Showing 72001 words to 75000 words out of 295116 words
a tunani kala-kala Sam na kasa samun nutsuwa". Tashi Zahra tayi ta shige ciki tana Fadin "Bari kawai bestie guy din nan ya fa karbe wayar tun ranar da Kika tafi ya dauketa da safe daya shigo, shine fa daya shigo ya tarar duk na
hargitse gado ina neman ta yace tana gurinsa, ya kama min wasu zantika akan Kiran da Musbahu yayi ranar ni kuma na kasa hakuri shine yayi min Rashin mutunci Kuma ya hanani wayar".
Ta fada kamar zata fashe Mata da kuka, tambayar ta tayi yanda abun ya faru
Bata rufe Mata komai ba ta fada Mata. Bata katse Mata hanzari ba har ta gama.
"Amma ban taba sanin Baki da wayo ba sai yau, Gaskiya Baki kyauta ba ko alama Ina hankalinki ya tafi kada ki Kara Koda Wasa saboda wani ki ciwa mijin aurenki fuska ai wallahi jar
imi ne daya iya hadiye fushinsa bakiji a jikinki ba".
Ta fada a kufule, kit ta kashe Kiran.
Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana kallon wayar a zuciyarta tana fadin ji a jiki na nawa Kuma ba ze fadu bane shi yasa.
Lokacin da zahrar ta fito wasu bakin ta tarar
sun shigo su biyu har Amatu ta kawo musu ruwa da drinks suna hira dasu Aunty safiyya, sallama tayi musu sannan suka gaisa Nan Amatu tace musu "ga matar gidan nan".
"Masha Allah"
Suka fada a tare sannan babbar wadda zatayi kamar sa'ar Aunty safiyya tace "
mune makotanki da hannun dama sunana Hafsat Amma ana kirana maman junior, wannan Kuma kanwata ce Nuratu da take karatu a Nan Abubakar Tatari Ali polytechnic (ATAP) aiki ne ya kawo Mai gidana mu 'yan Taraba ne".
"Masha Allah! Allah ya taimaka ya bada sa'a".
Suka fada.
Sun Dan jima ana hira dasu sannan suka tafi har gate Amatu ta rakasu da ledar kayan garar biki.
Suma mikewa Aunty safiyya tana goya Shureem da yayi barci, Dan langabar da Kai Zahra.
"Wai har zaku wuce ne Kuma Aunty?".
"Eh mana zan shiga gidan
fachalata data haihu bana Nan".
"Amman Banda ke dai Amah gaskiya tunda nasan kina garin Nan sai karshen wata keda jama'are".
Aunty safiyya ce ta tari numfashin zahra
"Ai ita ke driving dinmu ya zan barta a Nan ta dawo Miki special ko weekend ne".
Alamar bu
de kofar da akayi ne yaja hankalinsu, Mahmud ne ya shigo Yana musu sallama da katuwar leda a hannunsa, tunda ya shigo Aunty safiyya ke kallonsa ita dai tasan wannan fuskar amma ta Yaya za'ayi haka ko Kuma kama ce kawai.
A cikin takunsa na cikakken namiji y
a shigo, da sauri Zahra ta nufo gurinsa tana Fadin.
"Sannu da zuwa". Tana Mika hannu zata karbi ledar.
"Da nauyi bazaki iya dauka ba".
Ya fada Yana kallon ta.
Har cikin kitchen ya shiga da ita sannan ya wuce bedroom.
Amatu ce ta zunguri zahra.
"Ke! meye ha
kan Kuma? Kika wani sharesa Kada dai kice min sokoncin da kike bazawa a gidan kenan ko Kuma Dan kin gammu ne kikayi wani biris dashi".
"Gaskiya Kam ki dage ki Kama mijinki irinsu tsada suke".
Aunty safiyya ta fada tana nunawa Zahra hanyar daya bi.
"Kai! A
unty Kuma ......"
Bata karasa ba Amatu ta Kama hannunta ta nufi steps din tana Fadin "kije kawai tunda daman tafiya zamuyi saina shigo Saturday in Sha Allah".
Dan raurau tayi tana kallon Aunty safiyyar.
"Na gode Aunty ku gaida gida saina zo har gida ban ga
jiya".
Dariya Auntyn tayi.
'Haba dai sai dai mun dawo, wannan turaren kada kiyi Wasa dashi tun daga besse na taho Miki dashi kakata ta wurin Babana take haduwa da Kanta Yana da matukar kyau sosai ba sai fada Miki ba da kanki Zaki nema".
Dawowa tayi Saida
ta rakasu har gurin mota duk da mitar da Amatu ke mata, ta hadasu da kayan garar fal ledoji biyu dasu bokitan roba da mug masu kyau da plates Wanda Aunty Hasana ta bada aka kawo mata saboda Baki masu zuwa.
Saida suka fice daga gidan sannan ta dawo ciki.
Ba
ta shiga ciki ba a parlourn ta zauna tana mitar. "Idan na shiga me zan Masa wanda yake ganina a wata Mai neman rayuwarsa".
***
Saida Amatu ta dai daita a titi sannan da Dan dubi gurin da Aunty safiyyar ke zaune tana rungume da Shureem.
"Aunty nifa wani
Abu ya bani mamaki da daure Kai"
"Kamar me fa?".
"Duk gari ya dauka an aurawa zahra Almajiri k'olo saboda ita ba 'yar Alhajin bace, surutu dai gashi nan, ni Kuma yanzu Naga sabanin abinda ake fada, yaushe Zaki kalli wannan kice Yana Qasqantacciyar rayuwa
irin wadda ake fada?".
"Ni Nama fiki mamaki Dan ni dai Idan ba gizo idona yayi min ba ko Kuma kama ce ta halitta tunda ance kowa Yana da Mai Kama dashi a wani gurin, da sai nace Miki M.M DANGE na gani".
"Waye hakan?".
Amatu ta tambaya.
"Bazaki gane ba A
matu wasu Family ne a sokoto masu mahaukanta kudi Nima fa sau daya na taba ganin M.M DANGEN a bikin wata cussing Dina zainab data auri Dan Family din, Kai gaskiya bashi bane inaga Kama ce kawai, amma Kuma kamar harta baci sai dai ba yanda za'ayi DANGE ya i
ya rayuwa a nan".
"Kamar Yaya Aunty?"
"Tab kinsan kuwa waye shi? ai inaga kaf ba Wanda ya mallaki abunda ya mallaka a duk Family din, gashi yaro matashi Kinga gidansa na sokoto ma kuwa? Banda na Abuja da sauran garuruwa, to in kuwa shine me zeyi da Dan
wannan gidan ai ji zeyi kamar Yana rayuwa a kurkuku ne, bama shi bane shifa ko bodyguard dinsa abin kallon ne Suma sun Zama done fa"
Ido Amatu ta zaro.
"Kikace wannan gidan kamar kurkuku? Duk yanda na ganshi Aljannar duniya".
"Naki wasane Amatu. Allah ya k
awo dalilin da Zaki shiga ko gidan daya daga cikin families din DANGE ne kiyo kallon duniya me Kika gani a Nan kedai Allah ya Kai damo ga garawa kawai, Dan dai a wannan zuwan da nayi sokoto naje yiwa zainab din barka naji wasu a cikin family din sunata hir
ar MM DANGEN Wai ko ya bar kasar ya koma turai tun bayan samun wata matsala Mai zafi a cikin family din wadda ta tada kura har rayuka suka baci".
Da ire-iren hirarrakin suka karasa gidan barkar.
...
Tana zaune a Nan parlourn ya fito cikin kananun kaya da k
aramar leda a hannunsa direct inda take ya nufo ji tayi gabanta ya Fadi.
"Ya Ilahiy" ta fada a zuciyarta.
Gefenta ya zauna Yana Fadin
"Wash!! I am tired wlh samo min ruwa Mai dan sanyi".
Yayi maganar yana dan matsowa jikinta. Da sauri ta tashi yabi ta da
kallo Yana kissima abubuwa da yawa a kanta kunyar ta tayi yawa yasan sai yasha fama kafin ya rabata da ita yanzu dai most important thing ya samu shakuwa da ita sosai.
Ruwan da farm fresh yogurt da snacks ta bawo Masa, idonsa a limshe Kamar me barci Amma
Yana kallon ta yanda take tafiya kamar me counting steps sai rausaya take.
Table coffee ta janyo ta Dora tare da bude Masa ruwan ta Zuba duk Yana kallonta.
Ajewa tayi ta juya zata wuce taji hannuwan mutum duka biyun ya zagaye k'ugunta ya mannata a jikinsa
ta baya, yayi Mata bazata Dan ko motsin mikewarsa bataji ba ko alama, a tare suka sauke ajiyar zuciya juyota yayi gabadayan ta suna facing din juna Yana Mata wani duban kasa-kasa.
Narke fuska tayi Kamar zatayi kuka tace Masa.
"Menene Kuma? gafa ruwan Nan n
a kawo maka".
Fuskarsa ya matso da ita dai-dai tata yace.
"Haka ake tarbar miji? Ki bani abincin yunwa nakeji fa, tun safe banci komai ba tunda kika tada min hankali abincin ya fice min daga Rai, waini Kika kalli kwayar idona Kika gasa min maganganu son ra
nki ko?".
"Ni me nace, cewa fa kayi zanyi poison dinka ni banji haushi ba sai kai, kisa fa? To me kayi min, ni na daina abincin ma ba shike nan ba ban dafa ba bare na zuba maka guba".
Ta fada tana kokarin zame jikinta, Kara gyara rikon da yayi Mata yayi y
a nufi two seat da ita a jikinsa kan cinyarsa yayi Mata masauki, ya Kai hannunsa daya ya zame veil din da tayi rolling gashin ya shiga shafawa yana fadin.
"Nifa da Wasa nake Miki dazun bada niyyar na bata Miki rai ba na fada, so I am very sorry Baby in Sha
Allah bazan Kara fada ba, na Saba haka nake yiwa kakata Hajiya Inna a irin wannan lokacin na break shine na tunata da ita na fada Miki kema Ashe lefi zanyi, yanzu muje na tayaki ki Samar Mana light Abu muci bana son cin Abu Mai nauyi sosai da dare nasan
kafin mu Gama anyi magariba ko"
Ita dai tayi tsumu tsumu duk ta takura fatan ta ya saketa ta fece tunda Allah yasa yanzu ba 'yan tabe taben bane a Kansa a iya gashi kawai aka tsaya.
Dagota yayi daga jikinsa ya rike hannunta kamar wata 'yar baby suka nufi k
itchen, ledar daya shigo da ita ya dauko ya Dora a Kan cabinet din kitchen din Yana Fadin "zo ki cire wadan Nan daga ciki.
Kayayyakin amfanin gida ne masu yawa harda su biscuits su chocolate, sai da ta saka komai a muhallinsa sannan ta Fara hada abinda zat
ayi, kujerar kitchen ya samu ya zauna Yana kallon movement dinta friend spaghetti Mai vegetables tayi sai tayi gasmeat.
Lokacin data Gama komai an Fara Kiran sallah.
Tare suka fito ya mannata da jikinsa a haka ya nufi bedroom dinsa da ita suna shiga ya zau
nar da ita Kan sofa ya wuce toilet.
Sai daya rufe kofar sannan ta tashi ta wuce nata dakin wanka take sonyi.
Koda ya fito Bai ganta ba beyi mamaki ba yasan za'ayi haka, lokacin daya leka ya fada Mata ya wuce masallaci tana toilet.
Saida yayi insha'i sannan
ya shigo gidan abincin Mai gadi ya dauko ya futa ya Mika masa, daya dawo be nemeta ba,sport news ya kamo yana kallon labarun wasannin da akayi Bai gani ba.
Zahra Kuma da tayi sallah saita zauna tayi Azkar na yamma da Bata samu tayi ba, data Gama tayi s
hafa ta saka riga da siket English waars combination din milk da maroon tayi rolling da milk veil tayi kyau kamar ka dauke ka boye body mist kawai tayi amfani dasu kusan kala uku cikin Wanda ta gani a cikin locker din mirror dinta sai kamshin ya Bata wani
irin Dadi Mai kwantar da zuciyar me shaqarsa.
Plat shoes tasaka a kafarta ta nufi falon,jin gidan shiru batayi tunanin Yana Nan ba Saida ta shigo sosai ta ganshi a kishingide da remote a hannunsa Yana kokarin canza tasha.
Tashi yayi daga kishingidar ya zau
na sosai Yana binta da wani mayen kallon, tunda suka hada ido sau daya Bata Kara yarda ta kalleshi ba.
"Zo ga wayar ki Nan tunda Naga itama kinyi zuciya da ita kin bar min".
Ya fada yana Mika Mata hannunsa alamar tazo ba musu ta nufo shi cikin takunta na n
utsuwa, shi komai yarinyar Nan tayi burgeshi takeyi ga uwa uba Kuma ya fuskanci tana da tarbiyya da biyayya sabanin yanda yake kallonta, Bai zaci zata kwantar da hankalinta haka ba sai yaga ta tattara komai ta aje gefe abinda ya fuskanta kawai dai Bata dau
kar raini.
Tana karasowa saita zauna kusa da kafafunsa a kasa taki zuwa gurin hannunsa da yake Miko Mata. Dan murmushi yayi Shima ya sauku Yana facing dinta da karamar ledar dake hannunsa, Mika mata yayi."Gata Nan ayi hakuri ki hada ta batirin ma yana da f
ull charge da sim a ciki, duk numbers dinki important suna ciki.
Wayar ta bude sabuwa ce Kar jujjuyata ta Fara tafi wadda ya Fara Bata tsada nesa ba kusa ba kallon tuhuma ta Farayi Masa tana girgiza Kai tare da Mika masa wayar tana Fadin.
"A Ina kake samun
irin wadan Nan wayoyin na mahaukatan kudi wlh ba ruwa na ka rike kayanka bana so ka maido min tawa ta asali kawai".
✨✨
✨✨
✨
💎
AUREN HUCE HAUSHI
💎
✨
Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu.
Dukkan yabo da g
odiya sun tabbata ga Allah s.w.a, salati da daukaka da Aminci su tabbata ga Annabin Rahama Muhammad s.a w.w.
Page 25
📖🖋
️
________Dariya ya kama harda hawaye abinda bata taba gani ba.
Sororo tayi tana kallonsa, ita bataga wani abin dariya ba a magan
arta, hannu ya Mika ya karbi wayar kunnawa yayi ya Mika mata Yana kashe Mata ido tare da d'age gira.
"Kina son kisan inda nake samun mahaukanta kudaden Nan ne?".
Kai ta gyada Masa.
"Good ki Bari sai ranar da Kika Zama ni na zama ke na mallaki kayana, a ra
nar nayi Miki Alkawarin sanin komai nawa na duniyar Nan, Idan Kuma yanzu you are ready za'a taimaki Dan Malam a lullubeshi da bargon ni'ima to? yanzu kuwa kisha labari har wanda Baki nema bama zan fad'a Miki, tunda ke inda nake samun kudi kawai Kika bu
kata baki son sanin waye ni?daga Ina nake?meya kawoni garinku? Gasu nan rab'ab'a da yawa, to ki rubuta ki aje har abada ni Mahmud bazan tab'a ciyar dake ko shayar dake ko wani Abu na jindadin rayuwa da haramun ba, duk abinda na Baki ki tabbata da gumin hal
alina na nema, kinga wannan wayar da kudina na saka na saya Miki,wato kina tsoron kada na Sato kayan mutane na kawo Miki ko?"
Kai shiga gigizawa.
"Ni ba cewa nayi kayi sata ba, gani nayi kana ta abubuwan da sai Mai wadata ne ze iya yinsu Kai Kuma Naga...."
Sai kuma tayi shiru tana kallonsa.
"Oya continue Mana,kinyi shiru wato Kinga bana aikin komai ko?".
Shirun tayi Bata Kara cewa komai ba.
"Tashi ni ki bani abinda zanci idan na biye Miki da wannan yarintar taki sai yunwa tayi min illah kisa a Fara gulmarki
ace kina barina da yunwa, ganshi kin sani azumin da Babu lada".
"Ba Kaine kayi zuciya ba ka tafi kabar abincin"
Ta fada a shagwabe.
"Ki tashi ki bani kada lissafin ya canza fa"
Ya fada yana matsowa jikinta sosai, da sauri ta Mike ta nufi dining inda ta j
era abinci.
Table mat ta shimfida a Kan carpet din sannan ta dauko abincin ta aje.
Plate biyu ta dauko dayan ya janye.
"Ki Zuba Mana a plate daya ya Isa ai Kuma indai Ina gida plate din mu daya tunda Kika yimin horon yunwa yau daga Wasa Dan kawai kewar Haj
iya ta ta kamani shine Kika horani duk ranar dana kaiki gabanta saina fada Mata tasan irin zaman da zatayi dake, ni Dan gata ne a gurinta bana laifi zakiga yanda take sona".
"Ko?" Ta fada tana zuba abincin a plate, Dan tura Masa plate din tayi kusa dashi
"Gashi Nan ni bana Jin yunwa".
"Ashe zan Miki dura wlh, sai kinci kuji min yarinya da kinibibi Wai so kike da karfi sai kin koya min surutu ne? Kin iya kalato abin magana da wani bakinki chut".
Ya fada yana shafo pink din lips dinta.
Taci Amman ba wani n
a kirki ba da gaske abinci Bai dameta ba barta dai da 'yan ciye-ciye.
Bayan sun gama ne ta kwshe kayan ta gyara gurin duk Yana kallonta komai tayi kyau yake mata gata ba wata babba ba sai dai akwai Sama da kasa masha Allah.
Lokacin data gama ne ya yafito t
a da hannu,a hankali ta nufo shi kamar me counting steps sai rausaya take, wani yawu ya hadiye, Dan risinawa tayi a gabansa duka hannuwanta ya kamo ya zaunar da it kusa dashi.
"Zaki rakani unguwa?"
Ya fada Yana zame Mata veil din da tayi rolling gashinta n
e ya bayyana biki sidik dashi sai walqiya yake yasha gyara ga kamshin hair spray Yana tashi.
"Eh zani Bari naje na shirya".
ta fada Tana kokarin zare jikinta daga nasa. Duka hannuwansa yasa ya riko kugunta ya hade ta da jikinsa.
"Ina zaki?wane irin Shiri z
akiyi kinsan inda zamu ne kike sauri?".
Lakwas tayi a jikinsa da karfi da yaji so yake ya Saba mata da Zama a jikinsa gashi baya ko Jin jauyin taba Mata jikin sai dai idan Bai soba.
"Bazaki tambayi inda zamu ba, kina Neman sake canza Kaya".
"Nasan gida za
muje Mana".
"Ai kece gidan, kinaji da so nake muje gidan da gaske mu roki alfarmar a bamu aron me aiki daya Wadda zata zauna min dake kafin na dawo".
"Kafin ka dawo? Ina zakuje?".
"Au Ashe ban fada Miki ba, aikin NGOS din Nan ne ya taso suka gayyace mu zuw
a meeting da zasuyi a UK Kinga ai bazan zauna ba da dollars ko stalling founds suke biyan mu, idan Allah yasa na samu da Dan auki Kinga na Kara jarina tunda Naga Nima Ina sha'awar siyar da materials har munyi magana da Abba yace ze bani rumfa daya a Muda l
awal market na gwada ko ina da nasibi a cikin sana'ar, sannan Habib ma munyi magana zamu Fara siyar da spare parts na motoci a nan Muda lawal market din dai".
"Allah ya bada sa'a, Kuma idan ka tafi sai yaushe zaka dawo? Ko kaima shike Nan abinda yake faruw
a Dani ze faru a kanka kaima, kada ka tafi ka barni Dan Allah tunda nasan ba Sona kake ba baka ni akayi sadaka, Dan Allah ka taimaka ka kaini Jordan tunda Ina kudin flight