Showing 219001 words to 222000 words out of 295116 words

Chapter 74 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

min wannan aikin nafi son sai dai a bude ido a ganta ba'asan sanda tazo ba kafin Kuma a fashinci wacece ita din".

Wayar ya cire Yana furzar da iska daga bakinsa.

* AUREN HUCE HAUSHIN*

. AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

09061432330

Or

08055

362975.

Page 75

......... Tunda jirgin su zahra ya sauka a filin jirgin sultan saddiq Abubakar dake Sokoto gabanta ke faduwa,tasan a Nan ne komai fa ze iya tabbata ko ayi ko a fasa gata a Sokoto sai Kuma abinda Rabbi Izzati ya hukunta shi ne ze tabbata,

Afnan ce a sabe a kafadarta tana takawa a hankali tamkar Bata son taka kasar Dan da gaske ta Gama yin giving up a cikin Lamarinsu da mahmud.

Aunty Aishat ce tsaye a Kan kayan da sukazo dasu Saida komai ya kammala sannan ta nufo inda Zahra suke ita da Afnan

yayin da Abulkhairi yake biye da ita kafa ya kafa.

Kamar tare Aishat din suke da Sameer Dan tana karasowa shima Sameer Yana karasowa da waya a kunne da alama doguwar waya yakeyi, saida ya Gama sannan su zahra suka gaishe dashi har Aunty Aishat na fadin.

"

Nayi fushi kaje har India amma ka kasa zuwa mu gaisa".

"Kiyi hakuri kinsan halin kayanki bashi da lokacina a lokacin Kuma infact ma dai bai barni na zauna ba".

"Ai shikenan Daman ku Ina kuke Zama guri Daya tamkar marasa gaskiya Baku da standard gurin Zama

dole ku canza yanzu kun aje iyali suna da hakki a kanku baze yuwu ki ringa Abu babu lisafi ba Daman kasan tun farko Ammi Bata son wannan dabi'ar taku ko misqalazarratin Sai dai da yake Abbie ya tsaya muku ne yasa dole ta hakura".

"Wannan gaskiya ne Auntyn

mu za'a gyara in Sha Allah ko Baki fada ba zakiga canji ke dai kisa Ido kawai zakice na fada Miki".

"Allah yasa hakan ta kasance".

"In Sha Allah".

Sameer ya fada yana Dan kallon zahra ta gefen Ido tana ta yiwa Afnan Wasa.

"Madam barka da sauka sokoto Allah

yasa mun shigo kenan, yasa Albarka a cikin rayuwar da zakiyi a cikinta".

Dan murmushi tayi, yayin da Aunty Aishat ta amsa da. "Allahumma Amin, ni jikina ya Gama bani zahra Alkhairin mu ce".

Kayansu aka dunga jida ana kaiwa mota Sameer sai mita yake y

iwa Aunty Aishat akan sun lodo Kaya bayan Wanda suka turo jiya sukazo yauma ga wasu.

Kunnen uwar shegu tayi masa sufa sunfi son daga su sai kayan jikinsu, tunda suka dauko hanya zahra ke kallon garin, yayi matukar burgeta ba kadan ba tayi santinsa duk da h

ankalinta ba a kwance yake ba Amma ba karya sokoto tayi Mata

💯

% sai dai Bata San meze biyo bayan zuwan nata ba, wata zuciyar ta fada Mata.

"Khairan in Sha Allah"

Take ta Fara addu'ar sauka a sabon garin da kaje ba garinku ba, Dan harga Allah ta manta.

"RA

BBI ANZILNI MUNZILAN MUBARAKAN WA ANTA KHAIRUN MUNZILIN".

Ta fada a zuciyarta tana rokon ubangiji ya dafa Mata a cikin lamuranta gata ta shigo garin da babu uwa ba uba ba dangin iya babu na Baba sai wannan bawan Allahn shi kadai ta sani, kallon garin taci

gaba dayi daga kasan Zuciyar ta Kuma abubuwa ne rututu gasu Nan.

Wani katafaren gida taga Sameer ya dosa tamkar fadar shugaban kasa, Zahra hankalinta ta tattaro ta nutsu taga Nan kuma Ina ne Sameer ya kawo su Yana tsayawa a kofar katafaren gate din Mai Kam

a Dana kofar gari saboda girmansa wasu masu uniform suka taso su uku suka Karaso gurinsu Sameer kafin su Karaso sameer ya sauke glasses dan bada da baya,suna sameer ne suka gaisa sannan suka gaisa da Aunty Aishat da suke zaune a baya.

Katafaren gata din a

ka bude musu suka shige, " masha Allah".

Abinda zahra ta fada kenan a zuciyarta, wasu gine-gine take ganowa kamar a cikin film, an kawa gefen titin da flowes masu kyau da fitilu compound din ba mutane sosai sai 'yan tsiraru masu banruwan flowers har kofar

part din Ammi na baya sameer ya kaisu ita dai zahra ba baka sai kunne Dan ba karya gidan gida ne tamkar dauko ginin akayi aka Dora a gurin a zuciyarta take tunanin meya yi zafi da har Wanda yake rayuwa a nan ze tsallake ya bar shi yaje yana rayuwar kwanan

shago, ita dai saida Aunty Aishat ta Dan tabata ta dawo hayyacinta.

"Mu shiga ciki?"

Fitowa tayi dauke da Afnan a kafadarta tabi bayan Aunty Aishar wadda me rike da hannun Abulkhairi, numbers Auntyn ta saka ta bude kofar Dan juyowa tayi kadan tana fadin "

Bismillah".

A hankali zahra tabi bayan wasu parlours suka ringa ratsawa na garari sai da suka wuce parlour biyar sannan Aunty Aishar ta cewa zahra ta Dan jirata tana zuwa ta nufi upstairs tana rike da Abulkhairin.

A kan center carpet zahra ta zauna tana wa

sa da Afnan wadda duk tayi laushi ta gaji danma yarinya ce mai hakuri, dogon tunani zahra ta shiga bata taba tunanin maganganun Hajiyar makwarari gaskiya bane sai Yau wallahi duk a lokacin shirbtun tsufa ta dauki zancenta Ashe batama fada mata gaskiyar zan

cen ba.

A sama direct bedroom din Ammi Aunty Aisha ta nufa knocking tayi daga ciki taji Ammin na fadin "shigo mana batool kinsan bana son yawan damu da safe"

A hankali tura kofar ta shiga da sallama, ai Abulkhairi na ganin Ammi ya Zane hannusa daga na mama

nsa ya ruga ya rungume Ammi wadda tayi tsaye kawai tana duban Aishar Dan ba karamin mamaki ta bata ba."surprise ko Ammina?"

Ta fada tana shgewa jikin Ammin tana dariya.

"Kin kyauta kenan ki dauko jiki daga uwa duniya Amma bazaki fada ba ko Addu'a ayi muku

sai dai ba ganku ba zato ba tsammani".

" Afuwan my Ammi nima bansan da tafiyar ba sai shekaran jiya waccan, kinsa dan gidanki baya jira".

"Ina kika ganshi ko kuma daman yana tare dake kika ki fada? Ina kuma Afnan din take?".

" suna master parlour da bakuwa

mukazo fa".

"Bakuwa kuma?".

" Eh shigowa nayi na fada miki, to sannunku da hanya muje kasan a Samar muku abun break fast".

Suka nufo kasan takun takalmansu das das ya saka zahra dago kanta daga wasan da take yiwa Afnan tana bulbula dariya, caraf suka hada

ido da Ammi nan da nan taji gabanta ya fadi, itama Ammi wani shock ta shiga babu ko tantama wannan fuskar take gani tare da Hussein dinta a mafarki yau gata a zahiri, tayi mafarkin yarinyar nan yafi sau shurin masaki me hakan ke nufi kenan.

Suna shigowa k

amshin Ammin ya hade parlourn.

Zahra ba tayi tunanin haka zataga Ammin ba, babu Wanda zece ita ta haifi su Aunty Aisha sai dai ace yayarsu ce, 'yar gayu ce ta ajin karshe ga jindadin daya hana shekarunta nuna Kansu,a hankali take takowa idanunta na kan z

ahra wadda taji wata irin kunya ta rufeta, gurin da suke zaune Ammin ta karasa tana fadin.

"Sannunku da hanya, a kunya ce zahra ta bude bakinta tace.

" yauwa Ammy, ina kwana"..

"Lafiya kalau ya gajiyar hanya?".

Ta fada tana mika hannu zata dauki Afnan, mak

alewa tayi a jikin zahra alamar bazata zo ba.

Gaba Ammin tayi ta zauna tana fadin huta roro waken gizo yaqi 'ya'ya".

Aunty Aisha ce dubi Ammi tana fadin.

" Ammi ga zahra nan 'yar Amanar Hussein diyar mai gidansa ce bata da lafiya aka kaita India ganin liki

ta shine yace na taho da ita Nigeria kafin yazo su 'yan jihar bauchi ne katagum local government sunanta Fateemah zahra".

Dan gyara zama Ammin tayi tana kara kallon zahrar from head to toe, haka nan taji wani Abu yana mata kai kawo a kasan zuciyarta.

"Sann

u fateemah ya jikin naki?".

Kanta na kasa bata yarda ta dago ba ta amsa.

" Da sauki Sosai".

"Masha Allah, Hasana rakata sama dakin fake opposite da bedroom din ki bude Mata tayi wanka kafin a hada muku breakfast".

" To Ammi bari muje,ko kuma muje can guri

na saita zauna tunda duk cikin part din nan ne".

Kaita girgiza "kaita sama inda sauran 'yan uwanta yara suka can gurinki ba zataji fadi ba nan kuwa gasu Batool nan kuma ba kince bata jin dadi ba sai saida babba a kusa maza kuje lokaci yana tafiya gara taci

abinci ta kwanta ta huta tunda ba irin ujilarku ta iya ba".

A kunya ce zahra ta mike tana sabe da Afnan.

Saida suka bacewa ganin Ammi sannan ta dauke idonta daga kallon zahra.

" ya rabb kai kasan abinda ke boye da make nuna min yarinyar nan tare da Dana s

auran sirrin kuma bani da masaniyarsa, ubangiji ka tsareni jin abinda ze zamar min tashin hankali".

Ya fada a cikin murya mai rauni.

Suna shiga dakin Aunty Aishat din tace "wow! Lallai matarmu you are special ai bansan haka Ammi ta hada wannan bedroom din

ba, bari na sauka da wannan 'yar taki makale matar kawai"

Ta dauko ta tana kuka ta fice da ita, tana jin Zahra na magiyar ta dawo da ita tayi mata wanka Amma ta wuce kawai.

Lokacin da Aishat din ta sauko bata samu Ammi da Abulkhairi ba itama wata hanya ta

nufa tana dan jijjiga Afnan.

Kafin minti arba'in an hadawa su Aishat breakfast mai rai da lafiya, zahra tana fitowa daga wanka tayi tsaye a gaban mirror tana kallon kanta yanda tayi wani irin kyau na ban mamaki wato Inda ake gyaran jiki anayi dan tamkar a

nyi mata wankan inji,lotion din data gani ta Shafa tunda nata da take shafawa yana can cikin kayansu ba'a shigo dasu ba saida ta gama shafawa tayi turus Ashe bata da kayan sakawa kuma gashi towel din jikinta ma karami ne kusan Rabin cinyoyinta duk a waje s

uke, gefen gado ta koma ta zauna ita dai bazata iya mayar da kayan data cire ba, dan kwanciya tayi a jikin pillow dan tunda tayi wanka wata irin kasala ta saukar mata ba, tayi minti biyu ba barci yayi awon gaba da ita.

Jin shirun zahrar yayi yawa yasa Amm

i tacewa Aishat ta bita ta kirata ko nauyin saukowa takeji tunda taga yarinyar akwaita da kunya.

Sau biyu tana knocking Amma shiru, kamar ba mutum a dakin a hankali ta murda handle din ta tura kofar ganinta tayi tana barci,komawa tayi a hankali dan bazata

so ta gashi taga ta ganta a haka ba, haba dole bros ya rikice musu Ashe shi yasan sirrin kayansa Ashe a fuska wasa ne, tasan Allah ne yayi mass tukuicin kazafin da akayi masa ya bashi irin wannan yarinyar.

Sai data fara gangarowa ta tuna Ashe bata da kaya

n sakawa a tare da ita.

"Ya salam! Wallahi shaf ta manta tunda su basa dauko kayan sakawa suna dasu a nan.

******

Saida Mahmud yayi barcinsa mai isarsa ya tashi, sau uku Hajiya Inna tana zuwa ta buga masa daki tana jinsa a rufe, wanka yayi ya fito cikin

yadin filtex mai laushi fari tas, a parlour ya samu Hajiyar da Aminiyarta Innoni suna hira, kusa da Hajiya Innar ya zauna yana gaishe da innonin, kama haba tayi.

" kai kuma yaushe ka dawo garin namu?".

Tabe baki Inna tayi "kin gashi nan saida malamai suka

gama karbar nasu rabon ya mula ya Mile ya dauko jiki sinkin fakiti ya dawo, yazo kuma ya zaune min yaki ko leka kofar gidan nan, kofa gidan iyayen yaki zuwa ni naga ta kaina kasan da irin wannan ranar amma ka tsallake kayi naka guri sai yanzu zaka zo kana

daddofar na kaika gidan".

Wata dariyar da bai shirya ba ta kubce masa.

" Amma wallahi matar nan kin gama dani ni zaki cewa ina kamun kafa fake ki kaini gida,ni kadai na fito ni kadai zan koma kuma kinyi da dan halak idan na fice sai kin shekara baki sakan

i a idanunki ba".

Ya mike ya nufi kofa, nan da nan Hajiya inna ta rude.

"Idan ka bawa Annabi daraja ka dawo wallahi wasa nake maka ga abincinka can kazo kaci".

Ya tsaya Amma bai juyo ba.

"A aje min idan na dawo zanci lokacin magariba ya karato masallaci za

ni".

Yana gama fada ya bude kofa ya fice.

" miskili kawai idan ba haka nayi masa ba ko gidan baze leka yau ba duk kuwa yanda yake da kawa zucin uwa".

"Ai mutumin naki sai ke".

Saida ya gaisa da masu gadi sannan ya shiga motar da yazo a ciki ya nufi unguwar

su tunda babu nisa daga unguwar su Hajiyar, yana shiga ana kokarin tayar da sallah da sauri ya shiga cikin masallacin gidan nasu tunda da alwalarsa.

Sahun bayan su Abbie dinsa yayi sallah da aka idar masu fita suka fita shi daman a dabi'arsu yawanci basa f

ita sai sunyi insha'i zirillahi yaci gaba dayi Abbie din bai juyo ba shima bai matsa ba sai Babban yayansu Ibrahim da yake daga jikin ginin masallacin ta kudu yake mamakin yaushe Mahmud din ya dawo kuma uncle saminu ya dawo dazu yace Mahmud ya gudu daga In

dia, uncle mustapha ya bazu nemansa to ga Mahmud kuma a sokoto ga uncle mustapha ya sauka a abuja ze biyo jirgin karfe bakwai na dare zuwa sokoto to me kenan hakan ke nufi? Shifa daman ya dade yana zargin uncle saminu da wasu abubuwa marasa kyau a tsakanin

su.

Ana idar da insha'i Mahmud ya tashi ya fice kafin Abbie din su ya tashi, hannu kawai ya dagawa securities din ya wucesu suna faman murna dan sunsan kakarsu ta yanke saka mai yiwa dawa ruwa bare gashi a karkara,koda bayanan sakonsa yana iskesu to bare

gashi ya dawo.

Ya dan jima a parking lot na gurin Ammi yana Karewa harabar gidan kallo ko ina haske ne tar ga wata iska mai dadi da take busowa cikin motar tare da kamshin furanni mabanbanta, abubuwan da suka faru suka dunga dawo masa daki-daki lumshe idan

u yayi baiyi aune ba yaji ruwan hawaye suna bin kumatunsa abinda baiyi ba kenan duk badaqalar da aka sha a gidan nan a lokacin, kansa ya kifa jikin sitiyarin motar baiji alamun tafiya ko wani Abu sai dai jin hannun mutum yayi a bayansa bai dago ba, bubbuga

kafadarsa yaji an fara kafin ya tsinkayi muryar Abbie dinsa yana fadin.

"Haba! namiji baya kuka tunda ka iya jure kwaramniyar baya baka nuna rauni ba yanzu lokacin fuskantar gaba ne taso mu shiga ciki kada kannanka suga kana kuka, su raina min kai".

Da Sa

udi ya dago jin furucin da bai zata ba daga bakin Abbie idan yayi la'akari da lokacin da guguwar abun ta tashi tsine masa ne kawai baiyi ba Amma yayi masa wata irin tujara ta Ala tsine uwar mai karya.

Jikinsa ya fada yana fadin.

" wallahi Abbie ban aikata

ba! Ban taba zina ba, ka bani Qur'ani zan rantse da Wanda ya halicceni idan na taba zina a rayuwata Allah yayi min abinda yaso na azaba, ka yarda dani ka fadawa Ammi banyi ba sharri ne akayi min na fada Amma Baku yarda ba...kum..."

Sai jikinsa ya langabe y

a saki.

Da sauri Ya Ibrahim dake tsaye a gefe Wanda shima hawayen yakeyi ya zaburo yana fadin .

"Suma yayi Abbie bari na samo ruwa"

Ya tafi da gudu ya haura steps din part din Ammi, suna zaune ya bude kofar afujajun baiko kalli su Ammi ba da saura yaran y

ayi kitchen da gudu ya dauko ruwan sanyi da sauri Ammi da Aishat da Batool suka rufa masa baya Ammi na tambayarsa menene? Bai ko juyo ba yayi gaba,suma gurin daya nufa suka nufa turus sukayi ganin Abbie a tsaye rungume da mutum Ya Ibrahim yana bulbula masa

ruwan sanyi.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da shashsheka abinya yake fada yaci gaba da fada.

Ka fadawa Ammi ni ba nazinaci bane ban aikata ba".

"Pls kayi shiru mana ta sani ka kwantar da hankalinka bama zarginka kaga Amminka tana jinka fa".

Da sauri ya juyo

sai kuma jiri ya kwashe shi ze zubar Ya Ibrahim yayi saurin rike shi suna faman jera masa sannu, juyawa Ammi tayi idanunta fal hawayen tausayin dan nata kenan duk tsawon lokacin nan yana fama da wannan damuwar wadda sai yau ya fasata gashi zata janyo masa

matsala a lafiyarsa.

" Allah ka biwa yaron nan haqqinsa".

"Allahumma Amin".

Taji su Batool sun fada sai lokacin tasan a fili tayi addu'ar.

Su zahra na tsaye tana dauke da Afnan tun shigowar Wanda ya dauki ruwa ya fita su Ammy suka bishi taji gabanta yayi

wata irin faduwa, ta mike tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kuma taga an shigo da Mahmud din a rirrike yana layi kamar Wanda ya bugu da kayan maye.

Ai bata San yanda akayi ba ta dira a gabansa jikinta yana wata irin tsuma cikin rufewar idanu da manta

a ina ma take ne ta fara fadar

" Na shiga uku meya sameka meu amor...? Me akayi maka fada min dan Allah..."

Hannu Aunty Aishat da Dora a bakinta data bude tana fadin.

" kai? Wonderful...! the game is over".

* AUREN HUCE HAUSHI *

AISHAT ISAH MUSAH



Maman Fateemah.

Page 76.

.............. Aunty Aishat ce tayi sauri tazo gurin zahrar saboda kowa a gurin wutarsa daukewa tayi barema Abbie da Ya Ibrahim da Basu da masaniyar da wata bakuwar fuska a gidan, itama zahrar sai data fada ta dawo Cikin ha

yyacinta, wata irin kunya ce ta rufeta taji kamar kasa ta tsage ta shige Dan kunya, me tayi kenan shike Nan tayi abun kunyar da zata Dade Bata hada Ido da Amm bai wallahi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login