalii Amatullah tana fadin .
"Kunga mahmud sai a kyale shi, wato sai an rama masa bikinsa da ba'ayi ba kenan".
Aneesa ce tace .
"Aini yayi min dai dai wallahi saboda mahassada da 'yan bakin cik
i masu yiwa Zahra dariya da shewa da yi Mata tozarci a ranar da aka kaita gidansa suga yanda Ubangiji ke yin nasa ikon susan hassada ga Mai rabo taki ce Kuma dare ga Mai rabo hantsine, yau ga Zahra ganinta ma sai kayi da gaske Dan baka Isa ka haura inda ta
ke ba sai anyi maka iso Kinga kuwa ai ko yanzu Allah ya nunawa masu yi Mata hassada iyakarsu.
Shiru Hameeda tayi tasan wannan maganar da wannan ke saki an Bata labarin abinda ya faru ne lokacin da Mama da Salma suka sakata tayi rashin kirkin Nan Wanda ya j
anyo musu sabanin daya shiga tsakaninsu har inda yau din Nan take.
Aunty Nauwarah ce ta shirya Amarya da shigarsu ta Amaren larabawa, tunda Ammah ta fada musu halin da ake ciki suka dauro niyyar tahowa duk da daman suna niyyar zuwa ganin Zahrar,sai kuma g
a Kiran mahmud ya fadawa Ummee sannan ya tura Musa iv din dinner, shine fa Aunty Nauwarah to shiri na musamman akan dinner din gata Daman gwana a gurin makeup lokacin dasu Aishat suka shigo Basu ganu Zahra ba Dan juyewa tayi tamkar ba ita ba.
Dai dai kunne
n Zahrar Aunty Aishat din tazo tana Mata magana.
"Dan Allah a rangwanta Masa kada ya kasa rike Kansa a gurin fa, irin wannan Abu haka'.
Sunne kai Zahra tayi Dan ji tayi kamar kowa yaji abinda ta fad'a.
Sai da kowa ya tafi ya rage daga Zahra sai sajeeda wa
dda Aunty Hasana tace su zauna tare kafin a zo daukarta.
Suna zaune suna hira wayar sajeeda ta dauki wani slow music lokacin tana duba wasu kayan da Mama Haneefa ta kawowa Zahra, Jin special ringtone din nan yasa ta baro gurin da sauri tana fadin. "Sunzo
garin kenan".
"Waye kuma aka samu".
"Kinji ki waye kuwa Banda yayanki daya hanani sakat da soyayyarsa".
Picking tayi tana nufar kofar fita, saura kadan suyi karo da mahmud Wanda shi kuma ze shigo, da sauri tayi baya tana fadin. "Sorry ban kula yallabai"
.
"No ba laifinki bane nine banyi knocking ba".
Ya shigo ita Kuma ta fita da sauri.
Tunda Zahra taji muryarsa taji wani abu da batasan ko meye ba ya tsirga mata.
A hankali ya tako har inda take ta sadda Kai kasa,shigar babbar Riga yayi irin dai yanda mafi
akasarin angunan Hausawa keyi, dagota yayi ya Mikar da ita wani lunshe sexy eyes dinta tayi ba tayi zato ba taji iskar bakinsa mai dauke da kamshin Lister mint ta sauka a Kan fatar idanunta kafin ya zagayo da hannuwansa ta bayanta ya rungumeta tsan-tsan a
jikinsa Yana jera ajiyar zuciya a dai dai kunnenta ya rada Mata "preciousss kin gujeni why? kinsan yanda na azabtu da bakya kusa Dani kuwa? Rabon dana jiki a jikina haka fa tun muna India kinsa na Zama marayan karfi da yaji jiya nayi nayi kizo ko ganinki n
ayi kika k'i zuwa ko? Can gurin lalube lalubensa ya jiyo zif daga gefen wedding gown din ya zuge ya shiga Kai kawo da hannunsa dayan Kuma ya zame Dan veil din da aka makala shi a jikin kamar hula wadda aka saka mata ya Kuma hade bakinsu Nan da Nan ya rikat
a Mata lissafi, da kyar ya saurara Mata suna maida numfashi .
Cikin murya wadda ta dashe ya fara Mata magiyar tazo su wuce basai sunje gurin dinner din Nan ba, bazei iya Kuma tana nufin a haka zata fita duk Nan a waye ana kallo. Yasa hannu Yana shafa sama
n rigar wadda net ne a gurin.
*AUREN HUCE HASHI*
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.
09061432330
Or
08055362975
Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu da sallah muna tayi Al'ummar musulmi Baki idin qaramar sallah,muna rokon ub
angiji ya karbi ibadun mu ya Samu a cikin bayinsa Wanda yake 'yantawa Dan Alfarmar Annabi Muhammad s a w w.
Page 81
............Suna tsaye yana kallonta daga sama har kasa Yana Kai kawo akan zuwa dinner din nan yayi dana sanin jan lokacin nan,daya
bude aiki da Sai dai ya kawota da ciki ai da ya rufe babin duk wannan bidi'ar da aka bude, Dan zayyan ya turo Masa yanda gurin ya cika da Dan mutum tamkar anyi shelar bikin , ga mutanensa da Sameer ya ringa tura musu da iv ta email dinsu abun har mamaki y
a bashi. Dan sunzo ba kadan ba ga alert sai shigowa yake daga different people shi abun mamaki yake bashi to da bikin da aka shirya Masa ne Yaya kenan?.
Knocking yaji daga waje agogon hannunsa Rolex ya duba sai yaga lokacin yayi sauri hannunta ya kamo tamk
ar yanda India suke ya nufo kofar,key din ya murza ya bude. Aunty Aishat ce ita da Aunty Nauwarah,wata irin kunya ta rufe Zahra.
Dan Bata taba tunanin da sauran wani a part din ba Dan yau har masu aikin Ammi sun dauki wanka sun fice.
Wani irin kyau sukayi
yanda suka fito din Nan sai suka bada wata irin colour mai daukar hankali.
"Dan Allah menene haka ka wani kanainaye ta kaki Bari ku fita guri ya hadu ku kawai ake jira gara dana rako Auntyn Zahra da baka niyyar fitowa kenan?".
Dan matse hannun Zahra yayi y
ana kallonta kafin ya kalli twins sister dinsa.
"Kina da damuwa zuwa fa nayi mu tafi, nifa da wucewa zamuyi bana son wannan bidi'ar naga gurin ya cika da maza Kuma dubi rigar dake jikinta duk Nan fa a waje yake".
Ya Kai hannu yana nuna mata, Zahra ji tayi
kamar ta nitse a gurin, taga ta kanta shi Wai baya Jin kunyar Aishat din ne.
"Allah ya shirya gaskiya gara ku tattara ku Kara gaba Naga alamar idan tana kusa da Kai baka da saiti duk nutsuwarka barin jikinka take, sai kaje ka jiramu abinda Auntyn ta tazoy
i kenan tace wannan fitar batayi Mata ba ta dauka akwai wasu events din bayan wannan nace Mata Babu sai budar Kai gobe kawai".
Jinjina Kai yayi ya wuce Yana fadin.
"Ki fadawa Auntyn Banda Mai net a kirji Dan Allah".
Rike Baki Aishat tayi tana binsa da kall
o.
"Kai Kuma naka salon kenan? Auntyn Afnan kuje Auntyn ki na jiran mu gara ayi abunda za'ayi ku shiga ku kadai ake jira".
Kwalkiyar da akayi yanzu tafi ta farko daukar hankali nesa ba kusa sai Zahrar ta zama tamkar fure tayi kyau iya kyau Dan ta farko Wa
sa ce.
Aishat tayi Mata hotuna tamkar ba gobe, wani murmushi ne ya kubce Mata zataga yanda Dan gidanta zeyi da yake complain din wancen gown din to ga wata wadda tafi waccen sai dai ita babu ne daga sama ba'a ganin breast din kamar waccen.
Sajeeda ce ta d
awo tana fadin.
"Bestie kina Ina ne ki fito ana jiranki fa".
Ganin su Auntyn yasa ta Dan tsaya tana kallon Zahrar ganin Cikin abinda Bai wuce minti Sha biyar ba an sake Mata wani Shirin na musamman.
" Wow! Masha Allah bestie Allah ya kade bakin mutane king
anki kuwa?".
Dan murmushi tayi kawai.
"Ato gata Nan bansan ya angon naku zeyi ba Naga alamar dan banzan kishi gare shi, wa yace ya kawo ta gidan a haka? Ai dole ya kauda Kai Dan dinner dai sai anjeta babu fashi in Sha Allah".
Ita dai Aunty Nauwarah kallons
u take tunda ba Hausar takeji ba.
Wasu tsaraddun turarika ta shiga fesa Mata masu sanyin kanshi.
Tare suka fito suka raka Zahrar a cikin motar da zasu tafi a ciki, shi Dan gogan kasa magana yayi Dan yana kukan targade saiga karaya ta samu, Yana korafin wac
cen wedding gown din to Kuma saiga wannan ita ba transference bace Amma ta fiddo da structure din jikinta sosai.
Bai daiyi complain ba suka wuce Sameer na jansu, Suna fita motocin guards dinsa dake waje suna dakon fitowarsu suka saka motar a tsakiya suka w
uce. Su Aunty Aishat ma suka wuce da sajeeda.
Suna shiga harabar gurin sajeeda taga yanda motocin Alfarma suka cika wurin tasan ba karya anzo gurin, Dan tunda suka shigo sukaga yanda Families din mahmud suke suketa mamakin abun bare ita sajeedar da tasan k
omai a game da shi, tayi mamakin mema ya fitar dashi daga irin wannan daular ya gwammace rayuwar da yayi a Azare da wannan.
Ango da Kansa ya budewa Amarya ta fito Yana rike da hannunta suna tafiya Yana gaisawa da jama'arsa suna bin carpet din da a saka mus
u a hanya photographers sai aikisu suke masu dauka da wayoyin hannunsu Suma suna ta faman daukarsu Dan wani irin perfect match couple ne Wanda kafin a samu irin wannan hadin ana dadewa kyau ne ke dukan kyau.
Suna shiga da tawagar abokansa na kusa Dana nesa
sai kawayen Zahra,r music din Larabawa na tashi a hankali sai kus-kus mutane kowa na zaune gentle ba wani hayaniya Dan ba karya an hada manya masu ji da kansu a gurin kowa Yana cewa wane kauce bani guri.
M.C ne ya Fara bazawa Amarya da ango kirari har suk
a zauna a inda aka tanadar musu, Nan da Nan guri ya dauki surutun mutane wasu suka taso suna daukar video wasu suna daukar photo, 'yan Mata da yawa masu son mahmud sunyi giving up, sun San idan ba wani kwakwkwaran rabon ba babu yanda za'ayi DANGE ya dubesu
da sunan soyayya, wakar Auren su wadda Akayi mc ya saka.
A gurguje Sameer ya bada tarihin mahmud har ranar da suka Fara ganin Zahra ita da Abbanta a jirgi ya fada, sai lokacin Abban Zahrar ya tantance inda ya Fara ganin fuskokinsu tabbas anyi haka Dan Mai
maganar har Jordan sukaje tare, wato tun lokacin suke bibiyar ta kenan sauran bayanin ne kuma baisan yanda akayi ba.
A bagaren Zahra sajeeda ce ta fito ta fadi tarhinta a nan da yawa suka San ruwa biyu ce Dan duk Wanda ya ganta zeyi zaton gaba daya Arab d
in ce tunda su ta dauko sak, an tanadi abinci Kala-kala da nama ya Kai Kala goma gashin nan serve your self ne ga drinks Nan tamkar banza, Zahra tayi mamakin ganin su Abbanta Koda Wasa Bata taba kawo hakan ba tunda bece Mata zezo ba yace dai sai daga baya
ze shigo ya ganta, taga su Ya Abdul Hakeem dasu ya Hamza bare magaji da taga ya Zama Dan gida ya kasa tsugun.
An saka kidan larabawa wasu Mata Wanda da alama dasu Ummee sukazo suka shigo sukaga ringa rawar larabawa Mai ban sha'awa.
Daga Nan aka bukaci Ango
da Amarya suzo su yanka cake Zahra ji tayi duk ta daburce ganin Ido yayi Mata caaaa.
Ganin taki motsawa yasa mahmud ya murzawa idanunsa toka Kuma ma dai da biyu yayi hakan Dan yaga wata fuska sanye da musk Kuma ya hakikance Safna ce Dan ko me zatayi bazat
a taba bace Masa ba.
Tsam ya saka hannu ya Mikar da ita abunda yasa matasa dauka tafi Sai Kuma hasken plasher tako ina.
Shiya Fara Bata cake din sannan ta bashi duk a kunyace, mc Bai Bari suk koma ba announcement ya Fara Yana neman dangin Amarya da turanc
i tunda yagansu farare tas, ya saka wakar Amr Diab 'yar kasar Egypt.
Ummee ce ta taso wasu Mata biyu suna bayanta dauke da wata jaka tana zuwa ta Fara zazzaga musu ruwan stalling pounds na England sai Kuma su Mama Haneefa dasu Aunty Nauwarah suka shigo sun
a ruwan American dollars Nan da Nan guri ya dauki tafi, Ummee Bata koma ba saida ta yiwa ango kyautar estate a cikin garin madina sannan aka bashi jajayen rakuma goma da kyauta tickets na kashe biyar na Honey moon.
Aunty Hasana ma dasu Inna mainuna sunzo s
unyi rawar gani Dan shanu goma ris ta bawa ango sannan wasu goman biyar uwa biyar uba da kuma zunzurutun kudi har miliyan ashirin na dangin uwa da uba sai karsanoni hudu na abokan zaman Ammi sai guda hudu da million daya nasu Hajiya Inna da Hajja dari biya
r biyar.
Abinda ya girgiza da yawa daga Cikin masu ganin Zahra ba 'yar kowa bace irin fakarahun yayan larabawa Nan ne masu azabar kyau din Nan da yawancin mazanmu masu kudi ke aurowa Dan neman irin Mai kyau Cikin zuri'arsu.
Bayan gama tafi da sowar tuwon g
irman da Ummee tayi aka nemi dangin miji,sun shigo kamar Gori maza da Mata sunyi barin kudi kamar ba gobe Ammi ta fito da tawagarta ta yiwa Zahra liken CFA kudinsu na Niger Hajja ta bawa Zahra kyautar shanu da zunzurutun CFA million goma.
Da sarkar zinari
wadda kudinta sun tasarwa million tamanin take aka Miko cheque na eco Bank tunda shine bankin ecowas.
Amarya da angon sun Sha kyautukan girma suna niyyar komawa wurinsu wata Mata cikin sauri take ta yiwa mc magana, Nan da Nan ya dakatar da tafiyarsu Yana f
adin.
Ga Mai gayya Mai aiki tazo Fulanin Mai Damagaram aminiya ta hannun damar uwar ango Hajiya zainab.
Wata farar Mace Yar gayu tare da amintattun bayinta sai wata yarinya budurwa dake tare dasu Saida suka matso sosai Zahra ta gane yarinyar Wadda ta kafa
musu Ido ce a train station lokacin da zasu Jim Corbett national Park a Uttarakhand state. Take Zahra taji wani Abu ya tsaya Mata a kirji, yanda taga yarinyar na Mata wani kallon kasa kasa irin Mai nuna baka Isa din Nan ba.
Saboda a wancan lokacin taga iri
n kallon kurillar data kafesu dashi.
Fulanin na zuwa ta rungume Zahra tana fadin.
"Tabarakallah Masha Allah, Zahra diyata sannu da kwaramniya".
"Yauwa Mama, nagode".
Wani kallon banza yarinyar ta gara jifan Zahra dashi tana wani kawar da Kai gefe tana hade
rai.
Liken kudi Fulanin ta Fara Yi musu haka 'yan tawagarta ma haka da alama an shiryawa wannan ranar, amma ita yarinyar mahmud kadai take yiwa Saida mummy Badi'a tazo ta janye Fulanin daga gurin ganin lokaci ya Fara ja tasan abokansa da kawayen zahrar su
na son Suma su nuna tasu bajintar, a gurin dollars dai da pounds sunyi kuka.
Mama ta Raina kanta iya rainawa taga inda ake maganar arzikin da babu fariyar a cikinsa sai dai idanunka su fada maka, taga yanda matan uba ke kyautar mamaki Dan kowacce ta bawa Z
ahra tata kyautar.
Ba'a tashi ba sai kusan Sha biyu da rabi.
Sai da aka tashi sannan Ammi suka gaisa da Fulani wadda ta sauka a Daren Dan Bata kasar lokacin da Ammi ta kirata ta fada mata danta ya dawi har da tsarabar Daya dawo musu da ita.
A gajiye aka da
wo gida danma an kamawa mutane da yawa dakunan hotels Dan duk matar da tazo daga Azare a mota ta biyu duka hotel aka kaisu shi yasa sai a gurin dinner Zahra taga wasu mutanen harda su Aunty zilai dinta Dan har liken Yan dari biyar sabbi tayi Mata. Duk yan
da mahmud yaso ya wuce da Zahra Aishat da Aunty Nauwarah sun kasa sun